Showing 6001 words to 9000 words out of 82824 words

Chapter 3 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf

tagani me kyau akusa da Qasan
gadonsu, ta kalli Ihsan tace "natsani mutum yarasa abunsa yace nice nadauka masa, mutum ya
zauna yanata tsinuwa akan zobe, irin haka bashida dadi, haba, mutum ya dinga tsinewa
Kansa?"

Intisar tace "Ihsan dake take fa"

Ihsan tace "inti waye yafada miki Ana kula marar Hankali ta6a66e?" ���
Intisar tace "Hakane Kam, kika Sani ko maganin haukar tatane yaqare take takeso kibata
wani?"

Kallan su tayi tace "ai mahaukaci shine Ana masa magana yake Kai duka, danhaka saiku
banbance tsakanin nida ku waye mahaukaci Kuma ta6a66e?"

Tana fada musu haka ta daura towel ajikinta, sannan tafara cire botir din gaban rigarta,
hannunta yana dungurar breast dinta taji zafi, qaramin tsaki tasaki tashige toilet dinsu ta danna
makunnar ruwan zafi, yana zuwa tacire rigar sannan tacire brezia din ahankali, boobs dinta ta
kalla taga nipples din sunyi jajir, cikin ranta tace bazan taba yafe maba Didat, da wannan ruwan
dumin tagasa jikinta sannan tafuto tasaka doguwar Riga marar nauyi batare data maida brezia
dinba

Karfe uku da rabi a Airport tayi masa, cikin aji yake sakkowa daga cikin jirgin yana gyara Zaman
agogon hannunsa, fuskar sa babu yabo babu fallasa,wayarsa yatura cikin aljihun wandon Jeans
dinsa,idan bakasan Shiba bazaka taba cewa yana jin hausa ba, yana gama sauka mutane
sukace salamu alaikum, Nan da Nan samari suka cika agaban sa, tafiya yake Amma selfie
wasu suke masa Ahaka,dole saida ya tsaya domin su gaisa, Amma Sai daga Kai yake yanaso
ya hango su Sa'eed domin yariga yasanar dasu zuwansa, mutane kuwa basu fasa yimasa
godia dakuma jinjina akan temakon dayake yiwa talakawa ba, daga masu cewa Allah yatemaki
Big Brother Sai masu yimusu video tare dashi, wata budurwa kyakykyawa yar Gayu ta Matso
tace "Yalla6ai zan iya samun saka hannun sanaiya?"
Murmushi yayi mata, dimple dinsa suka futo, batare da yayi mata magana ba ya karbi takardar
hannunta yasaka mata hannu, Bai bata iya takardar ba saida yahada mata da dala Dari biyu,
aikuwa Nan da Nan aka dauki ihu anata masa kirari, saida yayi kyautar kudade a Nan Airport
din sannan su Sa'ad suka hangoshi suka qaraso suka janye shi, mutane Sai addu'ah suke
masa shikam saide yayi murmushi yace "Amin"

Sa'eed ne ya karbi Brief case din hannunsa yace "Sannu da zuwa Babban Yaya"

Yace "Sannu Sa'eed, kaje da wannan kudin ka can zasu zuwa Naira Please"

Yace "to Babban Yaya angama"

Sa'ad yabude masa Bayan motar yashiga, yana shiga ya Lumshe idonsa tareda dafe Kansa
Su Sa'ad da Sa'eed suka shiga gaba, suka tada motar Sai hanyar gida, suna hanya Sa'ad dake
driving yajuyo ya Kalle shi yayi murmushi tareda fadin "sannu Babban Yaya, gidanka zamu
wuce ne kokuma gida?"

Batare daya bude lumsassun idanunsa ba yace "no, muwuce gida kawai, I want to see my
mother"

Babu Wanda yasake magana acikinsu, saida suka qarasa gida sannan Sa'eed yafice daga
motar yashiga wata motar yafita wajan canji,
Babban Yaya da Sa'ad Kuma suka tsaya gaisawa da ma'aikatan gidan.

