Showing 21001 words to 24000 words out of 64514 words

Chapter 8 - BONONO BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN AFRAH f.pdf

30 Mar 2025

5093

Na ce Hajja tana ciki?"

"Uhm-uhm" Ta bashi amsa a ciki-ciki da sauri Umma da Hajiya Aisha suka dafe ƙirji jin
HEEDAYA ta bada amsa idanu suka zaro cike da fargaba! Tun da cikin sharaɗi ko uhm an ce
kar ta yi. Daga haka sai suka ganta ta je ta haƙa rami ta binne layar ta tashi ta bar wajen. Daga
nan ya saka yatsa a kan ƙwayar hoton bidiyon da suke kallo ya ɗauke.
"Ai na faɗa muku sai dai in sharaɗi aka ƙetara amma mu idan muka yi aiki babu makawa sai
aiki ya ci sai dai in mai aiwatar da aikin ne ya samu akasi wajen aiwatarwa"

"Bata faɗa mana ba ko kaɗan kawai dai mun ji ba a ɗaur auren da ita ba" Umma ta faɗa cikin
sanyin murya sai yanzu take jin haushin kanta na zargin laifin sa ne ashe dai HEEDAYA ce ta

kwaɓa musu aiki.

"Ai dama ba za a ɗaura da ita ba tun da ta ɓata aikin, amma da a ce bata ƙetara sharaɗi ba to
da yanzu da igiyoyin auren sa uku ras a kan ta da yanzu kuna can kuna shagali da
shirye-shiryen kai ta ɗakin ta, don babu wanda zai yi musu ko ya furta wata kalma marar kyau
dangane da auren kawai za a fasa ne da ƴar uwar ta a ɗaura da ita" Ya faɗa hankali kwance.

"Kai amma yarinyar nan ta jiƙa mana aiki amma a mana wani ƙoƙarin mana, ba yadda za a yi
yanzu a yi kwaskwarima?" Hajiya Aisha ta tambaya da zummar matsawar za a musu gyara a
lamarin su samu cikar burin su ta ɗauki nauyin biyan duk yawan kuɗin da zai yanka musu.

"Aikin gama ya gama sai dai wani aikin da ban sai dai iya bincike na, na hangi akwai aure
tsakanin ta da shi ABDUL ɗin tabbas ko ba yau ba akwai ranar da aure zai ɗauru tsakanin su su
zauna a matsayin ma'aurata sai dai ban san yaushe ne ba kuma a ina ba ne" Shiru duk suka yi
suna nazarin kalaman sa sun shiga ruɗani to yaya haka zai faru kuma yaushe ne hakan zai
faru? Bayan su kan su sun san HEEDAYA da RABEEYA ba za su taɓa auren miji ɗaya ba
saboda haramcin hakan ko dai yana nufin ABDUL ɗin ne zai saki RABEEYA ya auri HEEDAYA
amma in haka ne ai kwaɗon ya yi yawa, kwamacalar ta isa haka gaskiya ba ma haka bane
akwai dai wata maƙarƙashiya a gaba wacce basu san wace iri ba ce sai dai sun sanya a ransu
cewa za su jira wannan rana!. Wannan suka ringa rayawa a rayukan su kafin suka masa
sallama bayan sun jimƙa masa maƙudan kuɗi suka tafi a kan cewa idan buƙatar hakan ta taso
za su sake dawowa, amma dai za su zubawa sarautar Allah ido su jira zuwan ranar da ya ce
tana zuwa.


Lokacin da suka dawo su Abba basu dawo ba, cikin gidan suka tasamma. A farfajiya suka ci
karo da Hajja tsohuwa mai shegen rangwangwan ɗin tsiya.

"Zainabu, Zainabu" Hajja ta shiga kwaɗa mata kira kamar za ta ari baki dakyar Umma ta lallashi
zuciyar ta ta amsa tare da juyowa.

"Yanzu Zainabu ni ɗin kike wa magana getsetse kamar wata sa'arki fisabilillahi ina uwar mijin ki
amma saboda ba uwarki ba ce" Ta faɗa tana kama haɓa.

"Haba Hajja kin kira ni na amsa to ya kike so na miki ko sunkuyawa zan yi ki hau in goya ki"

Salati Hajja ta kwasa tamkar an yi gagarumin wani abu ta ce

"Oh in da ranka ka sha kallo wannan zamani ai na haifa miki miji na gama miki komai ko zagina
ma kya iya yi" Juyawa Umma ta yi za ta tafi don Hajiya Aisha tuni ta shige ta bar ta ga mutane
suna ɗan wucewa jefi-jefi.

"Au Allah tafiya kika yi Zainabu kika bar ni ina zuba tamkar kin kunna rediyo"

"Wai mai kike so da ni ne Hajja? Ki bar ni da abin da yake damuna mana haba da wanne zan ji"
Umma ta faɗa a zafafe tamkar za ta yi kuka don duniya ta rasa ina za ta saka ranta ta ji daɗi
komai gani take ya kwaɓe.


