Showing 27001 words to 30000 words out of 76958 words
Chapter 10 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf
layla tayi saurin Kai Masa duka a kafada tana cewa,
Mode spoiler.
Ajiyar zuciya tasake da qarfi tareda miqewa tabi bayansa da gudu tana cewa,
saidakasa zuciyana tsinkewa Allah saina ragewa coconut head 'din Nan naka girma.
Dakin ammy yayi Yana dariya tabisa Nan ammy taraba rigimar Layla tace,
Allah ammy ya rainamu yaron Nan jifa yanda yatashi saka kwalliyar damuka tsara"""tafada tana
gyarawa aleeya gyaran gashinta da sul6insa yasa yafara zarewa daga ribbon.
Sallamar siyama ce tasa dukkaninsu juyawa cikeda mamaki sbd ba Wanda yasakaran ganinta.
Fuska 'daukeda murmushi da farin cikin da baikai zuciba ta qaraso tareda rungume aleeya tana
cewa,
Wow cousin you're looking fabulous.
Murmushin yaqe tasaki tace,
Thank you siyama saukar bazata.
Eh wlh naso baku surprise ne,
Ammy ina wuni ya nasameku?
Lpia klau siyama,
Yasu anty Nana da babanki.
Duk suna gaisheku.
Kallon Layla tayi fuska asake tace,
Layla ya gida.
Lafiya qlau""tace tareda miqewa ta fice tana cewa,
Bari naje naqara duba cake 'din da Nana keyi koyayi.
Tana fita aleeya da siyama suka biyo bayanta suna 'dan fira.
Suna bedroom 'dinsu sukaji isowar baqin kusan atare zuciyoyinsu suka buga lokacinda Bilal
yashigo yafada musu baqin na Palon Abba.
Fira sukeyi Amma kowa kusan Rabin hankalinsa baya gurin.
Acan palon kuwa taheer ne yashigo taredasu dad dawood kuwa harabar gidan ya tsaya Kiran
numbern Layla Amma yakasa samu jiyake kamar zai zauce idan baiji muryarta alokacinba.
Ammy ta gaisa dasu sosai cikin girmama takalli taheer dake gaidata ta amsa a mutumce sbd
tunanin shine dawood din kafin sukai palonta da mum.
Nur ce agaba sai aleeya da siyama abayanta suka shigo palon ammy.
Zuciyar mum cikeda farin ciki ta amsa gaisuwarsu tana qara godewa Allah dazai cika Mata
burinta.
Nur dake gefen ammy ta kafawa Ido ganin wani irin hutu da kwarjini dake fita a jikinta Nan take
taji tana yiwa kanta sha'awar ace sirikarta ce,
Tabbas tafi dacewa da dawood 'dinta saidai lokaci ya qure saidai taheer 'dinta.
Ficewa sukai daga 'dakin ammy tace,
Layla kije ki qarasa da dawood din guests palour zaifi sakewa sbd su abban Naga hirar
business suke tukuna.
Ok ammy.
Aleeya da siyama bedroom suka koma ita Kuma ta nufi palon Abba Kai tsaye.
Da sallama ta shiga..
A cikin idanuwan taheer idanunta suka Fara sauka tayi saurin sunkuyar dakai numfashinta na
fita da sauri.
Gaidasu abban tayi tasanarda abinda yakawota Nan taheer daya Dade da mutuwar zaune
miqewa sbd baita6a tunanin Laylar ta zarce yanda take a hoto sosai.
Fitowa sukayi palon yace Mata dawood na harabar gidan.
Shigar dashi palon tayi suna qara gaisawa ta juya tana cewa,
Bari naje na shigo dashi.
Tundaga nesa ta hangosa ya bada baya Yana waya saidai kallo 'daya tayiwa bayansa ta tsaya
hakanan taji numfashinta na fita da sauri ta tsaya cak kamar wadda aka tsayar.
Wayarta yaqara Kira cikin sa'a tayi ringing.
