Showing 18001 words to 21000 words out of 82824 words
Chapter 7 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf
shiga mota yajuyo ya kalleta yace "Sunanta kenan?"
Tace "Yes, Maryam Ahmad, Yusuf Amin, shine muke ce mata Maya"
Kafin Yayi magana ta qaraso, cikin murna ta rungume Waheeda, tasake ta ta gaida Babban
Yaya cikin ladabi, Nan da Nan yayaba da Hankalin yarinyar, yasan idan Waheeda tana tareda
ita, zata qara Hankali, amasawa yayi yace "kudinga karatu sosai"
Dariya takama Waheeda Amma saita danne, Wai kudinga karatu sosai, wannan shine fadan da
akewa dalibai, Maya tace masa "insha Allah Babban Yaya"
Ta kalli Waheeda tace "Waheeda zan tafi gida, Sai wani lokacin"
Waheeda tace "Naga ba'a tashi ba, meyasa Zaki tafi?"
Idanunta ne suka kawo ruwa tace "Waheeda kudin School fee's ne baba bai kawo ba, shine
sukai kora"
Tausayinta yakama Waheeda, tasan Maya da naci akan karatu, tanason karatu sosai, cikin
sanyin jiki tace "kiyi hakuri Maya karkiyi kuka"
Babban Yaya yata6e bakinsa tareda ajiyar zuciya, Yara qanana suna wani Iyayi saika ce Wanda
suka San ciwon kansu �不
Motarsa yabude ya Dauko kudi dami biyu yan dubu dubu, aqalla zasu Kai kusan dubu Dari biyu,
yabawa Waheeda yace "kibata"
Daga Nan yashige mota tareda ficewa daga makarantar
Maya ta kalli Waheeda suka rungume juna cikeda murna, daga Nan suka tafi Class dinsu
Tafiya yake amota yanaso yaje gidan hajiya Anty tun kafin ta masa qorafi baya zuwa, wayarsa
ce yaji tana ringing, dauka yayi tareda karawa a kunnansa, daga d'ayan ban6aren principal
yace "Kayi hakuri yalla6ai, abun baikai da Sai ansako hukuma aciki ba, insha Allah zansa Akira
yaran a yimusu hukunci daidai da abunda suka aikata, sannan dole iyayensu zasu San abunda
suke aikata wa, ni bazasu 6atamin makaranta taba"
Babban yace "Yarage Naka, Amma muddin baka dauki mataki akan yaran nan ba, to zaka
ganni a cikin makarantar ka" yana fada masa haka yakashe wayarsa
Wata wayar ce tasake shigo wa, yayi tunanin principal ne yasake kiransa, cikin masifa ya daga
yace "Wai ya akayi ne Kuma?"
Daga d'ayan bangaren akace "babu abinda akayi Saide wadda za'ayi yanzu, Naga alama baka
gane me magana ba, to Abubakar ne yayan mahaifin ka Umaru" ���
Babban Yaya yadafe Kansa, ya tsaida motar agefe titi yace "Baba Ina kwana?"
"daban kwanaba zaka ganni ne Naufal balle harna kiraka awaya?"
Babban Yaya yace "kayi hakuri baba"
Baba Habu yace "Magana nakeso muyi dakai ta fahimta, nasan idan ka 6oyewa iyayenka Toni
bazata 6oyemin ba, tunda nasan cewa akwai alkunya tsakanin d'a da mahaifi, Naufal kafadamin
gaskiya idan kasan bakada lafiya munan damuke qauye akwai sassaqe yana Nan Kala Kala
saina had'o Maka shi na aiko kafara gwadawa ko za'a dace "���
Girarsa guda d'aya ya Sosa da key din Motarsa , yace"Baba lafiya ta kalau"
"to idan lafiyarka kalau meyasa kake gudun aure?"
"Akwai wacce nakeso Baba"
Yafadi hakan Kansa tsaye
Baba Habu yace "to Alhamdulillah, masha Allah, to kokai fa, a'ina yarinyar take? Yar wanne
Gari ce?"
Shiru yayi, yakasa Bawa yayan mahaifin nasa amsa, Sai can yace masa "Baba Nima bansan
inda take ba"
Cikin masifa Baba Habu yace "zancen banza zancen wofi, wannan ai shirme ne, tunda haka
kake so ai shikkenan, ka shirya kaje kaga Nadiya yar gidan abokin uncle dinka Usman, Usman
yacemin yarinya Tariga tasanka, saboda haka Sai kaje kaganta kaima" dif yakashe wayarsa,
yabar Babban Yaya da waya Akunne
To koyaya zata Kaya tsakanin sa da Nadiya?
