Showing 63001 words to 66000 words out of 82824 words
Chapter 22 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf
har abada bazata iya neman saki awajena ba, saboda tana
amfani da ilmin ta, ga takardar ki Nan" ya ajiye mata takardar yajuya zai fita
Ihu tasaka tace "wallahi ban saku ba, babu wadda zaka aura, wallahi bazan bud'e wannan
takardar ba garama kazo ka d'auke abarka, Allah ban saku ba...." kuka take sosai tana fad'a
masa hakan
Juyowa yayi ya kalleta yace "to idan kin gama kukan ki kulle min gidan,kitafi gidanku, Nima
natafi wajan masoya yi ta"
Yana fad'ar haka yafice daga falon yanata dariya, be koma gidan Ummah ba, Kai tsaye gidan
Hajiya Anty ya wuce
** *** **
Cikin kuka takira Uncle Usman, yana zaune a office d'in Daddy yayi tunanin Intisar ce saboda
number ta yagani, d'auka yayi tareda sallama, saiyaji shiru da alama kuka ake, zamansa ya
gyara yace "Intisar meyake faruwa? Lafiya kike kuka?"
Cikin shashshekar kuka tace "Ba inti bace.... Wa... Wahee.... Waheeda ce, Uncle Babban Yaya
ne yasakeni, gashinan yabani takarda ta...."
Uncle Usman yatashi tsaye cikin tashin Hankali yace "innalillahi wa inna ilaihirraji'un....,
innalillahi wa inna ilaihirraji'un....,kina Ina yanzun?"
"Ina gidansa" cewar Waheeda cikin Jan zuciya
Uncle yace "Kije gidan gamu Nan zuwa"
Daddy ya Kalleshi yace "meyake faruwa?"
Cikin damuwa uncle Usman yace "Wai Naufal ne yasake ta"
Gaban Daddy yafad'i, yace "what?! muje gidan, bari in kirashi, muje muje da sauri"
Cikin hanzari suka fita ko office d'in basu rufeba
Suna hanya Uncle Usman yakira Babban Yaya, yana d'auka ko amsa sallamarsa baiyi ba
yafara magana cikin fad'a "ashe bakada Hankali?" ��������領����儭?
Babban Yaya dayake kwance a cinyar Hajiya Anty yace yatashi da sauri yace "Innalillah....
Uncle me nayi?"
Cikin fad'a Uncle Usman yace "nikake tambaya me kayi? To duk abinda kake kabari kazo
gidanku ka sameni yanzu yanzun Nan"
Babban Yaya yayi shiru bece komai ba, Uncle Usman yakashe waya, Daddy yace "dabaka
kirashi ba Usman, na tabbatar laifi tayi masa shiyasa yakawo qarshan Zaman nasu, shiyasa
Nima ban kirashi ba, koma menene muje gidan zamuji komai ai"
Uncle Usman yayi shiru Sai hura hanci yake,tunanin irin yanda zai 6atawa Babban Yaya rai
yake, tayaya za'ai yasaki yarinya yamaidata qaramar bazawara?
Babban Yaya yamiqe tsaye yace "Anty zanje gida, uncle yana nemana, da alama nayi masa laifi
bansani ba"
Cikin damuwa Anty ta d'auki wayarta tace "A a, me zakayi wa Uncle d'inka? Kaide kayi tunani
me kayi masa?, kokuma inkirashi? "
Kwata kwata Babban Yaya ya manta da batun Waheeda, asalima tunani yake irin dad'in da zaiji
idan yakoma gidan, saboda yasan idan ta bud'e takardar daya bata taga abinda yake ciki zataji
dad'i Kuma yau zasuyi kwanan farinciki, saboda haka baya tunanin wannan Kiran yanada alaqa
da Waheeda
Girgiza Kansa yayi yace "karki kirashi, nasan banyi masa komai ba, Bari inje kawai"
Tashi tayi tace "saide mutafi, muje gidan kawai"
Futowa sukai dukansu, suka tafi gidan Ummah, suna zuwa shida Hajiya Anty sukaga kowa a
zaune, Daddy, Uncle, Ummah, dasu Sa'eed tareda yanbiyu, Kowa jiran zuwan Waheeda yake
Babban Yaya yazauna aqasa tareda gaida iyayen nasa, Daddy ne kawai ya amsa, Amma uncle
Usman kawarda Kansa Gefe yayi, mamaki yasake kama Babban Yaya, meya aikata haka ne?