Saurin kallon wayar hannunta tayi shikuwa Jin qaran waya bayansa yasashi juyowa.
Wani irin jirine ya 'dibeta tayi saurin juyawa ta shige Palo batareda tabari yaqarasa juyowaba.
Rawa jikinta yakeyi sosai daqyar ta lalubi kujera ta zauna tana qoqarin Jan numfashinta ya
tsaya.
Sake shigowa Kiran yayi tana gani ya katse zuwa lokacin ko wayar ta kasa riqewa rawa jikinta
keyi sosai arikice ta miqe tayi dakin Nana sbd can ne kawai tasan ba Wanda zai ganta cikin
wannan yanayin.
#mamuhgee
VOTE
COMMENT.
[1/8, 8:37 PM] 0mmr Farouk: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*19*
Kasa zama tayi kodata shiga 'dakin ta tsaya tsakiyar 'dakin tana qoqarin samarwa kanta
nutsuwar fahimtar abinda ke tabbatuwa arayuwarsu,
Wasu irin hawayene suka gangaro Mata tana qoqarin danne kukan dakeson biyo bayansu.
Dawood 'dinta shine dawood 'din da aleeyarta keso meyasa takasa fahimta tuntuni daya
sanarda ita garinda iyayensa suke.?
Meyasa dawood yaqi fada Mata cewar,
Iyayensa sun nemar Masa Mata...?
Wannen wane irin alamarine ya kusantosu.
Rufe Ido tayi tana tsananin Jin zafi azuciyarta,
Rawa qafafuwanta suka Fara yimata ta sulale tsakiyar 'dakin hawayenta na tsananta gudu
sabuwar doyayyar dawood takeji har cikin jininta,
Soyayyar dawood tariga tazamo wani 6ari na jikinta wani irin zafi da nauyi takeji ayanxu data
gansa amatsayin na aleeyarts to Yaya aleeya zataji idan taji shine dawood 'dinta.
Girgixa Kai tayi hawayenta na qara gudu cikin rawar murya ahankali tace,
Wlh zafi nakeji sosai cikin zuciyana aleeya bazanso kiji wannan zafinba Bazaki iya juresaba.
Ahankali tafara kuka Mai qaramin sauti har lokacin jikinta Bai daina rawaba.
Tunowa da ammy yasa ta tsayarda kukanta tareda tattaro qarfin Hali tasawa zuciyarta ta share
fuskarta tareda miqewa da sauri ta fice tana roqon Allah yasa ammy da dawood basuga junaba.
'dakin ammy ta nufa tana qara qoqarin danne halinda take ciki.
Ammy ce kawai a 'dakin itama wayarta tazo 'dauka takoma palon gurinsu Abba.
Ahankali ta qaraso gaban ammy ta riqo hannunta tareda dawowa bakin gado suka zauna.
Sunkuyar dakai tayi hawayen datake qoqarin dannewa sunason fitowa Amma ta 'daure ta
mayar dasu Amma idanuwanta sun jajir.
Sanyi jikin ammy yayi ta qura Mata idanuwa ta lurada yanda jikinta ke 'dan rawa ta riqo
hannunta da sauri cikin tsananin fargaba tace,
Layla?
'dagowa tayi takalli ammyn Nan take ammy ta qara shiga ru'dani ganin Jan idanuwanta tace,
Layla meke faruwa?
Ammy tunda na taso cikin quncin rayuwa da talauci na taso,
Babu Wanda ya ta6a yimin kallon mutum bare ya bani mutuntawa da darajar da Allah yabawa
mutum,
Ni Almajirace 'yar bola Mara asali da gata,
Ammy duk duniya bayan iyayena dasuka haifeni Babu Wanda nake tsananin so da qaunar farin
cikinta irin aleeya sbd itace takalleni amatsayin mutum ta miqamin hannu ta cironi daga
qanqantacciyar rayuwar titi da bolan danakeyi Wanda da yanxu na zama wata abar qyamar.,
Ammy har abada ina roqon Allah daya nesantani da abinda zaisa nakawo damuwa a fuskar
aleeya.,.....