"Allah baki haƙuri dama ɓangaren ki na je zan miki barka da arziƙi na auren ƴarki RABEEYA da
aka ɗaura na samu bakya nan shi ne zan tambaya ina kika tafi"

'Wannan tsohuwa da tsinannan sa ido take ko ina ruwan ta da inda na tafi"

"Gudawa nake na tafi asibiti"

"Ayyo! Ko da na ji ki ce babu lafi... Bata gama jin mai za ta ce ba ta juya da sauri ta tafi ganin
Hajiya Baturiya uwar amarya ta fito daga part ɗin ta sanye cikin wani dakakken leshi sai wani
annashuwa take irin ta farin ciki, ita kuwa Umma ji ta yi kamar ta je ta shaƙe ta ma kowa ta huta.

A falo ta samu Hajiya Aisha da Aunty Hafsa suna magana, ga mutane nan sai abinci suke ci
suna hira. Bugunzum-buguzum ta zo ta wuce ba tare da ta ce wa kowa ƙala ba ta nufi hanyar
bedroom ɗin ta ranta yana mata suya. Ƙofar ta banka da ƙarfi ta shiga tare da maidawa ta rufe.
HEEDAYA da take kwance fuska sharɓar da hawaye jin an buɗe ƙofa ta zabura haɗe da tashi ta
sakko daga kan gadon ganin Umma ta nufi Ummar tana fatan samun wani daddaɗan labari da
zai faranta mata ya tsamo ta daga dogon nutson da ta yi a cikin kogin tunani da damuwa.


"Umma!" Ta faɗa fuska a shagwaɓe tare da nufo Ummar. Umma da take cike da haushi da
baƙin cikin abin da HEEDAYA ta yi na jiƙa musu aiki wajen ƙetara sharaɗi na ƙarshe a aikin
bayan sai da ta yi kowanne cikin bin umarni amma sai da aski ya zo gaban goshi ta ɓata musu.

Umma sai da ta bari HEEDAYA ta zo gabanta ta ɗaga hannu ta zabga mata mari a ganin ta
hakan zai rage mata raɗaɗin da take ji a ranta...


Wasa farin girki

MAMAN AFRAH
09013181851

[2/12, 12:52 PM] MOM MASHKUR & AFRAH:
https://chat.whatsapp.com/F7TUZezpOWLKYnyTNFuy2Y


BONONO


(RUFIN ƘOFA DA ƁARAWO)


NA


MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.


*SADAUKARWA*

Daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne ga MARYAM SANI HAFIZ (Merry tah) Alkairin Allah ya
kai gare ki Allah lulluɓe rayuwar ki da tarin ni,imomi da albarkatu Allah raya mana Abdallah
fatan alkairi.

Daga marubuciyar:

Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*



PAGE 7



*HUSNA*

Zaune take a tangamemen falon ta sanye take cikin riga da wando wanda suka kama jikin
ta, sun yi matuƙar mata kyau! Duk wata sura ta ƴa mace ta bayyana kasancewar ta mai cikar
halitta da duk wani abu da namiji zai buƙata ta mallake shi. Sauke idanun ta ta yi daga kallon
TV take ƙarewa kanta kallo tana jinjina irin kyan da ta yi don kawai ta birge mijin ta wanda a
ƙalla yau wata biyu kenan bata saka shi a idanun ta ba, kullum yana yawon garuruwa wanda a
koyaushe yake faɗa mata cewa bussines ɗin sa ne yake sanya shi tafiye-tafiye. Waya ta ɗaga
ta duba ƙarfe biyar da ƴan mintina na yamma amma bai samu ƙarasowa ba daga Lagos ɗin da
ya ce zai taho. Ta yi nisa a cikin tunanin makomar rayuwar auren ta sai ta ji ƙaran buɗe get ɗin
gidan kafin ƙwaƙwalwar ta ta gama saɓunta mata tunanin dalilin buɗe get ɗin, ƙaran dirin motar
ya tabbatar mata da cewa mijin ta HAMEED ne ya iso. Duk da akwai damuwa a zuciyar ta
amma sai ta ji wani sanyi a ranta ko ba komai dai ta san za take ganin mutum a kusa da ita tun
da ita bata taɓa haihuwa ba sai ƴan aikin gidan kawai da suke kai kawo. Da sauri ta nufi window
ta leƙo ai kuwa ta hangi direba ya buɗe masa ƙofa bayan ya fito ya rufe ƙofar. Ganin ya nufo
part ɗin da ɗan hanzari ta shiga sakkowa daga saman domin tarɓar sa tana fatan kuma kada ya
mayar mata da murnar ta cikin ta. A tsakiyar falon ta cim masa, tun kan ta ƙarasa sakkowa take
sakin murmushi sai dai ganin ya cunkushe fuska, duk da ta ji babu daɗi na ganin yanayin sa
amma haka ta ƙarasa gaban sa tana ƙoƙari rungume shi amma ya ja da baya tamkar ya ga
wani abun tsoro, yana kuma ɗaga mata hannu saroro ta tsaya tana kallon sa dama ta san
wannan rubutaccen abu ne yana kallon ta tamkar ya ga kashi a daidai nan direba ya shigo
masa da jakar kayan sa amma ganin direban bai sa ya yi sassauci ga abin da yake son faɗa ba.


