Showing 51001 words to 54000 words out of 64514 words

Chapter 18 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5108

ta ya tafi masallaci. Ganin yarinyar tana ta bacci tamkar dai
wata matacciya wato ta hana su bacci ita yanzu tana ramako. Sai da ta je har gaban ƴar ta saka
hannu ya dungure mata goshi.

"Shegiyar yarinya tun kina zanen goyo kin iya kissa da kisisina da taya uwarki kishi, wato kika ƙi
bacci kika hana mu cin amarci sai da kika ga gari ya kusa wayewa kika kwanta kamar kasa kike
bacci. Little kuwa da yake bacci ya ci ƙarfin ta ko dingurin da aka mata bata ji ba bare ta falka


Tana idar da sallar ta kwanta baccj tana jiyo muryar Ya ABDUL a falo da ya dawo daga
masallacin maimakon ya shigo ya zauna yana karatun qur:ani ita dai har bacci ya ƙara surar ta
bata ji ya daina karatun ba.

Wajen ƙarfe takwas ya ta ji yana kiran ta idanu ta murtsuka ta tashi zaune.

Ki mata wanka ki haɗa mata madara ta sha" Ya ce tana miƙa mata yarinyar sai wasa take tana
dariya abin ta tamkar dai ba ita ce ta rufe ido take kuka da dare ba. Dakyar ta lallashi kanta ta
karɓi ƴar zani ta ɗauka a jakar kayan ta ta goya ta ta nufi kaicin ta ɗuma ruwan wankan, fidar ta
zo ta ɗauka ta wanke ta ƙara haɗa mata madarar sai ta ajiye ta je za ta mata wankan, ta cika
famfas ɗin da kashi takaici HEEDAYA har da ƙwallar ta. Haka ta wanke mata ta mata wankan ta
saka famfas ɗin a shara. Shirya ta yi ta zauna ta bata madarar yana zaune yana danna waya
da yake yau lahdi ma babu inda zai je.

"Akwai turarukan ta cikin jakar ki shafa mata" Da to ta amsa ta ɗakko ta shafa mata, ita ma
wankan ta yi ta je ta haɗa break fast ta kawo suka ci. Kwantar da Little ɗin ya yi ya haura sama
ya yi wankan ya shirya ya fito ya buɗaɗa ƙamshi. Ta lura ma dawowar yarinyar kusa da shi
kamar ma damuwar sa ta ragu don sai wani ɗan walwala take gani a fuskar sa.
"Bari mu je mu gaishe da Ammie" Ya ce yana ɗora Little ɗin a kafaɗar sa. Da a dawo lafiya ta
raka shi tare da cewa ya gaishe da Ammien. Ita mamaki take yi ma da yakr iya tuƙi da yarinyar
a hannun sa ko kuma a kujera yake kwantar da ita shi ya sani. Tabbas sai ta yi maganin
wannan tatsitaiyar yarinyar don ta ga yanzu ita ce kishiyar ta wato ma maimakon ita amarya ya
fita da ita sai wata yarinya hmmm!.

Yana fita ta ɗau waya ta kira Umma suka gaisa ta kwashe komai ta faɗa mata Umma tana ta
faman faɗin dole a samo mafita. Suna gama wayar ta kira MEEMA.

"Inyee amarya mau maganar sugar har an tashi kenan na ɗauka ku manya manya sai sha biyun
rana ko ƙarfe uku saboda amarci" Ta ce tana dariyar wasa.

"Hmmm!. Bari ke dai MEEMA" Ta ce tana kwashe komai ta faɗa mata.

"Kan uba!. Kuma kika yarda?"

"To ya zan yi?"

"Sai ka ce ba mace ba kika zauna ranar farin cikin ku ta tafi a banza da ya baki madarar bakya
samun maganin bacci ki haɗa mata a cikin madarar shegiya ta ɗaɗɗaka ta ringa bacci kamar
matacciya ku kuma ku raƙashe amarci abin ku" Shiru HEEDAYA ta yi tana sauraron MEEMA jin
ta zo mata da abin da ita da Umma basu hasaso ba.
"Wallahi kwanyata toshewa ta yi jiya ko kaɗan ban yi wannan tunanin ba kuma bana jin akwai
maganin mura a gidan nan amma zan ba me gadi ya siyo mini yau in ɗirka mata haba ina dalili"

"Ko ke fa ai in ya san wata bai san wata ba, namiji ai ya kasance a tafin hannun ki shi ne amma
ba wai ki zauna yana mulkar ki ba, duk wannan jiji da kan nasa sai kin cire masa su"

"Kin san waye Ya ABDUL kuwa?"

