Showing 21001 words to 24000 words out of 82824 words

Chapter 8 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf

Advertisement

yanmata, zan so Naga mijinki Waheeda"

"Zaki Gani Maya, kijira munayin candy Sai aure nikam, banaso naci gaba da karatu, nafiso nayi
aure na indinga kula da mijina, in shaga6ashi inyi masa abinda yakeso, kinga lokacin saina tafi
makaranta, tun yanzu ma mata suna nemana, idan natafi University wakike tunanin zai nemeni?
"
Kai tsaye Maya tace"Maza, Amma Kuma kinsan de Babban Yaya baya so ki dinga kula samari
ko? Tayaya Zaki samu mijin? Bayan munkusa gama makaranta?"

" can ta matse muku keda Babban yayan, nikam daga Candy Sai aure insha Allah "

Maya tace"gaskiya yarinyar Nan wuyanki ya'isa yanka, nikam yanzu Ina Bayan Babban Yaya,
tunda yabani kudin makaranta bazan taba mantawa da alkhairinsa agareni ba, Dan haka dole
indinga tuna miki dokarsa a kanki "

Kafin Waheeda tace wani abu anfara yaiyafi, neman wajan 6uya suke Amma sun Rasa, abun
Hawa suka fara tarewa Amma kowanne baya tsaya wa, ruwa yaqara karfi Nan da Nan mutane
suka fara gudu musanman maza, ruwa yayiwa su Waheeda duka saboda babu mafaka, suna
cikin wannan halin Babban Yaya yaqara so, yana zuwa yafuto daga cikin motar yanufesu,
Waheeda taga ya sauya wannan kayan daya saka na dazu, murmushi tayi, cikin shagwa6a tace
"Babban Yaya shine kaqi zuwa da wuri gashinan ruwa yamana duka nida Maya"

Bece da'ita komai ba, kawai gaban motar yabude mata, tareda fadin "I'm sorry, shiga"

Maya tana tsaye tana Kallan su, lalle Babban Yaya yana son Waheeda, wanne Yaya ne zai
budewa qanwar sa mota saikace wata budurwar sa? Anya kuwa yayanta ne?

Saida Waheeda tashiga sannan yarufe, itama Maya tayi sauri tabude gidan baya tashiga,
zagayawa yayi yashiga motar, yajuyo yana fuskantar Waheeda, cikin sigar lallashi yace "Sorry"

Bakinta ta turo gaba taqi magana, yasaka hannu yakamo kyakykyawar fuskarta yace "kinji"


Murmushi tasaki, dimple dinta suka futo, tace "shikkenan, Kuma alqawarin dazu, bazan fadawa
kowa ba"

Murmushi yayi Shima yace "good girl"

Maya tayi gyaran murya, Dan taga alamun sun manta tana motar ���
Tace "Babban Yaya Ina wuni"

Firgigit ya dawo haiyacinsa, shaf ya manta tana cikin motar, a taqaice yace "Lafiya"

Sannan yaja motar suka tafi, suna hanya Waheeda Sai zuba masa surutu take, Amma amsar
dayake bata batada yawa, har suka qaraso gidansu Maya, suka ajiye ta sannan suka dauki
hanyar gida, Bai wuce dasu gida ba saida yashiga tawani shago yasai mata waya qirar iPhone,
ya ajiye agaban motar sannan yaja motar suka qarasa gida
Yana tsaida motar a compound din gidan nasu, Waheeda tafara kokarin fita, tana kama handle
din kofar taji taqi buduwa, tajuyo tace "Babban Yaya bude"

Wayar daya siyo ya Dauko ya 'Dora mata akan cinyarta yace "Gashinan, nasan inda kinada
waya Zaki kirani kicemin kun tashi, bazan Bari ruwa yamiki duka ba kamar yau"

Waheeda tafara kokarin budewa, tana Ganin wayar tasaki wani ihun murna ta rungume shi,
yana jin yanda tudun qirjinta yake mintsininsa cikin ransa yace "yasalammmm!"