Masoyan BABBAN YAYA Ina godia sosai, nayi tunanin bazaku sayi littafin ba �對��對�
Amma abun mamaki tun kafin free page yaqare masu turo 400 sunfi masu 200 yawa, nagode
Allah yabar zumunci
Amnah El Yaqoub ����?
Amnah El Yaqoub ����?
1/28/22, 20:49 - Ummi Tandama���: BABBAN YAYA
Writing By Amnah El Yaqoub
Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/
9&10
Bakomai ne ya tsaya masa Arai ba Sai yanda yace yarinyar tariga tasan shi, hakan yana nufin
idan yaje zata soshi tunda Dama tariga tasan shi, shine bai Santa ba, duk yanmatan da ake
had'ashi dasu babu wadda ta sanshi, koda sun ganshi ma baya fadar sunan da aka sanshi
dashi saide yace musu sunan sa Naufal, Amma ita wannan ta wacce hanya zaibi yarabu da'ita?
Bashida burin auren mace biyu, kamar yanda ya tashi yagani a gidansu Ummansu ita kadai ce,
Hajiya Anty ma ita kadai ce, to ita da bata haihuwa ma mijinta yayi hakuri ya zauna da'ita, to
shida ba mazauni ba tayaya zaiyi ta aurar 'ya'yan mutane yana tafiya harkar qwallo?
Ajiyar zuciya ya sauke, yanufi gidan Hajiya Anty, gidan yayi kyau sosai,tsarin gidan komai da
komai irinna Ummah ne, saide furnitures dinne kawai suka banbanta
Tana Sanye cikin atamfa, tariqo mayafin a hannunta, wuyanta da yatsun hannunta duk sunsha
gold,tayi kyau sosai abinka da mace yar Gayu, Car key ne a hannunta tana kokarin fita sukaci
Karo da Babban Yaya, tace "A a, yaushe agari?"
Bai bata amsa ba Sai kokarin shigo wa falon da yake, bayansa tabiyo suka dawo falon suka
zauna, Kallan ta yayi yace "Anty fita zakiyi ne?"
"eh zan fita, akwai meeting din da zamuyi karfe daya"
Ajiyar zuciya yayi "ke Anty babu ruwanki bakida damuwar komai"���
"Kai din damuwar menene a ranka?"
Goshinsa ya dafa yace "gatanan dayawa Anty, yau matsalar Waheeda gobe matsalar ku"
Dariya tayi tace "To Waheeda matsalar ta ai takace, kaida ita ai qawaye ne, Kuma inda Sabo
kun saba, qanwar kace babu yanda zakayi da'ita, mukuma tamu matsalar ai bazaka kirata da
matsala ba, tunda mune akan gaskiya, Naufal har wanne lokaci zaka dauka babu aure? Ko so
kake Sai yanbiyu maza sunyi aure sannan zakayi? Maryam fa tayi aure harda takwara anyi
Maka, kaikuma gaka Nan gemai gemai dakai babu aure "
"Anty shi aure lokaci ne"
yafadi hakan cikin damuwa
Tace "Hakane, Allah ya nuna mana Naka lokacin, yaushe kazo qasar?"
"jiya nazo Anty, nazo na maida Waheeda school, sannan Baba Habu yamin waya naje Naga yar
abokin Uncle, Wai Nadiya"
"aiya wuce 'Wai' Naufal, Nima nasan yarinyar tun tana qarama, nasan wannan Karan insha
Allah baza'a samu matsala ba, mun kusa shan biki" ta qarasa maganar cikin murmushi
Ajiyar zuciya yayi yace "Anty kenan, ni yanzu babu wacce nakeso, Kuma bazan iya auren
yarinyar da banaso ba, maganar gaskiya kenan, idan kema kin gaji da ganina haka saiki Bani
'yarki" (tofa)
Kallan sa tayi, jikinta yayi Sanyi, hannun sa takama ta riqe tace "inda ace na Haifa ai zan baka
Naufal, ka daure kaje kaga Nadiya, insha Allah zata Maka"
Yace "to Anty insha Allah anjima da yamma zanje"
Tare suka futo daga gidan, saida yaga tashiga motar ta tafita, sannan ya qarasa wajan Maigadin
gidan, sallama yayi masa, Baba yusha'u yace "Yalla6ai ko akwai abinda kake buqata?"
"kayanka nakeso kabani Baba, zanyi amfani dasu"
"kayana Kuma Yalla6ai,kaida kanka? lafiya dai ko?"
