Showing 63001 words to 66000 words out of 76958 words

Chapter 22 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf

04 Jun 2025

5556

matuqar ta
tararda laylan da gangan tabarsu cikin wannan baqar wahalar ciwuka sunqi ci sunqi cinyewa
ayanxu kam tagaji itama tana buqatar kulawa da tata rayuwar iya so da qauna ta nuna saidai
tagaji dayi abanxa ana tsallaketa ana guduwa she needs to accept the fact hakanan.

airport taga sun nufa takalli bilal daya hana tasa rayuwar sukuni sbd su,
tabbas tasan yana tsananin kewar yar uwarsa saidai yana qoqarin dannewane yanuna mata
kulawarsa dan kusan duk sati saiyazo prthct dubata shi sam baya son dawood arayuwarsa sbd
shine silar komai daya samesu yake gani.


jirgi suka shiga itada bilal din da taheer kowannensu shiru da abinda yake saqawa shi kansa
taheer zuciyarsa bugawa takeyi da qarfi ta yanda zai kalli macen dayafi komai so amatsayin
matar dan uwansa harda qaruwa tabbas bazai ta6a iya qara zama akusadasuba zaicigaba da
rayuwarsa acan inda yafara ayanxu.

bilal kuwa zurfi yayi cikin tunanin yanda sukasha baqar wuya shida taheer kafin suka samu inda
take,

lokacinda suka fara nemanta a porthrct basu samuba duk iya kashe kudi da bincike taheer da
dad sunyi amma babu alamarta nan taheer ya yanke shawarar mayarda binciken abuja,

canma tsawon lokaci babu wani alamar zaaganta anan nan ya yanke shawarar komawa lagos,
komawarsa lagos yasa dole ya nemi bilal sbd jin ko akwai guraren dayake tunanin zata iya
zuwa maana acan rayuwarsu ta baya nandai suka fara bincike a 6oye shida bilal din da bincike
da dubara har qauyensu baffa dahiru sukaje amma babuta nan shima baffan hankalinsa yatashi
sosai musamman dayaji kusan tsawon shekara da 6acewarta.
shiru yayi cikin nazari kafin ya dago yace,

suje har adamawa inda komai yasamo asali sugani.

aranar suka koma abuja washe gari suka sauka adamawa,

lokacinda suka fara bincike daqyar bilal yagano unguwar dasukai rayuwarsu tada sbd canje
canje da gyara da gurare suka samu,

saida suka share sati biyu babu wani cigaba suka tattara suka koma aranar dazasu koma a
airport yahadu da wata matashiyar mace da yaranta biyu duka maza,

gudu sukeyi sukayo gurinsa suka boye mamar tabiyosu cikin fada tana cewa,

kuxo muje mana kokuwa so kuke sai ALEEYA tayita jiranku harta gaji.

da sauri suka fito sukayo gurinta kowannensu na cewa,

ummy nine anty zata bawa aleeya idan na girma.

dariya tayi tareda dagowa ta kalli bilal din dake kallonsu tace,

sorry sunxo sun damuqeka...

no its ok yarane ai koba komai naji sunada yar uwa mai sunan tawa yar uwar danake jida ita.

kallonsa tayi tasake kallonsa zuciyarta nadan rawa sbd kamar dayake mata da fuskar sani duk
da dai ya girma sosai yazama saurayi amma kamannin still sunanan,,,bilal ta furta ahankali ga
mamakinta saitaga ya juyo yace,

kinkirani ne?

baki ta rufe cikin tsananin mamaki da farin ciki tace,

bilal din laylah?

dawowa yayi da sauri shida taheer harsuna hada baki gurin cewa eh shine.

murmushin farin ciki tasaki tace,

bilal kaine ashe kaima zanganka raheenatu ce damukai zama tare tun baabanku nada rai
katuna kuwa?

tabbas ya tuna da ita sbd itakadaice mai nuna musu qauna da kulawa tun wancan lokacin
qawar layla ce jiyayi jikinsa yayi sanyi sbd ya dauka watace daban tasan inda laylan take,

sakin murmushin yaqe yayi cikin qarfin hali yace,

allah sarki nakuwa tuna duk da kamannin sun canza.

dariya tayi tace,

gaskia ne kam saidai ina kuka shiga tsawon lokaci haka.

shafa fuskarsa yayi cikin yanayi na damuwa yace,

abubuwa da dama sunfaru babban ciki shine nur muke nema yanxu tsawon lokaci mai tsayi
anata nema amma haryanxu shiru bamuda tabbacin tana raye ko tana....

katsesa tayi da cewa,

nur nanan raye saidai.....

ganin irin zaburowar da su biyun sukayo yasata saurin rufe bakinta tareda rintse ido cikin jin
zafin subutar bakinda tayi saidai ita kanta dama tanason sanin inda su bilal da aleeyar suke sbd
kawo qarshen komai tun kafin aleeya tafara tambayarsu ina daddynta dan ana gaf da fara
hakan.
juyawa tayi da sauri zatabar gurin sukasha gabanta atare bilal baisan lokacinda ya zube qasaba
cikin sanyin murya yace,

dan allah ki taimaka rayuwar mutane da dama na cikin wani hali sbd ita ka sanardamu inda take
idan kinsani..

kallonsu tayi cikin yanayi na tausayawa tace,

kubani numbernku zan kiraku na sanardaku idan na isa gida kuje kurage damuwa layla na
taredani tun ranarda tabaro gida aranar muka hadu.

