Showing 27001 words to 30000 words out of 82824 words
Chapter 10 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf
abun yataso, insha Allah
zamuyi Maka waya"
Babban Yaya yabashi wata takarda yace "ga wannan, abinda na bincika ne Nima, nasan insha
Allah Shima zai taimaka muku"
Cikin farinciki yad'ago kansa yana Kallan Babban Yaya Bayan yagama ganin bayanan dasuke
jikin takardar yace "taimako kuwa, sosai da sosai, godia muke yalla6ai"
Kawai d'aga masa kai yayi batare da yace komai ba, Dan muguwar gajiya yakeji, bacci kawai
yake buqata,gashi magrib har tayi
Wata matace dake Sanye da uniform din kaki, tazo tareda Waheeda, ta rissina ta gaida Babban
Yaya Sannan tajuya, Babban Yaya bai kalli inda Waheeda take ba yayi wucewar sa gaba, driver
ya Mara masa baya �不
Gashi de shine Babban yayansu, Amma muddin tafiya ta had'ashi da'ita shine yake bude mata
mota, tarasa dalili, Amma baya barinta tabude mota da kanta, yau kuwa yana zuwa yashiga
baya ya zauna, yasa hannu yarufe motar, Waheeda ta tsaya tayi shiru tana ganin ikon Allah,
wato in taga Dama ta6ude kofar ta da kanta kenan, yau ba mutunci, batayi gigin bude gefen
dayake ba, tayi sauri ta zagaya daya gefen tabude tashiga, tana shiga wani Sanyi da qamshin
turaren sa ya bugeta, tasa hannu tarufe motar, driver yaja suka tafi Lumshe idonsa yayi yana sauke wata irin ajiyar zuciya, lokaci d'aya wata irin nutsuwa take
shigarsa wadda baisan dalilin taba, Waheeda ta Kalle shi da jajayen idanuwanta, cikin sanyin
murya wadda take nuna tayi laushi, ta zubar da makaman yaqinta tace "Sorry Babban Yaya...."
Yana jinta yayi shiru, hannunta dake rawa saboda tsoro ta 'Dora akan tsintsiyar hannun sa
wadda take cike da gashi, cikin fishi yasa hannu yabige hannun ta yajuya mata baya yana
Kallan window, lokaci d'aya ta rushe da wani irin Kuka
Driver ya d'aga murya yace "kiyi hakuri Waheeda, ba gashi kin futo ba, gaki ga yayanku, ai kuka
yaqare"���
Waheeda tayi shiru tana goge hawaye, Amma kamar ruwa tana gogewa wanine yake sake
sakkowa, har cikin ransa kukan ta yana ta6a ransa, Amma dole ne ya nuna mata kuskuren ta
Suna zuwa gida ma kafin a dedeta parking yafice daga motar yayi ciki,itama tafuto tana goge
idonta tabi bayansa jiki a sanyaye, gaba d'ayansu family din na Arabo suna falon, daga kan
iyayen har 'ya'yan, yana shiga qannansa suka fara yimasa sannu da zuwa daga mazan har
matan, fuskar sa a d'aure yake amsa musu, yanemi waje ya zauna yana gaida su Hajiya Anty
da Uncle Usman, saikuma Daddynsa, Waheeda tana shigo wa 'yanbiyu da Anty Maryam sukayi
kanta suka rungume ta, cikin farin ciki suke fadin "Thank you Babban Yaya"
Saida suka saketa, sannan ta kalli kowa na falon, bata nufi kowa ba Sai hajiya Anty, tana zuwa
ta fad'a jikinta tasaki wani irin kuka, Hajiya Anty ta rungume ta aqirjinta, tanajin soyaiyar yarinyar
har cikin ranta, kasa bata hakuri tayi, Sai Bayan ta datake bubbugawa, Ummah ta Kalle shi tace
"sannunku, ai jinake acan zata kwana"���
Daddy yace "Nima abinda naso kenan, tunda bata jin magana"
Uncle Usman yayi murmushi baice komai ba, Ummah tajuya ta kalli Waheeda datake kuka a
jikin Hajiya Anty tace "kitashi kije kisaka muku abinci keda yayanku"
Har zuwa lokacin fuskar sa a daure take, cikin sauri yace "A a Ummah tabarshi kawai"
Waheeda tanajin irin amsar daya bayar tasake riqe hajiya Anty tana fashewa da sabon kuka,
Hajiya Anty tayi qasa da muryarta tace "sorry Baby na menene Kuma na kukan? Ba gashi kin
dawo ba?"
