Showing 12001 words to 15000 words out of 76958 words
Chapter 5 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf
wannan yafi.
Decorations din dakin aleeya aka canxa musu komai bibbiyu aleeya blue Layla pink Amma
gadonsu 'daya.
Kaya sosai ammy ta 'dinka musu kusan komai iri daya sbd gabaki 'daya aleeya cewa tayi
batason komai nata asiya musu sababbi iri daya da Layla.
Ba iyayenta da Masu aikin gidan kadaiba hatta ita kanta layla mamakin tsananin qaunarda
aleeya ke Mata takeyi sbd kaf rayuwarta ba'a ta6a nuna Mata qauna irin wannanba saidai
iyayenta.
Bilal kuwa 'dakinsa dabam da Mai kula dashi Shima komai ansaka Masa tundaga kan wardrobe
kayan wasa dana karatu sbd suna dawowa Basu wani jimaba aka sakashi makaranta primary 1
Amma ana hada Masa da lesson sbd yayi saurin fahimta Dan na class na Masa wuyar ganewa
tunda ba ta6a shiga aji yayiba.
Layla kuwa Mai lesson guda aka dauko Mata sunayi ba qaqqautawa ga malamin arabic dake
zuwa har gida Yana musu su duka uku Dan dama aleeya Bata zuwa islamiya saidai malam
yazo gida ya karantar da ita.
Kullum dare kafin su kwanta sai aleeya tayita nanata Mata karantunta na lesson na addini kuwa
sai sunyi sallar asuba.
Ada aleeya Batada wata walwa ko sakewa kullum tana daki kwance Wanda hakan ke matuqar
ta6a zuciyar iyayenta harsuka dauko siyama 'yar yayar ammy riqo Amma rawar kanta da rashin
nutsuwarta yasa suka mayar da ita gashi Sam basa shiri sosai da aleeya kullum cikin fada suke
da kokawa da komai sai anrabasu Amma yanxu zuwansu Layla yasa hankalinsu kwanciya
matuqa sbd ganin farin ciki a rayuwar 'yarsu su kansu yanxu hankalinsu yaqara kwantawa ganin
gidan yasake kammala da yara Dan kuwa dukkaninsu jinsu sukeyi kamar yayan dasuka haifa
uwa uba yanda Bilal yasake musu Yana yanda yakeso kamar sune suka haifesa ba ruwansa.
Lokacinda su aleeya zasu rubuta junior waec aka kutsa layla cikinsu ta zana duk da batai wani
kyauba Amma ba laifi tasamu 4 credit shima sbd antaimaka matane sosai gurin rubutawar
hutun shiga senior class suka fara cikin farin ciki sbd next hutu tare zasu koma and this time
around boarding school zasu duk da ammy bataso sune sukeso Abba yace kuma tunda sunaso
sai ankaisu.
Kwance suke a 'daki suna kallon hotunan dasukai a wayar ammy Bilal yashigo hannunsa riqeda
wayar ammy 'daya Yana game yace,
Ammy tace kubata wayanta.
Ba Wanda ya kallesa cikinsu aleeya tace,
Ka Kai Mata na hannunka wannan muna hotuna ne.
Juyawa yayi da gudu saidai suka jiyo ihunsa da qarfi Yana Kiran Layla.
Azabure suka fito suna kaiwa Palo suka tsaya kallon wadda ke tsaye da babban akwatinta da
alama shigowarta kenan sukaci karo tayi wani mugun ball dashi.
Da sauri aleeya ta qarasa ta riqosa daidai fitowar ammy tana cewa,
Lafiya waye ya ta6asa aleeya kune ko....
Ganin siyama tsaye yasa sake fara'a tana cewa,
Siyama kece daga zuwanki Kika ta6amin 'da.
Wani 'dacin baqin ciki ta ha'diye daqyar ta qaqalo murmushi tace,
Wlh karo mukayi bamu luraba.
Nasan arina dama bayason tafiya kullum saidai gudu,
Sannunki da hanya tafiyar bazata Kuma fa ko 'dazu nakira antin mun gaisa Amma Bata
fadaminba.
Eh wlh ammy ninace Dan Allah karta fada muku nafiso ku ganni.
To ai kin kyauta saiku wuce ciki ki huta kici abinci.
Dakinsu ta nufa da akwatinta batareda ta kalli ko gefenda Layla takeba sbd zata iya ha'diyar
zuciya sbd baqin cikin ganin yanda harta zarta aleeya kyan gani duk da aleeya ma ba bayaba
gurin kyau.
