Showing 60001 words to 63000 words out of 82824 words

Chapter 21 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf

Maya tace "Babban Yaya mungode, Allah yasaka da alkhairi"

Yace "Amin, idan kinsamu lokaci kije gidan ki lallasheta, kibata shawara" yafad'i hakan yana
Sosa girarsa d'aya ���

Tace "to insha Allah zanje"

Murmushi yayi yashiga motar, yana fatan ace ta fahimci shawarar dayake nufi abawa Waheeda,
fatansa d'aya Allah yasa tabata shawara irin wadda Ummah taji suna fad'a awaya
������������


Kafin su qarasa Airport yaga text yashigo wayarsa daga Ummi naban haquri, shareta yayi baiyi
mata replay ba, ya goge number ta daga wayarsa, ya tabbatar taji labari ne cewa Waheeda
lafiyarta kalau, shiyasa takeso ta lalla6o tadawo ���



** *** **



Sai wajan azahar Maya takira wayar yanbiyu suka kwatanta mata gidan da Waheeda take,
sannan ta shirya tatafi, tana zuwa megadi yatareta yana mata tambayoyi tayi masa bayani
sannan Yabarta tashiga

A falon ta dinga doka sallama Waheeda tana kwance ad'aki tana jinta taqi futowa, Maya dataji
shiru saita fara bud'e qofofin tana dubawa sannan tayi nasarar bud'e na Waheeda

Mamaki ya kamata ganin Waheeda idonta biyu, qarasawa tayi ta zauna akusa da'ita tace
"qawata kiyi haquri, nayi tunanin kin huce shiyasa nazo, ashe har yanzu Ina Nan acikin ranki"

Ba tareda ta kalleta ba tace "aina fad'a miki NI DAKE har abada Maya"

Maya tace "subhanallah, Waheeda me yayi zafi haka?nad'auka namiki gata ne akan aurenki da
Babban Yaya, ashe Bahaka bane Wai Waheeda harni kika shaqe duk qawancen mu"

Tashi tayi zaune, cikin masifa tace "eh na shaqe kin, kiyi abinda zakiyi, ai wallahi Maya Kin bani
mamaki, banta6a tunanin dake za'a had'a baki a auramin Babban Yaya ba, kin cuceni kuma kin
gama Dani"

Cikin sanyin jiki Maya tace "ban cuceki ba Waheeda, temakon d'an'uwanki nayi, Duk Wanda ya
zauna daku zaisan cewa Babban Yaya yana sonki, Kuma nasan cewa bazaki ta6a samun
masoyi kamar saba, Babban Yaya yana qaunarki Waheeda, Kuma kun dace da juna sosai"

"yanzu ke Maya idan kece akace ki auri yayanki Safwan zakiji dad'i?"

Maya tace "to menene aciki? Abu d'ayane zai dameni yanda zan sake inyi masa abubuwan
soyaiya na aure, Kuma Shima lokaci ne ahankali zan saba, kema kuma idan wannan ce
damuwar ki toki daina,Babban Yaya zaisa ki manta da cewa shi yayanki ne, sannan karki manta
da qaddara, kowa da irin tasa,Kuma munyi alqawari zamu yarda da'ita me kyau ko marar kyau"
Waheeda tana jijjiga qafa cikin damuwa tace "shikkenan ya wuce, Amma karki sake min irin
haka, ni banaso, Shima Kuma bazan iya zama dashi ba, saboda tsabar abun kunya rannan har
kiss yamin, Ina zan Kai wannan rashin kunyar?"

Maya tasaki dariya tace "yakaiki rashin kunya ne? Keda kowa yasan halinki ne haka bakida
kunya? To menene ma danya miki kiss? Haka zakiyi haquri ki yarda, kema kiyi masa, wannan
shawarar dakika Bani de akan za'amin aure itace zata dawo kanki, haka Zaki kama abun
mijinki ki wanke"
"Dan girman Allah Maya kidena min wannan maganar, kodan kinga na kulaki? Ni banason jin
wannan abun kunyar,inrasa wazanyi wa hakan Sai Babban Yaya?"