"Sau nawa zan ce miki bana son wannan al'adar turawan baki san irin waɗannan ɗabi'un lalata
tarbiyar yara yake yi ba, yanzu idan kika saba da wannan ɗabi'un ba za ki fasa yi ba ko da mun
haifi yara kin ga kenan yaran mu za su taso suna koya!." Ya ƙarasa faɗa a harzuƙe direban
jakar ya ajiye da girmamawa ya juya ya fita. Kallon sa na tsaya yi tamkar na ga sabuwar halitta
ina rayawa a zuciyata.

'Shin sai yaushe ne zan fita daga wannan baƙin ƙangin? Shin sai yaushe ne HAMEED zai
faranta raina a matsayina na matar sa mai ya sa ya gwammace kullum yake nuna mini kansa a
tukunya yake bai waye ba amma yanayin sa da yadda yake gudanar da al'amuran sa ya nuna
shi wayyayyan mutum ne, amma ba ya son ko kaɗan ya nuna hakan a kaina ya fi so kullum ya
yi fatali da duk wani abu da ya shafi auratayyar mu.


"Haba HAMEED yau tsawon wata biyu ban sanyaka a idona ba, shin laifi ne don na tunkare ka,
ko kewar ka da na yi a matsayina na matarka ka bari in ji ɗumin jikin ka" Ta furta tamkar ta yi
kuka saboda takaici da kuma yanayin yadda ya nuna.

"HUSNA!. Sau nawa kike so in faɗa miki ni bana son irin wannan rayuwar turawan ko so kike
kullum nake biya miki kamar karatu sannan ne za ki haddace wane ne ni? Mai ya sa ku mata a
koyaushe bakwa tsayawa ku yi tunanin halayyar abokin rayuwar ku, mai ya sa bakwa amfani da

kalmar nan da bahaushe yake faɗin in an san halin mutum sai a ci maganin zama da shi?" Ya
kai ƙarshen maganar yana mata wani kallon rainin wayo.

"Su turawan wasu mutane ne da ban? Su turawan sun fi mu son farantawa junan su ne da suke
halayyar ai a ganina don ma'aurata sun yi wani abu a tsakanin su hakan ba yana nufin laifi ba
ne tun da komai aka gabatar matsawar bai saɓawa addini ba to halal ne...

"Idan kuma ya saɓawa al'ada fa?" Ya katse mata hanzari da jefa mata wata tambaya da take
ganin da yin tambayar da rashin ta duk uwar uban su ɗaya.

"Baki da amsar tambaya ta, abubuwan da kike sun saɓawa al'adar malam bahaushe kuma
wannan ɓata tarbiyar yara ne iyaye suke rungume -rungume ko sunbatar junan su matsawar ba
a lokacin kusantar junan su ba wato a keɓantaccen wuri"

"HAMEED, da addini da al'ada wanne ne a gaba?" Bata jira cewar sa ba ta ɗora.

"A cikin gidan nan daga ni sai kai sai ƴan aiki, shin mun haihu ne da za ka fara maganar ɓata
tarbiyar yara...

"Ya ishe ki HUSNA, mai ya sa kike uzzurawa rayuwata? Daga shigowata gida ko hutawa ban yi
ba kin tsare ni da yawan magana to ki dakata!. Ni HAMEED ba ni da lokacin ɓatawa" Yana kai
wa nan ya wuce ya bar ta baki sake, sama ya haura ai kuwa bata daddara ba ta take masa
baya. Sai dai kamar yadda ya saba hakan ya mata yau ma yana shigewa ɗakin sa ya banko
ƙofar tana zuwa ta tura ƙofar ta ji ya saka mukulli ya kulle. Jingina ta yi da ƙofar tana jin yadda
zuciyar ta take suya tana jin yadda ruwa ya taru a kwarmin idanun ta, ta rasa sai yaushe ne za
ta yi farin ciki kamar yadda kowace mace take yi a gidan mijin ta sai yaushe ne HAMEED zai
sauke nauyin haƙƙin ta matsayin ta na matar sa ita duk wani jin daɗi da mace take samu na
dukiya da sauran abubuwan more rayuwa a gidan aure ta mallake su, babu abin da HAMEED
ya rage ta da shi idan ta ce komai tana nufin komai da komai, sai dai a cire abu ɗaya wanda shi
ne ginshiƙin aure kuma shi ne kashi saba'in cikin ɗari na aure wato HAƘƘI duk abin da yake na
haƙƙin auratayya ne to ita bata san shi ba duk abin da yake kulawa ce daga namiji ga matar sa
sai dai ta ji a labari ko wajen ƙawaye ko ta karanta littafin hausa kai ita har bata son kallon film
saboda duk inda take ganin ana soyayya ko ba mace kulawa wanda ita ta rasa sai ta ji hankalin
ta ya tashi sai ta ji da tana da ikon sauya HAMEED da ta sauya shi amma kash!.

