Showing 15001 words to 18000 words out of 64514 words
Chapter 6 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf
ta yana cewa ko lafiya, Inna kuwa wani murmushi ta saki.
Ruwa ya bata a buta ta wanke bakin ta ya kamo hannun ta, sai da suka kusa zuwa ya zaunar
da ita wani aman ya taho. Da sauri Inna ta tashi ta je wajen tana ƙarewa Maryama kallo.
"Maryama ko ciwon ciki kike, ko dai yunwar ce ta ci ta cinye ki shi ya sa rogon ya ƙi zama a
cikin?" Ya tambaya yana kallon ta da tausayawa.
"Haba Malam wannan ai ya fi ƙarfin ciwon ciki " Inna ta faɗa lokacin da ta gwala idanun
Maryama.
"To mene ne?"
"Juna biyu gare ta" Ta faɗa hankali kwance cikin halin ko in kula.
"Ci me?" Ya tambaya hankali tashe duk da ba wai ya yarda da shaci faɗin nata ba ne. Maryama
kuwa jin furucin Inna babu shiri sai ga ta a tsaye ta miƙe daga sunkuyon da ta yi tana aman jikin
ta sai karkarwa yake.
"Ciki mana ko bata isa ba? Ai dama tsintacciyar mage bata mage, shi ya sa tun a farko da aka
tsinci yarinyar nan tun tana jaririya na ce maka kar ka ɗauke ta amma ka murɗe kunne ka ƙi
yanzu ga shi nan dama duk wanda ya ƙi ji ba zai ƙi gani ba. Gefen ƙirjin sa ya dafe na hagun
saitin zuciyar sa yana mai nuna Maryama da yatsa tare da yanke jiki ya faɗi...
MAMAN AFRAH
09013181851
[2/9, 9:57 AM] MOM MASHKUR & AFRAH: BONONO
(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.
*SADAUKAR*
Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.
Daga marubuciyar:
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*
PAGE 5
Da sauri HEEDAYA ta juya za ta fita daga ɗakin Umm ta riƙo ta tana jefa mata wani kallo ta ce
"Gidan uban wa kuma za ki je?"
"Zuwa zan yi in tambaye ta ina ta kai mini ledar da ta ɗauka"
"Ashe baki da hankali to in bakaniya kama ɓarawo ba shi kama ka yake yi, sannan ki ce mata
magani mene ne?"
"Haba Umma kin san fa maganin nan yana damfare da kowane cikar burina kawai zan ce mata
maganin basir ne na ƙawata na taho da shi daga school a cikin jakata"
"Ita kuma layar fa?" Shiru ta yi ita sai a lokacin ma ta tuna cewa har da laya a ciki gabaɗaya kan
su ya ɗaure sun rasa wane kalar tunani za su yi.
"Ni fa Umma sai in ke ganin kamar Aunty RABEEYA ba za ta ɗauki maganin nan ba"
"To ƙafa maganin ya yi ya fita?" Shiru ta yi tana ɗan tunani.
"Ko dai mu ƙara bincikewa a nutse ko za mu gani"
"Hmm! Bincike na nawa kenan ban da wanda aka yi amma ba a ƙin ta mutane wai an ce
ɓarawo ya gudu" Umma ta ce tana nufar drower HEEDAYA ma ta bu bayan ta suka cigaba da
dubawa amma babu shi babu dalilin sa.
Shiru HEEDAYA ta ɗan yi tamkar wacce take tuna wani abu.
"Kin gani dai da idanun ki ba ya nan in dai ba wani bane ya ɗauka sai dai ko aljannu" Ta
katsewa HEEDAYA tunani.
"Tabbas! Jiya da zan ɗauki sleepin dress ɗina na ji faɗowar leda" HEEDAYA ta faɗa tana janye
kayan da suke ƙasa ta shiga dubawa.
"Kin ji faɗowar ledar amma baki ɗauka ba wace irin mutum ce ke kuwa ga shi kin rusa komai to
ina maganin yake. Ita dai HEEDAYA bata ce komai ba tana ta nazari.
"Ɓera!" HEEDAYA ta faɗa da ɗan ƙarfi jin ƙwaƙwalwar ta ta mata wani tunani ta san tabbas
akwai ɓera a ɗakin.
"Ɓera?" Umma ta tambaya da mamaki.
HEEDAYA bata bata amsa ba ta tafi ta fara duba kusurwar ɗakin da bayan gado Umma ma sai
ta bi ta suke ta dubawa duk da bata jin wani ɓera ne zai ɗauka ta fi ɗora zargin ta a kan Aunty
RABEEYA.
"Lah Umma kin ga ledar can a drower " HEEDAYA da ta hango ledar a batan drower ta faɗa
cike da murna. Da sauri Umma ta zo ta leƙa ai kuwa ta hango ledar baki washe ta shiga faɗin.