Cikin kuka tace "To ai Babban Yayan yaqi ya huce"
Anty tayi murmushi tace "rabu dashi, anjima kije d'akinsa kibashi hakuri"
'Daga mata Kai tayi, sannan tatashi daga jikinta ta wuce d'akinsu domin watsa ruwa.
Sai a lokacin 'Yan falon suke fara'ah, kana Gani kasan akwai had'in Kai dakuma jituwa a
tsakanin su, anan sukaci gaba da zama Bayan mazan sun iyo sallah sun dawo,'yanbiyu ne suka
had'a abinci, suka kawo falon aka baje anacin abinci, uncle Usman ya kalli Sa'ad yace "Kai jeka
kiramin yayanku a d'akinsa"
Sa'ad yaje yakira shi, yana Sanye da jallabiya fara qal, daga Gani kasan Sai mutum Ma'abocin
tsafta ne zai saka ta, tsugunna wa yayi agaban iyayen nasa, uncle Usman yace "munyi waya da
Yaya Habu, yanata tambayar ku, to tun kafin yafara korafi, yakamata ka shiryawa qannanka
tafiya,suje suyi masa kwana biyu"
Wani irin farinciki ne yakama Babban Yaya, yaji dadi da Uncle Usman yace ya shirya wa
qannansa tafiya,hakan yana nufin banda shi kenan, dama damuwar Waheeda duk ta isheshi,
Gara su tattara sutafi subar masa gidan dagashi da ummah ���
Kafin yabada amsa
Daddy yace "Usman yakake cireshi daga ciki? Yashirya su tafi gaba d'aya kawai, Sai suyi sati
d'aya,su huta saisu dawo"
Uncle Usman yace "ba aiki yake ba Yaya? Yaje qauye ya zauna har sati d'aya?"
Daddy yace "wanne irin aiki? Ai yayi retired, d'azu dayazo yace bazai sake komawa ba, saboda
idan yakoma ma matsalar Waheeda zata dawo dashi, to idan ya zauna anan ma babu abinda
zaiyi, Gara suje qauyen"
Uncle Usman yayi Daria yace "a a, suyi kwana biyar de, idan sukaga dangi saisu dawo"
Yana jin yanda suke tattaunawa yaji ransa ya6aci, baya son zuwa wajan baba Habu, saboda
idan yaje ya dinga masa maganar aure kenan, shikuma ba auren yake soba, lallausar sumar
Kansa ya shafa yace "zamuyi kwana biyu uncle, ya'isa, saboda aiki na" ���
Daddy yace "zaka koma aikin kenan"
Babban Yaya duk ransa babu dadi a taqaice yace "eh"
Ya tashi zai nufi d'akinsa, Ummah tace "bazakaci abincin ba? Kowa yana zaune shine zaka
koma d'aki ka zauna kamar sabuwar amarya?"
Yace "Ummah na qoshi"
"kamarya ka qoshi? Ban fahimta ba? Kadawo daga wannan doguwar tafiyar kace bazakaci
abinci ba? Yi hakuri Dawo ka zauna nabaka"
Yanbiyu suka had'a ido sukai murmushi, Daddy yace "a a, Usman kaji fa, ni banta6a ganin uwar
da bata 6oye son d'anta nafarko ba sai Hajiya, qarara take nunawa Yaron Nan soyaiya"
Uncle Usman yayi murmushi yace "ya qwace wa Waheeda kujerar tane, ga auta,me za'ayi da
tsohon tuzuru"
Babban Yaya yayi murmushi yace "Ummah Nasha madara, saida safenku"
Ummah Tajuya ta kalli hajiya Anty tace "kinga fishi yake, tun dazu nake masa maganar abinci
yaqi ci"
Hajiya Anty takalli Waheeda,tuni Waheeda ta d'auki haske, tatashi tafara zuba abincin tace "Bari
nakai masa Ummah"
Ummah tace "jeki Kai masa, idan yaqi ci kirabu dashi, shiyasan meyake damunsa Kuma"
Waheeda tadauki abincin ta nufi d'akinsa dashi
