Showing 24001 words to 27000 words out of 82824 words
Chapter 9 - BABBAN YAYA Book Complete by Fauziyya S Madaki.pdf
kuwa tun safe takasa
zaune takasa tsaye, yanbiyu tun kafin su tashi daga bacci tafara tashinsu, cikin ladabi tace "Inti
yau Soja zaizo, mezan shirya masa?"
Intisar tace "waida gaske zuwan zaiyi? Bakya tsorone Waheeda?"
Bakinta ta turo gaba tace "Toni Ina sonsa, Dan Allah Kuna 'yan'uwana mata idan Baku Bani
goyon baya nafita kunyar sa ba, wakuke so yabani?"
Tausayin ta yakama Intisar, tajuya ta kalli Ihsan, Ihsan tace "kinga Inti babu ruwana, idan
Babban Yaya yaji, mezamu ce masa?"
Waheeda tace "Kai Ihsan Dan Allah, idan Ummah ta tambaye ku karkuce saurayina ne, kawai
kuce mata Dan makarantar mu ne, ba shikkenan ba?"
Nan take,Waheeda ta kalallame zuciyar 'yan'uwan Nata, suka d'auki shawarar data
basu,Waheeda ta wuce kitchen tafara hadawa soja kayan makulashe
Karfe hudu na yamma, soja yazo, d'an sahu ne yakawo shi har unguwar ya ajiyeshi, yakira
wayar Waheeda yasanar da'ita yazo
Rabonta da saka mayafi harta manta,saboda Babban Yaya yahanasu, Amma yau haka taci
kwalliya cikin Riga da siket, kayan ya kar6i jikinta sosai, tayi kyau nesa ba kusa ba, fuska taci
kwalliya, tadauki mayafi Dan qarami ta yafa, sannan tadauki kayan data had'a masa tafita dashi
compound din gidan, Ummah tana daki ba tasan Wainar dasuke toyawa ba.
Kamar yanda yafada dinne kuwa, domin kuwa Waheeda tana zuwa ta ganshi baqiqqirin dashi,
gashi gajere, Amma duk da haka Saitayi murmushi ta qarasa wajan sa tace "qaraso gidan
mana"
Babu musu yabiyo Bayan ta Sai qarewa tsarin gidan nasu kallo yake yana jijjiga Kai, komai da
komai na tsarin gidan yamasa kamar tsarin ginin turawa, daga Gani yarinyar 'Yan manyan
mutane ce
Gidan suka shiga, baba maigadi dayasan cewa basa saka mayafi Kuma basa kawo samari, Sai
mamaki ya kamashi, Dan haka yanufi cikin gidan zai fadawa Ummah abinda yake faruwa yaji
koda sanin ta haka zata tafaru
Sas yana ganin shigar maigadi ya kalleta yace "ashe da gaske banyi qarya ba Dana saka miki
suna sarauniyar kyawawa"
Waheeda tayi murmushi ta rufe fuskarta da tafukan hannunta cikin kunya, sannan tace "tun
dazu nake jiran zuwanka, ashe saukar yamma zakayi"
Yace "eh wallahi,Ina hanya ma wayata ta dauke babu charge, yanzu ma kunna ta nayi na
kiraki,kinga harta sake mutuwa, gashi ban kira mama na nace mata na'iso wajanki lafiya ba,
kinsan me ma? Jiya fa dazan taho wajanki saida tace idan nazo na kula dake sosai, sannan
tamin lissafin abubuwan da babu acikin kayan lefen Dana had'awa budurwa ta tada, Wai babu
takalmi da jaka, yakamata aqara guda uku uku akan nada, da ansaka dozin d'aya, idan aka
qara uku akai, kinga ya zama Sha biyar kenan, yakamata ace nakira ta nasanar da'ita nazo
wajan Mai kyau,gashi wayar tawa tamutu,Bani Aron taki wayar nakirata"
Waheeda tanajin wannan dogon bayanin nasa taji dad'i, gashi de bashida wani kyau na azo
agani,Amma ita a haukan ta bataga laifin sa ba, babu tunanin komai ta bashi wannan sabuwar
waya tata, tace"gashi kakirata to"
Sas ya kar6i wayar yabata wata leda a hannun sa yace"ga kyautar Dana kawo miki, nayi niyyar
kawo miki Riga irintamu ta sojoji, sainace idan zan sake dawowa saina kawo miki rigar, Amma
yanzu ga wannan"
Waheeda ta kar6a tace"nagode"
Yace "Bari inkira mama"
yamatsa jikin get din gidan zaiyi wayar, Hankalin Waheeda yanakan kyautar daya bata, taji de
abu yana yawo aciki, Amma bata San menene ba, saboda anyi wrapping din abun da wata leda
me kyau, tana d'ago kanta, taga wayam! Babu Sas babu dalilin sa �����領����儭?
