Showing 45001 words to 48000 words out of 82824 words

Chapter 16 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf

ta kamashi yace "kuma anko da dubu Hamsin?Bari kiji, babu wani anko da zakuyi,
tunda bason auren nake ba, Kuma ta shafeku"

Tace "Dan Allah Babban Yaya kaji, wallahi muna so, Dan Allah muyi? To wai Kai meyasa baka
son auren?"

Cikin damuwa yace "nafad'a miki Bana burin zama da wadda banaso, karki sake min wannan
tambayar, Sai me Kuma kike so Bayan wannan?"

Lallausan Hannun sa takama tariqe cikin Nata, Kallan ta yayi cikeda mamaki ya kasa magana
haka Kuma ya kasa qwace hannun sa, cikin nutsuwa tafara yimasa magana tace"nikam ai
nagama samun abinda nakeso a rayuwa Babban Yaya, iyayena suna sona, Babban Yayanmu
yana sona, sannan Huzaifa yana sona, Bana tunanin komai akansa, nasan ko Bayan munyi
aure zai riqeni Amana kamar Babban Yayanah, saide Kuma naso ace nasamu me kama dakai
Babban Yaya"

Gabansa ne yake Dukan Tara Tara, tunda tafara yimasa wannan maganar, kwata kwata yafita
haiyacinsa, zuciyar sa ce take zigashi akan yafad'a mata komai, karyayi wasa da damar sa,
karya Bari abinda yadad'e yanaso yakufce masa

Cikin sauri kamar Wanda aka mintsineshi yace "koda nine....?"

Kallan idanunsa tayi, cikin rashin fahimta tace "kamarya?"

Shima Kallan qwayar idonnata yayi yace "Zaki iya auren me kama Dani, meyasa ni bazaki aure
niba....?"





Kuyi hakuri Dan Allah �����鳶������

1/28/22, 20:50 - Ummi Tandama���: SM



BB



Cikin sauri ta d'ago ta Kalle shi, tsananin mamakin abinda yayan Nata yafad'a ne yasa takasa
rufe bakinta, gabanta yafara fad'uwa ganin yanda fuskarsa ta nuna kamar da gaske yake, wata
zuciyar tace da ita ke mahaukaciya ce? Tayaya hakan zata faru tsakanin ku?yayanki uwa d'aya
uba d'aya tayaya? Dariya ta kwashe da'ita tace "Babban Yaya aure Kuma? Tayaya? Tayaya zan aure ka? Please
Mekake so kace? Nasan inajin sonka acikin raina fiyeda yanda nake jin huzaifa acikin zuciyata,
saboda Babban Yaya ubane, Kuma ba'a sauya uba,shi kuwa Miji Ana sauya shi"

Kansane yasara har saida yariqe goshinsa, lokaci d'aya ya dawo cikin haiyacinsa, yatuna irin
kato6arar da yayi, cikin sauri yace "lokaci ya quremin, Sorry....kuje kuyi ankon tunda Kuna so,
tashi kije"

Cikin murna Waheeda ta rungume shi tareda manna masa kiss agoshi, tafice daga d'akin

Tana fita yazube akan gadon nasa, duk yanda yake jin dad'i idan jikinsu yahad'u yau baiji komai
ba kasancewar yasan cewa akwai Babban aiki a gabansa, idan yarinyar ta amince da auren
sama Tofa bata sonsa, soyaiyar jini take masa,ba soyaiya ta masoyi da masoyiya ba

wani irin huci yayi yafitar da iska daga bakinsa,kwanciyar da baiyi ba kenan, ya wuce toilet duk
da safiya ce, ya d'auro alwala yafara kaiwa ubangiji kukansa.