'Dago Kansa yayi ya Kalle shi yace "Uncle Gani, meyake faruwa ne?"
Cikin 6acin rai yace "abinda kayi ka kyauta kenan? Harme Waheeda zata Maka kasake ta?"
Zaro ido Hajiya Anty dasu Sa'eed sukayi, yanbiyu kuwa har sun fara kuka, Sai yanzu ne suka
San dalilin taruwar iyayen nasu
Babban Yaya d'ago Kansa yace "Uncle wallahi ni ban...."
Katseshi yayi batare da yaji abinda zaice ba "babu abinda zaka fadamin"
Yanbiyu ne suka tashi zasu wuce d'akinsu ganin yanda ran iyayen nasu ya6aci, kuma basa
masa fad'a agaban su, Amma yau Idonsu ya rufe da masifa harsun fara yimasa
Ummah tace "Alhaji Usman ninace yasake ta saboda iskancin Waheeda yayi yawa"
Uncle Usman yace "kuma saiya saketa? Yanzu kamar shi idan akace yafad'a wuta saiya fad'a?"
Kafin Ummah tayi magana saiga Waheeda tashigo gidan hannunta aka, tana runtuma ihun
kuka, ita kuka yanbiyu kuka, su Sa'ad jikinsu duk yayi Sanyi qalau
Waheeda tana zuwa ta fad'a jikin Hajiya Anty tana kuka,kwata kwata bata lura da Babban Yaya
dayake falon ba, idonta ya rufe take fad'in"Anty Babban Yaya yasake ni, wallahi Ina sonsa, Allah
bazan dawo gidaba "
Hajiya Anty ta goge Hawayen daya zubo idonta tace" kiyi hakuri, wallahi saiya maidake d'akin ki
"
Babban Yaya ya shafa sumar Kansa tareda dafe Kansa �丹��領����儭?, Sai yaushe ne
Waheeda zatayi Hankali? ��
Daddy ya kalli Babban Yaya yace"Naufal, kar6o min takardar "
Babu musu ya qarasa wajan Waheeda yazare takardar daga hannunta, Hajiya Anty tazabga
masa wata irin harara, bece da'ita komai ba Sai qeyarsa daga Sosa, ya ninke takardar yariqe
ahannunsa yaqi basu, saboda yana kunyar suga abinda ya rubuta a takardar
Uncle Usman yace"kabamu takarda akace malam, kariga kayi abinda kaga yadace ai saika
bamu takardar muga saki nawane "
Babu musu Babban Yaya yabashi takardar, saboda bazai iya jayaiya dashi ba
Uncle Usman ya bud'e takardar ya karanta abinda yake ciki, Gani yayi anyi rubutu da Babban
baqi cewa I LOVE YOU SO MUCH BABY WAHEEDA
Tsaki yasaki, yayi wata irin ajiyar zuciya yace "af..., Alhaji Allah ya shiryi yarinyar Nan, duk ta
d'aga mana Hankali"
Daddy ya kar6a Shima ya karanta, ya jijjiga Kansa, sannan ya kalli Uncle Usman yace "muje
Alhaji Usman"
Hajiya Anty tabisu da kallo, ta janye Waheeda daga jikinta tatashi ta d'auki takardar, a fili ta
karanta abinda yake ciki tace "I LOVE YOU SO MUCH BABY WAHEEDA"
Su Sa'ad ma sukai murmushi suka koma d'akinsu, yanbiyu kuwa Waheeda suka kalla, haushi
yakamasu kamar su daketa, tasa sunyi asarar Hawayen su a banza ���
Waheeda ta d'ago da sauri ta kalli Babban Yaya, taga yana mata wani irin Kallan soyaiya ko
kunyar su Ummah bayaji, wata irin matsanan ciyar kunya ce ta kamata, tatashi tayi d'akin
Ummah da gudu tana rufe idonta da tafin hannun ta
Dariya su Anty sukayi mata tareda yanbiyu.���
Ganin hankalin su Ummah baya kansa yasa ya shafa sumar Kansa,sannan yabi Bayan
Waheeda Dakin Ummah
Yana shiga 'Dakin ta d'ago kanta ta Kalle shi, cikin sauri tatashi ta fad'a qirjinsa ta rungume shi,
tareda sakin kukan shagwa6a
Sake rungume ta yayi sosai, yafara magana qasa-qasa cikin rad'a ita kad'ai ce zata Iya jin
abinda yake fad'a
Sunkuyowa yayi da Kansa, dede Setin kunnan ta yace "kiyi shiru mana, menene abun kukan?"