"Shegen ɓera ashe shi ya ja ledar ɗan banza ya ruɗa mana ciki"
"Umma mu yi addu'a dai Allah sa bai cira ledar ba ko kuma ya taune ledar ya gutsitstsira
ganyen" Da haka suka shiga ƙoƙarin janye drower cikin sa'a kuwa suka babu abin da ya yi wa
ledar cike da murna suka rungume juna. Umma bata bar ɗakin ba sai da HEEDAYA ta ɗauki
ganyen ta shiga bayi ta yi yadda aka ce ta yi.
"Kin tabbatar dai fitsarin ya taɓa ganyen?"
"Ai Umma sai da na jiƙa shi jigif" Ta faɗa tana wata murna ganin ta fara taka tsanin da zai kai ta
ga cim ma burin ta.
Tun daga wannan rana kullum sai HEEDAYA ta ɗauki ganye ɗaya ta yi yadda aka ce sannan
ta iya takun ta tana nuna wa Aunty RABEEYA farin haƙori har ma da Ya ABDUL bata bari ta
furta masa ko nuna masa wani abu da ya danganci soyayya ba.
Kwanci tashi asarar mai rai biki har ya rage saura sati guda a inda ɓangarori da dama
kowanne yake ta shirye-shirye. Hajiya Fati uwar ango tana nata shirin don ita ma biki ta shirya
yi na kece raini gidan ango ya sha fenti komai saboda kayan Aunty RABEEYA wanda Hajiya
Fatin ce ta yi wa Momma rakiya suka zaɓo don koman su tare suke yi sai dai suna mamakin
yadda Umma bata nuna musu komai na auren ya dame ta hasali ma sai take nuna wa Momma
faran-faran a fuska wanda a zuciyar ta so take kawai tarkon da suka ɗana ya kama tsuntsu,
babu abin da ya rage illa kawai jiran ranar ɗaurin auren don daga Umma har ƙawarta Hajiya
Aisha tare da HEEDAYA sun saka wa ransu cewar auren da za a ɗaura babu makawa da
HEEDAYA za a ɗaura bisa lura da maganin da suka ci alwashin kyansa kamar yankan wuƙa. A
zahiri HEEDAYA tana nuna shirin auren Aunty RABEEYA take yi amma a baɗini shirin nata
auren take don tana da tabbacin ita ce za ta tare a ɗakin Ya ABDUL ba Aunty RABEEYA ba.
Umma da Hajiya Aisha da HEEDAYA su suka je wajen siyar da kujeru da kayan gado na kece
raini HEEDAYA ta zaɓa suka biya kuɗin a kan cewa za su zo su ɗauka daga baya don
kamfanin da suka siya katan sanannan kamfani ne. Kayan kicin ma haka suka loda kamar babu
gobe a nasu nufin idan ɗaurin auren ya juye zuwa kan HEEDAYA sai a kwashe kayan Aunty
RABEEYA a jera na HEEDAYA.
"Umma wannan lafayar fa?" HEEDAYA ta tambaya tana ɗaga kayayyakin da Umma ta kira ta
ɗakin ta ta gani.
"Wannan ita ce za ki saka ranar ɗaurin auren idan za a kai ki ɗakin mijin ki ita za ki naɗa"
Umma ta ce tana washe baki tare da ƙara kallon laffayar mai manyan fulawoyi irin kuɗin da ta
narka don fito da amarya HEEDAYA fess a idon masoya da ma maƙiyan baki ɗaya. Sosai
HEEDAYA ta ji daɗin ganin laffayar har ta fara hango irin kyawun da za ta mata a ranar da ta
naɗa don zuwa ɗakin mijin ta a matsayin amaryar sa lallai wannan rana za ta zame mata ɗaya
tamkar da dubu rana ce mai tsananin tarin tarihi a rayuwar ta.
"Ummana Allah ya bar mini ke ina ƙaunarki ina alfahri da samun ki matsayin uwa, wacce take
faɗi tashi don farin cikin iyalin ta" Ta ce tana kara laffayar a jikin ta lokacin da take tsaye gaban
mudubu tana ganin irin kyan da ta mata.
"Ni ma ina ƙaunar ku HEEDAYA burin kowace uwa ta sanya ɗiyanta farin ciki marar yankewa"
"Haka ne Umma amma ke kam kin sha bamban da wasu uwayen duba da yadda kike amfani da
aljihun ki da lafiyar ki don cikar burina haƙiƙa ba zan taɓa mantawa da wannan abin da kika mini
na jajircewa don ganin na samu zaɓin raina kuma muradin rayuwata, ba zan gushe ina miki
addu'a ba har ranar da numfashi na zai tsaya domin Allah ne kaɗai ya san irin tarin ƙaunar da
nake yi wa Ya ABDUL ga shi zan mallake shi a ɓagas cikin sauƙi cikin ruwan sanyi" Ta faɗa
lokacin da take rungumo kafaɗar Umma.