Karfe hudu daidai, gaba dayansu yanmatan su uku suna falo kowacce Sanye cikin uniform din
islamiya Mai launin light blue, sungama shirya wa Ihsan ce kawai bata saka hijab ba

Intisar tadubi Waheeda "Waheeda Dan Allah ki Ara mata hijab din, inda taga Nata ai bazatace ki
Ara mata naki ba"

Yatsina fuska tayi tace "tabdi, ai saikuyi Kuma,dazu dazunnan tagama cemin marar Hankali
ta6a66iya, tayaya zata saka kayan ta6a66iya?, kunifa Bari kuji banida mutunci akan
kayanaaaaaa" taja naaa din sosai sakamakon tozali datayi tashi a bakin kofa yana qoqarin
shigo wa falon nasu,dayake itace take kallon bakin qofa, sukuma ita suke kallo suna roqarta

hijab,lokaci daya taji tanemi nutsuwar ta tarasa, taji kanta yasara tundaga qeyarta har zuwa
goshinta, fuskar Nan tasa atamke, yahade girar sama data qasa, shikkenan magana ta qare,
tasan yau takade har ganyenta, yaji labarin meta aikata

lokaci daya tanutsu, cikin tsananin ladabi ta kalli Intisar tace "kidauki hijab din nabaki duka,
kinga wannan dayan bashida guga, Bari nadaukeshi, kekuma saiki dauki gogaggen" ���

Cikin falon ya qaraso, qamshin turaren sa ne yasa yanbiyu juyawa cikin sauri,suna ganinsa
suka juya suka kalli Waheeda, Sai yanzu suka gane abinda yasa ta basu Aron hijab din.


Wajan sa suka nufa cikin ladabi sukace "Babban Yaya sannu da zuwa"

Hannunsa ya daga musu kawai,tareda zama acikin kujerun dasuka qawata falon nasu masu
launin dark green, cikin murna suka tafi Dakin Ummah suna qwala mata kira, suna zuwa suka
tarar tana toilet

Kallan Waheeda yayi wadda ta qame a wajan tun shigo war sa, yamiqe tsaye batare daya
kalleta ba yace "ke biyoni"

Gabanta ne yake wani irin bugawa dak! dak!, tafiya take tana binsa Amma jitake kamar batada
nauyi, jitake kamar iska zata Iya dagata sama,suna shiga Dakin nasa wani irin qamshi yadaki
hancinta,Dakin ya qawatu da manyan pictures dinsa, dayawa daga cikinsu duk da kayan ball
yayi photon, qamewa tayi daga Nan bakin qofa saboda bai bata iznin qarasowa tsakiyar Dakin
ba, takunkumin dayasa a hancinsa yafara cirewa sannan ya kalleta yace"Kneel Down here"

Cikin sassarfa taqaraso cikin Dakin tazube gwiwarta aqasa tareda daga hannayenta sama,
zama yayi agefen gadon yafara cire takalmin qafarsa, sannan ya tashi tsaye yacire rigar jikinsa,
farar fatar jikinsa ta bayyana, murdaddan Hannunsa yasake futowa sosai, duk abinda yake idon
Waheeda quriiii akansa, tunda taga yafara cire Kaya take qarewa surar jikinsa kallo, cikin ranta
tace tunda Naga yafara cire Kaya inaga yau zamu raba raini, hukuncina nayau yafi qarfin duka
saide dambe ���

Wayarsa ce tayi qara ya dauka tareda bude fridge din Dakin ya dauki ruwan gora, sannan ya
dawo ya zauna, cikin aji yayi sallama yana fadin "wake magana?"

Daga d'ayan bangaren akace "ranka yadade Big Brother, Shema'u ce, Shema Lady, yanzu na
bude data ne, sainaga Ana bada labari kazo, ashe ka shigo gari yau"

"no, qaryar Yan media ne kawai Shema, banzo ba"

Fari tayi da idanunta, taji shi ne kawai, Amma bata yarda ba, cikin salon yaudara tace "Big B.
Kenan, saika ganni kawai" qit takashe wayarta, wayar ya janye daga kunnansa ya kalli screen

din wayar, aiko saboda wayar data kashe masa yanzu koda ace tazo, bazai saurareta ba,
saboda ba'a kashe masa waya saide yakashe

Tashi yayi yafara kokarin janye dogon wando jeans din jikinsa, har boxer din yafara bayyana
yajuya ya kalli Waheeda yaga ta qwara masa ido tana Kallan sa ���, saiya fasa cirewa
yamiqe tsaye yana mata wani irin kallo, cikin sauri ta runtse idonta, saida yaga tarufe idonta
sannan ya qarasa cire jeans din, dagashi Sai gajeren wando yashige cikin toilet dinsa, tanajin
shigarsa tayi wata irin ajiyar zuciya sannan tasauke hannunta qasa, sau dayawa tana mamaki
sosai dangane da tsakanin ta da yayan Nata, kamar bashine yayanta me sonta ba, bazata taba
manta lokacin dazai dauketa ya goyata abayansa yana zagaye compound din gidan da'ita ba,
Amma tunda ta girma, komai ya sauya, yadena wasa da'ita, yahanasu kula Samari, yahanasu
saka mayafi, idan tayiwa Ummah complain tace ai saboda bataji ne shiyasa Shima ya sauya
mata, Kuma mema take aika tawa dazaibi ya tsaneta? ����對�Idan akan samari ne tayaya
za'a Hanasu kula samari Bayan sun kusa yin candy, idan suka gama makaranta babu saurayi
qarshan zancen ace za'a hadasu da samarin dangi, ayi musu auren zumunci, Kuma a wannan
zamanin waye zaizo auren cushe, auren zumunci?