Kukan shagwa6a tasake sakar masa tace "uhm... Uhm..." tareda Dukan faffad'an qirjinsa
ahankali
Murmushi yayi yasake rage murya yace "nine ko?, nine nayi Miki laifi ko?"
Kasa d'ago kanta ta Kalle shi tayi, tanata mamakin sa Dama Babban Yaya ya'iya magana haka
ahankali irinta masoya? ��Kawai d'aga masa Kai tayi, takasa had'a ido dashi
Cikin sigar lallashi Yace "to kiyi haquri... Bazan sakeba kinji?"
Sake d'aga masa Kai tayi,bata yarda sun had'a ido ba
yace "kin haqura?"
Yanzu ma sake d'aga kan tayi ���
Murmushi yayi yace "kiyi magana mana"
Ahankali ta motsa lips d'inta, cikin sigar shagwa6a tace "nifa naqura, ni bakamin komai ba"
Tunda tafara magana ya zubawa lips d'inta ido yana kallo, ahankali yasaka hannun sa biyu
yariqo fuskarta, yahad'e bakinsu waje d'aya, ahankali yafara tsotsar lips d'inta, wannan Karon
wani irin dad'i Waheeda taji, ahankali ta Lumshe idonta tana kar6ar saqon, kusan minti biyar
yad'auka yana kissing d'inta, ahankali yacire bakinsa daga Naga, ya kalli qwayar idonta, cikin
muryar rad'a yace "your turn..."
Wata irin kunya ce takama Waheeda, mamaki yagama kashe ta kamar ba Babban Yaya ba,
tunani tafara kode ya manta acikin d'akin Ummah suke? ��
Babu yanda ta iya haka takama lips d'insa na qasa tafara Sha ahankali, wani irin dad'i Babban
Yaya yaji, ahankali yasake rungume ta yana sakar mata wani irin numfashi, tun yana haquri
yanajin yanda take tsotsar lips d'insa harya kasa haquri ya qwace lips dinsa, tareda kama Nata
yanasha cikin fitar haiyaci
Kwata kwata mutanan falon sun manta dasu, Ummah ta kalli Hajiya Anty tace "Antynsu Bari inje
toilet in dawo...." �����領����儭?
Zuciyarta d'aya takama handle d'in 'Dakin tabud'e, a tsaye ta gansu cikin wannan hali, cikin
sauri taja musu kofar tarufe gabanta yana fad'uwa ���
����?
1/28/22, 20:52 - Ummi Tandama���: JH
Qaran rufe qofar kawai Waheeda taji, tayi tunanin zai daina abinda yake, Amma saitaga yaqi
daina wa, cikin sauri ta qwace bakinta, Kallan ta yake da idanunsa dasuka fara canjawa,duk
jikinsa yafara mutuwa, Waheeda ta Kalle shi cikin tsoro tace "kamar qaran rufe kofar nanfa naji,
waye yashigo?"