"Wannan dole ne ma HEEDAYA cikar burin ki da kuma ambulawa maƙiya ƙasa a ido dole
ranar ɗaurin auren nan daga akala ta sauya an ɗaura da ke to har sai na zubar da ruwa a ƙasa
na sha" Ta faɗa tana dafa bayan HEEDAYA haka suka cigaba da tsare -tsare.
Yau laraba ya rage saura kwana uku ƙwarara ɗaurin auren Ya ABDUL da Aunty RABEEYA a
zahiri kenan amma a baɗini ta ɓangaren su Umma saura kwana uku ɗaurin auren HEEDAYA da
Ya ABDUL. Shiri ya kankama ta kowane ɓangare Aunty RABEEYA da ta ce HEEDAYA ta zo za
su tafi gidan ƙunshi da ƙwayaye ta.
"Haba Aunty RABEEYA ina ƙanwar amarya fa ango zan zauna in ke bin ku ah lallai ai ni ma
gashin kaina zan ci ni da ƙawaye na ku tafi naku ƙunshin mu ma mu tafi" Ta faɗa cike da zolaya
tana dariya, don ita ma ƙunshin amarya za ta je a yi mata tun da tana ganin ma ai ita ce amarya
ba Aunty RABEEYA ba a ganin ta Aunty RABEEYA wahalar da kanta kawai za ta yi tun da ba
aure za a ɗaura mata ba.
"Allah sarki my HEEDAYA na gode! Shi ya sa nake ƙaunar ki wallahi" Ta faɗa cike da jin daɗi
tun da tana tunanin HEEDAYAR duk shirin nan da take domin ita take yi bata san ita ma wani
nufin ne a ranta ba na ganin an ɗaura auren da ita.
Sosai HEEDAYA ta gayyaci ƙawayen ta ƙwan su da ƙwarƙwatar su, tana faɗin bikin yayar ta
za a yi don ta fi so sai sun zo su ji ita ce amaryar MEEMA babbar ƙawar ta kawai ta faɗawa
cewa tana sa ran a ɗaura auren ta da Ya ABDUL ɗin tun da ta san ya take son shi. Don ita
MEEMAR ma da ranar auren ta a kai suka kammala karatu.
Umma da Hajiya Aisha ma gayyata suka yi sosai suka gayyato ƙawayen su da abokan arziƙi
a cewar Ummar mijin ta ne yake aurar da ƴa amma ƙudurin zuciyar ta tafi so sai sun zo in aka
sanar da ɗaurin auren sai su taya ta murna da gayya.
Amarya HEEDAYA da amarya RABEEYA duk sun sha gyara ciki da waje an sha ƙunshi baƙi
da ja an sha saloon don HEEDAYA wani ƙananan kitso aka mata na ibra. Magungunan mata
kuwa da tsumi babu wanda Umma ta manta wajen gyaran har da su kazar amarya. Fatar nan
da ta sha gyara sai sheƙe take abin sai sam barka kowa sai yake zolayar HEEDAYA wai ƙanwar
amarya ta zaƙe da yawa sai dai ta yi dariya a fili ta ce
"Yo ba dole ba ana yi wa Aunty RABEEYA tah aure" A zuciyar ta kuma ta ce
"Hmmm! Iska tana yawo da mai kayan kara da sannu za ku gane ainihin dalilin gyaran nan da
na yi wallahi ko tausayin Aunty RABEEYA ba zan ji ba idan ta ji da ni aka ɗaura idanuna zan
shafawa toka i cigaba da hidimata don har ƙwarya-ƙwaryar party zan shirya a ranar.
'Hajiya Momma uwar amarya, ya aka yi kuma ido ya juye da mujiya? Yanzu dai kin gane lokaci
yana sauyawa a koyaushe ƙaddarar mutum kuma tana iya sauyawa daga mummhna zuwa
kyakktawa ko ta canja daga kyakkyawa zuwa mummuna' Wannan su ne kalaman da HEEDAYA
take ayyanawa a zuciyar ta za ta faɗawa Momma idan aka ɗaura auren ta.
"Yanzu kun yarda ruwa ya ƙarewa ɗan kada? Ko kun san cewa idan taƙamar mutum wuni ya yi
a zaune wani kwanan hanya ya yi, duk runtsi kar ka raina shirin wani don shirin ka ka sani shi
wancan baka san shirin sa ba amma Allah shi ya san karatun kurma!"Waɗannan su ne kalaman
da Umma ta tanada za ta yi wa Momma da Ammie martani da su idan aka ɗaura auren
HEEDAYA da Ya ABDUL.
