Showing 33001 words to 36000 words out of 82824 words

Chapter 12 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf


Inti tace "to yanzu ke menene naki aciki? Hanawa zakiyi? Mema za'ai da wannan Ummin, ni
wallahi Bana sonta, kullum kaganta tana magana da maza"


Ihsan tace "wallahi kuwa, inajin su Daddy basu Sani bane shiyasa, nifa shiyasa banyi murna ba
danaji ance itace, Amma Waheeda uwar rawar Kai harda tafiya wajan sa da gudu, dama yasani
yamiki shegen duka"

Waheeda tayi shiru tana tunani, tana so tace musu yafada mata yarinyar dayake so to Amma
Kuma data tuna yace mata sirri, Saitayi shiru, tayi ajiyar zuciya tace "nikam Ina sonta, tunda
Babban Yaya zata aura, mutumin dayake taimako na aduk halin Dana kasance tayaya zanqi
matarsa?"
Ihsan tace "to Allah yabada sa'a Waheeda, ke kikaga Zaki iya"

Daga Nan sukai shiru kowa da abinda yake saqawa Aransa


Ita Waheeda tana tunanin Babban Yaya, duk yanda zaiyi mata fad'a tana shiga damuwa muddin
ta ganshi acikin damuwa, saboda Shima baya barinta acikin matsala, ta damu da damuwar sa
sosai, batasan meyasa ba, wani lokacin zai mata hukunci akan laifin da tayi, gashi de shine
ya6ata mata rai ta hanyar yimata hukunci, Amma Hankalinta baya kwanciya Sai ta bashi hakura
taga ya haqura tukunna, gashi yanzu yana wani Hali saboda auran Ummi, batasan ta wanne
Hali zata taimaka masa ba,zuciyarta tabata shawara akan tatayashi da addu'ah, haka ta dauki
shawarar zuciyarta

Haka Babban Yaya ya wuni ad'aki yaqi futowa, Ummah Kota Kansa batabi ba, saboda tasan
fishin nasa akan aure ne, Kuma aure Kam babu fashi


Washe gari yafuto daga d'akin nasa, yana Sanye da kayan ball, suma 'yanbiyu maza shine
ajikinsu, zama sukai afalo kowa yana kokarin saka safa, yanmatan ne suka futo daga d'akinsu
suma de kayan Ball d'inne ajikinsu, Amma nasu wandon dogo ne, rigar ma me dogon hannu ce,
sa6anin na mazan dayake qanana, fita sukai zuwa filinsu na qwallo dayake gidan, shikuma
Babban Yaya yana falon yana saka takalmin sa, gaba d'aya iyayen nasu suna compound suna
shan shayi, da hajiya Anty da Ummah dakuma Daddy da Uncle Usman, akan idonsu yaran
suka futo zasu fara buga Ball din, Amma babu Babban Yaya, a lokacin harya gama saka
kambos dinsa, yana zaune ne yana amsa wayar Abokinsa dayake tambayar sa yaushe zai
dawo, yana gama waya da abokin nasa wata wayar tashigo, yayi mamaki da'aka kirashi ta
wannan number, saboda ba kowane yasan wannan number tashi ba, dauka yayi tareda sallama
daga dayan bangaren akace "Yayanmu Ina wuni? Sunana Didat, qanwarka ce tabani number
ka,Ina neman alfarma ne awajanka, maganar Gaskiya Ina sonta, idan kabani Dama inaso na
nemi aurenta"

Babban Yaya ya Sosa girarsa guda d'aya yace "Sister na kuma?"