Daurewa kawai yayi, ahankali yazareta daga jikinsa yace "bansan yaushe zakiyi Hankali ba,
kina ta6ani any how kamar wani muharraminki"

Kwata kwata Waheeda batama kalli inda yakeba bare tayi nazari akan kalamansa, cikin murna
tace "Toda menene inba Shiba? Babban Yaya, nagode, Allah yasa kadinga cin ball a koda
yaushe, Allah yaqara girma"

Saida ya hadiye wani irin yawu, sannan yace "Amin" yabude mata motar tafita dagudu tanaso ta
nunawa yanbiyu itama tayi waya


Da daddare suna kallo gaba dayansu, Waheeda tana saka number Yan gidan tana saving dinsu
cikin sabuwar wayarta, yanbiyu suna nuna mata wasu abubuwan da bata Sani ba, su Sa'ad da
Sa'eed tareda Babban Yaya Sai labarin qwallo suke, Babban Yaya anta6o masa inda yakeso,
wato zancen qwallo, Sai hira suke sunata dariya kamar bashi ba, Ummah ta Kalle shi tace
"Yayansu Yaya kukai kaida Nadiya ne?"

Kallan ta yayi yace "Ummah naje tace bata sona"

Gaba dayansu Yan falon suka Juyo suna Kallan sa, wacce yarinya ce zatace bata son
yayansu?

Ummah tace "kamarya?"

Juyowa yayi yasake Kallan Ummah yace "Ummah ki tambayeta kiji, naje nace mata Ina sonta,
kifada mata nine naje da adedeta saboda motata tasamu matsala a hanya, Kuma tace koda na
aureta bazata iya kula dakeba Ummah,sannan tare naganta dawani Gaye suna zance, kinga

kenan itama tanada Wanda takeso,to menene amfanin auren ta? Ummah duk wadda bazata iya
kulawa da mahaifiyata ba, bazan iya auren taba "

(Kai Babban Yaya irin wannan batu haka �不���)


Ummah tadauki wayarta takira wayar maman Nadiya, Bayan sun gaisa maman Nadiya tace
" Hajiya Baqon namu Kuma baizo ba, muna ta jira angama shirya masa abin motsa baki Amma
Nadiya tacemin baizo ba Kuma bai kira wayarta ba"

Ummah tace" Yanzu nake tambayar sa yacemin yazo tace masa bata sonsa, Wai tace bazata
iya kula daniba koda ya aure ta"

Maman Nadiya yace "Anya hajiya itace kuwa? Amma Bari inkirata"

Ummah tanaji maman Nadiya ta daga murya takira Nadiya, nadiya tana zuwa maman ta tace
"Big Brother yazo kince masa bakya sonsa, kince kokin aure shi bazaki kula da umman saba,
anyi haka ko ba'ayi ba?"

Nadiya tanajin wannan bayani tatuna mutumin dayazo wajan ta dazu a adedeta, ta d'ora
hannunta aka �����領����儭�tafashe da Kuka tace "wallahi mama bansan shibane,
yaudara ta yayi, Allah Ina sonsa" cikin kuka tanufi dakinta da gudu

Maman Nadiya ta sassauta murya tacewa Ummah "Hajiya komai fa ya lalace, zamuyi magana
daga baya" daga Nan ta kashe wayar


Babban Yaya ya kalli Ummah yace "Ummah kinji da kunnanki ai naje ko?"

Cikin bacin rai Ummah tafara girgiza kafarta tace "naji Naufal, ai banyi tunanin yarinyar zatace
bazata kula daniba, bansan haka tarbiyar ta takeba"

Wani farin ciki ne ya mamaye shi, yaga Ummah ta yarda da komai, to tun kafin waccan Nadiyar
tazo ta musu bayanin komai ta fada musu 6oye kamarsa yayi, Gara yagudu yabar qasar���

Cikin ladabi yace "Ummah, muna shirye-shiryen fara World cup very soon, zan fara training Jibi,
Insha Allah gobe da Asubar fari zan wuce" ������


Ummah tace "Allah yakaimu Son"

Firar da ba'a qarasa dashi ba kenan, ya wuce dakinsa ransa fess������

Sonake agano min iyayen wadannan taurarin guda biyu NAUFAL DA WAHEEDA





To Babban Yaya yatsira wannan lokacin, kome Waheeda zata aikata ya dawo dashi qasar?
















Amnah El Yaqoub ����?
1/28/22, 20:49 - Ummi Tandama���: BABBAN YAYA

Writing By Amnah El Yaqoub


Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/


11&12


Suna tashi da safe sukahau shirin school,awajan break fast Waheeda taga babu Babban Yaya,
anan taji cewa yatafi tun asuba kamar yanda yafada jiya da daddare

Bataci wani abincin kirki ba, Sai tea me kauri, ta kalli 'yanbiyu taga Sai lokacin zasu fara cin
abincin, tatashi tayi d'akinsu da gudu

Kowa yabita da kallo Amma babu Wanda ya tanka mata, wayarta tad'auko ta kunna ta sannan
takira Babban Yaya, a lokacin suna cikin jirgi har anfara sanarwa a kashe waya jirgi zai tashi,
yayi mamakin ganin number ta tana kira, already yanada number tun jiya yayi saving d'inta a
wayarsa Dauka yayi tareda cewa "Lafiya ko laifin kika sake yi?"