Kafad'a ya d'aga yace "Ina zan Sani? Ni banji Bama"
Zaro ido tayi ���"bakaji ba? Yanzu yanzu inji qara kacemin Kai bakaji ba?to d'an bud'e ka
duba kagano mana waye"
Wata irin dariya yasaki yace "nizaki yiwa wayo?ke Kifita kiduba mana,nasan ma babu wata
qaran qofa dakika ji, kawai kunnanki ne, kije kiduba mana may be ma basa falon"
Qafafunta tafara bugawa aqasa cikin shagwa6a tace "to wayace kabiyoni? Allah saide ka duba,
ni nace kabiyoni?"
Murmushi yayi yahard'e hannun sa a qirjinsa yana Kallan ta yace "matata tana d'aki sainaqi
binta? Kinga yanzu de abinda za'ayi shine, tunda kince kinji qaran bude qofa, kawai kiyi fuska
kifita, tunda ai bamusan waye yashigo ba, idan kinada kayan dazaki d'auka kije kid'auko kawai
mutafi gidanmu"
Kanta ta d'aga masa, sannan ta nufi qofar takama handle d'in ahankali kamar wata 6arauniya
Hajiya Anty ta kalli Ummah tace "Yaya, yanaga kin dawo? Lafiya kuwa?"
Ummah tace "hmm, 'ya'yanki ne a d'akin, Dan Allah kije kifad'a musu suzo sutafi gida, Zaman
ya'isa haka" ���
Hajiya Anty tayi murmushi, ta tabbatar akwai abinda Ummah tagani, shiyasa tafad'i haka.
tace"yaya Aida kin fad'a musu, tunda ke kin Riga kinshiga"���
Cikin sauri Ummah tace "A a, a a, mezai maidani Kuma? Idan sun gaji da zama zasu fito sutafi"
Kafin Hajiya Anty tayi magana, Waheeda tafuto daga d'akin kanta aqasa, sum sum ta wuce
tagabansu tayi d'akinsu, ummah ta kalleta tayi ajiyar zuciya, bata Jima da futowa ba Shima
yafuto, hankalin sa yana kan wayarsa yana danna wa, ya maze kamar ba Shiba, Ummah ta
Kalle shi, cikin ranta tace oh kamar bashi ba,ashede Yaron nawa yanada lafiya da alama���
Wajan su ya qaraso ya tsugunna sannan yace "Ummah zamu tafi"
"to Son Allah yakaiku lafiya, idan kunyi mantuwa basai kun dawo ba, za'a biyoku dashi"
Hajiya Anty tayi murmushi ba tace komai ba
Ahankali yatashi yana Sosa Kansa cikin kunya, yafice daga falon, yana fita yasaki ajiyar zuciya,
a fili yace "Allah yasa de basu gane ba"�綽�
A wajan motar sa ya tsaya yana jiran Waheeda
Hajiya Anty tamiqe tsaye tace "Bari intura ta sutafi" tafad'i hakan tareda wucewa d'akinsu
Waheeda
Tana shiga ta gansu suna hira Sai dariya suke kamar basu ba, afili tace "yau 'Yan zumuncin ne
akusa kenan, Waheeda taso"
Waheeda tatashi tabiyo Bayan ta, Hajiya Anty takama hannunta suka nufi compound, kafin su
qarasa wajan Babban Yaya ta kalleta tace "Kina amfani da magungunan Dana baki ko?"
Cikin sanyin jiki tace "inayi Anty"
Hajiya Anty tace "to shikkenan kidinga Sha kullum, Kuma karki Bari yasani"
'Daga mata Kai tayi sannan tace "to Anty"
Itama tace "to shikkenan Daughter Allah yakaiku lafiya kudinga haquri kinji ko?"