Daga d'ayan bangaren Didat yace "eh Yayanmu, na gansu ne abakin get d'in school d'insu,
akwai mutum biyu masu kama d'aya, toba suba, d'ayar nake nufi"

Babban Yaya yana jin haka ya Lumshe Idonsa, cikin ransa yace "Waheeda"

Dafarko har yayi niyyar dakatar da Yaron, but Saiyayi tunani tayaya rayuwa zataci gaba da
tafiya Ahaka? Yaushe ne zai daina hanata huld'a da samari? Duk Daren dad'ewa dole zatayi
aure, wazai fara fuskanta da maganar datake damunsa?qalubalen dazai fuskanta akan haka ba
d'an qarami bane, Kuma itama da alama sonsa take, tunda gashinan ta yarda harta amince a
tambayeshi? Cikin Yan seconds yayi wannan tunanin, wani irin huci yayi yafitar da iska me zafi
daga bakinsa sannan yace "Babu damuwa zaka iya zuwa"

daga Nan yakashe wayar tashi yafita zuwa compound da d'an gudunsa irin na 'Yan qwallo,
acan Gefe ya hangi su Ummah sun baje suna shan Shayi, yana zuwa kuwa suka fara buga ball
din mazan da matan, kusan mintuna talatin suka d'auka sunayi Amma Babban Yaya baici ko
sau d'aya ba, mamaki ya kama iyayen nasu dasuke Kallan abinda yake faruwa, shida a qasar
waje ma suke alfahri dashi akan iya ball, tayaya wad'annan yaran zasu dinga cinsa? Ada idan
sunayin ball d'in kowa saduda yake, saboda sunsan comfirm 'Yan team din Babban Yaya sune
da nasara, Amma yau Sa'ad da Babban Yaya, da intisar Sai sunci su Waheeda da Ihsan da
Sa'eed suke yi.

Sunkuyawa yayi yariqe gwiwarsu, damuwa tataru tamasa yawa, idan ya tuna da maganar
Ummi, yatuna da wayar da gayen Nan yamasa akan Waheeda, saiyaji gabansa yafad'i, daga
qarshe ma kawai juyawa yayi zuwa falon su, intisar datake jin haushi anata cinsu, tayi sauri ta
hura Whistle tace "wasa yatashi" ��� Akan idanun iyayen Babban Yaya ya wuce falo yabar yan'uwan nasa, Waheeda tariqe hips
d'inta cikin damuwa tana Kallan sa, daga Nan tabi bayansa, saide tana zuwa 'kofar 'Dakin nasa
tayi nocking din duniya yaqi bude mata, dole Sai haqura tayi, ta wuce dakinsu.


Washe gari da yamma Ummah tana zaune ad'akinta tana tunani akan rayuwar Naufal, damuwar
dayake ciki haqiqa itama tana ciki, yaqi yafuto fili yafad'a mata me yake tsoro dangane da aure
a matsayin ta na mahaifiyar sa, duk sa'anninsa sun dad'e da aure, Sai yaushe ne shi zaiyi? Tun
yanda ta ganshi jiya cikin damuwa har yanzu Hankalinta yaqi kwanciya, duk yanda yake dason
Ball yamaqi yakoma bare tace ball din zata d'ebe masa kewa, Waheeda ce tashigo Dakin tana
Sanye da dogon hijabi tace "Ummah zanje bakin get nayi baqo"

Ummah ta kalleta tace "Baqo kuma? Daga Ina kenan?"

Murmushi tayi tace "shekaran jiya nahad'u dashi abakin get din school dinmu, sunyi waya da
Babban Yaya ma, shine yace yazo"

Ummah tace "kin tabbatar abinda kika fad'amin gaskiya ne Waheeda yayanku yasan da
maganar sa?"