Ammy Jan Bilal tayi suka wuce dakinta layla kuwa na ganin haka tayi kicin gurin shafa'atu tana
tayata aikin abincin dare.
Aleeya ma kicin din tazo bayan taje sun 'dan ta6a fira da siyamar ta zauna kan freezer tana
kallonsu suna aiki sai surutu take musu na wani labari suna dariya hankalinsu kwance.
Da daddare ma kafinsu kwanta Saida siyama taso cin zarafin layla kamar ammy tasani ta Aiko
Bilal yakira layla tace tayi kwanciyarta a 'dakinta itakuma ta wuce dakin Abba.
Tunda siyama tazo gidan yazamewa layla wani iri sbd tsangwama duk da alamu dayawa sun
nuna su Layla sun fita matsayi agidan yanxu hakan ke qara Mata wata irin tsanar Layla har cikin
jininta takejinta duk da layla da ammy sunqi Bata fuskar wulaqantasu laylar duk saitaji zama
gidan yafita ranta daqyar tayi sati biyu ta tattara takomawarta gida ta shiryawa uwarta qarya da
gaskiya akansu laylar Nan itama umman ta qullaci ammy akan wulaqanta siyamar da'akayi kan
sadaka yallah 'yayan tsintuwa.
Siyama na tafiya gidansu yadawo yanda yake hankalinsu Layla ya kwanta gashi lokacin
tafiyarsu makaranta yayi tuni akayi musu komai aka kaisu Bilal harda kukansa shima akaisa
bording school akasamu aka lalla6asa bayan kwana biyu tuni ya manta da maganar bording
yafara sabawa da kadaicinsu danma shafa'atu ta iya debe Masa kewa sosai idan Abba na gari
kuwa shekanan yafi kowa farin ciki.
#mamuhgee
VOTE
COMMENT
[1/1, 11:04 PM] +234 701 680 1465: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*9*
Ranar dasuka Fara kwana a hostel aleeya na ganin dare yayi tsoro Yakamata tafara kukan
neman gida murmushi Layla tayi cikeda tausayin aleeyarta tadawo kusada ita ta kwanta tana
rarrashinta itakam data Sha kwana bola da titi sam bataji tsoron kwana anan dinba kawai dai
sai kewar gida dasu Bilal da ammy.
Kuka sosai aleeya tayi duk sai laylar hankalinta yatashi itama saidatayi kukan.
Tun ranar kullum tare suke kwana a gado 'daya sbd kullum sai aleeya tayi kukan dare Kuma
idan ba Layla kusada ita Bata iya bacci ahaka harsuka Fara sabawa da yanayin rayuwar
makaranta sukadai,
Sam basuyi wasu qawaye ba sbd basason wani yashiga tsakaninsu Wanda ammy tayi musu
fada sosai akan duk sukayi qawaye to saisun shiga tsakaninsu shiyasa Sam sinqi yarda suyi
qawa ko 'daya Dan kar a rabasu sbd zuwa lokacin jisuke bazasu iya rayuwa ba junaba..(ha'di
daga Allah).
Sosai aleeya ke dagewa tana fahimtarda Layla duk karantunda ake musu itama Kuma Layla
itake dagewa kulada komai nasu gurin zamansu na hostel sbd duk wata wahala aleeyar Bata
Saba da itaba.
Ahaka harsukai exams sukayi hutu
Ranar dasuka dawo Bilal da ammy murna kamar me Amma su ammy sunsha dariyarsu ganin
yanda suka rame sukai duhu musamman ma aleeya da Bata Saba da wahala ba ko kadan.
Sukuwa mamakin ganin girman bilal sukayi Dan dama shi jikinsa irin Mai girman Nan ne.
Tunda suka dawo hutun gaske sukeyi Dan koina basa fita so biyu kawai suka fita 'daya tareda
ammy 'daya Kuma sukadai direba yakaisu gidan qawar ammy gurin birthday party din 'yar
qaramar 'yarta.
Kamar qyatawar Ido hutunsu ya qare suka koma school.
Sannu ahankali harsukai ss3 lokacin tuni 'yan matanci ya bayyana Dan kuwa kowaccensu
tazama budurwa kuma ba laifi kowace nada sama da qasa daidai jikinta duk da dai dukkaninsu
baza'a kirasu da sirara ba ko Masu qiba jikinsu saidai aleeya tafi Layla jiki kadan ita Kuma layla
tafi aleeya tsawo kadan ta 6angaren kyawu kuwa saidai ace Masha Allah Dan kuwa 'yan matan
na ammy sunadashi Layla kyawunta na buzayen asali yafito aleeya kuwa kyawun asalin fulanin
adamawa.