Dariya tayi tace "Babban Yaya,Aina Dena laifi yanzu, nayi Hankali Nima"

Yace "Allah yasa, kinga de wannan Karon munrabu lafiya dake, banaso wani abu yasake
faruwa kisa in dawo qasar Nan kwana kusa, kinga yanda nasamu narabu da rigimar su Ummah
akan yarinyar Nan Nadiya, to banaso kisake aikata wani abun dazaisa nadawo Nigeria ta dalilin
ki "
Bakinta ta turo gaba kamar yana Kallan ta, sannan cikin shagwa6a tace" Babban Yaya to ai
wannan dinma ba nice da laifi ba, Basaida na nuna ma abinda akamin ba?"

Runtse idonsa yayi, Waheeda zata kashe shi, yadade da mantawa Amma saida tasa ya hango
cikakkun breast dinta a'idon zuciyar sa, cikin sauri yace"naji,naji, menene Kuma saikin tuna
min?" ���

Tace "to Babban Yaya kayi hakuri, yaushe zaka dawo?"

Kai tsaye yace "Babu rana, kuma nafada miki banaso kema kiyi sanadin zuwana Nigeria"

"Angama Babban Yaya, Allah yakiyaye hanya" daga haka ta kashe wayar Tata, Takoma
falo,Ummah ta kalleta tace "lafiya?"

Tace "Da Babban Yaya nayi waya"

Sa'eed yace "um kaji masu waya"

Dariya tayi kawai, ta jira yanbiyu suka gama sannan suka fita compound driver ya daukesu suka
tafi


Bayan uncle ya fita daga ajin nasu,Maya ta kalli Waheeda tace "Waheeda waiya kuke da
Babban Yaya ne?"

Kallan Maya tayi tace "Kamarya ya muke? Mekike nufi?"

Maya tace "Ina nufin Wai Ummah ce ta haifeku dukanku?"

Kai tsaye tace "itace mana, me kikaga?"

"babu abinda nagani Waheeda, kawai de Naga kinshaqu dashi fiyeda yanbiyu, sannan Shima
yana sonki sosai, shine nace koba Ummah ce ta haifeku ba"

Waheeda tayi mata wani banzan kallo tace "toba Ummah ce ta haifemu ba waye yakawo mu
duniya Kenan? Nasan nashaqu dashi yanda bakya zato, saboda tun Ina qarama nasaba dashi,
sannan dakika ce yanaso na wannan Kam Ina tantama, saboda idan yana sona ma, to wannan
soyaiyar dayakemin bata hanashi yamin hukunci, idan nayi laifi zaneni yakeyi wallahi, kinbani
mamaki Maya, ashe zarginmu kike "


Maya tace" innalillahi.... Waheeda zargi Kuma? Meyasa zan zargeku Bayan yayanki ne uwa
d'aya uba d'aya? Kawai de kun birgeni ne jiya danaga yanda yake baki kulawa, harfa mota
yabude miki, shine nayi tunani idan ku masoya ne abun zaifi dadin Gani, yana miki soyaiya kina
maida masa martani "
Cikin masifa Waheeda tace" A'uzubillahi.... Maya kamar wata marar Hankali Zaki dinga
dangantani da yayana?"

Maya ta kamo hannunta tace" yi hakuri qawata, nabata miki rai, kiyi hakuri Dan Allah "

Waheeda tayi banza ta qyaleta, har wani uncle din yashigo ajin yafita, bata sake kula Maya ba,
Sai tsaki take saki ita kad'ai


Bayan sun koma tana duba wayar ta taga missed call dayawa da wata number, cikin mamaki
tace "to waye wannan ya kirani har 5 missed call da number daya?"

Kiran number tayi, cikin zazzaqar muryarta tace "Naga kirane waye?"