"Allah Ummah yasani"

"to shikkenan kije, Amma karki dade" cewar Ummah

Waheeda tafuto daga d'akin, ta qarasa wajan Didat, yana Sanye cikin shadda Light blue, hular
daya saka ta dace da kalar kayan nasa, qarasa wa tayi tareda sallama, ta ajiye masa ruwan
roba guda biyu da Lemo guda daya, baba maigadi yataso da sauri yasake gaida shi, sannan
suka qarasa wajan wasu kujeru masu kyau Wanda aka qawata wajan da yar qaramar rumfa
domin shan iska, Didat ya kalli Waheeda Bayan ya zauna yace "Ranki yadade gimbiya"

Waheeda tace "mudade tare"

Murmushi yayi yace "bakice nayi kyau ba, Bayan duka wankan naki ne, kinsan kafin nafuto
daga gida saida nafadama mamana wajanki zanzo, tace nayi kyau sannan tana miqa saqon
gaisuwar ta zuwa gareki"

Tace "nagode sosai, Ina amsawa, idan kakoma kace ina gaisheta"

"zataji insha Allah,ni sunana Didat"

Tace "nikuma Waheeda"

Kallan ta yayi yace "sunanki yanada dadi Waheeda, Ina fatan ace kin zamo wani bangaren na
cikin rayuwa ta idan kin amince"

Tace "kamarya?"

"Ina nufin kibani Dama Nima adama Dani acikin Jerin masoyanki, Amma maganar gaskiya itace
inada kishi sosai akan abinda nakeso, shiyasa ma nakawo miki wannan kyautar"

Yafadi haka yana bata wata leda, saida ta karba Sannan yace "hijabi ne da niqab, dakuma safa,
gaskiya Ina kishinki Waheeda, aurenki nakeson yi bawai soyaiya ce ta kawo ni wajanki ba,
banaso muyi shekara daya batare da munyi aure ba"

Murmushi Waheeda tayi tace "gaskiya ne, nayarda kanada kishi, tunda gashi kyauta ta farko
daka fara min itace da hijab da safa da niqab, Amma Kuma duk kishinka baka Kai Babban Yaya
ba" �����領����儭���喫��?

Cikin mamaki ya gyara zama sannan ya kalleta yace "waye Kuma Babban Yaya?"

Murmushi Tayi tace "nasan cewa kasan Big Brother ko?"

Yace "sosai ma kuwa, waye zaice baisan Shiba? Aini shine 'Dan qwallon dayake mugun
birgeni"

Tace "to shi nake nufi, ai shine Babban Yayanmu"


Didat yace "ok, Allah sarki, haba shiyasa Naga gidanku unguwa guda gashinan aljannar duniya"
yafad'i hakan cikin sigar tsokana

Waheeda tace "Shima yanada kishi, yafi son muyi karatu karmu kula samari"

Yace "ya kyauta min, inda yabarku Aida Nima bazan sameki ba, nasan da tuni wani alhajin ya
dauke ki"

Murmushi tayi tace "nagode, zan koma gida, Ummah tace karna dad'e"

Shima tashi yayi tsaye, ya ajiye mata rafar kudi Yan hamsin hamsin guda daya, aqalla zasu Kai
dubu hamsin, daqyar da Fama Waheeda ta d'auki kudin, sannan suka rabu akan zai sake
dawowa gobe ko jibi, tanada son kudi Amma Bana hannun mutane ba, saide na Babban Yaya,

tasan yayanta ne bazai taba goranta mata a kan hakaba, abinda ta lura dashi shine, shi mutum
ne me kishi kamar yanda yafad'a, sannan daga Gani bashida matsala ko kad'an


Da daddare gaba d'ayansu suna zaune banda Daddy, Ummah ta kalli Babban Yaya dake danna
waya yana qara Bawa Corch dinsu hakuri akan dad'ewar da yayi,Kallan Ummah yayi yace
"Ummah nanda kwana hudu yaran Nan zasu tafi Umarah insha Allah, gaba d'ayansu"

Cikin farinciki Ummah tace "Alhamdulillah, Allah yayima Albarka, to Allah yakaimu lokacin, Kai
banda Kai ne?"

