Showing 54001 words to 57000 words out of 82824 words

Chapter 19 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf

a'idon Waheeda,wannan shi ake kira sai masifa ta sameka ne zaka
san me sonka da gaskiya, yanzu duk soyaiyar da Huzaifa yake iqrari yana mata ashe qarya ne?
Ashe saboda cuta ta sameta zai iya gudunta? Didat din datake wulaqantawa shine ya tsaya
tsayin daka akan yana sonta duk da haka, lokaci d'aya taji numfashin ta yana sama kamar zai
d'auke, yanbiyu da Ummah da Hajiya Anty, kuka suke sosai, duk falon anrasa Wanda zaiyi
magana guda d'aya


Gabansa ne ya tsanan ta fad'uwa, ya d'ago Kansa ya kalli iyayen nasa, daga Daddy har Uncle
Usman kansu yana qasa sun kasa d'agowa kamar Wanda suke jin kunyar had'a ido da yaran
nasu

Ya kalli Ummah yaga tana goge hawaye

Ya kalli 'yanbiyu yaga Sai gunjin kuka suke duka su ukun har Waheeda

Ya kalli su Sa'eed yaga kansu aqasa suma

Ya kalli Hajiya Anty yaga ta zubawa waje d'aya ido hawaye yana silalo wa daga idonta, idan
akwai Wanda yaqi jinin yaga kukan ta Aduk duniya to Hajiya Anty ce, zai iya jure kukan kowa
Amma banda Nata, har zuwa lokacin Hajiya ummi tana falon, ita bata tafi ba, Kuma takasa
Bawa kowa haquri
Zuciyar sa ce take zigashi akan yafad'i abinda yake ransa, tayaya za'azo har gida, harcikin falon
su aci mutuncin su kawai saboda maganar Aure? Tayaya zaiguji Waheeda? Tayaya zai raba
zuciyar sa da soyaiyar ta Bayan da soyaiyar Tata aka halicce shi?
Lokaci d'aya yad'auki shawarar zuciyar sa, yanaso yafad'i abinda yake ransa Kuma Yana tsoron
abinda zai biyo baya, gabansa yaqara tsananta fad'uwa, cikin sauri kamar an fuzgo maganar
daga bakinsa ya kalli inda Daddy da Uncle Usman suke zaune yace "Daddy nizan Aure ta"

'Diffff...... Sai aka nemi masu kuka a falon aka Rasa,falo yayi shiruuu, kowa ya d'ago Kansa
yana Kallan Babban Yaya, falon yayi tsit kamar babu wata halitta acikinsa, kowa Kallan sa yake
cikeda mamaki, gaba d'ayansu yaran gidan babu Wanda mamaki bai kamashi ba Sai iyayen ne
kawai dasuke Kallan sa cikeda d'inbum almara

Ummi ta miqe tsaye cikin tashin Hankali tace "ka auri wa? Wallahi saide ka za6a koni ko ita,
Amma Bazan ta6a yarda ka aure ta ka shafamin qanjamau ba, saide mu rabu...."


Ummah ta kalli Babban Yaya tace "Naufal meyasa....?meyasa zaka fad'i wannan maganar?"

ta qarasa maganar tana dafe kanta dayake barazanar rabewa gida biyu �丹��領����
儭?


Cikin tashin Hankali Waheeda ta zaro idonta��� Wanda yayi jajir kamar gauta saboda kuka,
kamar ba itace take ihun kuka yanzu ba
Kallan Ummah tasake yi ko zata qarya ta maganar da Babban Yaya yafad'a, Amma saitaji
Ummah tayi shiru, ta kalli su Daddy har yanzu kansu yana qasa sun kasa kallan mutanan falon,
cikin tashin Hankali tace "Zaman Zina? Ni wallahi bazan yarda ba, banason sa, bazan iya
Zaman aure dashi ba....."
tatashi tayi d'akinsu da gudu cikin tsananin kuka

Wani irin kuka ne yataso masa, yau shi Waheeda take cewa bata sonsa, wani irin abu yatokare
masa maqoshi, ko yawu yakasa had'iyewa.