Cikin salon yaudara akace "kira Kuma? Da wannan number?, Kai may be mistek ne"

Ba tace komai ba ta kashe wayarta

Bayan kusan minti biyar wannan number tasake kiranta, harta d'aura towel tana shirin shiga
wanka, tadawo ta d'auki wayar, "Amincin Allah ya tabbata agareki sarauniyar kyawawa"


"Amin, Lafiya?"
abinda tace masa kenan

Yace "bekamata mace kamar ki, tayimin wannan tambayar ba kyakykyawa, ai kinsan ta tsuniyar
gizo bata wuce ta qoqi, wallahi tunda kika amsa wayata dazu, naji hankalina ya kwanta dake,
nasan aduk inda kike, ke mace ce Mai nutsuwa, me tarin Hankali da cikar haiba, uwa uba tare
da kyau "
Kalamansa sun ratsa Waheeda, da atsaye take, Amma yanda taji yana zubo Nata kalamai,
saita nemi bakin gado ta zauna

Yanbiyu suka shigo Dakin kowacce tana ajiye Jakarta, Ihsan tayi toilet da gudu saboda fitsarin
daya matseta, inti Kuma ta kwanta agadon

Waheeda tajuya idanuwanta tace "nagode, naji dadin yabonka agareni, kafadamin meyafaru?"

Intisar tadago daga kwanciyar da tayi, ta kalli Waheeda, taji tawani sauya murya tana waya da
alama da wanine

Daga nasa bangaren yace "zan so kibani Dama indinga jin wannan zazzaqar muryar Taki koda
sau daya ne a rana"

Kai tsaye tace "inde Dama ce nabaka, menene acikin muryar tawa?"

Yace "bakisan menene acikin muryarki ba? Muryarki tana d'aukeda wani sinadari, duk Wanda
yajita, dole ne tatafi da Imaninsa"

Dadi yakama Waheeda, ashe muryarta tanada dadi shiyasa Babban Yaya yahanasu kula
Samari, ashe Dan karsu hadu da samari su dinga yabon baiwar murya me dadi irin tasu shiyasa
yaqi dadi yahanasu kula samarin

Cikin jin dadi tace "Nagode sosai, baka fadamin sunan ka ba"

Yace "Af... Aina manta ban fada miki sunana ba, gaba daya nagama shagaltuwa dajin wannan
daddad'ar muryar Taki ne, sunana Hassan, Ana kirana Sas, ni soja ne, iyayena da kowa da
kowa nawa suna zaune a kaduna, iyayena suna damuna inyi aure, nikuma har yanzu ban hadu
da wadda nake soba, tun Bayan rabuwa ta da budurwata ta farko "
Waheeda tace" Allah sarki, Allah yabaka mace tagari, nikuma sunana Waheeda, Ina Garin
kano, Ina zaune a unguwar, Amma inaso kabani labari menene yahada ka da budurwarka har
kuka rabu? "


Yace" Waheeda sunanki nada dadi kamar yanda muryarki Takeda dadi, zan baki labari anjima
idan kin Bani damar sake kiranki Akaro na biyu, saboda alfarmar Dana nema shine indinga

kiranki sau daya a rana "

Waheeda tace"nabaka Dama ka kira"

Cikin farin ciki yace "yanzu kin amince indinga kiranki sau biyu kenan a rana?"


Kai tsaye batare da tunanin komai ba tace "Na'amince"

Yace "nagode Yar'uwata, gaskiya kinada hali Mai kyau, please ki kula da kanki karki Bari ko
quda yata6a ki"

Cikin farin ciki tace "to shikkenan" sannan ta kashe wayar

Ihsan da Intisar da tun dazu suke Kallan ta sukace "dawa kike waya Waheeda?"


Harararsu tayi tace "miye naku? To da saurayi nake waya, soja ne, Kuma ni tundaga yanzu ya
kwanta min araina, so kuke naqi kula samari kamar ku daga qarshe a hadani da wani a dangi?
To banason auren had'i, danhaka samari na zan kula"

Intisar tace "aikuwa wallahi baki isaba, bazakija Babban Yaya yazo ya qwace mana wayoyin
muba, tunda yahanamu, kega me kunnan qashi ko?"

Waheeda tace "kunnan qarfe Bana qashi ba,nide saina kula samari, ku Kuma dakuka tsaya
Babban Yaya yamuku hud'uba, to saikuje kuyi tayi, bakusan halin Babban Yaya bane, kaiku
zaiyi yabaro"

Ihsan tace "Waheeda idan kika kuskura kika sake fadar wata magana dangane d Babban Yaya
na rantse da Allah Sai munyi miki duka a Dakin Nan, qarqari kice Ummah zatazo cetonki, to
wallahi kulle kofar zamuyi saimun nuna miki jiki, banza marar kunya" tafadi haka tareda kokarin
cire uniform dinta.
Waheeda tace "ku kasheni ku kaiwa uwata gawata, qarshe kenan" tafadi haka, tareda shigewa
toilet domin watsa ruwa