Tanajin alamun bude kofar toilet din tayi sauri ta daga hannun ta sama


Be kalli inda takeba, Kai tsaye gaban mirror ya wuce yana gogo lallausar sumar Kansa ta
buzaye da wani Dan qaramin towel, saikuma wani dayake daure a qugunsa, nocking din Dakin
akayi, ya dakata da abinda yake ya kalli kofar tareda fadin "shigo"

Sa'eed ne yashigo da wata leda ahannunsa me d'aukeda kudade Yan dubu dubu, ya rissina
cikin ladabi yace "B�b�簽 Yaya an canzosu"

Turare yafara fesawa a jikinsa yace "kaje kaida Sa'ad ku rabasu dubu goma goma, a saka
kowacce dubu goma cikin Envelope, anjima idan mun fita masallaci Sai arabawa mabuqata"

Waheeda tanajin zancen dubu goma tayi sauri tabude idonta, kudin ta kalla tagansu dayawa
yanzu duk wannan mabuqata zai bawa?jitayi kamar taje ta qwace, Gata, gasu yanbiyu agida
suma ai mabuqata ne ���

Sa'eed ya kalli Waheeda yadaka mata harara sannan yafice daga Dakin yaja musu qofa,tunda
yaganta a Dakin yasan laifi tayi

Kallan Babban Yaya tayi taga ya Dauko wasu kayan zai saka, maimakon ta dauke idonta saita
qura masa ido, yana Kallan yanda take kare masa kallo tagefen idonsa, ya tabbatar Waheeda
raini takeji, tunda har zata Iya zuba masa ido har haka tana Kallan sa to yasan cewa Dan ance
namiji yasha bakinta ba za'ayi qarya ba, da niyya yajuyo ya fuskanceta sannan yafara kokarin
cire towel din guqunsa, idan wani abun take so tagani saita Gani da hujja���

Gaban Waheeda ya yanke yafadi, cikin sauri ta runtse idonta, cikin qasa qasa da murya yace
"Ashe ke qaramar 'yar'iska ce"

Ita Kuma tayi tunanin magana yamata, tunda Dama haka yake magana qasa-qasa kamar baiso,
gudun kartayi laifi yace yayi mata magana ta qyaleshi shiyasa ita Kuma ta daga murya tace
"Na'am Babban Yaya Dani kake?"

Dawowa yayi ya zauna agefen gadon, Bayan yagama shirya wa tsaf ya kalleta yace "badake
nakeba qaramar marar mutunci, kullum aka ganni a Nigeria ta dalilin ki ne nake zuwa, haka
kawai Ina Kan har kokina saikin aikata abinda zaisa dole sainazo qasar Nan, ke wacce irin
mahaukaciya cene? Kwata kwata bakida aji bakida Hankali irinna yanmata, anturaki makaranta
ashe soyaiya kike harda su kiss, nakafa doka a gidan Nan kina take wa yafi a qirga, saboda ga
sa'anki, to yau idan jikinki yagaya miki, ko ance ki kalli samari ma bazaki kallesu ba, dangane
da makaranta Kuma nasan matakin dazan dauka a kanki"

Yana kaiwa Nan ya tashi yafice daga Dakin, Waheeda tafashe da Kuka, cikin kuka tace
"Nashiga uku na, ashe yaji, shikkenan Aryan yacuceni, Allah ya'isana" haka taci gaba da kneel
down tana kuka, babu damar tatashi yazo yaga tatashi nanma taqara wani laifin, tun yanzu ma
jitake gwiwowinta harsun fara zafi

Yana futowa daga Dakin yatarar da Dady da Ummah a zaune, gaida su yayi cikin ladabi sannan
yakoma gefen Ummah ya zauna tareda Dora Kansa akan kafadarta yace "Ummah"

Murmushi tayi tace "Yayansu ya hanya, maza tashi muje Kaci abinci, gashi can na shirya ma"
babu musu ya tashi, saboda yayi missed girkin umman tasa, saboda aturai koda yaushe baida
abinci saina gwangwani, Daddy ya kallesu itada Yaron yace "idan kin gama bashi abincin
inason magana dashi"
Ummah tace "to Alhaji"

Ita da kanta ta dinga bashi abinci abaki, kowa ya kallesu yasan akwai tsantsar soyaiyar uwa a
tsakanin su, Sai shagwaba yake mata abu kadan yace Ummah, ita Kuma Sai lalla6ashi take

Saida ta tabbatar ya qoshi sannan suka koma falon, wajan Alhaji Umar, Babban Yaya ya Kalle
shi yace "Daddy nagama, meyafaru?"

