Showing 60001 words to 63000 words out of 64514 words

Chapter 21 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5106

a shedar ɗan yau. Tun daga ranar ta kafa musu karan tsana da shi da
MARYAMA ta daina ba MARYAMA abinci sai dai shi ya dafa ya ba MARYAMAR. Idan zai tafi
wajen aiki sai dai ya siyo mata komai na buƙata ta ajiye a ɗakin nata har da ƙaramin gas take
girkin ta.

Duk da bata ji daɗi hakan ba kuma tana jin nauyin sa duk da ta yi yinƙurin sanar da Kaka
cewa ba cikin sa ba ne amma ya ƙi ya bari. Ko da ya zaunar da ita ya tambaye ta amsa ɗaya ce
dai ita ma bata san cikin waye ba amsa mai cike da ruɗani haka ya haƙura ya fawwalawa Allah
komai. Tana so ta gudu amma babu hali don bata da wajen zuwa.

*BAYAN WATA BIYAR*


Haka ake rayuwar babu daɗi kuma babu yabo babu fallasa tsakanin ta da su Kaka har
gwara Mero ma wani lokacin tana mata magana in ta ga Kaka bata wajen. Cikin ya tsufa sosai
ga shi duk ta kumbura dakyar take tafiya ksancewar haihuwa ko yau ko gobe. Hankalin Ya
HAFEEZ gabaɗaya a tashe yake bai san ya zai yi da abin da za ta haifa ba ga shi Kaka ta kafa
sharaɗin tana haihuwa za a ɗaura musu aure su bar mata gida, duk da ita ma tana cike da
tausayin su a ranta tana kuma shiga damuwa ganin HAFEEZUN ta ne yake da cikin ɗan shege
wannan abu yana ɗaga mata hankali.


Yau ya kama alhamis da misalin ƙarfe goma na safe tana ɗaki zaune tana ta kuka abin

tausayi ita kanta bata san ya za ta yi da lan da za ta haifa ba ga shi ta zo ta raba mutumin da ya
tainake ta da soyayyar Kakar sa sun dawo kamar aboka gaba. Kamar an ce ta ɗago ta gan shi
tsaye a cikin ɗaki idanun sa sun tara ƙwalla. Tabbas ya san MARYAMA iya gaskiyar ta take faɗa
sannan yana tausayin maraicin ta sannan ga soyayyar ta da take neman nakasta masa rayuwa.
Kai ta sunkuyar ga wannan cikin nata da ya mata gingirigim. Daga ta ci abu sai ta ji babu sai ta
sake cin wani abu wuni take tana ciye-ciye ga shi ɗan yake ta motsi.

"Ki saka hijabin ki zan kai ki asibiti a miki scanning domin sanin saura sati nawa ki haihu tun da
Kaka basa nan dama shi ya sa na kasa fita da ke" Ya faɗa cikin sanyin muryar tausayin ta yana
tsarga masa. Da to ta amsa dakyar ta dafa ƙasa ta miƙe tsaye ƙafafun ta duk a kumbure.
Hijabin ta saka ta bi bayan sa a mota ta same shi, buɗe mata ya yi ta shiga mai gadi ya buɗe
musu suka fita tare da haura wa saman titi.

A wani wajen scanning ya yi parking, ya buɗe mata tare da kamo hannun ta ya taimaka mata
ta fito yana riƙe da hannun ta tana takawa dakyar suka shiga.

"Ma sha Allah ina taya ka murna madam ta kusa sauka ko?" Mai scanning ya ce yana
murmusawa, murmushin yaƙe Ya HAFEEZ ya masa. Wurin suka shiga ta kwanta a kan gadon,
shi kuma yana zaune a kujera ya kifa tagumi. Fara mata scanning ɗin ke da wuya abin cikin
cikin nata ya bayyana a cikin computer daga mai scanning ɗin har Ya HAFEEZ a kiɗime suka
tashi tsaye ganin abin da ya kusa tarwatsa musu kwanya wanda tun da suje a rayuwar su baay
taɓa gani ba. Ita ma ganin sun tashi a kiɗimen ta ɗago idanun ta ta sauke a kan computer Idanu
ta zaro cike da ruɗani wani irin tsoro tana baibaye mata zuciya sai kuwa ta fara karkarwa tare
da haɗa haruffa ta ce

"Ya, Ya, Ya HAFEEEZZZZZZZZ"



*HEEDAYA*

"Mai kake faɗa ne wai Ya ABDUL ka san dai ko ana mini wasa a duniya ba na son
wasan kishiya amma mai ya sa ka zaɓi mini shi a yau baka san za ka iya tarwatsa ƙwaƙwalwata
ba?" Ta ce lokacin da ta ƙarasa gabansa don ta san tabbas! Sai dai in wasan yake mata amma
ta san wannan ba iyayyiyar magana ba ce ko a mafarkin ta bare a zahiri. Kalaman sun yj tsauri
da yawa.