Sosai jikin ammy yayi sanyi murya a sanyaye tace,
Layla meyasa kike tado da abinda yazamo tarihi?.....
Dr Dawood ne Wanda aleeya zata aura..
Yawu ammy ta ha'diye sbd gudun garajen fahimta tace,
Banganeba Layla sakemin bayani.
Ammy dr dawood shine 'dan abokin Abba dasukazo yanxu.
Mummunan fa'duwa gaban ammy yayi ta lashi busasshen bakinta sai alokacin tasake qurawa
layla Ido taqara hango mummunan halinda take ciki tana qoqarin dannewa.
Layla wannan ba abun damuwa bane tunda ba auren aka 'dauraba zanyiwasu abbanku bayani
yanxu..
Miqewa tayi laylar ta riqo hannunta tareda dawowa gabanta ta sunkuyar dakai cikeda qarfin Hali
tace,
Ammy ke uwace dabakyason kan 'yayanki ya rabu,
Kin manta nayi Miki alqawarin toshe duk wata hanya dazata kawo 6araka atsakaninmu,
Ammy wannan shine alqawarina dazan cika bazan ta6a Bari hawaye yasauka kan fuskar
aleeya ba ta hanyata,
Ammy kiyimin alqawarin har abada Bazaki ta6a fadawa kowa wannan maganarba...
Girgixa Kai ammy tayi cikin tsananin tashin hankali da damuwa tace,
Wannan shirme ne kikeyi layla sbd bazai ta6a yiyuwaba,
Idan har farin ciki kikesowa aleeya to Bazaki Bari ta auri Wanda baya sonta yanada wadda
yakeso wace irin rayuwar aure zatayi da Wanda keson wata mace ba itaba...
Hawaye ta goge da bayan hannu tace,
Ammy shine farin cikinta,shitakeso bazata ta6a iyason waniba bayansa....
Kidaina fadamin haka sbd wannan ba sacrifice bane Layla rayuwarku ce ku uku zata lalace,
Kalli halinda kike ciki yanxu,
Ji yanda kike qowarin danne quncin dake ranki Amma ina iya ganinsa,
Dawood ke yakeso bazai ta6a son aleeya ba sbd tun farko ba ita yakesoba.
Tsananta hawayenta sukayi tace,
Ammy Koda Baki yardaba na yafe dawood har abada sbd bazan iya cigaba dason abinda
aleeya kesoba,
Wannan alqawarina ne duk ranarda aleeya taji zancen Nan zan tafi tafiya ta har abada ammy
sbd bazan iya hada Ido da itaba nayi tarayya da ita akan abinda takeso nakasa cirewa zuciyata
cewa hakan ba laifina bane.
Tsananta tashin hankalin ammy yayi tace,
Layla meyasa zakiyi haka Dan kuwa hakan shine babban kuskuren dazaki tafka wannan ba
mafita bace.
Kuka tasake ahankali ammyn tayi saurin rungumeta tana danne nata hawayen sbd Laylan
tasakata a tsaka Mai wuya sbd rayuwarsu duka su biyun ne zata lalace garin toshe 6araka
za'ayi gaba Mara da'di.
Jin motsin shigowa yasa laylar zamewa ta miqe ta shige toilet 'din ammy.
Siyama dake jinsu tun farko ta gyara tsayuwarta tareda sakin wani shu'umin murmushi tace,
Hmmnn dagani abubuwa zasu zomin yanda suka Dace,
Dawood sukeso dukkaninsu hmmm,
I will make this my mission matuqar inada Rai da lafiya bazan ta6a Bari aleeya tasan da
wannan zancenba sbd dataji kamar koyaushe Layla xata samesa hakan na nufin koyaushe
itace a gabanta..