Kallan sa yayi yace "menene zai faru banda maganar Aurenka?ai tunda Naga kazo yau nasan
kun daidai tane kaida ita Habiban ko? Yaya kukai da'ita?" ���

Sunkuyar da Kansa yayi yana Sosa girarsa, yama kasa dagowa ya kallesu

Ummah tayi ajiyar zuciya tace "wacce Habiba Kuma Alhaji? Yarinyar da harma munyi magana

da mahaifiyar ta awaya sunce sun janye batun auren, nabawa mahaifiyar yarinyar hakuri Amma
Sai tace ai habiba tace bazata iya zama da mutumin da bazai bata kulawa ba, to tunda naji
haka, kawai saina bata hakuri tunda bansan me suka Tattauna ita dashi a wayar ba, shi yasan
meya qulla "tana fadar haka takawar dakanta Gefe tana girgiza qafa
Alhaji Umar ya Kalleshi yace"Naufal"

Ahankali yace "Na'am Daddy"

"bakada lafiya ne irinta maza?"

Maganar tayi masa nauyi, saiya kasa dago Kansa ya kalli mahaifin nasa, Ahankali ya girgiza
Kansa yace "A a Daddy"

Daddy yace "okay, iskanci ne yake damunka kenan?"

Nanma yakasa bashi amsa ya girgiza Kansa yayi shiru

Daddy ya ajiye Jaridar hannun sa yace "kaiba 6oyaiyan mutum bane dakake tunanin mutane
bazasu saka Maka ido akan aure ba, muna zaune lafiya bazaka ja mana zagi agari ba, zamusa
qafar wando daya dakai tunda haka kaza6awa rayuwar ka, Kuma neman aure yanzu muka fara
nema Maka, idan ma wani abun daban kake fadawa yaran mutane har suke gudunka kaika
Jiyo, mude bazamu fasa nema Maka aure ba, har a wajan Allah muna neman fita haqqin ka ne
a matsayin mu na iyayenka akan kayi aure gudun aikata Zina, mutumin banza mutumin wofi,
katashi kabamu waje Kuma aure dolen dole Sai kayi "

Runste idonsa yayi, maganganun Daddy sun shige shi sosai, yaji zafin maganar Daddy sosai,
tayaya ne zai futo fili yafada musu yarinyar dayake so Bayan tarin matsaloli dakuma qalubalan
dazai fuskanta ? Tayaya? Ahankali ya tashi daga gabansu yanufi dakinsa, zuwa yanzu magrib
har tayi
Yana shiga dakinsa yaga Waheeda yanda yabarta, gaba daya cinyoyin ta sun sage, Saitayi
kamar zata fadi qasa, saita dawo baya taci gaba da abinda take, bacin ran dayake ciki ne yasa
yanemi belt yanufeta gadan gadan, tana ganin haka tatashi tsaye tanaja baya, kuka take wiwi
tana bashi hakuri Amma idonsa sun rufe saida ya lafta mata belt dinnan ajikinta, qara tasaki
tana fadin "Dan Allah kayi hakuri, wallahi tallahi nadena Babban Yaya, Dan Allah kayi hakuri"

Cikin 6acin rai yace "kifadamin waye wannan Yaron dayake neman lalata ki?, harkinashan
bakin wani saboda bakida mutunci ko? "

Belt din tariqe idanunta cikeda hawaye tace "Dan Allah kayi hakuri, wallahi bazan sake ba, idan
nasake Kamin komai ma nayarda"

Fizge belt dinsa yayi yasake zuba mata shi ajikinta, zafin dataji ne yasa batamasan lokacin data
tashi ta rungume Shiba,yana jin yanda Albarkatun qirjinta suke tsikarinsa saboda bata saka bra
ba, lokaci daya jijiyoyin jikinsa suka kar6i saqon, ���Amma tsananin 6acin ran dayake ciki
yasa baza'a gane hakan ba Fizgeta yayi daga jikinsa yasake Dora mata wani belt din, cikin kuka tace "Akofar fada yake,
gidan Alhaji Hamza"

Tsaki yasaki tareda wullar da belt din qasa yace "Stupid"