Gabanta ne yafad'i, cikin ranta tace"wannan mutumin fa ba saninsa nayi ba, kar naje yagudu da
wayata, ba kowa ne ya fado mata araiba Sai Babban Yaya���
Ledar da Sas yabata ce tasulale tafadi daga hannunta, cikin sauri ta bude get din gidan tafita,
mayafin data yafa yafad'i qasa Amma batabi ta Kansa ba, haka tafuto titi tana waige waige,
Amma abu kamar wasa, babu soja babu dalilin sa, awajan ta tsugunna ta Dora hannunta aka
�����領����儭�tace "nashiga uku na, namutu na lalace!, wallahi Babban Yaya saiya
kasheni" ���
Baba megadi yazo da gudu shida Ummah, Ummah ta dakata daga bakin get din, baba megadi
ya qarasa wajanta yariqo hannunta yana fadin "Waheeda lafiya? Me yayi miki? Ina baqon naki
yake?"
Waheeda bata Bawa baba me gadi amsa ba, saboda kuka dayaci qarfin ta, cikin kuka tace
"innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, shikkenan namutu, nakade har ganye na, Wallahi barin garin
Nan zanyi tun kafin Babban Yaya ya dawo"
Baba megadi haka yakamota suka shigo gidan, suna zuwa compound din gidan tazube awajen
tana ihun kuka, yanbiyu suka qaraso da gudu suna tambayar ta menene, Ummah ta riqeta tace
"kimin bayani mana, Wai menene?megadi yacemin kinyi baqo, Wanne irin baqo kika kawo
gidan? Kuma me yayi miki?"
Waheeda de takasa magana, Dan Gani take idan ta fad'awa Ummah to zata kira Babban Yaya
ta fad'amasa
Yanbiyu suka dauki Ledar da Waheeda ta yar, Ihsan tabude Ledar da'aka yi wrapping dinta,
tana budewa saiga chesee ya bayyana, 'Yan hamsin hamsin guda biyu, hada baki sukai sukace
"Laaaa Cizi ne"
Kallan Waheeda sukayi, intisar tace "meya miki ne?"
Cikin kuka tace "Yagudu da wayata, naduba ko'ina baya Nan, wallahi gidan Nan zan Bari" tana
fadar haka ta kwasa da gudu tayi cikin gida
Anan Ummah ta fahimci komai, Kai tsaye tabi Bayan Waheeda har d'akinsu, tana zuwa ta rufeta
da duka, daqyar yanbiyu suka ceceta, Ummah taja kofar Dakin ta kulle Waheeda aciki, Dan tayi
alqawari wannan Karon Waheeda tadena fita bare taja mata wata masifar
Har dare Waheeda tana d'akinsu akulle, Ummah tahana kowa yabudeta, Daddy ne ya dawo
daga wajan aiki Sai masifa yake, ta inda yake shiga batanan yake fita ba
Duk sunyi shiru babu Wanda ya tanka masa, ita kanta Ummah ba tasan me zatace ba
Kallan 'yanbiyu yayi yace "kuje ku budeta tazo Nan Ina nemanta"
Inti taje ta bude Waheeda, akan gadon su taganta har lokacin kuka take, ta kifa kanta akan
cinyoyin ta,dogon gashin kanta yazubo gadon Bayan ta, wani Kuma yarufe mata fuska kamar
de mace me aljannu, kanta har ciwo yake saboda kuka, yanzu shikkenan wayarta tatafi, wayar
ko wata daya Babban Yaya baiyi da siya mata itaba, ta Ina zata Iya Kallan idonsa tace takawo
saurayi gida shikuma ya sace mata wayar? Intisar tace "kije Daddy yana kiranki"
Ahankali tataso, suna zuwa falon kowa yabita da kallo, su Sa'ad jisuke kamar Su make ta,
Daddy ya kalleta yace "Dan wanne gidane Yaron? A wacce unguwa yake?"
