Showing 9001 words to 12000 words out of 82824 words
Chapter 4 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf
futo sun shirya cikin uniform dinsu, suna zuwa compound din suka hangeshi
yana Dukan tayar motar da qafarsa yana Kallan agogo, suna ganin haka suka qara sauri suka
shige motar, shida Kansa yayi driving din, Kai tsaye yanufi makarantar su
Suna zuwa kuwa Kai tsaye yanemi iso zuwa office din director, teachers dinsu maza Wanda
suke harkar ball suna ganinsa suka fara zuwa suna gaisawa dashi, yana gaisawa da director
yanemi afwa akan yanbiyu, babu bata lokaci sukace komai ya wuce Yara sukoma aji, Amma
waccan dayar de kar akawota bazasu karbeta ba
Duk da haka saida yaqara basu hakuri sannan yayi musu ihsani yafuto daga makarantar, daga
Nan ma ba gida yakoma ba, kofar fada ya nufa, yana tambayar gidan Alhaji Hamza aka nuna
masa, futowa yayi ya jingina da motar yace ayi masa sallama dashi, Alhaji Hamza yana futowa
yaga farin buzu a kofar gidansa, qarasa wa yayi yabashi hannu suka gaisa, Babban Yaya yace
"Alhaji sunana Naufal, da Alhaji Hamza nake magana ko?"
Alhaji Hamza yace "nine samari, ba kaine yaranmu suke cewa Big Brother ba?"
"nine Alhaji, dama nazo ne akan maganar qanwata dakuma Yaron wajanka Aryan"
Alhaji Hamza yace "to menene yafaru?"
"Alhaji, Yaron wajanka yana soyaiya ne da qanwata, shine nazo muyi magana akan yaturo
iyayensa idan aure zaiyi yanzu"
Alhaji Hamza yace "Wai Aryan wannan Dana Sani Dan wajena kake magana akansa?"
"shide Alhaji"
Murmushi Alhaji Hamza yayi yace "samari Aryan fa shekararsa goma shatara ne Idan nayi
lissafi daidai, tayaya za'ayi masa maganar aure yanzu?"
Babban Yaya yace "hakane, to ita yarinyar dayake nema aurenta zamuyi, saboda haka Dan
Allah Alhaji ajawa yaro kunne yadena bibiyarta, jiya matsala ce tafaru a makarantar su har
hakan yasa suka Koreta daga makaranta, so aja masa kunne please"
Alhaji Hamza yace "Subhanallah, ashe yar'uwarka ce yaro, to kuyi hakuri Dan Allah, insha Allah
zanyi wa tufkar hanci"
Babban Yaya baice dashi komai ba yajuya yashiga motarsa yatafi gida
Yana zuwa gida ya tarar da Hajiya Anty da Ummah afalo, can ya hangi Waheeda a dinning tana
cin abinci
kwanciya yayi akan doguwar kujera ya Dora Kansa akan cinyar anty yasaki wani irin murmushi
dimples dinsa suka lotsa duka biyun yace "Anty nah ta kaina"
Sumar Kansa ta shafa tace "yayansu nayi fishi, kazo Amma koka leqoni, yanzu ma sannu da
zuwa nazo yima dakuma wani albishir"
Hannunta datake shafa sumarsa yariqe yayi kissing Bayan hannun sannan yace "Ina jinki
Hajiya Anty"
Tace "wallahi wata yarinya ce take zuwa Asbiti Ina dubata lokaci zuwa lokaci, shine nayaba da
Hankalinta, nace zan turo mata Dan yayata su daidai ta ko Allah zaisa ayi abun da'ita"
Cikin sauri ya tashi daga kan cinyarta yace "Anty me kikace?"
"abinda kaji nace"
Kansa ya shafa yace "Anty Kode neman Kai kuke Dani ne?"
Tace "mekake nufi yayansu?tayaya zamu nemi Kai dakai?"
Bata rai yayi cikin shagwaba yace "to Anty gashinan Kuma arasa da wadda za'a hadani Sai
majinyaciya?"
Ummah ce tasa musu baki tace "tunda kaqi lafiyayyu ai sai kakoma kan majinyata" tajuya ta
kalli hajiya Anty tace "ki fada masa komai, kidena wani Lalla bashi"
Hajiya tace "yayansu harna yiwa uncle dinka maganar yarinyar shida Dadynka, Amma Kai Yaya
kagani?"
Ummah tace "Yaya zai Gani kuwa? Yama amince kawai"
Tashi yayi daga wajan su yace "to Anty idan nasamu lokaci zanje naganta"
Ummah tace "yaushe zakaje?"