Ummi ta Kalle shi tace"Naufal jiranka nake, nabaka za6i tun d'azu kayi shiru, kana tunanin zan
yarda kahad'ani kishi da wannan yarinyar ne? Wallahi bazai iyu ba saide asan nayi, zanje in
fad'a agida yanzu yanzu "

Baqin cikin kalmar da Waheeda tafada masa ne yake addabar zuciyar sa, jiyake kamar yafashe
da Kuka kozaiji sauqi Amma kukan yaqi zuwa, ga Kuma wannan yarinyar datake qara masa
wata damuwar.
Cikin 6acin rai Shima yatashi tsaye, cikeda tsawa yace" toki fad'a mana, so what....? Idan kin
fad'a musu kiqara musu da cewa Bana sonki, Bana qaunarki, bazan iya zama dake ba, saboda
bakya respecting iyayena "

Yajuya ya nuna mata Hajiya Anty sannan yaci gaba da fad'in"matar dakika raina kike mata
Kallan sa'arki itad'in mahaifiyata ce..."



Lokaci d'aya ummi ta qame a wajan, gabanta yafad'i, cikin mamaki ta bud'e bakinta, takasa
rufe shi
Babban Yaya yahad'e hannun sa waje d'aya �����語a kalleta yace "Dan Allah Ummi kifita
daga cikin rayuwa ta, na roqeki"

Cikin kuka ummi Tajuya tafice daga gidan, Shima Babban Yaya batare daya kalli iyayen nasu ba
yafice cikin sauri, saboda zuciyar sa tagama karyewa, qiris yake jira yafashe da kuka, yana
zuwa compound yashiga motar sa yamata key yabar gidan a d'ari da Sittin, Kai tsaye gidansa
ya nufa, yanda yake danna Hon yasa maigadinsa yabud'e masa da sauri, shigowa had'ad'd'an
gidan nasa yayi tareda parking din motar sa, yad'ora Kansa akan sitiyarin motar yayi shiru, har
yanzu maganganun Waheeda yawo suke masa a ransa, yana jin yanda wayarsa take qara
Amma yaqi dubawa, saida kira na uku yashigo sannan ya d'auka

Daga d'ayan bangaren Mashkur yace " Bro... Ina kabar wayar ne?"


Sai a lokacin kukan dayake dannewa agida yataso masa, fashewa yayi da Kuka harda
shashsheka, daqyar maganar sa take fita, cikin kuka yace "Mashkur bata sona..."

�歹�
1/28/22, 20:51 - Ummi Tandama���: SQ



Cikin sauri mashkur yace "wacece? Wacce yarinya ce wannan tasaka friend d'ina kuka haka?"

Kai tsaye Babban Yaya yace "Waheeda!"
Mashkur ya gyara zamansa yace "Waheeda Kuma? Ba sister d'inka ce ba?"

"Sister nace"

Cikin mamaki mashkur yace "but... tayaya...."

Babban Yaya ya katse shi yace "she's my Cousin Sister"

"Amma friend abun ya d'auremin Kai dayawa, Wai kanaso kacemin Dama itace wadda kake
cewa kanaso bazaka iya rayuwa batare da'itaba? Itace wadda akanta mukaje Saudia muketa
ruwan Addu'ah?" ��

Ahankali Babban Yaya yace "itace...., inason ta mashkur, but nafad'awa su Daddy d'azu, shine
tace musu Wai ita bata sona..."