Maya tace "aikuwa saiki maraba da kishiya"

Cikin rashin damuwa tace "kofa abud'e take, tazo ta zauna ban hanata ba"

Kafin Maya tace wani abu yanbiyu suka shigo d'akin, sunci kwalliya iri d'aya ko ganesu bakayi,
abinci suka ajiye mata Ihsan tace "ke ga abincin ki Nan inji Ummah"

Kallan abincin tayi tace "wannan ai yayi mana kad'an, ko Babban Yaya zai iya cinyewa, yanda
yake cin abinci idan yasamu waje to wallahi shi kad'ai ma zai cinye wannan"


Intisar tace "wanne Babban Yaya Kuma shida yatafi England? Ni jinake ma dake zai tafi, ashe
shi kad'ai yatafi, ke yanzu Waheeda ba abun kunya bane wannan? Sabon aure Amma kibar
ango yatafi shi kad'ai? Kyaje yakula wasu matan acan wallahi, tunda yanzu ya d'and'ana yaji
dad'in mace "������
Cikin 6acin rai Waheeda tace" uwar me ya d'and'ana? Inti banason rashin mutunci wallahi, ba
England ba, yatafi kafi England ma,dayau yafara huld'a da mata? Da idona na ganshi mata
suna yanyameshi Sai yage musu baki yake, da idona nagani "


Ihsan tace" to babu so menene Kuma yakawo kishi? Keda kike cewa bakya sonsa miye
dankinga mata suna yanyameshi? d'an ball nefa, ba mata ba mazama yanyameshi zasuyi,
malama kinaso kina yiwa mutane ihu ke bakya so "

Tace" eh banaso, ba Kuma zan so ba, da yau yafara kula matan dazaku zo Kuna cewa nabarshi
yatafi, inda ace nasan baya gidan ma da tuni Nima na kama gabana, Zaman me zanyi yanzun
Ina masa gadin gida? Saikace wacce batada galihu, Nina tafi gida idan kun gama kwa taho
"tafadi haka tana Jan hijabin ta tafice daga d'akin ������


Babu yanda suka iya haka suka futo suka biyo bayanta, saida sukazo gida sannan Maya
tamusu sallama tatafi gida, sukuma suka shige cikin gida, megadi Sai tsokanar Waheeda yake
yana fad'in"Amarya kinsha qamshi"


Yau kwananta hud'u agida, Amma kamar bata gidan, Dafarko tayi tunanin zasu kulata, shiyasa
take wuni ad'aki, dataga babu Wanda yake shiga harkar ta, saita fara futowa tana abin gabanta,
daga Ummah har Daddy idan ta gaishe su daga sun amsa basa qara cemata komai, haka
yanbiyu ma tun lokacin dasuka mata fad'a tamusu rashin kunya suka tattara ta suka watsar,
Hajiya Anty tahad'o mata magungunan mata masu kyau, ta zaunar da'ita ta mata bayanin yanda
zata dinga amfani dasu, sannan tabata haquri akan Takoma gidan mijinta, Amma Waheeda tayi
mursisi taqi komawa, magungunan ma ta ajiye su taqi shan kod'aya aciki.


Yau satinta uku agida, Kuma har zuwa wannan lokacin bata kira Babban Yaya ba, Shima bai
kirata ba, Kuma babu Wanda yace tattara kayan ki kikoma, kowa yazuba mata ido kawai.

Yau suna break fast afalo gaba d'ayansu, banda Daddy, Sa'eed ya kalli Waheeda sannan ya

kalli Ummah yace "Wai wannan yarinyar Zaman me take a gidannan Ummah?"

Ummah ta Kalle shi tace "gatanan ka tambayeta"

Kallan Waheeda yayi yace "keme kikeyi har yanzu baki koma ba?"

Idonta ne yayi qwalqwal yakawo ruwa, tana juya spoon acikin cup d'in tea d'in dake gabanta
tace "ni Bana sonshi...."

Sa'ad yayi sauri yace "to cemiki akai shid'in sonki yake? Banda qaddara ma me Babban Yaya
zaiyi dake? Ga yanmata Nan had'ad'd'u suna bibiyarsa zai tsaya anan Ana Rena masa Hankali"

Sa'eed ma yace "okay bakya sonsa ko? To Alhamdulillah, Ummah kawai idan yazo kibashi
shawara yasake ta kawai"

Ummah ta ajiye bread d'in hannunta tace "na fad'a masa tun shekaran jiya da mukai waya, idan
yasamu lokaci Yazo ya rubuta mata takardar, saisu koma makaranta itadasu Ihsan"

Sa'eed yace "Hakan ma yafi, Dan wannan yarinyar Dama ba ajin auren sa bace, kawai de Dan
Allah ya rubuta Sai anyi ne, ni Gara ma dayake shirya abinda yafi masa, abinda Yayanke d'in
yayi daidai, yanzu ne yasan zaiyi aure"

Gaban Waheeda yayanke yafad'i, ahankali ta zaro idonta ��豚atare datace komai ba

Shima Sa'ad yace "eh gaskiya Kam ya kyauta"

Hajiya Anty ce tashigo falon zata yiwa Ummah sallama kamar yanda tasaba idan zata tafi wajan
aiki, tajisu suna fad'in eh ya kyauta Kam tace "waye ya kyauta?"