Waheeda tace "to"
Saida suka kusa zuwa wajansa Sannan tasake ta tareda juyawa, Waheeda Kuma ta qarasa
wajan Babban Yaya daya zuba musu ido tundaga nesa yana kallonsu, yaso yaji me ake fad'a
mata haka suke tafiya ahankali kamar basaso
Kanta aqasa har tazo kusa dashi ta tsaya takasa had'a ido dashi, Kuma mamaki yaqi barinta
Wai Babban Yaya ne mijinta, shine yabud'e mata qofar tashiga sannan yarufe yashigo suka tafi,
a hanya ma kasa nutsuwa tayi, kwata kwata taqi Kallan inda yake, Sai window take kalla, Shima
anasa 6angaren baiyi mata magana ba, wani irin nishad'i yakeji, Sai juyawa yake yana Kallan ta
yana murmushi, yanzu Kam yana jin Kansa a matsayin kowanne ango, abu kad'an yarage
masa,������
Suna qarasawa gida, megadi yabud'e musu, Babban Yaya yayi parking suka futo, yabud'e
booth d'in motar yad'auko wata babbar jaka, megadi yana hango su daga nesa, mamaki ya
hanashi magana, dazu dazu fa Hajiya tafita tana kuka Kuma yanzu ikon Allah gata tadawo
lafiya, dama ance mata da Miji Sai Allah �弘
Babban Yaya yaja kayan suka shiga ciki, afalo ya zauna, ya ajiye jakar agefensa,Waheeda
kuwa tunawa tayi d'azu zata d'ora abinci wannan abun yafaru bata d'oraba, danhaka tayi sauri
zata wuce kitchen
Hannun sa yasaka ya fuzgota, ta fad'o Kansa, kunya ce ta kamata, ta6oye fuskarta a qirjinsa
Kallan ta yayi yace "Ina zakije kibar mijinki?"
Cikin qaramar murya tace "Babban Yaya zan dafa mana abinci ne"
"no, karkiyi komai, nine zanyi mana, waye ya fad'a miki amarya tana abinci?"
Cikin rashin fahimta tace "tana yi mana, Toni tun yaushe nake yi? Tun lokacin daka tafi kabarni"
Murmushi yayi yace "ai yanzu qafata qafarki, kibud'e wannan kayan, tsarabar kice keda Ummi,
nataho muku dashi" yafad'i hakan cikin sigar tsokana
6ata fuska tayi tace "Babban Yaya banso"
Mamaki ya kamashi,yanda lokaci daya take nuna kishin sa qarara, da gaske de tana sonsa
itama, hannun sa yahad'e waje d'aya �����語ace "Tuba nake, ni wasa nake miki, nakine
ke kad'ai"
Cikin murna tace "duka gaba d'aya cikin akwatin?"
Yace "yes, kiduba, zanje wajan megadi in dawo"
Yana fad'ar haka ya ajiye ta d'am akan kujera shikuma yafuto, Yabarta tana bud'e jakar
Yana zuwa compound, yakira megadi, cikin sauri ya qaraso wajan sa yana fad'in "yalla6ai Gani,
akwai aikene?"
Hannu yasaka cikin aljihunsa, yamiqa masa kud'i masu yawa yacey"ga wannan kaje gida kaga
iyalanka, idan kagama hutawa idan zaka dawo saika min message "
Hawaye ne yafuto daga idon megadi, yafara yimasa godia, har Babban Yaya yagaji da amsawa
yajuya, Shima megadi yanufi d'akinsa yana fad'in"dole intafi gida wallahi, irin wannan kud'i
haka? Ai ko baka turani gidaba, dole ne inje inbarku kusha Amarci" ���
Waheeda kuwa akwatin kayan tasa agaba tayi tagumi hannu bibbiyu ���Ahaka yazo ya
sameta yace "lafiya?"
"Babban Yaya wannan kayan fa dukansu sunyi shara shara dayawa,Kuma...."