Gaba d'ayansu 'Yan falon Saida furucin Ummah ya basu dariya, Wai shiyasan meyake
damunsa
Anty Maryam ta shirya zata tafi, Sa'eed ya d'auketa shida Sa'ad, zasu rakata gidanta
Waheeda na zuwa kofar d'akin nasa batama nemi izni ba tatura 'Dakin nasa tashiga, yana
zaune agefen gadonsa abun duniya yataru yamasa yawa, ga zancen tafiyar su qauye gakuma
6acin ran Waheeda
Yanayin data ganshi aciki ne yasa tayi sauri tayi qasa da idonta, daga shi zai gajeran wando da
alama bacci zaiyi, inde yayi wannan shigar Dama tasan bacci zaiyi, agaban sa ya ajiye abincin
kanta aqasa tace "gashi Wai inji Ummah"
Tafad'i haka Sannan ta takure awaje d'aya kamar wata baquwa
Yace "ki d'auka kimaida mata, ai nace Nasha madara"
Muryarta ce tafara rawa tace "Dan Allah Kaci"
"kindamu dacin abinci nane? Inda bakya son damuwata ai bazaki dinga batamin rai ba, idan
aure kike so saiki futo fili kifadamin aure kike so Sai Amiki"
Cikin sauri tace "Allah Bahaka bane, ni banason aure, Dan Allah kayi hakuri Kaci abincin"
"nafada miki bazanci ba, Ummah ce ta aikoki kikawo min, Kuma nariga nafada mata banajin
yunwa"
Kanta aqasa tace "qarya fa nake, nice nakawo ma"
"to saiki koma dashi, bazanci ba"
Kukane yazo mata, ahankali hawaye ya silalo daga idanunta, cikin kuka tace "Babban Yaya
Dan Allah kayi hakuri kadena fishi Dani, wallahi bazan sake ba, kakawo paper da biro muyi
dakai arubuce bazan sake 6atama raiba"
"ko gaban alqali mukaje bazaki daina halinki ba, kitashi kije kawai, rayuwa ce, ta'ishi kowa"
Tanajin wannan furucin nasa tasake fashewa da Kuka, da sauri ta nufeshi tad'ora kanta akan
cinyarsa tana bashi hakuri cikin kuka
��喫��訣aro idonsa yayi, cikin sauri yahad'e qafafunsa waje d'aya, sannan ya janye kanta
daga wajan,gudun karta sake aikata abinda tayi yanzun, ta6aro masa aiki, yasa cikin sauri yace
"naji... Naji, Nina haqura, shikkenan komai ya wuce, Bani abincin"
Cikin sauri ta bashi abincin, sannan tace "kona baka Babban Yaya?"
Yace "a a, tashi kije, zanci da kaina"
Tashi tayi tsaye sannan tace "thank you" tafuto daga Dakin, shikuma yasaki wata nannauyar
ajiyar zuciya
Bata dad'e da futowa daga falon ba su hajiya Anty suka tafi, suna fita Maya tazo gidan, Bayan
sun gaisa dasu Ummah, Waheeda tajata sukayi cikin d'aki, zama sukai akan gado Maya ta
qarewa Waheeda kallo, tace "lalle Waheeda kinga rayuwa, 'yanbiyu suka cemin 'Yan sanda sun
tafi dake bakiji yanda gabana yafadi ba"
Waheeda tayi ajiyar zuciya tace "Maya ai rayuwa Kam Ina kan ganinta, Babban Yaya nefa yace
sutafi Dani" �朮
"ai Dama saida nace Miki ki dinga jin maganar sa" cewar Maya
Waheeda tace "to Maya mutum saiya zauna babu saurayi? Candy fa muke shirin yi, idan ya
hanani kula samari shine zai aure ni?"
Maya tace "kika Sani"
Cikin masifa ta hayaiyaqowa Maya tace "kamarya nasani,? Me kike nufi? Koji kike agarin
maguzawa muke?"
Maya ta dafata tace "maida wuqar qawata, ke kinsan da hakan meyasa zakice min idan bakiyi
samari ba shizai aure ki?"