Ummah tayi murmushi tace "Wai suna magana ne akan auren yayansu, kinsan jiya Daddynsu
yamasa waya yace idan zai taho yahad'o wasu kayan lefen Sai akai gidansu ummin, tunda
tabada haquri Kuma Shima Naufal d'in yace ya haqura zai aure ta" ���

Waheeda taji numfashinta yana yin sama kamar zai d'auke, gabanta Sai fad'uwa yake, takasa
d'agowa ta Kalle su, sukwa yanbiyu Sai lodar abinci suke ko bakinsu ba'aji

Hajiya Anty ta kalli Waheeda tace "yanzu Yaya ba zakuyi haquri da maganar Ummin nanba?
Ayita yin abu de? Duka duka yaushe yayi aure dazaku sake da'aura masa wani auren?"


Ummah tace "to Antynsu Yaya zanyi dashi? Jiyafa kirana yayi kamar zaiyi kuka shide ayi ayi a
aura masa Ummi,yanaso yazo gobe ko jibi ayi agama magana, so yake yazo yatafi da'ita
England, ita Kuma Waheeda tunda tana zaune agida, saitaci gaba da Kula da gidan, idan

sukazo hutu kinga har saga gida tsaf dashi 'yar aiki ta gyara musu "

Waheeda tacika tacika tazo wuya, batasan lokacin data Fashe da Kuka ba, cikin gudu tayi
d'akinsu tad'auki wayar inti takira Maya, bugu biyu Maya ta d'auka tace"inti ya akayi Ina
qawata? "

Waheeda tasaka mata kuka tace" Maya yanzu kowa baya sona, Shima Babban Yaya yadena
sona, Wai ummi zai aura, Kuma Daddy yace yazo yakawo kayan lefe idan anyi auren yatafi da
ummi, Nina shiga uku na Maya ya zanyi? "

taqara sa maganar cikin kuka

Maya tace" kema Waheeda kinada laifi, bakya bashi kulawa dole hankalin sa yakoma kan wata"

"to ya yakeso namasa Maya? Rannan fa kuka yakemin saikace qaramin yaro, ni wallahi yafi
qarfina bazan Iyawa shagwa6ar saba"

"babu Wanda yazo da iyawa Waheeda, kowa dakika Gani Koya yayi, kikasan me Ummin ta
qulla masa? Tayaya za'ai ki zauna kinada kamar Babban Yaya?"

Cikin hawaye tace "to tashi zanyi?"

Dariya takama Maya, ganin duk tsiwa irinta qawar Tata yanzu Babban Yaya kad'ai yana nema
ya rikita ta, tace "ni bance ki tashi ba, ba zama ba kiyi kwanciyar ki ma, lokacin dakika ce yana
kuka kamata yayi kijashi ajikinki, ki rungume abinki ki lallashe shi, na tabbatar bakiyi hakan ba,
Waheeda dole saikin ajiye wannan yayan agefe ki d'aukeshi as mijinki, inba hakaba wallahi
tunda kikaji maganar Ummi tashigo to tsaf zai aure ta, Dan maza idan sukai niyyar qara aure
ba'a hanasu,kikama hanya kitafi gidanki, kikirashi awaya kibashi haquri kiyi masa
shagwa6a,tunda kince Ummah tace zaizo to idan yazo kicire kunya kinuna masa soyaiya
tsantsa, sonake yanda yace zai auri ummi ya dawo da Kansa yace yafasa "

Waheeda tayi ajiyar zuciya tace"zan iya kuwa Maya? "

"Mezai Hana? Wai Waheeda Ina wayonki yake ne? Naga kece me Bani irin wannan shawarar,
kitashi kiyi abinda nace kawai, wannan gidan naki ne ke kad'ai insha Allah qawata, babu wadda
zata shigo "

Ahankali tayi ajiyar zuciya tace"to Maya"

sannan ta kashe wayar

Kai tsaye truly d'inta tad'auko, magungunan da Hajiya Anty tabata shita fara d'auka tasaka a
jakar ���

Sannan tadauko duk kayanta, tasaka aciki, ta janyo jakar tafuto falo

Suna zaune Sai ganin Waheeda sukai tafuto da jaka
Mamaki ya kamasu, basuyi tunanin wannan plan d'in dasuka had'a zaiyi tasiri akanta ba, ko
sallama bata musu ba tafice daga falon cikin fishi


Tana fita suka kwashe da dariya, Hajiya Anty ta kalli Ummah tace "lalle Yaya kin kawo point"
���



����?
1/28/22, 20:51 - Ummi Tandama���: AL


Driver tasa yakaita gidan, suna zuwa kuwa megadi ya kar6i kayan hannunta yakai mata shi har
ciki, sannan yajuya yakoma gate.