Ranar dasuka gama makaranta ranar abbansu yayi musu kyautar manyan wayoyin da kyautar
zuwa umrah gabaki 'dayansu gidan Nan suka hau murna da tsalle tsalle.
Bilal zuwa lokacin Yana js3 ne Amma girman jikinsa harya kusa kamosu Kuma lokacin tuni
yarinta ta tafara tafiya yafara sanin kansa Dan har musabaqar qur'ani yashiga sabuwar
islamiyar da aka kaisa bayan tafiyarsu makaranta Kuma yazo da uku kuma hakan ba qaramin
alfahari yasa su Abba ba sbd zuwa lokacin kowa tunanin yake dukkaninsu 'yayansa ne.
Satinsu biyu suka wuce umrah dukkaninsu.
Lokacinda layla taganta gaban 'dakin Allah tayi kuka sosai sbd ko acikin mafarki Bata ta6a
gangancin tunanin samun irin wannan rayuwarba saidai batasan Mai Allah yatanadar wa
rayuwarsu agaba ba Ashe,.
Tayiwa mahaifanta dasu Abba addua ba iyaka kafin musamman ta roqi Allah karya kawo komai
na duniya dazai shiga tsakanin qaunar dasukewa juna itada aleeyarta sbd aleeya wani
6angarene na rayuwarta dasai mutuwace zata rabata dashi duk da tasan qaunar da aleeya ke
Mata bazama ta kwatanta da wadda ita take mataba.
Tana gamawa ta juyo ahankali ta nufi gurinda su aleeya da Bilal ke jiranta sbd ammy da Abba
suna tareda baqi a masaukinsu yau Basu fitoba.
Fitowa sukayi daga masallacin suka tsaya wani tsadadden gurin Shan coffee da cake sbd shine
yawanci Layla fitiso takasa iya cin abincin garin aleeya da Bilal kuwa komai rashin da'din abinci
sai sun gwada cinsa.
Su aleeya ne agaba tana bayansu wayarta take dubawa kanta na qasa.
Karo tayi da mutum gabanta yayi mummunan fa'duwa saita kasa 'dagowa ta durqusa qasa ta
'dauki wayarta ta ta6a da sauri zata wuce......
I think you're taking what's mine miss...
Cak ta tsaya jikinta ya 'dauki rawa Nan take Sam hakanan takejin batason ha'da Ido da koma
waye
Saurin kallon hannunta tayi taga ba wayarta bace ta 'dauka da sauri ta miqa Masa batareda ta
juyoba..
Hannu yakai zai kar6a....
Dawood...aka kira sunansa daga bayansa kar6ar wayar yayi batareda ya sake kallon gefentaba
ya juya Yana kallon maska daya kirasa..
Come on man the coffee will get cold.
Qarasowa yayi ya zauna suka Fara Shan coffee 'dinsu suna tsokanar sufyaan dayayi wani iri
waishi missing Mariam 'dinsa yake amatse yake dasu koma gobe.
Murmushi dawood yayi yace,
You know you're unbelievable sufyaan Sam idiot baka gajiya da sex.
Dariya maska yasaki Yana sipping coffee 'dinsa yace,
Oh my see who's talking..I think gwara sufyaan sbd ko yaushe yaso zai daina idan yaso Amma
kana tunanin that crazy girlfriend of yours zata barka gaba...
Tayani fada Masa maska and the idiot keep saying she's not my type I'm just managing Amma
he's always inside her legs...
Murmushi yasaki Jin wulaqancin dasuke Masa yace,
Two idiots.
Amma deep inside sun tado Masa da kewar saraah dinsa taso biyosu yaqi yarda sbd matuqar
tana kusa dashi bazai iya haquraba saidai har abada baya fatar aikata makamancin hakan gari
Mai tsarki suda sukazo ibada.
Kallonsa maska yayi Yana cewa,
Ji Wanda kewa wani fada he's missing his chewing gum already.
Qyalesu yayi tareda lumshe fararen oily eyes dinsa yanajin yanayi na farin ciki na shigarsa.
Zama sukayi aleeya ta kar6o musu coffee da cake Fara Sha sukayi suna fira Wanda duk
yawanci surutun aleeya da Bilal ne ita kuwa lumshe idanuwa tayi ahankali tana Shan coffee 'din
tana sauke ajiyar zuciya ahankali sbd har lokacin jikinta sanyaye yake da kukan datayi gaban
kaaba.