Kansa yadafe da hannun sa �丹��領����儭�yace " wayyo Allah Ummah, zanje wallahi,
anjima zanje"
Anty tace "to idan katashi zuwa ga wannan kayan kwalliyar kakai mata"
Uwar ledar data turo masa gabansa ya kalla, cikin ransa yace Dama de sun shirya komai
Yace "to"
Bai dauki ledar ba ya wuce ta gaban Waheeda yayi dakinsa,yanaaji yana cewa "good morning
Babban Yaya" Amma ya shareta
wani qullutun taqaici ya to kare mata maqoshi, tasan yanzu Babban Yaya ya tsaneta, gashi ya
maida yanbiyu makaranta Amma banda ita.
Hajiya Anty tana tafiya gida Waheeda taje wajan Ummah ta zauna, Ummah ta kalleta tace
"Lafiya Waheeda?"
Girgiza kanta tayi tace "Ummah, Babban Yaya baya sona yanzu, ya tsaneni"
Ummah ta kalleta tace "yayanki uwa daya uba daya tayaya zakice baya sonki Waheeda?
Halinki ne baya so, Waheeda bakya jin magana, saikin masa laifi Kuma kizo abun ya dameki,
yanzu ni me zanyi muku akan haka?"
Idanunta ne yayi qwalqwal hawaye yana shirin futowa tace "to Ummah kinajifa nagaidashi
Amma ya share ni"
"bai gama hucewa bane, kibari zuwa anjima ai zai sauko"
Hawayen data riqe ne ya silalo daga idanunta, tasa hannu ta share, sannan tayi dakinsu domin
ta watsa ruwa
Umma na ganin tafiyar ta ta nufi Dakin Babban Yaya, yana kwance agadon sa yayi mata shi da
hannayensa, duniyar tunani yatafi ita wannan yarinyar ta wacce hanya zaibi yarabu da'ita?
Turo kofar tayi tashigo, yana ganin shigowarta ya tashi zaune, zama tayi akusa dashi tace
"Yayansu, magana nakeso muyi"
Nutsuwa yayi yace "to Ummah"
Tace "akan Waheeda ne, yakamata kadinga Jan 'yan'uwanka ajiki, qannanka ne bakada kamar
su, idan Bama Raye kaine zasu kalla a matsayin ubansu, yarinya qanqanuwa Waheeda har
tana min magana akan rashin kula da'ita da bakayi, tacemin yanzu kadena sonta, hannunka fa
baya ru6ewa ka yanke kayar, yakamata kadinga janta ajiki kanuna mata fari da baqi, tunda
Dukan bazaisa ta sauya ba saika dinga yimata nasiha "
Kallan ta yayi yace"Ummah nasiha bazata shiga qwaqwalwar yarinyar nanba, batajin magana,
kullum itace takemin sanadin zuwana Nigeria "
Ummah tatari numfashinsa tace" kaikuma gashi baka son zuwa Nigeria saboda kar muyi ma
maganar aure ko? "
Qasa yayi da Kansa yace" Bahaka bane Ummah, insha Allah zan jasu ajikin kamar yanda
kikace "
Tashi tayi tsaye tareda fadin" Allah yamaka Albarka "
Cikin jin dadi yace"Amin Ummah tah"
Dayamma suna kallo afalo, Amma dukansu su ukun suna saka kayan makarantar islamiya, jira
suke kawai lokaci yayi sutafi, futowa yayi daga dakinsa yayi wankan qananun Kaya kamar ka
saceshi kagudu, wandon Jeans yasaka baqi, Sai Riga me kama jiki ruwan toka, dakuma yar
sama me ratsin baqi, yasaka kambos Shima baqi me ratsin brown, yayi kyau sosai sumar Nan
tasa Sai sheqi take, Ummah ta Kalle shi tace "masha Allah, yayansu Sai ina?"
Kansa ya shafa yace "inda hajiya Anty tace naje"
Fara'ah ce ta wanzu a fuskar Ummah, tace "kace gidan surukar tawa zakaje, irin wannan wanka
haka ai dole a dedeta, Bari in Dauko Maka kyautar Tata"
Baice komai ba, yanemi kujera ya zauna, tareda daukar remote ya maida tashar Kallan ball,
Kallan Waheeda yayi, suna hada ido tayi qasa da kanta, yace "4 o'clock kuke tafiya islamiya
ko?"