A falon tabar kayan Nata ko d'aki bata shiga dashi ba, tacire hijabin ta tafara gyara gidan, bata
gama ba Sai wajan azahar, takai kayan d'aki sannan tayi wanka tasaka Riga yar qarama,
iyakarta gwiwarta, tadafa indomie ta zauna tanaci tana kallo a TV, d'aki tashiga tad'auki
magungunan ta Tasha, sannan ta kwanta tahuta, Sai wajan qarfe uku tadafa musu fried rice, ta
kaiwa megadi sannan ta kulle falon tayi kwanciyar ta, kullum haka takeyi, idan tadafa abinci
zata kaiwa megadi nasa, sannan tarufe falon saikuma washe gari, magungunan ta kuwa bata
wasa dasu kullum Sha take, ita kanta tanaji ajikinta, yanda maganin yake mata aiki

Saboda magungunan sunada kyau sosai, satinta d'aya da komawa da sukaga bata dawo ba,
Sai hankalin su ya kwanta, ganin haka yasa Hajiya Anty tatura mata Dame gyaran jiki take
zuwa har gida takeyi mata, kullum Maya zatazo tatayata aikin gida, ita Kuma ta zauna ayi mata
gyaran jiki, wataran yanbiyu suzo suhad'u su hud'u a gidan sutayata hira, kasancewar gyaran
jikin yanzu a zaune take agida babu inda take zuwa Sai yafi kyau fiyeda na wancen Karon,
jikinta yayi wani fresh, ko'ina yasake cika saboda yanda Hajiya Anty tahad'ata da magungunan
ingantattu masu kyau, tsawon sati uku suka d'auka anayi mata gyaran jiki da turere Kala Kala
na jiki dakuma na tsugunno, yau matar tagama aikinta danhaka bata zoba, suma su Ihsan basu
zo ba, gyaran gidan tayi, ko'ina yad'auki qamshi, tayi abinci daidai cikinta, ta zauna taci Sannan
ta wuce d'aki, bacci ne ya d'auketa, bata tashi ba Sai wajan shad'aya, futowa falon tayi zata je
kitchen ta d'ora abinci, d'azu bata Bawa megadi ba, 'yar qaramar Riga ce ajikinta, iyakarta
gwiwarta, bata saka brezia ba, kana ganin yanda boobs d'inta suke a tsaye ta cikin rigar, kanta
babu kitso duk gashin ya bazu a fuskarta, fatarta Sai qyalli take tana d'aukan ido kamar ka
latsata jini yafuto

Tana bud'e kofar d'akin tana futowa falo ta tsaya tayi wata irin miqa tareda hamma, kwata kwata
bata lura da mutum a falon ba, Babban Yaya dayake zaune yad'ora kafa d'aya kan d'aya yana
waya da mashkur, lokaci d'aya yanemi nutsuwarsa yarasa, soyake ya d'auke Idonsa akanta
Amma yakasa, yanda ta turo qirjinta gaba yafi komai Jan hankalinsa, daqyar ya sunkuyar da
Kansa yana Sosa girarsa d'aya sannan yace "inaji"

Daga d'ayan bangaren mashkur yace "Dan Allah Abokina katemaka kabani number yarinyar
Nan, yanzu tun dad'ewa Ina bin kanka akan yarinyar Nan Amma ka hanani number ta?"


Tun lokacin daya ce inaji, Waheeda taqame a falon tana kallon sa, yaushe yazo? Duk saita
rikice tarasa me zata masa, inda ace dane da gudu zataje ta fad'a jikinsa, Amma yanzu meyasa
ta kasa? Anya zata Iya amfani da shawarar Maya kuwa? Kalli yanda ya shareta Shima kamar
be ganta ba, ahankali ta juya zata nufi kitchen
Babban Yaya ya kalleta qasa-qasa, yaga yanda hips d'inta suke juyawa, wani irin yawu ya
had'iye sannan ya sauya wayar dayake da mashkur, yayi kamar da Mace yake waya, memakon
yabawa mashkur amsa saiyace "na fad'a miki ko awa d'aya bazan iya a gidannan batare Dana
ganki ba, tun jiya nake mafarkin had'uwa dake, ko minti talatin banyi da zuwa Bama, yanzu
zanzo naganki, kibani abinda kika tanadar min"