"dakata Bro,tayaya kake tunanin zatace tana sonka dan Allah? Koni Nan nayi tunanin Kai
yayanta ne uwa d'aya uba d'aya, haka kawai Kai tsaye yarinya taji kace zaka aure ta, Dan Allah
tayaya kake tunanin zata amince Karon farko? Kaine kake mata Kallan masoyiya, ita Kallan
yaya take Maka, Amma kayi hakuri, kabar komai yalafa, insha Allah zata fahimce ka, kayi hakuri
"

Babban Yaya yakashe wayar, ba tareda yace komai ba, sannan yafuto daga motar yashiga ciki


** *** **


Sa'eed ya kalli Ummah yace "Ummah ku fitar damu daga duhu mana"

Yasake Kallan iyayen nasu maza yace "Daddy, Uncle Dan Allah kuyi mana bayani, me Babban

Yaya yake nufi? Tayaya zai iya auren Waheeda Bayan shi Yayanmu ne?"

Daddy yayi ajiyar zuciya yace "Naufal zai iya auren Waheeda"

Yanbiyu da Sa'eed da Sa'ad suka maida Kallan su wajan Daddy

Daddy yaci gaba da fad'in, "koda ace Naufal bai bud'i baki yace zai auri Waheeda ba Toni
dakaina zan d'auketa nabashi, saboda banta6a tunanin Yaron Nan Huzaifa zaimin haka ba,
ashe bashida tarbiya tunda har zai iya Kallan idonmu, a matsayin mu na iyayensa, ya fad'a
mana irin wannan maganganun,abinda yake faruwa Wanda ku Baku saniba shine....

Tun muna Yara nida Usman ne kawai mukai karatun boko, Yaya Habu baiyi ba, shiyasa Lokacin
da muka bar nijar muka dawo Nigeria da zama, a lokacin muka zauna da Yaya Habu akan
Garin dazamu Yada Zango, a lokacin ya nuna mana shi yana jin dadin Zaman Garin jigawa,
saboda haka mubashi wata dukiyar tamu da mukai gado a wajan iyayen mu, ya zauna yaci
gaba da juya mana ita acan qauye, mukuma muje birni muyi abinda muka ga yadace

A lokacin babu Wanda ya haihu acikin mu duka mu ukun, Bayan mun dawo Nan da zama a
lokacin muka qara karatu, mukasa iyayenku mata a a makaranta, Antynku tana fara karatu Sai
Allah yabata ciki, Tasha wahala a lokacin, Yaya Habu yazo ganinta, anan yake sanar damu
cewa Shima me d'akinsa tasamu juna biyu, munyi farinciki sosai, Bayan wasu watanni Matar
Yaya Habu ta sauka, Aka sakawa yaro suna Yahya, a lokacin muka shirya muka tafi jigawa
Wajan suna, tun muna hanya Ummanku take cikin damuwa, saboda tasan zata had'u da
danginmu na Niger a gidan Yaya Habu, Kuma sha'anin surutun dangi, tabbas Sai sun fad'a
mata magana akan haihuwa, na tambayeta dalilin damuwar ta, ta fad'a min komai bata 6oyemin
ba, ashe aloakcin Uncle d'inku dakuma Hajiya Anty, suna jinmu, munje anyi taron suna lafiya
angama lafiya, abinda Ummanku take gudu saida yaso yafaru, domin kuwa duk Wanda yaga
Anty Da tsohon ciki ita Kuma bata dashi saide su dinga yimata wani Gani-Gani, saida na
tsawatar musu