Washe gari da safe Bayan sun gama break fast, compound suka fita buga ball, kowa yana Nan
banda Waheeda data tafi makaranta

Sun dad'e sunayi sannan suka koma ciki, abinci sukaci kowa yakama harkar gabansa, Babban
Yaya kuwa shirya wa yayi zaije wajan abokinsa mashkur, Wanda Dama can shine de abokinsa
guda daya, sun dad'e tare, hatta 6angaren sana'ah ma Shima mashkur ball yake bugawa, saide
kowa da Club d'insa, Amma duk a England suke rayuwar su, yana barin d'akinsa anan falo yaga
baqi maqota suna shigowa gidan nasu, Sai a lokacin Ummah take fad'a masa kayan lefen
Waheeda ne za'a kawo, ba qaramin kokari yayi ba wajan saita Kansa, daga qarshe yafice yabar
gidan, domin kuwa abubuwan qara ta6ar6are masa suke ���

Baidawo gidan ba saida yamma, a lokacin baqi Wanda sukazo aka kar6i Kaya dasu suntafi,
daga Sa'ad da Sa'eed Sai 'yanbiyu da Hajiya Anty da Ummah ne a falon, ga akwatunan Nan

agefe hajiya Anty tana duba kayan da aka zuba aciki, Sai kuma uwar gayya wato Waheeda
tana zaune kusa da Hajiya Anty tana shan tea da waya a hannun ta tana karanta saqon Huzaifa
Sai murmushi take, gabansa ne yafad'i, ganin da gaske de ankawo kayan lefen Nata, lokaci
d'aya ransa yayi baqiqqirin

Shigowa falon yayi duk da yanda yake ganin duhu-duhu kamar Idonsa yana son rufewa
�����領����儭?

Adede lokacin daya qaraso tsakiyar falon yaji hajiya Anty tana cewa "Hajiya yaushe zamu saka
rana akai na Naufal ne? Tunda sunbar mana komai a hannun mu ai yakamata mukai musu
kokuwa?"

Cikin sauri yayi hanyar d'akinsa, Babu Wanda ya lura da yanayin sa Sai hajiya Anty, ta Kalleshi
cikin tsananin mamaki, yashigo falo babu Wanda yayiwa magana Kuma ya wuce cikin d'akinsa
da wannan sauri haka,tasake juyawa ta kalli Waheeda, kanta ta jijjiga tareda cizon lips d'inta,
yau d'aya de yakamata ace tayi wani abu akan wad'anan 'ya'yan nata a matsayin ta na uwa
���(tofa)

Kallan Waheeda tasake yi, tana jin qaunarta acikin zuciyarta, koda wasa bata son abinda zai
ta6a lafiyarta balle yasaka ta cikin wani Hali, Amma Yaya zatayi.....?


Ahankali tatashi tabi Bayan Naufal, tana tura kofar 'Dakin tana shiga ta ganshi a tsaye yana
Kallan p.o.p din d'akin, Kansa ne yaji yasara lokaci d'aya jiri ya d'ebeshi zai fad'i, cikin sauri
hajiya Anty ta qarasa tatareshi yafad'o kanta

"subhanallah....Naufal lafiyarka kuwa?"


Idonsa ya runtse, yasaka hannu yadafe goshinsa, but kwata kwata yakasa magana, janyo shi
tayi ta kwantar dashi akan gadon, itama ta zauna sannan tad'ora Kansa akan cinyarta


Lallausar sumar Kansa take shafawa, saida taji yad'an nutsu sannan tasake tambayar sa
"meyake damunka?"

Hawaye ne yafuto daga idanunsa, mamaki yakama hajiya Anty, Naufal ne da Kuka yau? ��
Tun yana hawaye harya dawo yana kuka harda shashsheka,bata hanashi ba, rabuwa tayi dashi
bata hanashi ba, saida yayi me isarsa, sannan yayi shiru Sai Jan zuciya yake, ajiyar zuciya tayi
akaro na biyu tace "meyake damunka?"

Cikin rawar murya tamkar ba Babban Yaya ba, yace "Allah idan na rasata mutuwa zanyi....."

Gaban Hajiya Anty yayi wata irin fad'uwa, cikin sauri ta Kalleshi tace "what....? Wacece?"