Girgiza mata Kai yayi sannan yace "su kad'ai"

Ummah tace "To madallah, Allah yaqara hore Maka,"

Murna suka hauyi gaba d'ayansu, Nan take suka fara zuba masa ruwan godia, Waheeda kuwa
jitake kamar taje ta rungume shi Dan murna, Amma babu Dama yanda taga ya d'aure fuskar
Nan tana zuwa kusa dashi tsaf zai maketa ���

Ummah ta sake Kallan sa cikin farinciki sannan tace"Yauwa yayansu ga wannan kud'in,
saurayin Waheeda ne yabata dazu"

Kallan kudin yayi Asheqe sannan yace "ok"

Ummah tace "bangane Okay ba, bazaka kar6a kasa mata Albarka ba?"

Yatsina fuska yayi yace "Ummah dubu hamsin d'in kamar Wanda yayi kyautar bajinta?" �對�

Mamaki yakama Ummah, sukuwa su Sa'eed dariya suka saka, Sa'ad yace "haba Babban Yaya,
dubu hamsin fa, kodan Kai mekud'i ne shiyasa, wallahi Ummi tahuta"���

Wani irin banzan kallo yamasa, lokaci d'aya yashiga taitayinsa

Kafin su qara cewa komai wata yarinya 'yar kimanin shakara 11 tashigo da sallama hannunta
d'aukeda wani flask na abinci, ta tsugunna ta gaida su Ummah sannan tace "Wai gashi inji Anty
Ummi abawa Yaya Naufal" ���

Haushi yakama Babban Yaya, ya kalli yarinyar yayi tsaki a ransa, ko'ina ya zama yayanta harda
wani Yaya Naufal,?

Ummah ta saki ranta tace "Allah sarki, to kice ya gode, zai kawo mata kular da Kansa kinji,
Allah yamiki Albarka,"

tad'auko fos dinta dake Gefe tabawa yarinyar dubu biyar, yarinyar cikin murna ta karba tafice
daga falon

Waheeda ce tataso tabud'e flask din taga abinda yake ciki, sannan tayi murmushi ta kalli
Babban Yaya tace
"Babban Yaya farfe...."

kafin ta qarasa cewa farfesu ne, yatashi cikin fishi, yabar falon gaba d'aya, Ihsan da intisar suka
zabgawa Waheeda harara suma sukai d'aki, Waheeda ta kalli Ummah cikin shagwa6a kamar
zatayi kuka, Ummah ta janyo ta jikinta tace"rabu dasu, idan sun gama fishin zasu sakko"


Washe gari da safe, suna break fast, wayar Daddy tayi qara, yayi mamakin me Kiran nasa,
domin kuwa ba kasafai suke waya da minister of Education ba, d'auka yayi Bayan sun gaisa,
Daga d'ayan bangaren minister Abdullahi Wakili yace "Alhaji Umar Arabo"

Daddy yayi murmushi yace "ranka yadad'e, kwana dayawa ba'a jinka"

Minister yace "wallahi kasan koda yaushe muna ta Fama da jama'ah, yanzu ma yarona ne
Huzaifa yasaka ni agaba lalle lalle saina kiraka"

Daddy yace "a a ikon Allah, Huzaifa ya dawo qasar ne?"

Minister yace "wallahi ya dawo, cikin ikon Allah ya kammala karatun sa lafiya ya dawo, yazo ya
sameni ne akan maganar 'yar wajanka, last week yaje 'Dauko sisters d'insa daga school sunyi
party na candy, anan yaga yar wajanka Waheeda yace yanaso, shine da yayi bincike yagano
'yarka ce, Kuma kasan akwai sanaiya a tsakani, shine yace ayi masa tambaya aji ko an yiwa
wani alqawari? "

Daddy yace"A a babu alqawarin kowa, Allah ya tabbatar musu da alkhairi "

Daga d'ayan bangaren minister yayi godia tareda kashe wayar

Babban Yaya yanajin wayar da Daddy yake jikinsa yabashi akan Waheeda ake magana, Bai
nuna komai akan fuskar saba, lafiya kalau suka gama cin abincin sannan ya dauki key din mota
yafice daga gidan