Washe Garin haihuwar Yahya a ranar Antynku ta haifi Naufal, Halaccin da bamu ta6a tunanin
zasu mana ba itada Usman shi suka mana, saida suka kira Yaya Habu Dani da umman ku,
sannan suka d'auki Naufal suka bamu shi halak Malak, Dafarko naqi yarda nakar6a, saboda
suma shi kad'ai suka mallaka, Amma sai Yaya Habu yace mana mukar6a tunda sune suka
bamu, tunda ita Antyn tafara haihuwa insha Allah zata sake Haifar wani, Amma yanzu mubarshi
ta shayar dashi, saimu kar6eshi, tunda muka dawo gida Ummanku take kula da Naufal,
tsakanin sa Da Antynku shine shayarwa dakuma wasa irin na d'a da uwa, har Allah yasa aka
yaye Naufal, tazo da kanta ta kawo mana shi,a lokacin yaqi yarda ya zauna damu duk da
yasaba da ummanku, dare yanayi zai fara kuka yana Kiran Anty, haka muka haqura saida ya
tasa, sannan ummanku ta kar6eshi, a lokacin da hankalin sa Sarai ya dawo gidannan, yasan
komai, yasan bamu ne muka haife shi ba, Amma abun mamakin koda wasa baita6a nunawa
wani cewa bamune iyayen saba.

Ahankali ahankali soyaiya take sake shiga tsakanin sa da ummanku, har suka saba babu inda
zasuje ace shi ba d'anta bane, cikin dangi kowa yasan Yaro na Ummah ne Amma Anty ce ta
haifeshi

Bayan wani lokaci tun muna jiran Antynku tasake haihuwa har muka gaji muka barwa Allah,
muka d'auki son duniya muka d'ora wa Naufal duka mu hud'un, har tsawon shekara goma

A lokacin kamar wasa ummanku tafara zazza6i muna zuwa Asbiti akace tanada juna biyu, a
lokacin Nan gidan Antynku tatare take kula da komai, har Allah yasa ummanku ta sauka ta haifi
Yan biyu maza, nida Usman Muka sanya musu Suna Sa'ad dakuma Sa'eed

Daga baya tasake samun wani cikin muka sanya mata sunan mahaifiyar mu, wato Maryam,
Bayan shekara biyar tasake haihuwar wasu yanbiyun muka sanya musu suna Intisar dakuma
Ihsan, a lokacin munyi tunanin Usman da Antynku zasu kar6e Naufal daga wajanmu, Dan har
Ummanku tafara zazza6i tana tsoron arabata dashi saboda yanda yashiga ranta, tasaba dashi
fiye da 'ya'yanta na cikinta, Amma koda wasa basu ce mu basu Shiba, Bayan shekara biyu da
haihuwar su Ihsan muka sake Haifar Waheeda.


Tunda aka haifi Waheeda Naufal ya liqe mata, tun alokacin muda kanmu mukasan cewa yana
qaunar ta sosai, shaquwar su ta daban ce, shine meyi mata wanka, shine goyo, shine siyo mata
sweet, gashi ita Kuma batajin magana, Amma haka zai zaneta yamata hukunci yanda ya
kamata, Dafarko munyi tunanin soyaiyar dayake mata ta aure ce, to damukaga yanda yake
zaneta idan tayi laifi, yake mata hukunci irin Wanda koda ace mune zamu mata hukunci to irinsa
zamu mata, Sai muka saduda muka daina tunanin komai akan alaqar su, muka bar komai a
matsayin shaquwa,tunda yanbiyu maza kansu yana had'e, suma yanbiyu mata kansu ahad'e
yake, Maryam kuwa tana d'akin mijinta, shiyasa bamu damuba Dan shaquwa me qarfi tashiga
tsakanin Naufal Waheeda, to yanzu Kuma ga abinda Allah yasa ya kasance, wannan shine
labarin. "


Shiru falon yayi, Ummah de tana mamakin Naufal Wai yau shine yake cewa yana son
Waheeda, inda tasan cewa haka abubuwa zasu faru, da tuni Waheeda ta dad'e a gidansa,
Hajiya Anty kuwa farinciki takeji acikin ranta, Allah yagani tana mutuqar kaunar Waheeda, tanaji
da yarinyar sosai, Sai gashi yau Naufal d'inta yafad'i abinda yake ransa, dama ta dad'e tana
wannan zargin, to Abaya tana tsoron ace ya nuna yana son Waheeda, saboda su kansu ba
Susan tayaya zasu yiwa yaran bayanin abinda yafaru Abaya ba, Amma yanzu da Allah yasa
hakan tafaru, ai shikkenan.