Ummah tana Jiyo kukan Waheeda tata6e baki tace kanku akeji kunfi kusa, Daddy ne yake
tambayar ta meta masa, anan ta fada masa komai ciki harda wayar Babban Yaya data daga
batare data saniba

Futowa yayi daga Dakin yabarta anan, su Ummah suna zaune har lokacin, suna ganinsa yafuto
fuskar sa a daure, yana shirin fita daga falon, anan yaci Karo da Yanbiyu harsun dawo daga
islamiya kasancewar anfara Kiran sallar magrib, yanda sukaga fuskar sa sunsan ransa a6ace
yake, cikin sauri suka bashi waje yafice daga falon
Suna qarasowa falo suka gaida Daddy, Shima ya tashi yayi shirin tafiya masallaci, Dakin
Babban Yaya aka bude ahankali, kamar me koyon tafiya hake take takawa, idanunta sun
kumbura sunyi jajir, Sai yarfe hannunta take, hawaye wani nabin Bayan wani, Ahaka tashige
cikin dakinsu babu Wanda yace da'ita uffan daga Ummah har Yan biyu, tana zuwa daki wani irin
zazza6i yafara kokarin rufeta, kawai zubewa tayi agadonsu taja Bargo tarufa.���

Da daddare duk suna zaune afalo gaba dayansu suna kallo, har wajan karfe takwas da rabi
Waheeda bata futo falo ba
Babban Yaya yana zaune yana danne danne a wayarsa, Sa'eed da Sa'ad Kuma suna gefen sa
suna bashi labarin 'yanmatan dasuka hadu dasu wasu yanbiyun suma, magana suke masa
Amma hankalinsa yanakan wayar dake hannun sa, ahankali yake amsa musu, su yanbiyu suna
zaune suma, suna Kallan film din da'akeyi, Ummah da Daddy suna can Gefe suna zance qasa
qasa, Daddy ya kalli Babban Yaya yasake yin qasa da murya yace "ke baki lura da abinda
nafada miki ba? Ki lura dashi sosai qarya yake mana bashida lafiya"�不

Itama Ummah Kallan sa tayi tace "Aina yarda Alhaji, kunyar fada mana kawai yake, Amma duba
fa yanda 'yan' uwan suke bashi labarin yanmatan su Amma yayi mursisi, maza dason zancen
yanmata Amma shi kaduba kagani fa suna masa magana kamar sunayi da dutsi"

Daddy ya girgiza Kansa yace "dole zan dauki mataki hajiya"

Shikuwa Babban Yaya baisan sunayi Bama ���Kallan intisar yayi yace "ke tashi ki kira
wannan yarinyar tazo tayi kallo"

Intisar tasan da Waheeda yake, ita kadai ce bata futo falo ba, cikin sauri ta nufi dakinsu, tana

shiga tahau kan gadon ta yaye bargon da Waheeda tarufa, bude idon ta tayi ta kalleta, duk
yanda Waheeda take gane yanbiyu, take banbancesu dukda tsananin kamar dasuke, yau kasa
ganesu tayi,�不 intisar ce tazo kiranta Amma Waheeda tana qare mata kallo cikin wahala tace
"Ihsan Dan Allah ki temaka ki taro ruwan zafi a toilet kizo ki gasa min cinyoyina, jikina yayi
tsanani bazan iya tashi ba"

Dariya ta kama Intisar, saita danne gudun karsuzo suna fada, tace "Babban Yaya ne yace kifuto
kiyi kallo kowa yana falo banda k....." kafin ta qarasa magana taga Waheeda ta duro daga kan
gadon ���
Kokula sauran zancen batayi ba tafice daga Dakin, tana zuwa falon babu Wanda ta nufa Sai
shi, har gefen qafarsa ta zauna, hawaye yazubo daga idanunta, a Hankali tace" Babban Yaya
Dan Allah kayi hakuri kaji.... "

Babu Wanda yasan metake fada masa, saboda ahankali tayi masa maganar, Shikuwa banza
yayi yarabu da'ita, hawayen tasake gogewa tace"kaji" memakon yabata amsa saiya tashi daga
falon yashige dakinsa, haka ta zauna a wajan tana Kallan dole, saida takusa minti talatin tana
kallo Amma bata fahimtar komai, Dan haka tatashi Takoma dakinsu tafara gabatar da sallah

Karfe bakwai daidai afalo tayi masa,yayi kyau sosai cikin manyan Kaya, yanda yaqara cika da
kamala zakace yanada aure, agogon hannun sa ya kalla yadubi Ummah yace "kice musu Idan
sun gama Ina waje Ummah"

Ummah tayi dakin yaran tace "kuyi sauri kufita yayanku fa kuyake jira"

Yanbiyu ne suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login