"Ni sa'an wasan ki ne da zan miki wasa?" Ya jefa mata maganar cikin dakewar muryar sa babu
ko alamar wasa ko sassauci a furucin sa sai ya koma mata Ya ABDUL ɗin na asali wanda ya
canja mata bayan auren sa da Aunty RABEEYA. A hankali ta sulale ta durƙushe a kan gwiwoyin
ta ta ɗora hannuwan ta a kan gwiwar ƙafar sa hawayen nan shaɓe-shaɓe kamar an ce mata
Ummar ta ta mutu cikin rawar murya ta ce

"Aure Ya ABDUL? Ni za ka yi wa kishiya?"

"Aure mana ba a auren ke aka aure ki? Ina so ki sani aure babu fashi, sannan ki sani haƙar ki
bata cim ma ruwa ba domin kuwa ABDULHAKEEM ya daɗe da hango tubalin ginin da kika yi
wa rayuwar sa shi ya sa ya nemar wa kansa mafita ni na fi ƙarfin juyawa a wajen ki HEEDAYA
kar ki manta zaɓina RABEEYA ce wacce Allah ya karɓi abin sa amma ni kaina ba zan ce ga
yadda aka yi na aure ki ba na san dai ni na yi furucin kuma ina tuna komai amma babu
takamaiman dalilin. A yadda RABEEYA ta tafi ta barni tafiya ta bazata a shekaru ƙalilan ban
tama kawo zan kalli wata mace da sunan so ba sai ga shi a watanni ƙalilan na yi aure auren na
wai ke HEEDAYA?Abu bai tsaya a nan ba har kike rabani da uwata da ta yi silar wanzuwata a
duniya ta sha wahala ta ta raine ni shin adalci ne wannan ke za ki so a raba ki da taki uwar? Ko
so ne wannan ki kai ni hanyar shiga wuta tun da wofintar da iyaye ai hanyar wuta ce to ki sani
ko don Abba ba zan saki ki ba amma kuma ni ma zan auro muradina sai ku zauna zaman kishi
tare da ita wataƙila ita ta ƙaunaci jinina Little RABEE ta bata kulawar uwa wacce ta rasa a wajen
ki kuma matsayin kina ƙanwar mahaifiyar ta ki ji tsoron Allah kuma ki sani shi ramin ƙarya
ƙurarre ne" Yana gama faɗar hakan bai jira cewar ta ba ya tashi tare da janye hannuwan nata
da take riƙowa tana roƙon sa don ta kasa furta komai sai zancen bebaye take hawayen nan
kamar an buɗe famfo.


Bai saurare ta ba ya haura sama abin sa yana riƙe da mukullin motar sa. Bizigir ta yi a
tsakiyar falon ta kwanta reran tana kuka tare da ambaton ta mutu ta lalace. Gabaɗaya duniyar
take ji tana juyawa mata ta rasa makama da tunanin abin yi ta kwashe sama da minti ashirin
tana kukan kafin ta tashi zaune ta fara jidar akwatinan tana jefa su kan benen. Ya ABDUL da ya
watsa ruwa fitowar sa kenan bayan ya shirya ya ga kiran wayar masoyiyar sa yana shirin ɗauka
ya fara jiyo ƙara abu hakan ya ankarar da shi wani abu yana faruwa da alama HEEDAYA ce
take masa hauka shi kuma ba zai jura ba kuma ba zai ɗauka ba.

A fusace ya fito tamkar kumurcin zaki lokacin HEEDAYA ta ɗaga ƙaramin kit ɗin za ta yi jifa.

"Ba na son hauka HEEDAYA ki sani nan gidan ABDULHAKEEM ne ba turun mahauka ta, ki
sani ba zan lallaɓa ki ba idan kin ga ba za ki iya ba hanya a buɗe take dama kara na miki
saboda su Abba wallahi da a ce wata bare ce a yau sai na yanke igiyar aurena duka uku a
kanta don ba matar zama ba ce za ta yi abin da kika yi" Yana faɗar hakan ya juya ya koma. Da
ido ta bi shi har ta ɓacewa ganin ta jin maganar sakin da kuma cewa ƙofa a buɗe take sun
razana ta. Tana ta mamakin yaushe Ya ABDUL ya zama haka ko dai aikin ta ne ta karye da
wannan tunanin ta ajiye kit ɗin hannun ta ta tafi ɗaki tana zuwa ta ɗaga waya ta kira Umma ta
zayya ne mata wannan ne abin da ya ruɗa su gabaɗaya.

Tun da ta kira HUSNA take rusa kuka gabaɗaya aun shiga tashin hankali suna jimantawa ita
ma HUSNA kukan take taya ta tana mamakin ashe dai duk kanwar ja ce duk mazan haka suke.