Atare suka amsa da "eh"
Yasake dubanta yace "tashi ki rakani"
Cikin murna tatashi tayi dakinsu, farinciki take yayan Nata da alama yahuce, uniform dinta tacire
tasaka doguwar Riga, sannan ta dauki dogon hijab dinta tasaka, tana futowa Ummah ma tana
futowa daga daki, ta bashi ledar kayan, ya nuna mata Waheeda ataqaice yace "bata"
Ummah tace "yanaga kincire uniform din ko tare zakuje zancen?"
Waheeda tasaki wani murmushin jindadi, tace "eh Ummah"
Kallan ta yayi sosai, sautari idan yarinyar tayi wani abu saiya ga Takoma photocopy dinsa sak,
musanman idan tayi dariya ko murmushi duk dimples dinta suka bayyana kamar de nashi,
kauda tunanin yayi daga ransa yafita daga falon ita Kuma ta Mara masa baya, saida tajuyo
tayiwa yanbiyu gwalo �云Sannan tafita
Ummah ta girgiza kanta cikin ranta tace gaskiyar sane daya ce bazata sauya ba
Motar dasuka shiga glass din motar tint ne, ba zakaga naciki ba, mafi yawan lokaci irinta yake
Hawa saboda shi mutum ne na mutane, ko Yaya yafuto awaje dole ne kasamu Wanda yasan
shi
Suna cikin tafiya ya kalleta yace "Bani labari"
Kallan sa tayi tace "Babban Yaya wanne labari gashinan muna shirin zuwa Naga Anty"
"wacece Anty?"
"Babban Yaya wadda zamuje wajan ta, budurwarka, harna matsu naganta wallahi"
Haushi ne yakama shi, yace "to naji Dan Allah, ni labari nace kibani bawani shirme ba"
Kallan sa tayi, cikin ranta tace zancen budurwar tasa yake cewa shirme to in hakane komai ma
ta fada bazai birgeshi ba, duk da haka saita Juyo tana fuskantar sa tace "Babban Yaya inaso
Naga kana Ball, ka'iya ball sosai, wani lokacin idan ka saka qwallo araga Sai inji jikina yana
tsuma kamar nice nasaka"
Dariya tabashi, saida yayi dariyar sa sannan yace "ke meyasa bazaki Koya ba?"
"Bayan wacce kake Koya mana agida?"
"yes, idan kinaso saina sake Koya muku"
"muna so wallahi Babban Yaya,nafiso nafi yanbiyu iya Ball"
Kallan ta yayi kawai yayi shiru, saboda qarasowa dasukai gidan yarinyar da Hajiya Anty tabashi
address, a kofar gida suka tsaya yakira Hajiya Anty ya tambayeta sunan yarinyar tace masa
naja'atu, daga Nan yakashe wayar yatura wani yaro Akira masa ita
Yaron ya dawo yace ance su shigo, har falo suka shiga suka zauna, babu laifi gidan sunada
rufin asiri, kusan minti biyar da zamansu Sai gata tafuto tana Sanye cikin atamfa Riga da siket,
Sai wani Dan qaramin mayafi data saka, da farko tsorata tayi data ganshi, saboda lokaci daya
yadaki zuciyarta, gayen yahadu dayawa, fatanta daya Allah yasa Shima ta masa Zama tayi tareda gaidashi, ya amsa cikin kulawa, acan Qasan ransa yaji dadi dabata ganeshi
ba da alama bata ganin ball, Waheeda ce itama ta gaidata fuskar ta d'aukeda murmushi, ta
amsa mata
Shiru Waheeda tayi tana jira taji irin kalaman soyayyar da Babban Yaya zai tsara mata kamar
yanda Didat yake mata idan sun hadu a school, saitaji yace "Naja'atu Anty nace taturo ni
wajanki, basai nayi Miki dogon bayani ba nasan kinsan dalilin zuwana wajanki"
Murmushi tayi tace "Hakane, nide daga wajena babu wata matsala, Ina fatan kaima haka?"
Babban Yaya yace "a a, banda wata matsala Nima, saide inaso namiki tambaya guda daya"
Kafadunta ta daga�仄��領����儭�tace "babu damuwa Ina jinka fadi duk maganar
dakake so"
Yace "Kina school ne yanzu?"
Tace "a a, tunda nayi candy bankoma makaranta ba"
Yace "masha Allah, Nima banda burin yarinya tayi dogon karatu batare da aure ba, but meyasa
ke kinyi candy Amma bakiyi aure ba har kika dade agida kina neman tsufa?