Sai a lokacin Babban Yaya yatuna abinda yafad'a, hawaye ne yazubo masa, Sannan yace "Anty
ni bazan iya rayuwa da wadda banaso ba, bazan iya Zaman aure da'ita ba...."


Ajiyar zuciya tayi, Amma maganar sa ta farko Sai yawo take mata acikin qwaqwalwarta, karfa
tunaninta ya zama gaskiya.....idan hakan ta tabbata Yaya zasuyi da wannan tsohon al'amarin
da wannan Yaron yake son tado musu shi?

Kallan sa tayi tace "shine damuwar?"

Kasa magana yayi, Sai Kansa daya d'aga mata kawai
Tace "to shikkenan, zan samu ummanku muyi magana da'ita, ka kwantar da hankalin ka
banason wannan kukan"

Sake d'aga mata Kai yayi, Ajiyar zuciya tayi, sannan ta rungume shi sosai ajikinta, ta sunkuya
tayi kissing goshinsa, sannan tad'ora masa Kansa akan Fillo tafita daga d'akin

Tana futowa daga d'akin taga yaran basa Nan,Sai Ummah kad'ai tana kallo, godia tayi wa Allah
cikin ranta, sannan ta qarasa wajan ta tace "Yaya a Kwai matsala fa, nasamu yayansu yanzu,
maganar gaskiya baya son auren Nan har yanzu"


Cikin tsananin damuwa Ummah tadafe kanta �丹��領����儭?"nashiga ukuna,Yaya zanyi
da wannan Yaron ne, banaso Naga Naufal cikin damuwa, Bari inje in sameshi...." tafad'i haka
tana kokarin tashi

Cikin sauri hajiya Anty tace "Zauna Yaya, Wai meyasa bazaku zaunar da Yaron Nan yafad'a
muku wadda yake so ba?"

Ummah ta kalleta cikin damuwa tace "to inda zai fad'i wadda yakeso d'in ai zanji dad'i Nima....,
idan an tambayeshi fa cewa yake shi har yanzu babu wadda yakeso, ayi namiji baligi Amma
ace kullum babu wadda yakeso?"

Anty tace "to yanzu ya za'ayi?"

Cikin damuwa Ummah tace "tunda ke yafara sakewa dake har yana fad'a miki damuwar sa,
kifad'a masa zai iya qarawa da yarinyar dayake so d'in, yanzu su Alhaji sun Riga sunyi magana
tayaya zamu ce a banje wannan auren mu maida su qananan mutane?"

Hajiya Anty tace "Eh hakane Kuma, tunda yanada damar dazai iya qara auren shikkenan, Allah
ya tabbatar musu da Alkhairi, Allah ya basu Zaman lafiya Kuma"


Ummah ta jijjiga kanta kad'an, ba tareda tace komai ba.



Bayan kwana biyu aka shirya aka Kai lefen Babban Yaya,su Daddy sunyi magana da iyayen
kowa daga cikin su, Ummi dakuma Huzaifa, danhaka aka tsaida date din 'Daurin aure sati hud'u
masu zuwa���

Su kuma su Sa'ad da Sa'eed aka tsaida nasu bikin Bayan shekara d'aya ������

Yau duk suna zaune afalo gaba d'ayansu,yana jin yanda intisar take cewa "akai musu wannan
uban kayan Amma abada tukwicin dubu ashirin?"��

Ihsan tace "ai sai kiyi tayi, kanki akeji, tunda sude bazasu qara komai ba, ni dazu danahau
Instagram ma kayan nagani anata turawa, mutane Sai cewa suke anyi almubazzaranci dayawa,
Kuma nasan Yan gidan sune suka saka kayan a internet"