Da yamma Didat yazo tareda abokinsa Mukhtar, yau wankan qananun Kaya yayi, ba qaramin
kyau yayi ba, suna cikin zance da Waheeda yace "Gimbiya inaso kije gida ki fad'awa Ummah
zamuje shopping idan ta amince"

Babu musu Waheeda ta wuce gida ta fad'a wa Ummah abinda Didat yace, Ummah tace "to
karki tafi ke kad'ai, kuje keda yan'uwan ki"

'Dakinsu ta wuce, ta tarar Ihsan na wanka, Sai intisar dake karatu, tare suka futo da intisar basu
jira Ihsan ba, suna zuwa kuwa Didat yace "lalle babbar Yaya, yanzu ashe Kuna ciki kun 6uya,
ko sau d'aya bantaba ganinku ba"

Intisar tace "Wallahi muna Nan, abubuwa ne sukai yawa, yakake"

"Alhamdulillah, Ina lafiya kamar yanda gimbiya Waheeda take, dafatan de tare dake zamuje
shopping din?"

Intisar tace "babu damuwa muje"



Tsayawa sukai suna jira yabud'e musu kamar yanda Babban Yaya yake musu, shikuma harya
shiga motar, saida yajuya ya gansu a inda suke sannan yayi murmushi yazo ya bud'ewa
Waheeda gaba, intisar Kuma suka zauna Abaya tareda abokinsa, suna hanya abokin Sai Jan
intisar yake da zance, tana amsa masa kad'an kad'an, a wajan shopping d'inma Didat Kam
kawai binta yake yana aikin kallon ta kamar wani sakarai, itace me za6ar komai, saida yakashe
mata kud'i me yawa sannan suka Juyo gida, tun a hanya yaga tana amsa masa daqyar, Sai
yatsina fuska take, suna qarasa wa gida kuwa intisar tayi ciki, ita Kuma Waheeda ta tsaya suna
sake tattaunawa, Kallan ta yayi yace "Meyake damunki ne? Naga kamar bakya jin dadi"

Yatsina fuska tayi tace "wallahi jinake zazza6i yana son kamani"

Cikin rud'ewa Didat yace "Subhanallah, Amma shine kikai shiru? Meyasa baki fad'amin ba muje
Asbiti?"

Tace "Babu damuwa, zansha pracitamol agida"

Didat yace "no, ga Mukhtar Nan yayi miki injection mana, akwai saura acikin motata Ina siya
Dama saboda 6acin rana, idan kikaje gida saiki kwanta kihuta, Shima doctor ne"

Cikin damuwa Waheeda tace "no, karka damu wallahi"

Didat yace "a a, tsaya yayi miki please"

Bud'e motar yayi, ya 'Dauko allurar yabawa Mukhtar, Mukhtar ya kar6a yafasa ruwan allurar, ya
kalli Didat yace "Ina sirinji?"

Didat yace "aikuwa na manta wallahi babu, but ga Wanda akamin allura dashi ban yarda shi ba,

kayi mata dashi kawai"�����領����儭?

Kallan Waheeda Mukhtar yayi yace "babu damuwa ayi miki gimbiya?"

Tace "babu damuwa"

Kar6ar sirinjin yayi yazuqe ruwan allurar, sannan yayi mata a hannunta, basu qara ko minti biyar
ba, sukai sallama, tajuya zata tafi gida, adede lokacin Babban Yaya ya dawo gidan, fuskarsa
ad'aure take babu wasa, ya gansu Amma saiya nuna baima gansu ba, Didat da baisan da shigo
war Babban Yaya ba, ya qwalawa Waheeda kira, tana juyowa yayi kissing hannun sa, sannan
yahura mata tareda kashe mata ido, yashige cikin motarsa

Babban Yaya yana Kallan su, yakashe motarsa Bayan ya ajiye ta a parking space yafuto, adede
kofar shiga falon suka had'u da juna, cikin ladabi tace "Sannu da zuwa Babban Yaya"

Cikin 6acin rai yace "aikece za'ayi wa sannu,mahaukaciyar banza mahaukaciyar wofi, Kin tsaya
yana miki hauka Amma ko ajikinki, kwata kwata bakya kishin kanki, idan kikai wasa naqara
ganin qafar Yaron Nan a gidan Nan saina kakkarya qasusuwanki ...."