Ta cikin qatuwar mirror glass din dake cikin gurin ta hangosu zaune a table 'din bayansu,
Su ukune kowannensu na dukan kyau da hutu daya bayyana jikinsu qarara.
Ido ta qura Masa zuciyarta ta buga da qarfi tayi saurin sunkuyar dakai tareda aje cup din
hannunta ta miqe tace,
Ta gama su tafi Dan dama Suma sun gama.
Tunda suka dawo masauki ta kwanta shiru tanajin numfashinta na fita da sauri daqyar tasamu
bacci ya 'dauketa tattareda sabon alamari atareda ita.
#mamuhgee
VOTE
COMMENT
[1/1, 11:07 PM] +234 701 680 1465: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*10*
Daga umrah Dubai suka wuce acan sukayi siyayyar sabbin kayan sawa sbd Fara rayuwar
University dazasu shiga.
Satinsu 'daya a dubai suka dawo gida dawowarsu da kwana biyu sukaje adamawa Basu wani
dadeba suka dawo sbd hutun Bilal daya qare nakomawa school.
Aiki suke akicin na abincin dare itada ammy da shafa'atu aleeya na 'dauka tana jerawa a dining
sbd yau Abba zai dawo daga tafiyar dayayi zuwa Miami gurin tsohon babban amininsa former
CJ ASSIDDEEQ DAUDA.
Suna gamawa ana fara Kiran sallar magrib suka nufi bedroom 'dinsu da yanxu aka sauya musu
komai zuwa na matured 'yan Mata.
Tubewa tayi tareda 'daura coffee brown towel Mai girma ta fada toilet tana cewa aleeya data
kwanta agado tana browsing sbd ita tana cikin period Bata sallah...
Aleeya kamar naji shigowan motan Abba.
Da sauri ta aje wayarta ta sauka gadon tayi palour.
Girgixa Kai tayi tana murmushi kafin tashige toilet 'din.
Wanka tayo tareda alwala tafito tashafa mai tasaka doguwar rigar yadi Mara nauyi tasaka hijab
ta tayarda sallah.
Tana gamawa ta cire hijabin sallar ta saka hula ta rufe gashinta ta fito direct palon Abba datake
jiyo hayaniyarsu ta nufa fuskarta 'daukeda farin ciki a ladafce tace,
Abba sannu da dawowa.
Yauwa Laylan ammy zance Kota aleeya??? Yafada da sigar tsokana.
Aleeya ta kalla tana murmushi tace,
Laylan ammy...Bata qarasaba tace Aa Abba Laylan aleeya sbd ganin kallonda aleeyar ke Mata.
Dariya dukkaninsu sukayi ammy tace,
Damacan ba wani gulma Dan nasa baza'ace niba ko ance Ni na gulma ne.
Ammy qyalesu Allah ina gani lokacinda aleeya ta harareta shine za'a wani ce ke Dan kawai
6arnar suna.
Jifansa laylar da aleeya sukayi lokaci 'daya da pillow yayi saurin kaucewa Yana cewa,
Eh ai gskia nafada ko ammy.
Sosaima kuwa 'dan ammy barni dasu inanan zasu sameni neman wani Abu.
Abinci sukaci a dining gabaki 'dayansu cikin Raha harsuka gama Basu wani jimaba apalo kowa
yayi 'dakinsa sbd kowa da abinda yakesonyi.
Lokacinda results dinsu yafito yayi kyau sosai amma wannan shekarar basuyi jamb ba sai next
year duk da ammy sosai taso ache anfara yimusu aure kafin su wuce University Amma Abba
Sam baiyi na'am da hakanba kasancewarsa riqaqqen 'dan boko dakeson 'yayansa subi
sahunsa Koda zai musu aure saisun gama University sun Fara aiki sun zamo independent.
Kamar dai yanda aka sani Lagos garine da mutanen cikinsa sukeda tsananin wayewa Wanda
wata wayewar harta zarta tunanin Mai hankali tazama iskanci tsagwaro,
Duk iya inda wayewar Masu ilimi take sun waye ga uwa uba hutu daya gama ratsasu da gata,
Ayanzune suka shiga University Kuma ayanzu shekarunsu na haihuwa suke ashirin da uku uku
zuwa da hu'du.,
Zuwa lokacin sunyi friends tsirara wayayyu Yan gata irinsu Kuma zuwa lokacin kowacce da
motarta saidai hakan baida amfani Dan kuwa basa ta6a fita dabam dabam.