"Shi ba namiji ba ne? Ai boka ya gama miki aiki tun da har kika zama matar sa yanzu kuma sai
ki tashi da kan ki ki ƙarasa aiki, ki murza kambunki yadda kowace mace take murzawa kar ki
zama bora a cikin mata"

"Sai luluƙani daji kike ni ban fahimci kurman baƙin nan da kike faman karanta mini ba ki mini
dalla-dalla"

"Magungunan mata za ki nema na mallaka da duk wanda kika ji ana gara kan namiji daga nan
salon wasan zai sauya, akwai wani group na MANYAN MATA da nake ciki zan saka a sanya ki
ki shiga ki ga yadda ake bajin ta ki ga yadda mata suka zama sarakuna kuma gimbiyoyi a gidan
mazajen su babu ruwan su da ɓacin rai da wulaƙancin namiji rayuwar turawa suke namiji yana
nan-nan da su yana buɗe musu bakin aljihun sa, sannan tarairaya sai kin ce bakya so"

"Don Allah MEEMA?"

"Wallahi kuwa yanzu bari zan ba direbana magani ya kawo miki yanzun nan tun da ba ya nan
ya fita, ƙulaƙulai ne guda uku sunan sa uku bala'i a ƙasan ki za ki saka su narke maganin
mallaka ne namiji ko kan dutse gare shi kan tauri sai ya ladabtu sai ya zama raƙumi da akala"

"Dan Allah turo mini MEEMA wallahi wannan in ban tashi tsaye ba na ga alama ko ƴar soyayyar
nan ta amare da ake nuna wa mata sai dai in ga ana yi kuma don Allah ki saka a saka ni a
group ɗin don ni har na matsu na je na fara ganin me ake yi a ciki"

"Yanzu zai kawo miki ai mazan ne sai da tashi tsaye ana haɗa musu tarko amma in ka tsaya
kallon ruwa tuni kwaɗo yake maka ƙafa, ai hatta ƴar nan tashi sai dai ki ɗakko mai reno take
kula da ita amma matsayin ki ya wuce a ce kin zama ƴar wankin kashi, amarci ne ya fi dacewa
da ke"
"Shi sa nake son ki MEEMA ta in na mallaki Ya ABDUL na gama warkewa a duniyata na samu
komai ai ni wallahi in dai zai nuna mini ƙauna da kulawa to wallahi ko haihuwa ba zan yarda in
yi a kwana kusa ba bare har na yi saurin tsufa, sai na gama cin duniyata da tsinken tsire"

"Yo ai dama haihuwa mayar da soyayya baya take yanzu ba ƴarsa ce ta hana ku morewa jiya
ba to in ɗanku ne ma haka zai hana ku soyayya daga kun fara soyayya cikin dare ɗa ya tashi ya
yi ta tsallara ihu sai dai ki haƙura ki bashi shiga shayar da yaro shi kuma miji ya ƙullace ki don
ya shirya yin uzuri sa ɗa ya hana shi, in kin ga kin sake sai kin yaye yaro wataƙila kina yin
yayen wani cikin ya kawo kai shukenan fa ke sai haihuwa da reno shi ya sa namiji in ya ga ba
ya samun mai yake so sai ya ɗirko miki kishiya...

"Bari faɗin haka ni kin san na tsani kishiya"

"To ai kowace mace ma bata son kishiya sai dai dole don haka yanzu shawara ta ragewa mai
shiga rijiya" Haka ta ringa mata kuɗuba ita kuma ta hau ka ta zauna. Suna gama wayar jim
kaɗan ta mai gadin gidan ya zo ya mata nocking ya ce mata an aiko wani direba. Saƙon ya
karɓo mata cike da murna ta dawo ciki tana ta tsara yadda komai zai wakana. Bayan ta yi wa
maganin maɓoya ta dawo falo ta kwanta ta hau whatsapp ai kuwa ta ci karo da sunan MANYAN
MATA group sai sannan ma ta tuna da shi ne group ɗin da MEEMA ta ce za a saka ta cike da
murmushi da kuma son ganin mai ake yi a ciki ta shiga. Saƙonni ne suke ta shigowa.

Ai sai yanzu na matsa masa ya fita.

Wata kuma ta ce
Ai wallahi mu dai babu ruwan mu da matsalolin gidan aure ai in namiji yana nuna maka
soyayya ji kake babu ya kai sannan baka da wata damuwa. Yadda kowacce take fitowa tana
faɗar yadda alaƙar ra take da mijin ta abin ya birge HEEDAYA irin rayuwar da take mafarkin
samu.

MEEMA ce tana hawa online ta shiga group ɗin ta gabatar da HEEDAYA matsayin ƙawarta.
HEEDAYAR ma magana ta yi tana yi wa MEEMA godiyar gabatar da ita tare da cewa Allah sa
su ƙaru da juna.