Waheeda ta zaro ido ��速a Kalle shi da sauri
Itama naja'atu ta Kalle shi tace"me?, nice na tsufa babu aure? "
Batareda damuwa ba yace"idan bakiyi shekara ar'ba'in ba tokin kusa, tunda Naga idanunki na
tabbatar kedin Nan sa'ata ce, bazan girmeki ba, nikuma gaskiya nafison na auri yarinya
qarama, wadda zan Koya mata komai"
Haushi yakama naja'atu, ta jinjina kanta tace "ni Dama nasan babu wani namijin Arziqi daza'a
dinga neman Kai dashi haka kawai, na tabbatar kaima kyan Dan maciji ne dakai tunda har ake
neman Kai dakai duk wannan kyan Naka, tunda kana tareda P.A dinka ai shikkenan saikaje ka
aure ta"taqarasa maganar tana Kallan Waheeda
Cikin sauri Waheeda tace "kaiiii Yaya nane fa"
Naja'atu ta miqe tsaye tace "Au...to Allah yasa gware kukai kuka futo" ���
Waheeda ta kalli Babban Yaya ko zai dakatar da naja'atu daga tafiyar datake shirin yi, taji yayi
shiru, ahankali tace "Haba Babban Yaya"
Kallan ta yayi ya daga murya yace "Naja'atu"
Cikin fishi naja'atu tajuyo tace "kutashi kubar mana gida tun kafin nakira Yara su tule ku da
qasa"���
Dafe Kansa yayi �丹��領����儭?, sannan yadago yace "Dama wannan ledar ce kika
manta bakidauka ba, Inji Anty tace akawo miki"
Tsaki naja tasaki tace "kuje da tsiyarku" daga Nan tashige tabar su afalo, ita kanta Waheeda taji
babu dadi, tayi tunanin haquri zai bata Wai ashe leda zai bata, wannan rashin mutuncin ko ita
akayiwa Allah ne kadai zai rabata da saurayin ranar ���
Haka suka futo daga gidan Waheeda jiki a sanyaye, shi kuwa ransa fes
Amota kasa magana Waheeda tayi, Shima bece da'ita uffan ba, cikin ranta tana so ta
tambayeshi meyasa yake gudun aure? Amma tarasa ta'ina zata fara? Duk cikin iyayensu babu
Wanda yataba zama dashi yaji menene dalilin sa naqin matan da'ake hadashi dasu, kawai sude
iyayen burisu suga yayi aure kawai, tana so taji menene matsalar sa, meyake so? Amma tana
tsoron abinda zai biyo baya, saboda zai iya cewa ta raina shi
Tunanin tane ya tsaya lokacin dataga sun tsaya awani super market, p-cap dinsa ya dauka
yasaka me d'aukeda sunansa ajiki, sannan yashiga wajan, itade Waheeda tana binsa Abaya
taga Sai provision yake yi, itama yace tayaya shi haka suka dauki , su suger, cornflakes,
madara, Maggi, kayan zaqi dangin su biscuit da chocolate, saida yagama hada komai tsaf, har
tana mamakin Ina zaikai wannan uban kayan,? Wasu yanmata ne suka ganshi su kazo sunaso
yayi photo dasu, babu musu ya tsaya sukayi sannan suka nufi wajan biyan kudin, a lokacin wani
saurayi Shima yana wajan zai biya nasa kudin, ganin Babban Yaya yasa farinciki yarufe shi,
Yama Rasa inda zai Dora ransa, Sai magana yake masa, Babban yaya yayi murmushi Shima
yasake da saurayin kamar ya sanshi, shida Kansa ya biya kudin saurayin danasu kayan sannan
yamasa sallama suka tafi gida
Suna zuwa gida taga yabawa Sa'eed wannan kayan dasuka zo dashi, sannan suka wuce Dakin
Ummah, tare suka gansu itada hajiya Anty Sai hira suke da shewa kamar ba facaloli ba���
a lokacin biyar da rabi har tayi, Ummah ta kallesu cikin farinciki tace "harkun dawo? Jinake ai
sai dare"
Hajiya Anty tace "yayansu nasan de Najaatu tayi hundred percent"
Zama sukai gaba dayansu babu Wanda yayi magana, Ummah ta kalli ledar kayan kwalliyar
dasuka tafi dashi tace "yanaga kunyi shiru, meyafaru ko bakuje bane?"
Waheeda ta janye hannunta daga tagumin da tayi tace "hmm Ummah cewa tayi mutashi mutafi
tun kafin tasa atule mu da qasa, gashi mayafi take sakawa, shikuma Babban Yaya baya son
mayafi, shine ya tambayeta meyasa ta tsufa batayi aure ba, ranta ya6aci tace masa yaje ya
aureni tunda ni p.a dinsa ce, Wai ai Dama neman Kai kuke dash.... " Hajiya Anty ce ta katse Waheeda cikin tsawa" ke dallah can rufe mana baki shashasha kawai.