Cikin kuka tace "Dadday bansan gidansu ba, ni bansan shi ba, yau nata6a ganinsa, Dan girman
Allah Daddy karka fadawa Babban Yaya, Allah kasheni zaiyi"
Cikin fishi Daddy yace "yau kika fara ganinsa har kika d'auki waya kika bashi saboda ga
yayanku me kudin banza yasiya miki waya ko?"
Ihsan tace "Daddy kayi hakuri, insha Allah bazata sake ba"
Sa'eed yakalli Ummah yace "Ummah kikira Babban Yaya kifada masa Dan Allah, sonake ya
dawo ya kakkarya yarinyar Nan, Danni idan nakamaki saina miki Dukan mutuwa, inyaso
nakawo gawarki, tunda haka kike so Dama"
Waheeda de tayi shiru, takasa cewa komai, Sai Jan zuciya take, fuskar Nan tayi jajir saboda
kuka
Ummah tace "bazan kirashi ba Sa'eed, kullum Waheeda cikin janyo mana masifa take, kullum
ninake kiransa nafada masa, yanzu Kam, bazan kirashi ba, idan kullum zan dinga kiransa Ina
fada masa matsala ai Kuma idan yaga kirana gabansa faduwa zai dinga yi,sannan Kuma bance
kufada masa ba, kubarshi yayi aikinsa, Daddynku zai dauki mataki akan haka"
Haka suka zauna a falon kowa yayi jugum, anrasa takamaimai Wanda zai kira Babban Yaya
yafada masa abinda yake faruwa ���
Washe gari Waheeda bataje school ba, haka ta zauna tayi shiru adaki kamar marar lafiya, ko
sunan Babban Yaya taji an ambata gabanta faduwa yake,yanda ta nutsu awaje daya, Sai gidan
yayi shiru, idan ka kalli Waheeda saita baka sha'awa yanda tazama wata kamila, saide kowa
taciki na ciki
Tsawon kwana biyu kenan da 6atan wayar Waheeda, har yanzu babu Wanda ya fad'awa
Babban Yaya, sannan daddy bai d'auki wani qwaqwaqwaran mataki ba, asalima fishi yake
da'ita, Kuma a kwana biyun Nan Waheeda bataje makaranta ba, tana zaune agida abun duniya
yataru yayi mata yawa, yau da yamma suna zaune, Anty Maryam tashigo gidan cikin tashi
Hankali, tana zuwa ta nufi Ummah tace "Ummah yajikin Waheeda? Ashe batada lafiya Amma
Ummah kukasa fadamin? Awanne asbitin aka kwantar da'ita?"
Kafin Ummah tasake magana, Maya tayi sallama cikin falon nasu tana sharar hawaye, ta
qarasa wajan Ummah tace "Ummah ashe Waheeda batada lafiya? Shiyasa Bata shiga
makaranta kwana biyu? Na tambayi 'yanbiyu sunce min lafiyarta kalau ashe 6oyemin sukayi"
Kan Ummah ya d'aure, ta kalli Maryam dinta dakuma Maya tace "Wai wacce Waheeda kuke
magana a kaine?"