"Subhanallahi .... Naufal?"
Cewar Hajiya Anty da shigowarta kenan taga yana zazzaga wa Waheeda masifa

Kallan ta yayi, yayi qasa da Kansa, idanun Nan nasa sunyi jajir tsabar 6acin rai, Sai huci yake
kamar zai Fashe, ita kanta hajiya Anty ta tsorata da yana yinsa, ta kalli Waheeda datake share
hawaye tace "Ke wuce ciki"

Kallan sa tayi tace "Kayi hakuri" sannan ta wuce cikin falon nasu

Hajiya Anty ta kalli Babban Yaya tace "yanzu bakaji kunya ba? Kagama yimata fad'a Amma
daga qarshe haquri take baka ko kallo bata isheka ba? Hakan dakayi daidai ne kenan?"

Yace "Anty kissing dinta fa yayi" yayi maganar kamar zai Fashe da Kuka

Hajiya Anty tace "to naji tayi laifi wannan fad'an dakake mata shine zaisa ta nutsu? Qanwarka
cefa, jininka ce tayaya bazakaja yarinya a jikinka ba zakadinga mata fada irin haka,?to tun tana
jin tsoron ka, watarana zata daina, kaja Qanwarka a jikinka kaji nafada ma, fad'a ko duka basa
shiryar da yaro"
Qwalla ce take son futowa daga idanunsa yana dannewa, idan yatuna yanda Didat yake huro
mata kiss, jiyake kamar yayi ihu, cikin 6acin rai yace "Anty niba qanwata bace, kidena cewa
Qanwata"

Hajiya Anty tayi sakare tana Kallan sa, a fili tace "ikon Allah, to ba Qanwarka bace, karka jata a

jikinka, gata Nan ka kashe ta"

Daga haka tajuya cikin gida tabarshi a wajan, Shima shigewa yayi ransa a6ace


Tunda yashigo 'Dakin yakasa sukuni, tunani yayi masa yawa, daga qarshe ma tashi yayi yafara
had'a kayansa, gobe da safe zai koma England bakin aikinsa, kwata kwata bayajin zai iya zama
yana ganinta tana mu'amula da wani namijin bashi ba


Cikin qanqanin lokaci yagama had'a komai,kawai jiran wayewar gari yake



Kamar wasa Waheeda tana kwanciya bacci ya dauketa marar dadi, sakamakon abinda yafaru
tsakanin ta da Babban Yaya , haka Shima anasa bangaren, baiji dadin baccin ba, har yanzu
wannan kiss d'in ya tsaya masa aqahon zuciyar sa,washe gari kalau tatashi babu wani alamun
zazza6i atare da'ita, 'yanbiyu basa 'Dakin Sai ita kad'ai take juyinta akan gadon, doguwar Riga
ce ajikinta ta bacci Amma me kauri, bata nuna shape dinta ba kwata kwata, saide kana iya
ganin tsayayyun breast dinta yanda suka tsaya a tsaye cak tacikin rigar, brush taje tayi tadawo
'Dakin nasu taga Maya na kiranta awaya, d'auka tayi tace "uwar 'Yan Fassara ya akayi?"

Maya tace "ke dalla malama yau babu Fassara,Wai baqi mukai daga Abuja, shine wani daga
cikin su yace yanaso na, ya tambayi mama yaushe zan gama karatu tace masa nanda wata
shida, nikuma gaskiya Waheeda banason aure yanzu, nafison nayi karatu me zurfi, sannan baki
ganshi ba Babba nefa, yakai Babban Yaya girma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login