Yen yen yen Sai magana kike Babban Yaya baya son kaza, Babban Yaya baya son kaza,
kunhada Kai kunje kunci mata mutunci kun dawo toshknn Hankalinku saiya kwanta, ita
yar'iskace dabaza tace yaje ya aureki ba? Ina aka taba tafiya zance , ganin farko adiba atafi da
qanwa? Saikune zaku nuna mata ku yan'uwan jini ne, banji dadi ba dabatasa anmuku wanka da
qasa ba, tashi kibawa mutane waje manya suna magana kin tsomo baki kamar maganar
aurenki ake "
Sum sum Waheeda tatashi tabar Dakin, shi kuwa Babban Yaya kasa hada ido yayi dasu
Ummah tace"ashe abinda kake fadawa yaran mutane kenan shiyasa kowacce Sai tace bata
sonka, Toda kake cewa ta tsufa batayi aure ba kaidin shekarar ka nawa?" ��
Shiru yayi yakasa Bawa Ummah amsa, Ummah tace" dakai nake, nace Kai shekararka nawa
bakayi aure ba? "
Kansa aqasa yace" Ummah kuyi hakuri, Nima ba laifi na bane "
daga Nan ya tashi yafuto daga Dakin Shima
Yana fita hajiya Anty tace" Yaya kinji me yace kuwa? Ba laifin sa bane Anya kuwa Yaron Nan
kalau yake ba Sanyi da basir ne sukai masa mugun kamu ba? "�不
Ummah tace" to Hajiya Anty tayaya zan Sani? Kuma yaqi yayi auren balle mugani kalau yake
koba kalau yake ba "���
Hajiya Anty tace" kaiii ninama Rasa mezance wallahi, tunani na ya tsaya Hajiya, Bari inje gida,
idan nasake wani tunanin saina dawo "
Washe gari da sassafe ya shirya cikin qananun Kaya, so yake yabar qasar saboda jibi sunada
match a Qatar, sannan muddin yaci gaba da zama to bazasu daina hadashi da yanmata ba,
suna gama bresk fast, ya kalli Ummah da Daddy yace" Ummah, Daddy, zan wuce England
yanzu, jibi munada match a Qatar, kuyimin addu'ah "
Atare sukace" Allah yabada sa'a "
Ya Juya ya kalli Waheeda, yabata 10k yace" gashinan, kiyi amfani da wannan idan kinje
makaranta, anjima su Sa'ad zasu kaiki Boarding school, nariga nayi magana da principal din ta
waya, Shopping din da muka iyo jiya nasan komai yamiki tunda ke kika za6o da kanki, Tunda
bakya jin magana Dan Allah kisake aikata wani laifin Wanda zakisa nasake dawowa Nigeria
saboda ke kinji..... "
Spoon din hannunta ne yafadi qasa tace" nashiga uku Babban Yaya Boarding Kuma? "
Kallan qwayar idonta yayi yace"yes, nafiso a kaiki inda zasu kasheki su kawo mana gawarki"
Duk me buqatar Babban Yaya yakirani kokuma yamin magana ta whtsapp 08033300034
Share please ������
Amnah El Yaqoub ����?
1/28/22, 20:49 - Ummi Tandama���: BABBAN YAYA
Writing By Amnah El Yaqoub
Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/
5&6
Tanajin abinda yace tayi dakinsu da gudu tana kuka, Shima yajuya yafita daga falon, wannan
Karon driver ne yakai shi Airport, Bai dade da zuwa ba jirginsu ya tashi
A wannan safiya Waheeda breakfast din da batayi ba kenan, tana daki tana kuka, Sa'ad ne
yashigo Dakin yace ta shirya kayanta karfe goma zasu tafi, tanajin abinda yace tasake rushewa
da Kuka, harta Bawa yanbiyu tausayi suma suka fara share hawaye ���, sune suka shirya
mata kayanta tsaf, sannan Ummah tazo ta lalla6ata taci cake da madara, sannan suka tafi,
tabawa kowa tausayi a gidan, Hajiya Anty Kam dataji labari kasa zuwa gidan tayi, zuciyarta
bazata dauki hakan ba, gashi babu damar Hana tafiyar Tata tunda Babban Yaya ne ya yanke
hukuncin, iyayen nasu sun bashi power sosai babu yanda za'ayi ya yanke hukunci aqetara shi.
Lokacin dasuka kaita,riqesu tayi tanata kuka, saida principal din yasa wata yar ss3 ta riqeta
suka tafi hostel tareda kayaiyakinta.