Murmushi yayi yace "karka damu baba, nine zanyi amfani dashi, kahada mun harda wayar ka"
Jiki na rawa Baba yusha'u ya 'Dauko masa kayan, tareda wayar "
Ya kalli kayan yaga sunyi yanda yakeso, sannan ya kalli Baba yusha'u yace" Baba wannan
wayar ai kalau take, babu wadda tafita tsufa? "
Baba yusha'u yace" eto, saide wata tsohuwar wayata data lalace idan aka kirani banaji Kuma
ba'a Jina, Kuma murfin wayar baya zama da kyauro nasa nariqeta, kafin hajiya ta sauya min
wannan "�不
Babban Yaya yace
"yawwa, Bani ita"
Baba yusha'u ya Dauko yabashi, yakar6i kayan yajuya yashiga motarsa sannan yabar gidan
Kai tsaye Gida yakoma, yabar kayan acikin motarsa, yanbiyu da Waheeda suna falo sunacin
abinci, Ummah tayi masa sannu da zuwa tana Bawa yanbiyu magani, zama yayi a kujerar yace
"Ummah wace ba lafiya Kuma?"
Yanbiyu ta nuna masa tace "gasunan, kasan halin jinyarsu ai, idan daya tafara dayar ma
Saitayi, Wai cikin su ne yake ciwo"
"ok Allah yasawaqe"
Ya kalli Waheeda yace "ki gama nakai ki islamiya tunda su babu lafiya"
Ranta ne ya6aci cikin shagwa6a tace "to Babban Yaya subazasujeba saini kadai? Lafiyarsu
kalau wallahi, tsabar sharri ne kawai"
Wani irin kallo yamata, Nan take tayi shiru ko qwaqwqwaran motsi bata sake yiba
Dinning ya nufa da Kansa, yazuba abincin yanaci yana Kallan TV sama sama, har Waheeda
tagama taje daki tafuto cikin shirin islamiya, ta kalli Ummah tace "Ummah zan tafi, saimu dawo
tareda Maya, tunda yanbiyu bazasuje ba yau"
Ummah tace "saikun dawo"
Tashi yayi zai fita, ya kalli Ummah yace "Ummah naje gidansu Nadiya"
Murmushi Ummah tayi tace "Aida kabari Sai gobe, yanzu Naga alamun Garin akwai hadari,
Amma idan kaje gobe zakufi sakewa ku Tattauna"
Yace "no,Ummah zanyi sauri naje insha Allah"
Cikin farinciki tace "to a dawo lafiya, ka kula da kanka"
Waheeda tace "to Ummah karki damu Nima zan kula dashi"
Ummah tace "Allah ya shiryeki Waheeda"
Waheeda tashiga gidan gaba taja murfin motar tarufe, tajuyo taga Babban Yaya yana Kallan ta,
idanunta tajuya tace "Babban Yaya lafiya?"
"meyasa kikasa Ribom a kanki?"
Dariya tayi tace "laaa Babban Yaya bafa Ribom bane"
Muryarsa ya rage kamar yana tsoron wani yaji sannan yace "qarya kike yi, to mugani"
Hannu tasa tajanye hijabin daga kanta, dogon gashinta Mai tsantsi ya baiyana, ta dago tana
Kallan sa tace "kagani?"
Ahankali yakai hannunsa kan gashi Nata, ya gyara matashi, sannan yace "nagani, mayarda
hijabin"
Kallansa tayi tace "Babban Yaya idan baka so nadinga acuci da gashina kabani kudin kitso"
Kafadarsa yadaga yace "no, karkiyi kitso, kibarshi haka yafi"
Babu musu tace masa "to, mutafi karna makara"
Gyara zama yayi yace "kinsan de Banason aure yanzu ko?"
Mamaki yakama Waheeda, takasa magana saita gyada masa Kai kawai, ajiyar zuciya ya sauke,
yakai hannun sa Mai laushi yakamo Nata hannayen yace "su Baba Habu sun hadani da wata
yarinya Nadiya, idan na saukeki a islamiya wajan ta zanje yanzu, inaso na gwada sa'a ta ko
Allah zaisa narabu da'ita"
Waheeda ta kalli qwayar idonsa, tana so ta tambayeshi abinda yadade Yana yawo a ranta,
Amma tana tsoro karya mata fada, dakewa tayi, tayi jarumtar cewa "to Babban Yaya meyasa
baka son auren? Sune baka so kokuma auren ne duka baka so?"
Kai tsaye yace "sune banaso"
Cikin mamaki tace "towa kake so?"