Babban Yaya Ko Kallan su baiyi ba,bare ya tanka, yasan suna magana ne akan 'Yan gidansu
ummi, wayarsa ce ahannunsa yana Kallan pictures din Waheeda, wasu tun tana zama, wani
Kuma ahannunsa take yana bata fida tana Sha, wani Kuma tana cikin baho yana mata wanka,
wani Kuma yad'agata sama yana kissing Kumatunta, a lokacin tafuto daga d'akinsu wayar
Ummah tana hannunta, Kai tsaye wajan sa ta nufa ta zauna, yana ganin ta yayi saurin rufe
wayarsa kartaga abinda yake Gani, wayar Ummah ce tasake qara, cikin 6acin rai ta dauka tace
"Wai Dan Allah Didat mekake so nama? Nafad'ama gaskiya kadena kirana anriga ankawo
kayan aure na"

Daga d'ayan bangaren Didat yace "wallahi Waheeda idan kika kuskura kika auri wani baniba
wallahi saikin kashe auren kin futo kin aure ni...."

Cikin 6acin rai tace "au haka kace?"

"eh haka nace, Dan renin hankali kince min Inturo iyayena baki tsaya kinji abinda zan fad'a miki
ba kawai saiki cemin yanzu ankawo miki kayan aure.... A a, sadaki aka kawo miki ba Kaya ba,
wallahi idan kika yarda aka miki aure da wanina dagani harke Sai ran kowa ya6abaci "
Dif... Yakashe wayarsa


Waheeda tasaki tsaki ba tareda tace komai ba, tajuya ta kalli Babban Yaya har zata masa

magana saitaga ya daure fuska, dolenta taja bakinta tayi shiru ���


Da daddare abokinsa mashkur yazo,zaune suke akan had'ad'd'iyar motar Mashkur din, wadda
yayi parking dinta a compound din gidan, mashkur 'Dan Gayu ne na gaske, akwai d'aukar
wanka tamkar Babban Yaya, Ihsan ce ta kawo musu lemuka ta ajiye akan 'Dan qaramin wani
dinning table dake gabansu,ta gaida mashkur sannan tajuya, har tayi Nisa Idonsa yana kanta,
bata dad'e da tafiya ba intisar takawo musu cups, cikin mamaki ya kalleta yace "kaiii, Wai daga
shigar ki har kika sauya Kaya kika futo?"��

Murmushi tayi tace "a a, Bani bace, Ihsan ce dazun"

Murmushi yayi tareda shafa qeyarsa,intisar tajuya tatafi, mashkur ya dubi Babban Yaya yace
"tsakani da Allah kunada wannan kyawawan yanmatan Amma kabarni Ina shan wahalar neman
matar Aure? Gaskiya Allah yamuku kyau Abokina, Wannan kyanta ace zan'iya had'asu duk su
biyun, da lokaci d'aya zanyi wuf dasu"
Babban Yaya ya Kalle shi yace "banason is'kanci mashkur...."

Mashkur ya d'auki lemo guda d'aya ya tsiyaya acikin cup sannan yace "to na tambaye ka
meyakamata mu tsara na bikin kaqi cewa komai, to bagara inyi abinda ya shafeni ba, Kai
kasamu matar ne shiyasa kake mana is'kanci, nikuwa Sai yanzu nagani, Dan Allah Bro wannan
ta farkon datazo, Ina ciki...."
Babban Yaya yayi ajiyar zuciya, cikin ransa yafara godewa Allah daba Waheeda ce takawo
musu lemon ba �不
Yatsani yaji wani namijin yana cewa yana sonta

Ya kalli mashkur yace"ni bazaka Jamin raini awajansu ba, kamusu magana da kanka, sannan
babu abinda zamu tsara, ayi bikin haka, mashkur inaji araina matsawar narasa yarinyar danake
so, to wallahi mutuwa zanyi...."

Mashkur dayakai cup din lemo bakinsa cikin sauri yafasa Sha ya ajiye, sannan ya Kalle shi da
mamaki yace"kasan mekake fad'a kuwa Naufal?"

"yes, bazan iya daina sonta ba"

Mashkur yace "wacce me sa'ar ce wannan? Why not kafad'a mata? Mekake jira?"