Duk Wanda yayi qoqarin ha'dasu kuwa saita 'dorasa adaidai inda bazai qara kallon matsalar
waniba tasama tafi qarfinsa.
Mission 'dinta na biyu kuwa taheer,
Kallo 'daya tayi Masa ya tafi da zuciyarta Dan haka kuwa duk duniya batasaran zata zauna ta
huta batareda burinta na aurensa ya cikaba.
Daki takoma tana zuba murmushin farin cikin samun sauqin abunda yakawota.
Aleeya kuwa tunda sukaje palon taheer kawai suka tarar suka gaisa siyama kallo 'daya tai Masa
tasaki Baki tuni tafara tunanin yanda rayuwarta zata canza idan ta auresa.
Ganin zata zubarwa da kanta aji gurin kallonsa yasa tamiqe takoma 'daki anan kunnuwanta
sukayo Mata farin ji.
Fira suke hankalinsu kwance akai akai saiya Fadi sunan Layla saidai kawai tayi Masa dariya
sbd tun acan tafada Masa akwai Wanda Laylar keso.
Daqyar taheer yaje yashigo dashi sbd lokaci 'daya ya burkice sbd rashin Jin Nur gashi yanxu ta
kashe wayar gabaki 'daya ma.
Kodaya shigo Sam mantawa yayi da maganar inda yake daqyar taheer yayita basa Baki yadan
sassauto ya nutsu.
Kallon inda take yayi fuska a ha'de..
Lumshe Ido yayi cikin tsananin takaici,
Mum Sam batamasan abinda zai iya soba,.
Fa'duwa gabanta yayi ganin irin kallon daya jefeta dashi amma duk da haka zuciyarta cike take
fal da farin cikin ganinsa Wanda tuni sonsa yaci gaba da ninkuwa a zuciyarta.
Kasa magana yayi sbd yanda nutsuwarsa ke qara hautsinewa ya miqe tareda fiddo wayarsa ya
fice Yana cigabada Kiran Nur.
Taheer ne yabiyosa da nufin fada Masa abinda yayi Bai daceba Amma ganin yanayinsa sai
jikinsa yayi sanyi yace,
Dawood please relax kabari zuwa anjima saika sake Kira yanxu bakaga muna gidan kunya
bane.
Wani mugun kallo ya watsa Masa tareda juyawa ya tada motar dasukazo da ita daga gidansu
nanan yabar gidan gaba 'daya.
#mamuhgee.
Vote
Comment.
[1/8, 8:38 PM] 0mmr Farouk: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*_godiya da jinjina ga members na DAWOOD fans group_*í ½í²‹
*20*
Jingina jikin qofar toilet 'din ta jingina tareda zamewa ta durqusa tareda sakin kukan datake
dannewa gaban ammy ahankali,
Shesheka takeyi sosai tasa hannu ta rufe bakinta kukan ba tsananta.
Rarrashin kanta tayi ta miqe ta tsaya gaban mirror tareda kallon fuskarta taga yanda lokaci
'daya tayi jajir.
Wanke fuskar tayi jiki ba qwari ta goge fuskar da towel tareda qara tattaro juriya ta fito.
Har lokacin ammy na zaune bakin gadon ta rafka tagumi da hannuwa biyu takasa miqewa bare
ta fita takoma Palo.
Fitowarta yasa ammy 'dagowa ta qura Mata ido ta yanda fuskarta tayi jajir lokaci 'daya har wani
fa'dawa fuskarta tayi.
Qofa ta nufa zata fice ganin kallon da ammy ke Mata taji tace,
Layla matuqar Bazaki auri dawood ba aleeya ma bazata auresaba.
Da sauri ta juyo tana kallon ammyn.
Eh wannan nawa hukuncin ne sbd Babu dalilin dazaisa ta auri Wanda baya sonta ko ka'dan 'yar
uwarta yakeso.