Yau za a yi kamu tun la'asar ɗin fara HEEDAYA ta shirya cikin rantsatstsen leshin ta dark
blue mai fulawa ja da light blue ɗin mai make up ɗin da Umma ta ɗakko musu ta musamman ita
ce ta tsantsare HEEDAYA da kwalliya mai ɗaukan hankali aka mata ɗauri sosai ta yi kyau ta fito
a amaryar ta sak don ta ɗau aniyar yau sai dai su saka angon a tsakiya don ita ce amarya ba za
ta taɓa yarda ta zauna a inda babu ango. Umma da Hajiya Aisha ma make up ɗin su aka musu
suna sanye da atamfa iri ɗaya an musu ɗinki sai zabga ƙamshi suke ita dai Aunty Hafsa tana ta
jin babu daɗi tub da ta san shirin na su Umma kuma tana fatan Allah kar ya basu nasara duk da
tana fargabar ranar ɗaurin auren, tun da dai ta san asiri gaskiya ne sannan hausawa suna cewa
camfi gaskiyar mai shi. Kowa ya fito cass Ammie ma uwar amarya da Momma uwar ango su ma
ankon su suka yi. Aunty RABEEYA ma an mata make up ɗin ta simple make up ne ta yi kyau
kamar ka sace ta ka gudu. Sosai take jin farin cikin tana jin daɗi a ranta ashe ita ma da rabon za
ta yi aure tana son ganin ranar da za a ɗaura mata aure ba ta san inda za ta saka ranta ba
saboda daɗi.
Motoci sun hallara inda masu anko ƙawaye da ƴan uwa suke shiga motocin da aka tanada
don zuwa wajen kamun. HEEDAYA da duk ta samawa ƙawayen ta motoci amma ita sai ta ƙi
shiga kowace motar da aka tanada ta amarya da ango bayan sun shiga sai ga ta ta zo ta tsaya
a jikin windown ta yi nocking Aunty ARABEEYA da fuskar ta take rufe da mayafin ta ta ɗago
ganin HEEDAYA da sauri ta sauke glass ɗin ta ce
"HEEDAYA tah"
"Aunty ni a motar ku zan tafi" Ta faɗa tana yin raurau da ido tare da zunɓuro baki, shiru Aunty
RABEEYA ta yi tana jinjina irin soyayyar da HEEDAYA take mata tare da cewa
"To shigo mu tafi" Momma da ta hango HEEDAYA tana shirin shiga motar amarta da ango da
sauri ta taho har tana neman yin tuntuɓe cikin ɗaga murya tun kafin ta ƙaraso ya ce.
"HEEDAYA ke HEEDAYA!" Dakatawa ta yi tana juyowa tare da haɗe rai ta yi wa Momma wani
kallon rainin hankali ba tare da ta amsa sunan ta da Mommar take kiran ta ba.
"Duk motocin nan da aka tara sai a motar amare za ki tafi?" Ta tambaya tana aika mata harara.
"Haba Momma ki bar ta mana ai wajen zai isje mu" Aunty RABEEYA ta faɗa tana kallon
Momma da ta mayar da kallon hararar kanta don ta ji haushin furucin.
"To sai dai ta shiga gaban motar"
"Momma ki ƙyale ta mana HEEDAYA ai tamu ce" Ya ABDUL ya faɗa yana dariya don shi ya
ɗauka kawai rigar HEEDAYA ce.
A ƙufule Momma ta kuya cike da takaici ba tare da ta furta komai ba, da sauri HEEDAYA ta
juya ta bar jikin ƙofar da Aunty RABEEYA take ta koma saitin ƙofar Ya ABDUL.
Kawai sai buɗewa ta yi shi kuma sai ya matsa kusa da Aunty RABEEYA ita kuma ta shiga ta
rufe ƙofar ya zamana sun saka shi a tsakiya sai sannan hankalin ta ya kwanta ganin ga ta ga
angon ta kyawun da ya yi ya tafi da ita sai satar kallon sa take tana jin kishin Aunty RABEEYA
da take kusa da shi.
A haka gabaɗaya motocin suka lula a kan titi. Yadda aka tsaro wajen shiga wajen kamun yara
a gaba sai ƴan mata wanda suke sanye cikin anko. Amarta da ango da suka bi sahu har da
HEEDAYA. Waje ya kaure da kiɗa amarya da ango da HEEDAYA saboda ƙoƙari faɗawa mijin
baya tariya har da ita suka zauna a kujerar amarya da ango masu hoto sai haska su ake yi.
Bayan MC ya buƙaci amarya da ango a fili HEEDAYA ta buɗe bakin jakarta tana liƙi wa Ya
ABDUL ita kuma Auntt tana liƙawa HEEDAYA shi kuma yana liƙa musu su duka. Sodai aka raƙa
she har aka tashi kowa ya watse.
Washe gari ma ko a wajen