Babban Yaya yace "lokaci yaqure min mashkur, bazan iya fad'a mata ba, Amma wani bangaren
inaji ajikina ita d'in tawa ce"

Cikin sanyin jiki mashkur ya bubbuga kafad'arsa, yace "kayi hakuri Abokina, yanzu meka yanke
akan hakan? Wanne irin mataki ka d'auka?"

Cikin damuwa yace "band'auki kowanne mataki ba, kawai Ina addu'ah de..."

"no, hakan ai yayi kad'an Friend, saura sati hud'u bikinka fa, kamata yayi mushirya muje
Saudia, Nima zan tayaka da addu'ah Allah yabaka za6inka, idan har zai kasance alkhairi
agareka, idan Kuma ba alkhairi bane Allah yabaka haquri da juriya akan rashinta "


Ransa duk adagule ya kalli mashkur yace "mashkur lokaci yariga yaquremin.... Itama aure
zatayi, tayaya za'a fasa dawani ayi Dani? Tayaya zan rabu da wannan nacacciyar yarinyar
ummi? Wallahi haushin ta nakeji, idan ta kuskura ta aure ni ko.... Wallahi saina mata filla-filla
aranar da aka kawota kuma da niyya"

Mashkur ya kwashe da wata irin dariya sannan yace "Abokina bakada Dama wallahi, kadena
wannan tunanin, kasa aranka zaka yarda da qaddara mekyau ko marar kyau, sannan karka
manta komai yayi zafi maganin sa Allah, a lokacin daka shiga cikin matsala kadinga tunawa
cewa akwai Allah.... Saboda haka yanzu ma shi zamu kaiwa kukan mu, me muke yanzu a
qasar? Mushirya gobe mutafi Saudia, daga Nan kawai muwuce England.... "


Sai a lokacin Babban Yaya yasaki wata irin ajiyar zuciya, yace
" nagode Friend"

cikin farinciki suka rungume juna




Washe gari karfe goma a compound tayiwa Babban Yaya, sunyi waya da mashkur zasu had'u a
Airport, Waheeda da Yanbiyu ne suka rakoshi har wajan motar dazai shiga, wayar Ummah tana
hannun Waheeda, Huzaifa ne ya kirata cikin murna ta d'auka tafara masa magana Sai wani
kashe murya take.... Babban Yaya yabude motar zai shiga ya kalleta yace "mahaukaciya..." �



Yanbiyu sunji abinda yace, sunsan cewa akusa yake, danhaka sukai murmushi suka juya ciki

Waheeda ta katse wayar sannan ta Kalle shi tace "Babban Yaya mekace?"

Cikin 6acin rai yace "bansani ba"

Jikinta ne yayi Sanyi, ta qarasa wajan sa tace "nayi laifi ne Babban Yaya? Kayi hakuri...."

Fasa shiga motar yayi, yafuto tareda d'ora hannun sa akan murfin motar, cikin masifa yace "au
tambaya tama kike me kikayi? Kullum kina liqewa mutum saikace kaska, kwata kwata baki iya
Jan aji ba, to Bari kiji, namiji tsanar mace me naci yake, marar aikin yi kawai..."

Kukane yakama Waheeda, ita tarasa meta masa tun ranar da aka kawo lefen ta yake daure
mata fuska,komai tayi saiya dinga Jin haushinta, bata iya haqura ba saida ta rushe da Kuka
Sannan tayi cikin gidan da gudu

Tsaki yasaki yanajin haushin zuciyar sa Kuma, Dan me zaisa Waheeda kuka? �不Yanzu haka
kukan ma ya haddasa mata ciwon Kai, wani tsakin yasake saki, yarufe motar zaibi Bayan ta,
domin yabata haquri

"Salamu Alaikum"

Juyawa yayi yaga meyi masa sallama, budurwa ce Babba, wankan tarwad'a, tanada tsayi
had'eda jiki, saide babu alamun kyau atare da'ita, hannunta d'aukeda wani flask d'in
abinci,Kallan rashin Sani yayi mata, beyi mata magana ba yajuya zaiyi cikin gida

Cikin sauri Tariqo rigarsa tace "Husband baka ganni bane?"