Wayar Ummah ce tayi qara, ta d'auka tare fadin "sa'ad ya akayi?"
Yace" Ummah, wannan gayen daya sace wayar Waheeda fa inaga Dan damfara ne, ba'iya
wayar yakeso ba, harda damfara a tsarin nasa, yanzu Ina zaune yaturo min saqo Wai me
wannan wayar batada lafiya, tana kwance agadon Asbiti, Ana buqatar tallafin kudi, Sai kuma
account number aqasan saqon"
Ummah tace "innalillah.... Sa'ad shiyasa na kulleta Adaki fa, saboda muna Zaman zamanmu
wata Rana zatasa azo har gida a sacemu"
Sa'eed ne yake Kiran wayar, Ummah tace "Sa'ad kashe, ga dan'uwanka Nan Shima yana kira"
Tana daukar wayar Sa'eed din, Shima abinda yafada mata kenan, Ummah ta kashe wayar ta
kalli su Maryam "wallahi lafiyar Waheeda kalau......" anan Ummah ta basu labarin abinda yake
faruwa, Maya tace "Kai Amma wannan anyi tsinanne, yazo har gida yasace mata waya sannan
ya dinga turawa mutane cewa batada lafiya aturo Masa kudi?, Ummah Ina Waheedan?"
Ummah ta nunawa Maya d'akinsu Waheeda, tatashi ta nufi Dakin, anan taga Waheeda ta zauna
tayi shiru tana tunani
Maya ta dafata tace" Alhamdulillah, har hankali na ya kwanta wallahi qawata, text fa akamin
bakida lafiya, kina gadon Asbiti a kwance, Wai Ana buqatar tallafin kudi ta wani account Number
dayake Qasan saqon "
Waheeda tayi shiru takasa Bawa Maya amsa, Maya tace" Waheeda kalau kike kuwa? Inata
magana kinyi shiru? Yanzu Waheeda shawarar Dana baki ashe baki d'auka ba saida kika kula
saurayi?"
Waheeda tacire hannunta daga tagumin da tayi tace"Maya Babban Yaya"���
*** ** ***
Motsa jiki yake cikin nutsuwa da kwanciyar Hankali, wayarsa dake ajiye acan Gefe yaji tana
ringing, kafin ya dauka harta katse, dakatawa yayi da abinda yake ya d'auki ruwa yasha,
sannan ya d'auki wayar, number datake kiransa ma baisan taba, saikuma saqo guda daya,
daga Waheeda, yayi mamakin ganin saqon ta, saboda yasan bata masa text message, Kiran
ma ba sosai take neman saba, shiyasa saqon ya d'auki Hankalinsa, wajan zama ya nema,
sannan ya bud'e saqon Nata, abinda yagani ne yasashi yatsina fuskar sa, kamarya yatura kudi
ta wannan account din? Waheeda ce batada lafiya Amma akasa fada masa har wani account
number ake turowa atura tallafin kudi tanan? Account number waye wannan din?
"mashirmaciya" yafadi hakan a fili
Sannan yayi Dialing number Tata, har ta kusa katsewa sannan aka d'auka, memakon yaji
muryar Waheeda, Sai yaji muryar wani, lokaci d'aya yanayin fuskar sa ta sauya,wani irin baqin
kishi yataso masa, cikin 6acin rai,yace "waye?"
Daga d'ayan bangaren Sas soja yace "yayan me wayar ne, dama batada lafiya ne, tana kwance
agadon Asbiti, muna neman tallafin kudi ne Wanda za'a mata aiki dashi, shine mukabi list din
contact dinta muka tura musu"
Sumar Kansa ya hargitsa, cikin ransa yace Waheeda zata kasheni, Amma a fili saiyace "za'a
turo" daga Nan yakashe wayar
Yana kashewa wani Kiran yasake shigo wa, number da'aka kirashi da'ita d'azu ne, ya d'auka
tareda sallama, daga d'ayan bangaren akace "dawa muke magana?"