Tashi tayi tsaye ta nuna wa Maya qofa da hannunta, tace "tashi kifice daga 'Dakin Nan kafin
namiki rashin mutuncin Dana saba Maya, nasan irin Zaman da zanyi dake wallahi"
'Yanbiyu ne suka shigo 'Dakin suka tarar da drama, Ihsan tace "kema de Maya da naci kike,
Ana wulaqantaki kina liqewa, ai shikkenan"
Tana fad'ar haka tatada kabbarar sallah duk da ba tasan menene dalilin fad'an nasu ba
Intisar tace "Maya muje na rakaki hanya, mungode, Dakin Sani ma bakizo ba, Dan waheeda
ba'a mata gwaninta, gobe ma qauye zamu tafi muyi kwana biyu"
Maya ta kalli Waheeda tayi murmushi tace "a dawo lafiya qawata" daga Nan suka futo daga
'Dakin, Waheeda kuwa ko uffan ba tace musu ba, tayaya ma Maya zata dinga had'ata da
Babban Yaya? Yayanta uwa d'aya uba d'aya saikace wasu kafirai ba musulmai ba? Tsaki tasaki
Bayan fitarsu tashige toilet domin d'auro alwala
Washe gari haka suka had'a kayansu, kowa ya shirya Amma banda Babban Yaya, yana
d'akinsa yaqi futowa, kwata kwata baya son zuwa, Amma babu yanda ya'iya, haka yafuto suka
had'u afalo, sukayi wa Ummah sallama
Suna zuwa compound yaja ya tsaya, jiyake kamar yafashe da Kuka, Sa'ad ya Kalle shi yace
"Babban Yaya ya za'ayi ne?, Naga kamar mota d'aya tayi mana kadan"
Waheeda tayi zuruf tace "eh wallahi, aqaro mana wata, kowa yabaje son ransa" ���
Babban Yaya ya kalleta, sannan ya kalli Sa'ad yace "bawata mota daza'a qara, mushiga Prado
din can kawai muje, babu driver acikin mu ai bare muyi kayan motoci"
Waheeda tayi qasa da kanta, cikin ranta tace wannan Dani yake, sukuwa yanbiyu dariya suka
saka, ta Kalle su ta share su
Sa'ad ne zaiyi driving, Babban Yaya yana gefansa, Bayan motar Kuma Sa'eed da Yanbiyu da
Waheeda suka shiga, kasancewar glass din motar baqi ne Sai sukai tafiyar su cikin salama
babu Wanda yake ganin Babban Yaya bare masoyansa su tsayar dasu
Tafiya tayi tafiya yanmatan duk sunyi shiru kowa yana danna wayarsa banda Waheeda, �對�
Saisu Babban Yaya dasuke fira shida yanbiyu maza, Waheeda taga kowa harkar sa yake ba'a
Tata, ta kalli Babban Yaya tace "B�bban Yaya yunwa nakeji"
Sa'eed yace "Ina abincin dakuka Dauko?"
Waheeda tace "wanne abinci? Ai bamu Dauko komai ba"
Babban Yaya yajuya ya Kalle su gaba daya yace "waiku wanne irin mashirmata ne? Ku baku
iya komai na mata ba komai Sai ance kuyi? Babu irin shirin Nan da mata suke yi kamar su
snaks? Saide kici babu kuwa" ya qarasa maganar yana hararar Waheeda
Cikin sauri tayi qasa da kanta, saida suka yi gaba sannan yaga wani yaro yana saida qwai,
suka dakata yasauke glass din qasa kadan ya cewa Yaron "basu su juye subaka bucket din"
Waheeda ta leqo kanta tace "B�bban Yaya nikam guda uku ma ya isheni, bazan iyacin sama
da uku ba"
Cikin mamaki ya kalleta yace "Toda nawa zakici ya isheki inba ukun ba?"
Bakinta ta turo gaba tayi shiru, kowa saida ya Debi qwan yanda yakeso, sannan yabawa Yaron
kudin da yafi karfin qwan gaba daya harna bucket din, sukaci gaba da tafiya, Waheeda ta 6are
guda daya tad'an tashi kadan daga wajan zamanta, tamiqawa Babban Yaya saitin bakinsa tace
"Babban Yaya haaa"
Dafe Kansa yayi da hannunsa yayi shiru �丹��領����儭?
Cikin fada Sa'eed yace "ke Dalla malama kimana shiru, haba, duk kin damemu, yarasa qwan
dazaici saina bakin titi saikace ke?"
Babban Yaya yayi murmushi, yasaka hannun sa ya riqe hannun Waheeda data miqo masa
qwan, sannan ya karyi Dan kadan, yasaki hannun Nata, Waheeda Takoma wajan zamanta ta
zauna, tanacin sauran Wanda Babban Yaya ya karya, har suka kusa Garin, bata sake magana
ba, daga qarshe ma bacci ne ya dauketa, saida suka qarasa Garin sannan suka tasheta
Sosai Baba Habu da yayansa sukai murna da zuwansu, Sai Nan Nan ake dasu, matarsa mama
Haajara ta shimfida musu tabarma a tsakar gida kowa ya zauna, Ana sake sabuwar gaisuwa
Shayinsu na buzaye tatashi tadora musu,suna fira tana ajiyewa kowa agabansa,ta miqe tace
"Bari adora muku abinci, ga miya Nan nagama ta tun safe, Waheeda tatashi tacire hijabin jikinta
tace"zauna mama, zan Dora"
Tafadi haka tana nufar inda aka ajiye tukwanen gidan, Babban Yaya ya daga Kai ya kalleta,
cikin ransa yace kamar me Hankali
Baba Habu ya dauki wayarsa yafara magana "gasu sun qara so mekuke jirane Baku zoba?"