"Ya zan yi HUSNA Ya ABDUL ya shammace ni, a lokacin da nake tsaka da sakin jikin ni
kaɗai zai rayu da ni ashe dai ba haka ba ne ashe dai akwai wani ɓoyayyan shiri da yake a
bayan fage, ashe dai da ya nuna mini ya daina kula kowace mace sannan boka ya tabbatar
mini da cewa ba zai taɓa sha'awar aure ba an fitar masa shi a ransa ashe dai ƙarya bokan yake
yi na shiga uku hankalina ya kai ƙololuwar tashi mafita kawai nake neman ko ta wane hali"

"To mai zai hana ki dage da addu'a ni ma in taya ki tun da aikin bokayen da malaman ba su ci
ba?"

"Haba HUSNA kin san dai ana jinkirta karɓar addu'a ni kuma wuri ya ƙure mini tun da yau saura
sati guda fa ya ce wannan wace iriyar baƙar ƙadsara ce da raba tsaka ta kunno kai" HEEDAYA
ta faɗa cikin kukan da ya ƙi tsaya mata.

"To yanzu ya kike ganin za a yi ni ma wallahi kaina ya kulle na rasa mafita da a ce ina da iko ina
da yadda zan yi da sai na dakatar da auren nan haba wace ce wanna mai rawar kan za ta shigo
cikin gidan ki, da a ce ma za mu san wace ce da sai na zo mun je har gida mun tsoratar da ita
don ta janye ƙudurin ta na auren sa" HUSNA ta kai maganar ranta yana ƙuna.
"Ai ni ban san ma wace ce ba da alama abin an yi shi ne a munafurce don Umma ma da na kira
ta yanzu hankalin ta ya tashi don bata sani ba, ni na fi zaton wataƙila wannan ƙeƙashshshiyar
uwar tasa ce za ta saka shi yin auren wataƙila ma ita ta sama masa matar ko ma ƴar gidan
ƙawarta ce wa ya sani"
"Amma na yi mamaki bayan bokan ya ce miki ya makantar da ido da zuciyar ABDUL ɗin daga
ganin duk wata ƴa mace" HUSNA ta ce cike da jimantawa.

"Bari ke dai ina zuwa zan kira ki wallahi zuciyata zafi take ji nake tamkar na haɗiyi zuciya ba
mutu ko na kashe kaina"

"Haba aminiyata musulma kike fa duk komai ya yi tsananj maganin sa Allah" Tsabar ma kuka ya
ci ƙarfin ta kashe wayar ta yi.

Tana kwance tamkar matacciya ta rasa abin yi kamar an tsikare ta ta ɗauki waya ta kira
MEEMA dakyar ta ɗauka bayan ta tsinke.

"Ya aka yi ne?" Ta jefawa HEEDAYA tambayar HEEDAYAR tana jiyo ƙaran taunar wani abu da
alama wani abu take ci. Kunya ce ma ya kama HEEDAYA don sai ta rasa ma bakin magana
gani ta daina kula MEEMA sai yau da komai ya caɓe.

"MEEME wai Ya ABDUL ne zai yi aure nan da sati ɗaya" Ta faɗa cikin muryar kuka.

"Ayyiriri" MEEMA ta saki guɗa sannan cikin nuna jin daɗi da bayyana farin ciki a muryar ta ta ce

"Ya mini daidai Allah sa nan gaba ya rufe ƙofa wato ya auri mata huɗu kin ga kishiyoyin ki uku"

"Haba MEEMA don Allah ki manta da komai ki tausaya mini zan zo gidan ki ki daure ki raka nj
wani wajen bokan mai aiki sha yanzu magani yanzu ya mini aiki ko nawa zan biya don a janye
maganar auren nan in ya tabbata mutuwa zan yi"

"Allah suturi buƙwai in ji kishiyar mai doro, ai ba mutuwa ba wallahi ko mushe za ki sai dai ki yi
amma ni babu ni babu ke marar mutunci da bata san halacci ba. Da kin manta da halaccin da
na miki har yau baku bani amsar saƙon da na tura miki ba saboda kin sake ƙawaye shi group
ɗin MANYAN MATAN ma na ga ni na kai ki to ki ƙare ƙalau da sabbin ƙawayen naki" Tana gama
faɗa ta kashe waya jifa ta yi da wayar a kan gadon ta kwanta ta rushe da kuka jim kaɗan ta
ɗakko mayafi da jaka ko ta kan Ya ABDUL ɗin bata bi ba ta fita ta hau napep sai gida. Falon
Abba ta nufa tana share hawaye Abba kuwa ganin ta ya san mai ya kawo ta amma sai ya nuna
bai san mai yake tafe da ita ba. Kwashe komai ta yi ta faɗa masa a ganin ta zai dakatar da Ya
ABDUL daga auren amma abin mamaki sai ta ji ya fara mata nasiha a kan ta rungumi ƙaddara
ta zauna a ɗakin ta dama namiji mijin mace huɗu ne.