Kai tsaye yace "Naufal Umar Arabo,a.k.a Big Brother"
"Ok ikon Allah, ashe Big Brother ne, wato yalla6ai abinda yake faruwa shine, akwai wata
yarinya da akai kidnapping dinta, kidnappers din sun nemi atura musu kudi, Kuma iyayen
yarinyar sun tura musu kudin, daga qarshe Sai suka aikowa iyayen yarinyar da gawar 'yarsu, to
Wanda aka turawa kud'in mun bibiyi Sim card din dayake amfani dashi mungano yana waya da
iyayen yarinyar ne ta wata number waya, munyi bincike akan number, mungano number wata
yarinya ce sunanta Waheeda Umar Arabo, kamar yanda mukagani a rigister Sim card din,
saboda haka munyi tracking number Waheeda Umar Arabo mun dauki wasu daga numbers din
dayake kira, aciki muka Gani harda taka number,yanzu haka ma kunyi waya, shine mukeso ka
temaka mana, kafada mana inda yarinyar take, zamuje da'ita office dinmu, domin ta amsa mana
wasu tambayoyi dangane da wannan Mai laifin ko Allah zaisa mu kamashi "
Babban Yaya yayi shiruuuu yadafe goshinsa da hannunsa �丹��領����儭?,Yama Rasa
abinda zaice, har sukaji yayi shiru sukace"yalla6ai lafiya dai ko?ko bakasan yarinyar ba?"
Ajiyar zuciya yayi yace"nasanta, she's my Sister, kuyi hakuri kubani awa hudu, zanzo qasar,
saina Baku ita"
Godia sukayi masa dangane da had'in kan daya basu,sannan suka kashe wayar
Yajima a zaune a wajan, Yama Rasa wazai nema domin qarin bayani? Menene yahad'a ta da
wani har zata d'auki waya ta bashi? Tashi yayi yaje ya shirya, yayi mutuqar kyau cikin qananun
Kaya, saida ya toshe kunnansa da Bluetooth sannan ya d'auki wayarsa ya futo daga gidan
Karfe hudu na yamma ne yakawo shi gida, yana zuwa yakirasu, yafad'a musu yazo,su qara so
sutafi da yarinyar, tun karfe uku yakamata ace yazo, but saida yagama da jama'arsa sannan
yaqara so cikin gidan, kowa ganinsa yayi afalo kamar anjefo shi, gaba d'ayansu suna Nan 'Yan
gidan, zama yayi akan kujera, cikin mamakin ganinsa Ummah tace "Son, lafiya naganka
agida?"
Kansa a qasa yace "aina Dena zuwa ko'ina Ummah, haqura zanyi da aikina, saboda idan natafi
ma, Waheeda Virus zata dawo Dani"�對�������
Ummah tayi shiru kamar andoka mata sanda, cikin ranta tace yaji komai kenan, su Ihsan ne
suka tafi da gudu d'aki suka fad'awa Waheeda Babban Yaya yazo
Gabantane yafadi, ahankali tatashi tad'auko hijab d'inta ta6oye shi abayanta, tare suka futo falo,
Waheeda tafara bin bango zata gudu, a lokacin Yan sanda sukai sallama cikin falon
Babban Yaya yad'ago Kansa ya Kalle su, idanunsa sunyi jajir saboda tsantsar 6acin rai, ba
taredaya Kalle taba yace "ke Zonan"
Hawayene suka fara sintiri akan kyakykyawar fuskar ta, agaban sa ta tsugunna tafara
sheshshekar kuka,but takasa magana,kwata kwata taqi d'agowa ta kalli qwayar idonsa, cikin
6acin rai yace "ni Baban kine?"