Yanbiyu sukai ajiyar zuciya, yanzu ashe Babban Yaya Yaron hajiya Anty ne?

Sukuwa su Sa'eed kasa magana sukai, haqiqa idan hakane sunfi kowanne qanne sa'ar samun

Yaya nagari kamar Babban Yaya, Kuma Waheeda da taqi data so, Zaman aure dole ��

Wayar Daddy tayi qara, ya d'auka tareda fad'in, "minister yaya gida ya iyali?"

"Alhamdulillah Alhaji Umar, ashe Kuma abinda yasamu Waheeda kenan..."

Daddy yace "wallahi"

"kayi hakuri Alhaji Umar, kasan Yaron yanzu ka haifeshi ne baka haifi halinsa ba,Nan uwarsa ta
zaunar dashi tagama hure masa kunne, Amma ba laifin Huzaifa bane, kuyi hakuri Alhaji Umar"

Daddy yayi wani murmushi me ciwo yace "Babu damuwa Alhaji, ai har wanima yafuto, Kuma
mun bashi"

Cikin sanyin jiki minister yayiwa Daddy sallama, shi Kansa baiso Huzaifa yamasa haka ba, da
har yana murna zai samu jikoki kyawawa �朮

'Yanbiyu ne suka tashi sukabi Bayan Waheeda d'aki, suna zuwa suka ganta a kwance akan
gadon ta zubawa waje d'aya ido tana kallo tana zubar da hawaye

Zama sukai kusa da'ita, inti tace "Waheeda kiyi hakuri, nasan abinda ciwo mutum kana soyaiya
dashi Amma saboda wata cuta ta sameka yagujeka, wallahi Huzaifa yabamu mamaki, Allah
yasaka miki, Amma tunda bakida haqqinsa, ai gashinan yanzu kin samu Wanda yafi shi komai
da komai, ga kud'i, ga kyau, ga aji, ga kwalliya, ga Kuma farin jini, sannan kinsanshi kinsan
halinsa, uwa uba ma d'an uwanki ne "

Ihsan tace" wallahi kuwa, Allah sarki Didat Shima yabani tausayi wallahi, ashe da gaske yake
yana son Waheeda, kiduba kiga yanda ya yarda zai aure ta a hakan, Amma yanzu tunda ga
Babban Yaya Nan Shikkenan, saikiyi hakuri ki aureshi, Su Daddy sun fad'a mana Hajiya Anty ce
ta haifeshi, saboda haka saiki daina cewa zakiyi Zaman Zina dashi... "
"Dan Allah kurabu Dani, waiku idan ku akace zai aure ku zakuji dad'i ne? Tayaya zan iya Zaman
aure dashi? Yayana? Tun Ina qarama da wannan fuskar nake Kallan sa"


Ihsan tace "to Sai menene Dan kin Kalle shi a matsayin yayanki? Nawa akayi hakan?"

Waheeda ta goge Hawayen idonta, tatuna lokacin data nuna masa Breast d'inta, da yanda take
rufa masa asiri idan ya had'a plan d'in rabuwa da yanmatan da ake had'ashi dasu

tatuna lokacin dayake fad'a mata zata Iya auren me kama dashi meyasa shi bazata aure shi
ba?

Tatuna lokacin dayake cemata wadda yakeso suna kama da juna, Kuma sunan su daya ,
Amma karta fad'awa kowa

tatuna yanda take fad'awa jikinsa any how, ta rungume shi yanda takeso, gaba d'aya yagama
jin d'umin qirjinta

tasake tuna yanda take kokarin nuna masa Breast d'inta yana kauda Kai Amma saida ta nuna
masa, baqin ciki yakamata, cikin kuka tace "yacuceni,yagama Dani, shikkenan yagama ganin
komai...."