Ko cikin gidan bata shiga ba ganin haƙar ta bata cim ma ruwa ba a wajen Abba ta nufi gidan
su Ya ABDUL ɗin ra kwashe komai ta faɗawa Daddy nan ya lallashe ta a kan ta yj haƙuri Abba
ne a cikin maganar kuma Abba ne gaba da shi. Gidan Hajja ta wuce tana zuwa ta fashe da
kuka ta shiga faɗa mata.
"HEEDAYA auren ne sunnar ma'aiki bakya so a raya? Ita uwar ki ita kaɗai take zaune a gidan ta
ko kuwa tana da abokiyar zama? To ni ba na ciki da faɗan rashin gaskiya, babu wanda zan
faɗawa a fasa aure ke da aka ce ƴar marainiyar nan ma baki bari ba HEEDAYA ko kin ɗauka
duk ba mu san abin da yake faruwa ba? To ki sani yanzu kiwon mutum ake kiwo ba dabba ba"
Kamar ta shaƙe Hajja haka ta ji nan ta baro gidan ta rasa ya za ta yi. Sannan babu ma wanda
ya faɗa mata wace ce amaryar bare ta je ta ɗauki mataki.

Daga ita har Umma sun bi boka da Malam har sun gaji, sai kashe kuɗi suke amma babu biyan
buƙata. Hajiya Aisha sai da ta raka ta wajen wasu manyan bokayen amma jiya i yau babu sauyi.
Yanzu har ɗaurin aure ya rage kwana uku.


Part ɗin Ya ABDUL wanda ba a ƙarasa ba aka ƙarasa sai kuma ɗaya part ɗin da yake a rufe
dama an gama shi. Shirye-shirye ake ta yi don Umma har gida ta je ta yi wa Ya ABDUL wankin
babban bargo ta je ta yi wa Ammie da ko kallo ma bata ishi Ammien ba ta mayar da ita
mahaukaciya.

Duk ta zabgr ta yi baƙi ta sa baƙin kishi a zuciyar ta, HUSNA ce kaɗai abokiyar shawarar ta
duk wani shiri da take da shi a kan kishiyar take kwashe komai tana faɗa mata. Tun da dai sun
yj jimami sun yi iya ƙoƙari ganin batun auren ya ruguje amma abin ya ci tura!.

"Wallahi HUSNA na ji babu daɗi ga shi yanzu ko kula ni ba ya yi, a tawa wautar so na yi gobara
ta ƙone mu ni da shi ƙurmus mu mutu kin ga ban barshi a duniyar ba ma bare ya auri wata ko
kuma mu yi hatsari mu...

"Haba HEEDAYA ki daina wannan tunanin, tun da dai har ta kusa shigowa ki mayar da hankali a
kan zaman kishin da za ku yi kar ki bari ta zo ta ƙwace miki fada"

"Yo ƙwacewa ta nawa kuma, ni yanzu gaba ma nake masa ba na masa magana, sannan ma ni
duk magungunan matan da nake sha waɗan da nake baki labarin yana santin su idan na yi
amfani da su duk na tattara na ajiye kin san dai kaf sirrina ai na sanar da ke hatta magungunan
mata da nake amfani da yadda nake amfani da wajen da nake siya da kuma yadda Ya ABDUL
yake in ya kusance ni ai duk ina baki labari to mene ne ya yi saura wanda bana yi da zai mini
kishiya"

"Ki ɗauki ƙaddara kawai kuma kin san dai wanda ya riga ka da kwana ya riga ka da tashi don
haka ki maida komai ba k" Katse HUSNA ta yi don in ana maganar kishiyar ma ƙunci take ji.


A yau ne aka ɗaura auren Ya ABDUL da amaryar sa, ranar da ta zama baƙar rana a wajen
HEEDAYA babu wanda ta tara kuma babu abin da ta yi matsayin ta na uwar gida. HUSNA ce
take kwantar mata da hankali tun ana gobe ɗaurin aure. Kuma yau da ake ɗaurin auren tun da
safe HUSNA ta tafi wata ƴar uwar su HUSNA ta rasu suka tafi gidan makoki ba su sake waya
ba. Da la'asar lis HEEDAYA tana zaune bayan RAUDA ta zo suna zaune kamar kurame abin
duniya ya haɗe musu goma da ashirin don a ganin HEEDAYA abin kunya ne su yi gayyata
ƙawaye za su rainata ita kuwa dama MEEMA bata zo ba. Sai Umma da take kiran ta a kai-a kai
tana tambayar an kawo amaryar. Aunty Hafsa da ta zo da safe HEEDAYA ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login