Waheeda ta tsaya cak, gabanta yana fad'uwa, sake Kallan ta yayi, yayi tunanin zata taho da
gudu ta fad'o Kansa kamar yanda tasaba, yaga ta tsaya ko juyowa batayi ba, mashkur yace
"man ni zakayi wa wulaqanci ko? Zamu had'une, inama magana kanamin wani irin zance"

cikin sauri Babban Yaya yasake cewa "a a, karki damu wallahi, qanwata tana zaune agidan,
dama itace me kula da gidan, shara, wanke wanke, da duk ayyukan gida, zata kula da wannan,
Gani Nan zuwa"
Qitt yakashe wayar sannan yatashi yafice da sauri, gidan Ummah ya nufa, Dama yayi tunanin
zai samu kar6uwa ne a wajan Waheeda, da babu abinda zaisa Ummah ta ganshi yau �對�
Amma tunda bai samu hakan ba, Gara yanemi Ummansa Kota d'ebe masa kewa da hira


Tana ganin fitarsa ta tsugunna a wajan tafashe da Kuka,d'aki tashiga da gudu, wayar inti data
manta a gidan ita ta d'auka takira layin Ihsan, Ihsan tace "Waheeda yagida"

Fashewa tayi da Kuka tace "Wai Babban Yaya ne zai tafi wajan Ummi, ko magana bemin ba,
yatashi yabar gidan, saboda yanzu baya qauna ta"

Ihsan tace "yazo qasar ne? Kiyi hakuri Bari infad'awa Ummah, kiyi shiru"

Kashe wayar Waheeda tayi, gaba daya saitaji komai ma yafice mata Arai, girkin ma fasa

dorawa tayi, ta zauna a wajan tana kuka


** *** **


Ihsan tafuto daga d'akinsu, saita tsaya turus ganin Babban Yaya zaune agaban Ummah tana
bashi abinci, Sai hirarsu suke cikin nishad'i

Qarasawa tayi tagaidashi, sannan ta kalli Ummah tace "Ummah Waheeda ce take kuka, Wai
Babban Yaya yatafi Wajan Ummi, ko magana beyi mata ba"

Ummah tayi murmushi tace "jeki Ihsan"

Ahankali Ihsan ta juya, Saida yaga tatafi sannan ya kalli Ummah yace "Ummah tana kallo nafa,
ko sannu da zuwa batamin ba, shine na nuna mata da Ummi nake waya, nikuma da mashkur
muke magana akan Ihsan, yadage Wai yana sonta"

Ummah tayi murmushi me ciwo, duk da yafad'a mata abinda zaisa taji dad'i akan maganar
mashkur da Ihsan, hakan baiyi tasiri a ranta ba, tafi damuwa da batun Waheeda, taga alama
Waheeda bazata sauya ba, Naufal yadad'e baiyi aure ba, yana buqatar kulawar matarsa,
inbanda itan ce ta sameshi ta tabbatar idan wata ya aura da tuni yafara kula wasu
yanmatan,ajiyar zuciya tayi tace "to Allah ya tabbatar da alkhairi, Son kaje kakaiwa Waheeda
takardar ta...."


Cikin sauri ya d'ago ya kalleta yakasa magana, beyi tunanin wannan maganar daga bakin
Ummah ba, haushin Kansa yaji, daya Sani be fada mata laifin Waheeda ba, cikin sauri yace
"Ummah Dan Allah kiyi haqurrr....."
Hannu ta daga masa����? tace "kaje kayi abinda nace kawai"


Beqara ce mata komai ba yafice daga gidan, driving yake Amma baya tareda nutsuwa, tayaya
ummah zatace yaje yasaki Waheeda? Ko batasan cewa sakin Waheeda daidai yake da sakin
zuciyar sa ba?Anya kwa Ummah tasan irin wahalar dayasha akan Waheeda?

Har yazo gidan yarasa abinda zai aikata takameme, falon yashigo anan ya ganta zaune kan
kujera tana share hawaye, wucewa yayi d'akinsa, ya kwanta akan gado tareda fad'awa cikin
duniyar tunani, wani tunani ne ya fad'o cikin ransa, cikin sauri yatashi yanemi paper da biro yayi
rubutu aciki, ya ninke takardar sannan yafuto daga d'akin, Kai tsaye wajan ta ya nufa, yad'aure
fuskarsa yace "idan ban manta ba, last time kince min in temaka in sakeki ko?"

Cikin sauri ta Kalle shi takasa magana, ya kalli qwayar idonta tayi jajir da alama Tasha kuka,

cikin kuka tace "Bana baka haquri ba?"

Dariya ce taso kamashi, Amma sai yayi fuska yace "lokaci yaqure Waheeda, akwai wadda
zatamin abinda narasa awajanki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login