Cak! Yaja ya tsaya a'inda yake, sannan ya Juyo cikin nutsuwa yacire hannunta data riqe masa
Riga, ya kalli idonta yace "Dama kece?"

Ummi tayi farrrr da idonta, cikin yanga tace "nice, meyafaru ne Naga kamar kana cikin 6acin
rai? To kayi hakuri ga girkina nakawo ma da hannu na nayishi, idan Kaci zakaji dadi"


Cikin tsananin 6acin rai yanunata da hannu yace "Ummi!!!, kidena damuna, kidena shiga cikin
rayuwa ta, waike Ana so dole ne? Sau nawa zan fad'a miki Bana ra'ayin ki? Ba girki ba, ko
kanki Zaki Bani bazanyi ra'ayin ki ba"


Cikin rashin kunya tace "qarya kake wallahi, Kai d'in wa? Dazaka dinga fadamin baqar magana,
cemaka akai ni dinma sonka nake? Inaso na aure ka ne saboda duniya tasan cewa eh Nima na
auri mashahurin mutum, Naga alama bakasan darajar mace ba, Amma duk lokacin daka aureni
saina koyama yanda ake...... "

Cikin 6acin rai yakai hannu zai wanketa da Mari tareda wata irin tsawa yace"Ummi!!!"

Tsananin tsoro ummi ta tsorata da yana yinsa,jikinta ya d'auki rawa batasan lokacin da flask din
hannunta yafad'i qasa ba, jallop rice din ciki ta zube���


Idanunsa harsun sauya Kala sun koma ja saboda 6acin rai, cikin sauri Hajiya Anty taqaraso
wajan su tariqe hannunsa, shigowarta kenan gidan, ta tarar da wannan drama, cikin 6acin rai ta
Kalle shi tace "Duka Kuma Naufal....?"

Yanda yaji tafad'i kalmar duka d'in kamar zatayi kuka duk Sai jikinsa yayi Sanyi, Amma sai huci
yake, tunda yake ba'a ta6a yimasa rashin kunya kamar yanda ummi tamasa ba yau, Hajiya Anty
ta maida Kallan ta wajan Ummi tace "kiyi hakuri, d'auki flask d'inki kitafi"

Ummi ta tsugunna ta d'auka, sannan ta d'ago ta kalli Hajiya Anty sannan tasakar mata tsaki, ta
wuce tabar gidan

Babban Yaya yana ganin abinda Ummi tayiwa Hajiya Anty yabi Bayan ta zai damqo ta, Hajiya
Anty ganin yabi Bayan ummi tasan tsaf zai lakad'a mata duka, Dan haka cikin sauri ta ruqoshi,
tace "karabu da'ita nace"

"Amma Anty... Kina.... Kina ganin abinda tamiki fa..."
Yafad'i maganar a rarrabe cikeda qunan rai


Murmushi tayi tace "naji, karabu da'ita"

Jijjiga Kansa yayi, sannan yashiga motar sa yamata key yabar gidan,wajan Waheedan ma fasa
zuwa yayi ��




���������
1/28/22, 20:51 - Ummi Tandama���: QN




Kwanan su uku a Saudia suna gudanar da addu'ah shida mashkur, gaba d'aya kashe
wayoyinsu sukayi, ibada kawai suka sa agaba,Sai akwana na hudun ne sannan suka koma
England.

Kwanansu hud'u da komawa England yakira wayar Hajiya Anty, Bayan sun gaisa yace "Anty kiyi
hakuri akan abinda yarinyar Nan tamiki, na lura kwata kwata batada kunya...... Sannan duk
laifin ku ne dakuka liqa min ita"

Murmushi tayi "son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login