Sas soja bai sake Kiran Waheeda ba Sai dare, a lokacin harta matsu ya kirata, a zaune suke
afalo yakira, tana dagawa tayi cikin dakinsu da gudu, kowa yabita da kallo gaba dayansu sunyi
tunanin Babban Yaya ne ya kirata, yan biyu ne kawai suka San abinda take 6oyewa, kwanciya
tayi akan gado,tana yi masa sallama, Bayan sun gaisa tace "Ina jinka, tun dazu nake jiran
kiranka, Amma baka kiraba"

"kiyi hakuri sarauniyar kyawawa, oganmu ne ya kirani, kinsan sojoji babu zama"

Murmushi tayi tace "Ina jinka, kabani labarin abinda yarabaka da budurwarka"

Yace "Mun dad'e tareda yarinyar,kinga nide soja ne, Amma bantaba yin kuka ba Sai akan
yarinyar Nan, nayi kuka kamar zanyi hauka, Waheeda muna cikin soyaiya da yarinyar Nan har
ankai kudin gaisuwa da komai, mamanta tace ai akwai Wanda ta yiwa alqawarin auren ta, waje
daya suke aiki dashi, haka aka bamu hakuri, akwai gida na bakiga yanda na tsara Shiba, Sai
hakura nayi dashi nabawa qanina shi, gashi nine Babba a gidanmu, kowa so yake nayi aure,
yanzu haka lefen Dana hadawa yarinyar suna Nan, kawai wasu qananun abubuwan ne ba'a
saka ba, yanzu gashi narabu da'ita komai ya zama tarihi, saide in nemi alfarma awani waje ko
za'a Bani Dama "

Waheeda ta Lumshe idonta tace" wacce irin alfarma kenan?"

Yace" Alfarma mana, nasamu Dama nashiga cikin zuciyar ki, kibani key dinta na kulleta, ta
yanda babu wani d'a namiji dazan iya bud'ewa bare yasamu damar shiga "

Tace"to inde wannna ne, nabaka Dama, Allah ya tabbatar mana da alkhairi "

Farinciki yakama Sas, yace"amma inaso namiki wata tambaya guda daya"

Tace "Ina jinka"

Yace "gashi bamu taba ganin junaba har mun qulla alaqa, meyasa kike sona?"

Ajiyar zuciya tayi tace "gaskiya nayaba da Hankalinka, dakuma tarin nutsuwarka, wannan kawai
shine"

Murmushi yayi yace "zakici gaba da sona Waheeda idan kikai tozali Dani? Karnaje dadin baki
kikemin, saboda nide baqi ne, banida d'iqon fari kod'aya ajikina, ni baqi ne"

Waheeda tayi shiru tatafi tunani, tatuna wata hira dasuka ta6ayi dasu Neenah aboarding, sunce
mata maza baqaqe sunfi lafiya ko a wajan aure, sunfi fararen mazaje bada himma���
Sas yace "kinyi shiru Waheeda"

Cikin sauri tace "ai nafison irinsu, Allah yabarmu tare"

Yace "Amin, yaushe zanzo naganki kiganni? Banaso ki ganni awaya kiji bakya sona Waheeda,
Gara nazo ki ganni a zahiri, sannan inyi magana da babanku cewa Ina sonki, inaso na aureki
idan kin kammala makaranta"

Waheeda tasake yin qasa da murya tace "Allah yakawo ka lafiya"

Yace "to shikkenan, ki kulamin da kanki, karki manta kiyi alwala sannan kiyi addu'ah kafin ki
kwanta"

Waheeda tayi hamdala cikin ranta, ta San cewa tabbas tayi dace da samun Miji na gari


Duk abinda take 'yanbiyu suna ganin ta, basuce mata komai ba saboda idan sunyi mata
magana ma rashin kunya zata musu, kawai de sunsa aransu duk lokacin da taja Babban Yaya
yahanasu riqe waya Sai sunyi mata dukan mutuwa ���


Tsawon sati biyu Waheeda ta d'auka tana waya da soja, ba tareda kowa nagaidan yasani ba,
daga ita Sai yanbiyu ne kawai suka sani, zuwa wannan lokacin Hankalin Babban Yaya ya
kwanta, yanayin ball d'insa cikin nutsuwa bashida damuwar komai, tunda yaga yayi sati d'aya,
yayi biyu, har uku, ba'a kirashi agida akan matsalar Waheeda ba yasan cewa taqara Hankali,
idan yaga Kiran Ummah har d'auka yake cikin nishadi, yasan cewa kawai gaisawa zasuyi.


Cikin sati na hud'un ne Sas yace mata zaizo yaganta ranar asabat, ranar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login