Su intisar da basu fahimce ta ba sukace "me kike nufi?"

Cikin rashin kunya tace "bansani ba, Kuma ai bayansa kukebi, bakwa sona Dama can nasani"
Ihasan tasaki dariya tace "inti, dole ne muje muyi anko, muna murna da wannan aure"

Waheeda tace "uwar anko zakuyi ba anko ba"

Intisar tace "to karde kimana rashin kunya yarinya"

Tace "Nayi..., ku kashe ni idan kunso"

Intisar tayi murmushi tace "da ace Dane, zamu kashe ki mukai wa Ummah gawarki, Amma
yanzu ba zamu kashe kiba, saide mu barki araye danki auri Babban Yaya"
Daga Nan suka fice suka bar mata d'akin
Suna fita ta kalli hannunta, tacire zoben da Huzaifa yasaka mata tayi jifa dashi, taci gaba da
gunjin kuka.


Washe gari Hajiya Anty da qawayenta suka shirya aka maidawa su Huzaifa lefen su, ko tsinke
basu d'auka aciki ba.

Har tsawon sati d'aya, Waheeda bata sake da kowa ba a gidan, tun yanbiyu suna bin kanta, har
suka daina, Ummah ma tayi Tata nasihar Amma a banza, Waheeda Gani take sun kasa
fahimtar tane, tayaya zata Iya Zaman aure da Babban Yaya? Su kwanta gado d'aya,ta tsotsi
bakinsa, tamasa romance, abinda take karantawa a littafi Shima tayi masa, ta'ina zata fara
hakan? Ina taga fuskar dazata masa duk wad'annan abubuwan?


Kwata kwata falo ma Dena futowa tayi, duk inda tasan zata had'u da Babban Yaya gujewa
shiga wajan take, gyaran jikin data fara zuwa ma Shima tadena zuwa,
Daddy daya ga abin Nata Bana qare bane, saiyace surabu da'ita, yasamu Uncle Usman sukai
magana, washe gari kuwa Yaya Habu yazo, suka gama abinda yadace, Aranar aka d'aura mata
Aure da Babban Yaya akan sadaki naira dubu 'Dari, Babban Yaya yana tareda Mashkur Wanda

yazo qasar shekaran jiya, yana jin farinciki a ransa but idan yatuna da Waheeda, jikinsa yana
yin Sanyi

Yan gidansu Ummi sunajin labarin 'Daurin auren suka tattaro kayan su na lefe da aka Kai, suka
dawo dashi, saboda suma anasu bangaren babu yanda basuyi da Ummi ba, Amma tace ita
bata shirya kar6ar qanjamau ba

Da yamma gidan baqi sun zazzo duk da bawani taro zasu yi ba, Amma maqota sun shigo
musu,gakuma tawagar Baba Habu, Waheeda tanajin labarin 'Daurin aurenta da Babban Yaya
taji wani irin zazza6i yakamata, lokaci d'aya tafara rawar Sanyi, jikinta yayi zafi zau..., Hajiya
Anty da taci kwalliya cikin wani leshi me mutuqar tsada, Sai walwali take, tashigo 'Dakin ta
dubata, sannan tayi mata allura, ruwan Sanyi ta d'ebo zata koma d'akin ta goge mata jikinta,
saiga Babban Yaya yashigo gidan kana ganinsa kasan yana cikin damuwa, Kallan sa Anty tayi,
duk ya fad'a saboda tunani, bashi ruwan tayi tace "wuce kaje ka gogewa matarka jiki,jikinta yayi
zafi dayawa, zazza6i takeji"

Kansa ya Jinjina ya kar6i ruwan da towel yace "to Anty"

Kofar d'akin yatura yashiga, tana tareda 'yanbiyu, idonta biyu, Amma tanajin qamshin turaren sa
ta Lumshe idonta kamar me bacci, yanbiyu suna ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login