Kallan manyan idanunta yayi yakasa bata amsa, Waheeda taga Sai Kallan ta yake tace
"Babban Yaya kayi shiru kana kallona"
Hannunta yasake riqewa cikin nasa hannayen yace "Aike qanwata ce, damuke uwa daya uba
daya hakane ko?"
Waheeda ta gyad'a masa kanta alamun hakane
Yaci gaba da fadin "tunda ke qanwata ce, ke jini nace, idan kika kalli qwayar idona, zakiga
yarinyar danake so" (tofa)
Matsowa tayi kusa dashi haryana jin saukar nunfashin ta akan fuskar sa, tazuba masa ido tana
so ta tabbatar da maganar sa, Sai can tadawo ta zauna yanda take da, tace "banga komai ba
Babban Yaya banda baqi dayake cikin fari na idonka" ���
Murmushi yayi dimple dinsa suka futo, yace "naji, wannan maganar tazama sirri tsakanin mu,
banaso kowa yaji, sannan baqin gawayi nakeso kisamomin acikin gida yanzu"
��訣aro ido tayi tareda rufe bakinta da hannunta tace "nashiga uku Babban Yaya qona
Nadiyar Zakayi idan kaje?"
"banason shirme Dan Allah, amfani zanyi dashi, guda daya nakeso kisamomin"
Tunani tafara saida tagama ta Kalle shi tace "Babban Yaya ai kasan Bama qona gawayi, Amma
Naga Ummah tanada wani na leda Wanda take sakawa akan gas idan yayi zafi saita saka
turaren wuta, saide inje in Dauko mashi, Amma idan kaji tana jaje karkace nice"
Yace "nida kika kawo min tayaya zan fada? Yi sauri kije ki dauko"
Cikin sauri tafice daga motar tashiga falon da gudu, taje Dakin Ummah Allah yaso tana toilet,
tayi sauri ta dauko ledar gawayin guda daya, ta6oye acikin hijab,ta kawo tamiqa masa tace
"gashi"
Cikin mamaki tasake Kallan sa tace "Laaaa Babban Yaya yanaga ka sauya Kaya kasaka
wannan tsumman? Cemata zakayi Kai mahaukaci ne?" ������
Kallan ta yayi yace "saide in kece mahaukaciya" ya dauki gawayin guda daya yarabashi abiyu,
yafara shafawa a fuskar sa da hannun sa, ya dauki wani rawani ya nada a Kansa,yacire agogon
hannun sa, yanda yayi baqi ba zakace shine ba, Waheeda tayi shiru tana Kallan ikon Allah,
saida yagama 6oye kamar sa sannan yaja motar suka tafi, agaban islamiyar ya faka motar yaqi
fita, saida ta Kalle shi tayi murmushi sannan tayi masa bye bye tafice daga motar
Gidansu Nadiya ya nufa
Kafin ya qarasa ya tsaya yafaka motarsa acan nesa da gidan, sannan yafuto yatare wani Dan
adedeta yace "Aron Napep din nake nakeso"
Dan adedeta ya kalli adedetan sa Sabo fil dashi, sannan ya kalli Babban Yaya yace "kamarya
aro?, malam bansan kaba tayaya zan dauki sabon adedeta na nabaka?"
Babban Yaya yace "kaga mota na Nan, ka tsaya anan kajirani yanzu zan dawo"
Dariya Dan sahun yayi yace "hauka nake zan yarda dakai? Tayaya zaka mallaki wannan motar?
In hakane meyasa zaka nemi Aron abun Hawa?"
Kansa yadafe, ya nufi motar ya Dauko agogonsa yabashi yace "yanzu kaga shaida mota tace ai
ko? Kariqe wannan agogon idan ban dawo ba kaje ka saida shi zai iya siya Maka sabon
adedeta harda Yan canji"
Dan adedeta yayi shiru yana nazari, badan ransa ya soba yafuto yabawa Babban Yaya, Nan da
Nan Babban Yaya yahau yatuqa da bissmillah aikuwa adedeta yafara tafiya, baiyi gudu ba
ahankali yake tafiya harya qarasa gidan, yana zuwa yahango wata budurwa tana tsaye dawani
saurayi me mota, motar ya kalla ya kalli wayar hannun sa, wayar hannun sa kadai zata Iya
siyan motar gayen, cikin sauri yakashe ta, yasaka acikin aljihu, sannan yafuto daga adedetan
nasa ya tsaya yana Kallan su yana daddanna wayar baba Yusha'u megadi wadda taji wahala
harda kyauro ajikinta
Kallan sa budurwar tayi suka kwashe da dariya itada saurayin, Babban Yaya ya qarasa wajan
su tareda Bawa saurayin hannu yace "Salamu Alaikum"
Saurayin ya Kalle shi daga sama har qasa yaga wani fatattakekken takalmi aqafarsa, yaga
fuskar Nan tayi wani irin baqi, ya girgiza Kai tareda dauke Kansa, budurwar ta Kalli saurayin
suka hada ido suka sake kwashewa da dariya
Babban Yaya yasosa girarsa guda daya da key din adedeta dayake hannun sa, abunda yariga
ya zama dabi'arsa
Ya kalli Budurwar
Yace "Dan Allah Ina neman Nadiya ne"
Tace "nice Nadiya, ya akayi?"