Daga daya bangaren akayi magana, saiya sake cewa "wanne irin zabbi? Ga kaji Nan tun jiya
Haajara take aikin su, zasuci, kutaho kuga yan'uwanku, banason rashin zumunci ni" �不
Kallan mama Haajara yayi yace "su Yahya ne, Suda yakamata ace suna gidan Nan dasu zamu
karbi baqi Amma ke kiji Wai sun tafi neman zabbi zasu kawo asoya musu"
Murmushi sukayi dukansu, yajuya ya kalli mazan yace "to ku aiba zama zakuyi ba, tashi zakuyi
mutafi ku gaisa da yan'unguwa, daga Nan muje na nuna muku gonakin mu, nida iyayenku"
Babban Yaya ya sunkuyar da Kansa baice komai ba, Dan tsoro yake yasan halin tijarar baba
Habu karya jaji6o masa wata yarinyar awannan qauyen
Sa'eed yace "Baba yanzu fa kagama cewa baqi,inamu Ina Gona? tokuje dasu Babban Yaya ni
zan d'anyi wani abu"
Baba Habu yace "kaji wani sakarci, tokai kana namiji Ina kaga ta zama? Sa'adun ne ko
Sa'eedu? Namiji baya zama, kutashi muje"
Sa'ad yayi dariya yace "Sa'eed ne baba, ka ganeshi dakyau"
Haka suka fita badan ransu yasoba, mama Haajara ta kalli tukunyar da Waheeda ta 'Dora, tace
"Waheeda wannan tukunyar a6ule take" Waheeda hankalin ta yana kan girki batajiba
Ihsan tace "Waheeda tukunyar da kika Dora a6ule take fa"
Juyowa tayi ta Kalle su, dama aciki take dasu, suna ganin ta tana aiki Amma babu Wanda ya
taso acikinsu,sun Barta tana Fama da hayaqi, dankwalinta ta turo gaba, tulun dogon gashinta
yafuto ta qeyarta, tace "kibarta taita zuba, Ina wuta tana ruwa, Sai muga wa Allah zai Bawa
sa'ah"
Mama Haajara tayi dariya tace "a a Waheeda, ba za'ayi hakaba" tatashi ta nufi wajan girkin,
suma yanbiyu suka taso, saita basu salat da tumatir su yanka
Majalissa Majalissa Baba Habu yake yawo dasu Babban Yaya yana nunawa abokai da
yan'uwan Arziqi su, kan kace me, matasa sun taru a wajan Babban Yaya, wasu suyi photo wasu
Kuma videos, wasu Kuma kawai binsa suke sunata zance, ayawon zaga Garin dasuke suka
hadu dasu Yahya, sune suka janye Babban Yaya kasancewar su sa'anni,sannan suka nufi
gonar dashi, daga baya baba Habu ya qaraso tareda su Sa'ad, gonakin yafara nuna musu yace
"wannan Babbar gonar ta Usman ce, gata Umaru can agaba, duk ni nake kula musu dashi,
dazaku iya da munje wasu gonakin daku duk kun Gani"
Babban Yaya yace "Baba gobe Sai muje ai, Sai muga gari ma"
Baba Habu yayi fara'ah yace "eto Kuma kaima kace wani abu, yanzu to riqe wannan fartanyar,
gyara min Nan wajan kacire ciyawar nan data futo" ���
Sa'ad yace "baba muda mukazo ganin gona Kuma saimu fara aiki?"��
"aiku ba mazaje bane, kubar namiji yayi aiki"
Babban Yaya yarasa abinda yake masa dadi, haka ya karba yafara cire ciyawar dasuka futo,
abokan baba Habu ne sukazo wuce wa ya daga murya yace "malam idi, ku qaraso ku gaisa da
yarana Yan birni"
Su malam idi suna zuwa sukace "masha Allah, Wai duka Nan yaran Usman da Umaru ne?"
Baba Habu yace "a a, duka yaran Umaru ne, shi Usman ai babu yaro awajansa"
Ya nuna musu Babban Yaya da Kansa yake sunkuye yana Fama da fartanya, yace "ga Babban
yayansu Nan nasashi aiki, kuduba kuga qwanjinsa fa, inda zai haqura da wannan tamolar ya
dawo Nan mudinga noma Aida yaji dadi, dashi kadai zanbarwa wannan gonar ya nome min ita,
haba meza'ai da wata tamola" �對�ya qarasa maganar yana yatsina fuska
Shide Babban Yaya baice komai ba, Sai abokan baba Habu dinne dasuke dariya dakuma su
Sa'ad
Baba Habu yasake Kallan sa yace "kunji yayi shiru kamar salihi, Nan kuwa qungurmin