"Barka da zuwa sister" HUSNA ta yi tagging na maganar HEEDAYA ta mata barka da zuwa
amsawa ta yi tana godiya daga nan duk aka shiga mata sannu da zuwa. Ta ji daɗin yadda aka
tarɓe ta sannan kuma ta ƙara mamakin yadda kowa yake faɗar sirrin sa na zamantakewar
auren cikin group ɗin tabbas idan ta cigaba da zama a yadda ta fara a gidan Ya ABDUL lallai za
take shaƙar baƙon ciki yadda matan MANYAN MATA group suke faɗar zamantakewar su da
mazajen su ya tafi da ita sannan hakan ya sa ta ɗaura ɗamarar ƙwato nata ƴancin a gidan miji!.


Wayar ta ajiye ta ajiye bayan sun yi magana da MEEMA a private tana ta faɗawa MEEMA
mamakin dama ana samun haka irin wannan kulawar da matan group ɗin suke bada labari nan
ta tabbatar mata da kaɗan ta gani ta cigaba da zama a group ɗin za ta ga zahiri ma. Da wannan
ta shiga kicin ta yi girki, basu shigo gidan ba sai la'asar ya ce ya ci abinci a gidan Hajiya da yake
ma bacci Little RABEEYA take sai ta karɓe ta ta kwantar da ita don ya ce ta sha madarar ta a
can.

Da dare ko da ta tashi haɗa mata madara a kicin dama ta akiye maganin tarin da ta ba
mai gadi ya siyo mata na yara a cikin madarar ta zuga ta gauraya sannan ta saka a fidan ta ba
yarinya ta sha sai kuwa bacci ya ɗauke ta ta kwantar da ita. A bayi ta saka uku bala'in wajen
MEEMA. Yana ta danne danne a waya har sai da ya kammala ya kwanta ta ɗauki ƙaramar
kafifa ta shimfiɗa a ƙasa ta ɗauki Little za ta mayar da ita can.

"Dama ba ke za ki kwanta a katifar da kika shimfiɗa ɗin ba?" Ta ji ya jefo mata tambaya mai
kama da ta rainin hankali ta ji haushi sosai amma kuma sai ta danne ta ce

"Ka san yara da juyi to ba na so ne ta faɗo cikin dare wani abu ya samar mini ita" Jim ya yi sai
kuma ya ji ya gamsu da maganar tata kwantar da ita ta yi a ranta tana cewa

'Ashe dai da ake cewa namiji yaro ne za ka iya masa wayo ashe dai gaske ne kin ga har na
masa wayo, hmmm!. Sai ma ka ji uku bala'i ' Da dibara har sai da ta sanya burin ta ya cika!. Ba
ƙaramin ƙara son sa ta yi ba kuma sai yanzu ne ta ji tana mahaukacin kishin da bata so kowace
mace ta raɓar mata shi, ji take ina ma bai taɓa sanin wata mace ba sai ita amma ƙaddara ta

riga fata tun da ya auri Aunty RABEEYA ta aure shi sai dai za ta yi iya yin ta na ganin har duniya
ta naɗe bai sake sanin wata ƴa mace ba don ita ce matar sa a duniya a ƙiyama ma ita take so
ta zauna da shi.

Ya ABDUL tun da ya kusance ta sai ya ji wata zazzafar ƙaunar ta tana fisgar sa ya ji ya aminta
da ita sai ya ji gabaɗaya damuwar da take danƙare a zuciyar sa ta washe yanzu son HEEDAYA
yake yi. Zaune suke a falo suna hira irin ta masoya ya fara mata zancen Aunty RABEEYA da
yadda yake jin ciwon rashin ta har yau. Amma ta ƙeƙashe ƙasa ta ce ita bata son maganar
kowace ƴa mace wai kishi take ji. Yanzu kam sai yadda ta yi da shi don a yanzu wata mata ta
samu wacce ta ɗan manyanta haka take rainon Little ita take mata komai kuma ba ya iya yi
mata musu domin yanzu tsoron ɓacin ranta yake.

Yau ta kama juma'a don haka bayan ya shirya cikin shadda sky blue ya saka hula sai tashin
ƙamshi yake.

"Baby nah zo mu yi hoto" Ta ce tana kashe masa ido ɗaya. Babu musu ya zo tana rungume da
shi ya sunbace ta a kumatu ta ɗauki hoton. Sun matuƙar yin kyau don ita ma material ne sky
blue ɗin mai jar fulawa a jikin ta. Har bakin ƙofa ta raka shi tana masa a dawo lafiya. Yana fita ta
dawo falo ta kwanta a kan doguwar kujera ta hau whatsapp group naau na MANYAN MATA ta
shiga kamar yadda ra zata haka ce ta faru domin kowacce tana turo hotunan ta da suka ɗauka
da mijin ta haka suke duk ranar juma'a. Sai dai idan za su tura hoton ba a buɗe fuskar miji sai a
samu ɗan emoji a rufe saitin fuskar sai dai a bar jikin sa ita kuma matar ana ganin ta tangararai.
Alfanun hakan don kowacce ta nuna majinta da irin soyayyar da suke ita da mijin ta haka za a
ringa yabawa kowacce ana fasa mata kai shi ya sa ma ba sa barin ƴan mata ko zawarawa su
shigar musu group.