Ta daɗe a jingine a ƙofar tana jin sa har ya shiga bayi ya daɗe kafin ya fito hakan ya mata
alama da wanka ya yi, bayan wasu mintuna ta fara jiyo dirin maganar sa da alama waya yake.
Kunne ta ƙara kasawa a jikin ƙofar.

"Haba Baby ni ma ai ban ce na gaji da ke ba, ke kin sani bakya taɓa ginsa ta a rayuwa iya
magana da taushin kalaman ki kaɗai sun isa ki janye alakar duk wani ɗa namiji da yake jin
kansa domin ke ta daban ce" Waɗannan kalaman ne ta jiyo su a cikin dodon kunnen ta, wanda
ta ji shigar su tamkar tafashashshen ruwan zafi a hankali cikin sanyin jiki ta bar jikin ƙofar

dakyar take ɗaga ƙafafun ta har ta sakko ƙasa a ɗaya daga cikin kujerun ta yi wa kanta
masauki, tare da saka hannuwan ta biyu ta rufe fuskar ta hawaye masu ɗumi suka ci gaba da
wanzuwa a dakalin kyakkyawar fuskar tata.

'Sai yaushe ne? Mai na rasa a halitta? Wane irin gyaran jiki ne bana yi? Tsafta kwalliya tatttali
tsara kalamai duk don in ja hankalin mijina, duk wani abu na gyara da mace za ta buƙata don
gyaran auratayyar ta ina yin sa amma sai dai ban yi dace da mijin ƙwarai ba. Shin dama duk
matar da mijin ta bai damu da ita ba bata da wata dama a wajen mijin ta? Duk namijin da
hankalin sa yake kan matan waje matar sa ta gida bata dame sa ba? Duk haɗuwa da ladabi da
biyayyar ta? Mai ya sa matan irin mazan nan suke tamkar duwatsu ko bishiyoyi a cikin gidajen
su? Mai ya sa suke rayuwa tamkar ba ma'aurata ba kuma duk gyaran da za su yi basa birge
mazajen su, sai ki ga macen marar aji marar galihu wacce ma kina mata kallo ɗaya za ki mata
kallon raini wacce bata ma kai su yi ko da gaisuwar fatar baki da namijin ba saboda rashin
kamun kai da aji amma sai ta ɗauke masa hankali, shin kowace macen ce take fama da irin
ciwon ko kuwa ita kaɗai ce?' Ta shiga rattabowa kanta waɗannan tambayoyin duk da har yanzu
zargin sa take bata tabbatar da cewa yana neman matan ba amma dai abubuwa da dama suna
mata kama da hakan. Ai shi ba dutse bane kuma ba icce ba ne da za a ce matarsa bata dame
shi ba, to don mai aka y auren, tun da yana da lafiya amma kullum maganar sa ɗaya ce shi
yana da raunin sha'awar mace ne, wanda tana ganin amsar nan tashi rainin wayo da rainin
hankali ne kawai.

Duk da ta san mafi yawan maza kashi casa'in cikin ɗari basa zama ba tare da suna da ƴan
mata ko zawarawa ba, tun da kowane namiji ƙarya yake ya ce bashi da budurwa ko bazawara
sai dai in munafurtar matar yake, kai ko da a ce akwai su a cikin mazan to basu da yawa, sai
dai ita irin yadda yake banzantar da ita ya yi yawa irin yadda yake waya da sauran su da wasu
mazan ya sha bamban kuma irin yawan tafiye-tafiye da yake ya yi yawa kai ko da a ce yana
tafiyar ai kamata ya yi yake yi da ita in ba zai yi ba aƙalla idan ya dawo ya tarayraye ta ya bata
kulawa tare da sauke haƙƙin ta amma ina!.

Wasu daga cikin ƙawayen ta mazajen su matafiya ne wasu aiki mijin yake wasu kuma
kasuwanci amma yadda mazajen su suke ma'amala da su ya sha bamban da yadda HAMEED
yake a ko yaushe kuma duk daɗewar da za su yi ba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login