Dawowa tayi ta zauna murya a karye tace,
Ammy kenan niba 'yar uwar aleeya bace.
Me kike fada layla??har abada aleeya Yar uwarkice.
Idan har 'yar uwatace Ni 'yarkice to ammy bazaki hanata samun abinda takesoba sbd ni
bansamu ba.,
Ammy mezamu fadawa su Abba idan kikace aleeya bazata auri dawood ba?
Kowa zaisan abinda yake faruwa daganan za'a iya samun rashin fahimta daga wasu Kinga
qarshe dai abinda ake gujewar zai faru Kuma dukkanin 'yayanki zasu rasa farin cikinsu hakan
zai ta6a zuciyarki da kwanciyar hankalin gidannan,
Ina roqonki ammy daki Bari aleeya tasamu farin ciki da Wanda takeso.....
Katseta tayi cikin 'dan 'daga murya da cewa,
Layla kin kasa ganewa farin cikin ne bazata samuba har abada idan ta auresa.,Kuma me zai
faru idan dawood ya ganki amatsayin 'yar uwarta kina tunanin zaiyi shiru ne?
Numfashi Mai ciwo ta sauke murya a karye tace,
Bazai qara ganinaba ammy sbd na yanke duk wata alaqa dashi saita wadda zamu Fara yanxu
bayan aurnsa da aleeya amatsayin 'yar uwar matarsa.
Ammy kiyimin wannan alqawarin na bazaki fadawa aleeya ba.
Me kike cewane Layla?""sukaji anfada daga bakin qofa.
Itakadaice ta juya da sauri tana qoqarin danne halinda dake ciki ganin aleeya a tsaye bakin
qofa.
Ammy kuwa miqewa tayi ta fice batareda takalli su duka biyunba sbd zuciyarta na ingizatane ga
fadar gskia saidai Kuma fadar gskiar zai iya kawo rashin fahimta sbd shaidan zai iya saka musu
kishin juna ko yayane sbd za'a iya cewa ya auresu duka Wanda kwata kwata har abada
bazataso hakanba Dan Dole watarana za'a samu sa6ani.
Qarasowa tayi jikinta amatuqar sanyaye,
Da sanyin jikin abinda dawood yayi Mata ta shigo Amma Jin abinda Layla ke fada ya qara
sanyaya jikinta.
Zama tayi kusada laylar tana kallonta cikeda mamaki da fargabar ganin sauyi sosai atareda ita,
Idanuwanta dasukai jajir da fuskartama gaba 'daya takalla tuni kafin taji koma meyene
idanuwanta suka cicciko Nan take damuwar datake ciki ta dawood ta 6ace asanyaye tace,
Dama Layla akwai abinda harzaki saka wani alqawarin kar afadamin??
Wane irin sirrine da Ni bazan iya 6oye mikiba har kike guduna dashi....
Jin muryar aleeyar tafara rawa yasa tayi saurin riqo hannunta tana qoqarin Hana hawayenta
fitowa Amma Saida suka gangaro tace,
Har abada Babu wani sirri dazan 6oye Miki idanma akwai to kisaka aranki Dan ciganki da farin
cikinki ne...
Inason sanin koma menene Layla kifadamin tun kafin zuciyata ta buga da fargaba.
Share hawayenta tayi ahankali tace,
Dawood iyayensa sun Masa Mata har antsayar da ranar aurensu bazai ta6a aurena......
Tun kafin laylar takai qarshe kukan datake riqewane ya kubce Mata tayi saurin rungume laylar
cikeda wani irin tausayinta dama tanason yin Kuka Dan rage zugin zuciyarta na tsantsar
qiyayyarta data hango a idanuwan dawood idan ba kuskuren gani tayiba.
Kuka take sosai na tausayin Layla da kanta saidai tafasa fadawa Layla damuwarta Akan
qiyayyarta data gani a idon dawood sbd karta qara Mata damuwa ko ammy bazata fadawa ba
zata bar maganar aranta ta Taya 'yar uwarta jimamin abinda yasameta..