Layla tafi aleeya haske da tsawo tareda bajewar mazaunai ma'ana hips.,
Duk da tsawonta tayiwa kanta mugun sabon koyaushe heels ne takalmanta sbd sabawa datayi
dasu sa6anin aleeya datafison wedges.
Gagayen turkey gowns da Kuwait gowns sune suturar Layla sbd sune sukefi komai yimata
kyawu sbd full package shape dinta Sam jeans ko native wears Basu dameta ba saidai can ba'a
rasaba take sawa musamman jeans dayafi komai fitarda full package 'dinta sbd hips din gske
takedasu.
Aleeya kuwa qananun Kaya Amma irin loose dinnan Masu shegiyar tsada sai native itama sai
can ba'a rasaba.
Kallo 'daya zakayiwa Layla ta'dau hankalinka sbd wani irin kwarjini da fuzgar hankali datake
dashi uwa uba sarqar qafarta da ita kadaice abinda suke gani na mahaifiyarsu dake tsananin
qara sa ta'dau hankalinka,
A ra'ayi kwalliya Bata damu Layla ba saidai tsadaddiyar oriflame powder da lips balm 'dinta take
amfani dasu suke qarawa fuskarta kyau da kwarjini sabanin aleeya dake makeup Koda yaushe.
Lokacinda Abba yabasu admission letter dinsu suka bude atare sukace ABUJA...
Yes...yace Yana cigaba da duba saqon email daya shigo laptop dinsa yace,
Kufara shiru end of this month zaku wuce.
Cikin tsananin farin ciki suka nufi bedroom din ammy
Koda sukaje waya suka tarar tanayi da umman siyam Bilal kuma na kwance kan gadonta Yana
karatun wani Islamic book a laptop dinsa.
Sallama tayi da umman siyama tana cewa lafiyarku kuwa wannan ihu hardai ke aleeya sarkin
harshe Kin girma bakisan kin girmaba.
Layla ce ta miqa Mata takardar hannunta tareda zama kusada ita aleeya kuwa gurin Bilal tayi.
Tana karantawa fuskarta ya canza sbd har cikin ranta tana tsananin Jin damuwar karatunsu
hankalinta zaifi kwanciya idan akai musu aure kowacce tayi karatun a gidan mijinta sbd
hakanan takejin fargaba da tashin hankali ga karatun nasu koyaushe itadai Bata fatan abinda
zai shiga tsakani ya raba kan yayanta.
Ganin yanda fuskarta ya canza yasa jikin layla Jin sanyi sbd Sam ta tsani ganin damuwa a
fuskar ammy,
Lokuta da dama idan taga ammy cikin tunani ko damuwa hankalinta tashi yakeyi saitayita
rarrashinta tana nuna damuwarta Akan koma menene yake damun ammin harsai tafada mata
shiyasa koyaushe sukafi kusanci yanxu sosai akan aleeya,
Tazamo ita kadai ammy kefadawa sirrinta da damuwarta amatsayinta na yarta.
Dafa ammyn tayi cikin sanyin murya tace,
Ammy Dan Allah karkisa damuwa aranki.
Riqo hannunta ammyn tayi tareda kallon aleeya dake dukan Bilal suna wasa da dariya murya a
mace tace,
Layla kinfi aleeya nutsuwa da sanin yakamata Dan Allah kiyimin alqawarin toshe duk wata ga6a
ko mafakar daxata shigo da tashin hankali ko rashin fahimta tsakaninku inason nacigaba da
ganinku cikin farin ciki haka ko bayan Raina.
Hawayene suka ciko idanuwanta ta riqe hannun ammyn murya na rawa tace,
Ammy karki saka damuwa aranki komai zai zauna ayanda yake insha Allah na Miki wannan
alqawarin.
Thank you my daughter Allah yayi muku albarka.
Amin ammy.
Aleeya ce matso tana cewa,
Sirrin me akeyi mommy and daughter wai Bilal bakaga yanxu gidannan ana Mana banbanci ba.
Nasoo oo my sister na 'dauka nikadai nake lure.
Hararsa layla tayi tana cewa,
See his big coconut head.
Eh naji ai gskia muka fada Abi my sister.
Hararsa ammy tayi tana sake saka musu albarka gabaki 'dayansu.
Anan 'dakin sukai sallar Isha kafin suka nufi dining sukai dinner kowa yakama hanyar
bedroom'dinsa.
#mamuhgee.
[1/1, 11:07 PM] +234 701 680 1465: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_