"WOW! Amma HEEDAYA kina hutawa kalli wata kulawa da ya nuna miki ji yadda ya sumbace
ki" Wata ta yi magana da ta ga hoton HEEDAYA da Ya ABDUL duk da ta rufe masa iya fuskar
sa amma ana iya ganin yadda suka yi hoton tana jifan sa da wani shu'umin kallon soyayya.

"Ai na faɗa miki tana shimfiɗa soyayya a gidan ta tana taka bazarta" Wata ma ta faɗa tana saka
emojis na dariya. Kan HEEDAYA ne ya fashe ta tuno wancan satin video ne ta ɗauka tana
bayan Ya ABDUL yana mata doki irin wanda yara suke yi wato ya sunkuya ta hau bayan sa
yake zaga falon da ita, dama kuma ta saita wayar ta tana ɗaukan bidiyon, shi ta tura wancan
satin a matsayin goron juma'a.

Husna wacce zuwanta yanzu kenan ta turo hoton ta ita kaɗai twna zaune a kan kujera a falo
tana murmushi. Gabaɗaya aka iyo mata caaaa ana cewa ai bata more ba ita kullum sai dai ta
turo hoton ta babu miji.

"Na sha faɗa musu mijina matafiyi ne ba ya zama sai ya yi wata biyu ma ban saka shi a idona
ba, kuma ko ya zo ma wallahi ba shi da lokacina bare har ya kulani mu yi wani hoto ba ya
girmama buƙatata ma" Kowa jajanta mata ya yi suna cewa bata dace ba wata mai shegen

surutu ta ce

"Wai shi kuwa wane irin bussines ne wannan yake tafiya har wata biyu kuma idan ya dawo na
ya ƙi baki lokacin sa?, Fisabilillahi ina Kano ina Lagos?"

"Eh mana aikin kamfani, kamfani ne da shi na yin robobi"

"To ai ba kamfanin robobi ba ko kamfanin silbobi yake da akwai wata biyu ya yi yawa sai ka ce
wani soja, to mai ya sa ma ba zai tafi da ke ba"

"Wallahi ya ƙi"

"Wannan da sake ni ba zan ma iya wannan rayuwar ba" Wata ma ta faɗa.

"Gaskiya kina cikin jarabawa" MEEMA ta ce tana jimantawa.

"Allah kyauta!" Cewar HEEDAYA.

HUSNA kuwa maganganun da suka yi sai ta ji zuciyar ta ta karaya don ita sai take ji ma
tamkar bata da maraba da wacce bata da aure bambancin kawai ita akwai igiya a kanta kuma
dai mijin yana ɗaukan ɗawainiyar ta amma da sai ta ce babu.


Tana fitowa daga group ɗin ta samu saƙon wata baƙuwar no tana buɗewa ta ga haka.

"Slm suna na HEEDAYA ni ƴar garin Dutse ce da yake jihar jigawa, ina da aure na ɗauki no ki
ne a MANYAN MATA group" Amsa mata HUSNA ta yi tana mata godiya da jin daɗin ta na
kulawar ta gare ta.

"Ni suna na HUSNA ni ƴar garin Kano ce sannan ina aure a Kano" Nan suka shiga taɓa hira
HEEDAYA tana mai kwashe komai ta faɗa mata game da yadda za ta jawo hankalin mijin ta don
har ta ce za ta saya mata uku bala'i ta aika mata Kano godiya ta ata sosai don ita ce ta uku da
HEEDAYA ta ɗauki no ta bi pc tana son samun ƙawaye matan aure don yanzu duk ta watsar da
ƙawayen ta ƴan mata ko Ifteehal da ta zo gidan ta warning ta kora mata a kan kar ta ƙara zuwar
mata gida idan kuwa har ta ga sun cigaba da ƙawance to ta tabbbatar aure ta yi don ba za ta yi
ƙawance da marar aure su ƙwace mata miji.


Yau kwana biyu kenan sa boka ya musu aiki a kan Ammie don farraƙa tsakanin ta da ɗanta
kamar yadda suka yi alƙawarin yin haka. Tun da dai sun kasa raba shi da Little ɗin duk da yana
son HEEDAYA amma yana nuna wa ƴarsa kulawa. Tsawon kwanaki biyun nan YA ABDUL bai je
gaishe da Ammie ba. Abin ya bata mamaki don haka ta shirya da magriba direba ya kai ta
gidan nasa don ta gani ko lafiya don ko kiran sa ta yi a waya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login