Sosai tayi qarfin Hali ta nunawa aleeya ta rumgumi hakan amatsayin dama bashine mijinta ba.
Girgixa Kai aleeya tayi tana fitarda sabbin hawaye tace,
Yanda kikesonsa har abada bazaki daina sonsaba,
Tun zamana dake akwai wasu farin ciki da annashuwa dashine kadai yake sakiyinsu koni bana
sakaki duk kuwa danasan babbn matsayin danake dashi agunki,
Layla bazaki iya babushi ba Ni zanje har gurinsa na roqesa yadawo gareki zan qasqantar da
kaina na roqesa qasqantarwa ta qarshe Dan yadawo gareki..
Share hawayenta tayi tana qaqalo murmushin qarfin Hali sbd so take arufe maganar dawood da
ita gaba 'daya ayau basai ankwanaba ga kanta dake tsananta ciwo zazza6i Mai zafi takeji sosai.
Aleeya na dangana nabarsa har abada Dan haka daki tayani nemosa gwara kitayani mantawa
dashi.
Sake rungumeta aleeya tayi cikin tsananin tausayinta da Jin zafin dawood 'din daya za6i wata
yabar Layla Nan take taji ta tsanesa Koda zai dawo bazata ta6a barinsa ya auri Laylan ba sbd
Bai cancancetaba
Laylanta ta cancanci Wanda yasan darajarta fiyeda komai.
Jin jikin laylar da zafi yasa ta ja hannunta suka koma bedroom 'dinsu ta kwantarda ita tareda ja
Mata bargo cikeda kulawa tace,
Have some rest zakiji qarfi zuwa anjima.
Miqewa tayi ta zame kayanta tasa jeans da vest tadawo bakin gadon da laylar ke kwance ta
rafka tagumi cikeda tunani da damuwar kanta data laylar.
Itama Layla rufe idanuwan kawai tayi.
Daqyar ammy ke sakin murmushin yaqe hardai Abba ya tambayeta maganar iyayen manemin
Layla kawai suke jira su qaraso yanxu.
Rufe idanuwa tayi tareda ha'diye wani 'daci a maqoshinta cikeda damuwar abinda zata fada
tace,
Saidai ayi hkr akwai wadda iyayensa keso ya aura Dan haka sun fasa zuwa saidai zuwa gaba
idan ansamu fahimta.
Fada Abba yahauyi Rai a6ace yace,
Dama dai bada gskia yakeyiba Dan da bazai Raina Mana hankaliba yace zasuzo.
Hakuqi CJ yabawa abban Yana cewa,
Agodewa Allah bama Saida akazo 'daurin aure yace yafasaba.
Exactly fa ai gwara da tun yanxu akasan stand nasu""""mum ce tafada hakan tana nuna
tausawarta ga ammy datayi nisa a tunani ko abinda suke fada bataji.
Zuciya ba da'di hakanan Abba da dad suka tsayar da bikin wata biyu Masu zuwa hakanan mum
ta haqura badan tasoba sbd da wuri taso ayi.
Koda suka koma gida dawood bayanan Kota kansa batabiba tayita harkokinta cikin farin ciki.
Baidawo gidanba sai dare sosai kallo 'daya zakai Masa yabaka tausayi sbd kwata kwata Bai
saba da wahala ba Amma yau ko ruwa baisawa cikinsaba haukacewane kawai baiyiba gurin
Kiran layinta yakira yakira,yayi yawo agarin harya 6ata saidaya Kira taheer yaje yadawo gida
dashi.
Ganin yanda daqyar yake bude bakinsa daya bushe yasa mum da taheer hankalinsu Fara tashi
Nan tahau lallashinsa akan yasha Koda juice ne Amma yaqi.
Wasa wasa saiga zazza6i Mai qarfi ya kwantar dashi adaren Babu Wanda ya rintsa cj