Kai tsaye yace "Ina son magana dake"
Yatsina fuska tayi tace masa "me?"
Saurayin Nata yace "a a Beby, jeki kiji abinda yazo dashi, kika Sani ko neman sadaka yake?"
Babban Yaya baice dashi komai ba yajuya yakoma jikin adedetan sa,Nadiya ta biyo bayansa
tana mamaki gashi talaka futuk daga Gani Amma yanayin tafiyarsa kamar ta manyan masu
kudi, suna zuwa jikin adedetan ya kalleta yace"Nadiya inason ki, idan bazaki damu ba inaso mu
qulla alaqa dake, alaqa ta har abada,Amma ni banida kudi, talaka ne ni idan har kina sona
tsakanin ki da Allah, ni banida matsala, bazan 6oye miki komai ba, gidanmu munada yawa
kusan mu talatin ne, sannan Mahaifiyata batada lafiya, Paralyze take yi, aikinsan Paralyze ko?
"��喫�����領����儭���?
Nadiya ta jinjina masa Kai tana jin wannan labari nasa,inbanda rainin Hankali meyake nufi da
mahaifiyarsa babu lafiya? Tsayuwa ta gyara tace"kana nufin nice zanyi jinyar mahaifiyar ka
kenan idan ka kaini gidanka? Sannan acikin mutum talatin din zanyi rayuwa?"
Babban Yaya yace "Allah yamiki Albarka, nasan tunda kinada Hankali Zaki kula da Mahaifiyata,
sannan kinga wannan adedetan?" yafadi haka yana buga jikin adedetan���
Nadiya ta daga masa Kai tace "Nagani"
Yaci gaba da fadin "to sojan hayane, banawa bane, kudin nake Tarawa idan suka cika dubu
Dari shida saina Bawa meshi, kinga shikkenan daga Nan yazama nawa" ������
Nadiya tasake jijjiga Kai tace "cigaba Ina jinka"
Babban Yaya yace "idan kika amince Dani, ba zakiyi DANA SANI ba
(My First Novel DANA SANI)
tun lokacin Dana fara ganinki naji duk duniya babu wadda nakeso saike, insha Allah namiki
alqawari idan kika amince Dani, ba zakiyi nadama ba, saboda zan hada miki lefe nagani
nafada, Sai Wanda yagani, sannan Kuma.... "
Kafin yaci gaba da magana Nadiya ta daga masa hannu ����裨ace" dakata malam, nayi
ma kama da wadda zatayi jinyar mahaifiyar ka?,konayi ma kama da wadda zata auri Dan
adedeta? Bari kaji, ni matar manya ce, akwai Wanda nakeso, Big Brother yana Nan zuwa, kar
yazo yaganni dakai ya raina min Hankali, danhaka Sai anjima... " tajuya tayi gaba, Babban Yaya yafara kiranta yana fadin "Nadiya! Nadiya!!"
Amma tayi banza dashi,Shima Dama Kiran Nata dayake qarfin Hali ne kawai, dama baya so
tajuyo ���
Babu musu yashiga cikin adedetan yatafi, yana zuwa wajan Dan adedetan ya futo yabashi key
dinsa yace "nagode gashi"
Dan adedeta yace "Wai harka gama? Naga ko Minti talatin bakayi ba"
Motar sa yabude yashiga yace "nagode"
Cikin sauri Dan adedeta yace "toga agogon Naka"
Babban Yaya yace "Kabarshi kawai" yarufe motarsa yatafi,saboda hadari ne yake San tasowa,
Kuma yanaso yaje ya Dauko su Waheeda a islamiya
*** ** ***
Tafiya suke ahankali suna zancen su gwanin sha'awa, Maya tace "Waheeda ki dinga sauri
mana, ko bakya ganin hadari"
"ke barni inyi tafiya ta yanda nakeso, idan sauri nakema jikina ya dinga rawa kenan, nikuma
banason wannan rawar"
Maya ta kwashe da dariya tace "su Waheeda manyan