Cikin sauri ya katseta yace "Kuma me?, ni su nakeso kina Sakamin, kefa yanzu ba yarinya
bace, kinfi su Ihsan, kawai abinda yarage kizama cikakkiyar mace, saboda haka kindena saka
Kaya masu kauri, inde Ina gidannan"
Waheeda taji ya kurantata,yayabeta yabata girma Sai kanta yaqara nauyi, ita Ala dole tafi su
Ihsan,���
Cikin sauri ta d'aga kanta tace "to shikkenan zan saka"
"kizo muje muyi wanka, nasa megadi yatafi"
��訣aro ido tayi tace "wanka Kuma?"
Kansa yadafe da hannunsa�丹��領����儭?
ya manta da sabon shiga yake tare, yace "eh, akwai kayan wanka aciki, kisaka ki sameni a
swimming pool, Ina jiranki..."
Yana fad'in haka ya tsugunna yaduba cikin kayan Nata yad'auki na wankan yad'ora mata akan
cinyarta, sannan yafita
Waheeda ta bishi da kallo cikin ranta tana fad'in wannan mutumin bashida kunya Allah�朮
Tad'auki kusan minti talatin tana tunanin fita da wannan kayan
Rigace me launin ja, tsawon ta iya gwiwa, batada hannu Sai d'an siriri, gaban rigar normal wuya
ne, saide daga wajan Boobs d'in anyenke wajan, anyi d'an qaramin round a wajan, Ana Iya
ganin Boobs d'in sosai
Futowa tayi tana tafiya Sai Kalle Kalle take kamar tana jin tsoron wani yaganta Ahaka, tana
zagayawa baya inda swimming pool yake ta hango shi dagashi sai d'an qaramin wando
dakad'an ya wuce pant, yana kwance cikin ruwan akan katifar roba, waya tana kange a
kunnansa yana magana ahankali, gabanta ne yafad'i ganinsa haka, tasan de koda yaushe tana
ganinsa da gajeren wando tunda a TV ma kowa haka yake ganinsa, Kuma idan yazo gida ma
shi yake sakawa wani lokacin idan zasuyi ball tare, Amma bata ta6a ganinsa da wannan d'an
fificin wandon ba, cinyoyinsa ta kalla farare tas kamar sauran jikinsa, Sai gashi dayawa daya
kwanta me laushi kamar na qirjinsa,kamar wacce batada laka haka ta qarasa wajan taja ta
tsaya,tareda sunkuyar da kanta qasa.
d'agowa yayi da Idonsa ya kalleta,hannu ya miqa mata, babu musu tasaka qafarta a
matattakalar dazata kaika cikin ruwan, tana shiga ya janyo ta zuwa jikinsa tareda Lumshe ido,
ahankali yace "mashkur zansa yarinyar Nan takira ka Dan Allah, banda lokacin turoma number,
inaso na Gana da amarya ta Sai anjima" yafad'i haka tareda kashe wayar
Waheeda ya kalla yaga tacusa kanta cikin qirjinsa, yad'ebi ruwa ya watsa mata a fuskar, cikin
sauri tabud'e idonta, murmushi yayi yace "kinyi kyau sosai, idan kinaso ki hanani fita kiyimin irin
wannan shigar" yafad'i haka yana kissing wuyanta
Cikin shagwa6a tace "Babban Yaya babu abinda zamu cifa"
"zanyi mana oder abinci, Naga alama mecin abinci na aura"
Bakinta ta turo gaba tace "Allah kafini cin abinci"
Dariya yasaki yace "Alhamdulillah tunda kinsani, kinga saiki sake d'aura d'amarar girki, natural
duk d'an qwallo yanada cin abinci, Bani kad'ai bane, nasan kin iya girki irinna Ummah, so banda
matsala akan haka"
Murmushi tayi ba tace komai ba,hanunsa yasaka yaruqo fuskarta yace "Waheeda,Ina sonki
dayawa, nikaina bansan irin son danake miki ba, natsani inji kina min maganar wani,Ina shiga
cikin tashin Hankali sosai, please ki riqeni, ki mallakeni ke kad'ai, banaso daga yau idan Zaki fita
ki yarda wani namiji ya Kalle ki,