Cikin kuka ta girgiza masa Kai hawaye wani nabin wani
Yace "to tunda ban haifeki ba, bazai iyu ki kasheni da raina ba"
qafarsa takama tariqe, cikin kuka , tace "Babban Yaya, Allah natuba, bazan sake ba, Babban
Yaya kayi hakuri karka sa sutafi Dani, wallahi Allah bazan sake ba"
Kuka ne yakama 'yanbiyu, su kansu Waheeda tabasu tausayi, sukuwa 'yanbiyu maza Sa'ad da
Sa'eed, wayarsu suka d'auka suke dannawa, Ummah ma tayi shiru tana Kallan su
Gaba d'aya falon ya kaure da kukan Waheeda dakuma na 'yanbiyu, Babban Yaya ya kalli 'Yan
sandan dasuke tsaye a bakin qofa yace "Yalla6ai gatanan kutafi da'ita"
Volume din kukansu ne yaqaru, wata daga cikin police din mace, tazo takama hannun Waheeda
tana janta, cikin kuka Waheeda take fadin "wayyo Allah na zasu tafi Dani, Babban Yaya!
Babban Yaya!! Babban Yaya!!"
Har suka jata, suka tafi da'ita, bata daina kiransa ba.
Amnah
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandama���: BABBAN YAYA
Writing By Amnah El Yaqoub
Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/
13&14
'Yanbiyu ne sukai d'akinsu da gudu suna kuka, Ihsan ta d'auki wayarta cikin kuka ta fad'awa
Anty Maryam halin da ake ciki.
Kwantar da Kansa yayi ajikin kujera ya Lumshe idonsa, yanda take qwala masa kira har yanzu
muryarta takasa barin kunnansa, Ummah ta Kalle shi tace "kaje Kaci abinci kahuta"
Ajiyar zuciya yayi, sannan ya bud'e idonsa yatashi yanufi qofa
Ummah tace "Ina zakaje Kuma?"
Cikin damuwa yace "Zanje ayi bincike akan Yaron ne"
Sa'eed dake danne danne awaya yad'aga Kansa yace "Babban Yaya Dan Allah ka rabu da
yarinyar Nan, kaje ka huta"
Wani irin kallo yayiwa Sa'eed ba tareda yace komai ba yafice daga falon, Ummah tayi ajiyar
zuciya tareda miqewa, tana mamakin irin wannan shaquwa ta Naufal da Waheeda, tasan bazai
iya barinta acan ba,haqiqa yana kula da qannansa yanda ya kamata, Albarka tashiga saka
masa acikin zuciyarta, tasan cewa tayi sa'ar samun sa acikin a matsayin Babba, koda babu
ransu, zai iya riqe qannansa sa.
Yana zuwa compound driver ya d'auke shi suka fita, saboda yagaji
Kai tsaye mtn office suka nufa, yasa aka rufe layin Nata, sannan sukaje police station sukai
report,sannan yayiwa d.p.o magana akan abinda yake faruwa,d.p.o ya basu wani 'Dan sanda
suka nufi banki dashi, acan banki ma Kai tsaye yanemi ganin manajan bankin, yayi sa'ah kuwa
yana Nan, saide yana shirin fita ne, kasancewar sa sananne Sai kowa yake Kallan sa acikin
bankin, suna qarasa wa office din manaja, yafad'a masa abinda yakawo shi, manaja yanemi
account din da gayen yake turawa, sukayi bincike akan account din, anan aka Gano asalin
sunansa, da sunan iyayensa dakuma sauran bayanai, Babban Yaya yayi masa godia sannan
yasa driver yakai shi inda aka Kai Waheeda, suna zuwa aka basu wajan zama, d'aya daga cikin
ma'aikatan yace "yalla6ai yarinyar Nan fa tunda mukazo take kuka, daqyar da lallashi muka
samu tabamu amsar abinda mukeso"
Babban Yaya yace "Baku daketa bane, inda taji duka zata muku bayani ai"
Murmushi yayi yace "ai hakan ma mungode sosai wallahi, ta fad'a mana itama damfarar ta yayi,
yanzu zaku iya tafiya,mukuma zamuci gaba da bincike, idan wani