jiki na rawa suka rubuta mata numbibinsu sbd dagewar datayi bazata iyayi musu komaiba
ayanxu.

da wannan suka fasa tafuya suna zaman jiran kiranta shiru shiru babu bayani suka tattaro suka
dawo aranarda suka sauka lagos aranar tayo musu txt na address din gidanta dake adamawa
kuma aranar sukayo porthcrt suka damqawa aleeya address din.

juyowa yayi ya kalleta lokacinda jirginsu ya sauka yaga har lokacin idanuwanta na rufe.

saukowa sukayi babu 6ata lokaci suka dauki drop zuwa address din.


kallon tangamemiyar gate din gidan tayi taja numfashinta dake fita da sauri ahankali tanajin
wani irin qarfi da jarumta azuciyarta duk da sosai takejin nauyi aciki,

mai gadi bai hanasu shigaba sbd madam dinsa ta sanardashi zuwansu suka shigo kowanne da
kalar bugunda zuciyarsa keyi,

suna gaf da shiga palon taji ankira sunanta,,

ALEEYAH..

cak ta tsaya tareda jan numfashi kafin ta juyowa ahanki bugun zuciyarta na tsanan,

yarinyace fara sosai kyakkyawa dabata baro ko yatsa daya na mahaifintaba da kakarta dan har
jajayen lips dinsa saidata dauko da kalar tafiyarsa cikin sanyi,
sanye takeda riga da wando red an gyara mata gashinta andaure,

qurawa yarinyar ido tayi jin yaron yasake kiranta da aleeyah.

rufe bakinta tayi da duka hannayenta biyu sbd kukan dakeson zuwar mata zuciyarta na
karyewa,
basai anfada mataba tasan wannan itace 'yar dawood da layla kuma sunanta laylanta tasawa
yarinyar batasan lokacinda hawayenta suka saukoba lokaci daya taji quncinta yafara gushewa
ganin yarinyar sbd mutanen datafi sone suka sameta,

dafata raheenatu data fito tayi tana kallon little aleeyah tace,

aleeyah zoga mummy aleeyaan ummynki.

juyowa yarinyar tayi suna hada ido da aleeya tazo da gudu ta fada jikin aleeya cikin wani irin
shauqi aleeya ta rungumeta sabbin hawaye na gangaro mata,

bilal da taheer ma daurewa kawai sukai basuyi hawaye ba daqyar suka qarasa palon little
aleeya na damqe ahannun aleeya sbd kobada laylaba yanxukam tasan little zata kawo sauqi
arayuwarsu insha allah,


zama sukayi aka kawo musu ruwa amma babu wanda keda nutsuwar kallon ruwan amatse
suke dasuji inda layla take,

cikin sanyin murya tace,

mijina ya rasu yabarni da yarana biyu a porthct daga baya na shirya tareda tattara duk wata
dukiyar damuka gada nida yayana nayi shirin dawowa gida adamawa
aranarda layla tabar gida aranar cikin qaddarawar allah nice na bugeta da mota a porthct kuma
bugu sosai dan kuwa qaddarawa da ikon allah kawai yasa cikin dake jikinta ya tsaya bayan
doguwar wahalar jinyar datasha kafin daga baya muka dawo adamawa tare muka cigaba da
jinya tsaqon lokaci harta haihu, haihuwarma tazo da babbar matsala saida muka koma jinyar uwa da jaririyar bayan haihuwa
kafin daga baya komai ya daidaita ga jaririyar inda da kanta ta6arwa yarta sunan aleeyah saidai
haryanzu ita babu wani sauqi sai agurin allah,

layla tafada mini komai sbd acewarta duk ranarda ta rasu nakai little aleeya gareki aleeya sbd
tanasakaran bazata sake ganinkuba arayuwarta,

tuntuni naso mu nemoku sbd halinda take ciki amma tasani alqawarin rshin yin hakan saidai
kullum da fargaba nake kwana da ita nake tashi sbd gudun karta rasa ranta ahaka cikin
damuwa da qunci shin mezai hana ataru anemi mafita wa wannan alamari sbd sam wannan
bashine hanya mai 6ullewa ba,
little aleeyah ta taso da tsananin qaunarson ganinki aleeya sbd mahaifiyarta data cusa mata
qaunarki mai tsanani aranta ta hanyar yimata maganarki kullum duk da tanacikin mawuyacin
hali.

zubewa qasa raheenat tayi cikin yanayin na hawaye tace,

na roqeki aleeya ji yafewa layla abinda tayi sbd hakan yasa takasa cire damuwa aranta harya
zamar mata ciwo ki yafe mata kodan darajar qaunar dakike mata,
ki yafe mata sbd kashe kanta takeyi ahankali batareda tasaniba.


kasa dagowa aleeya tayi sbd tsananin kukan dayafi qarfinta wannanwace irin rayuwace sukeyi

mara tsari da tawakkali,


kallon aleeya tayi tareda cewa,

bismillah muje nakaiki gurinta,

miqewa sukayi wannan karon qafafuwanta har rawa sukeyi sbd bugawar da zuciyarta keyi suka
nufi sama zuwa wani daki.

bude qofar raheenat tayi tareda matsawa gefe aleeyar tasaka qofa tashiga dakin itakuma ta fito
tafeda ja musu qofar,

tsayawa cak tayi tsakiyar dakin tareda qurawa nur din dake zaune qarshen gado ta takure,

wasu irin hawaye masu zafi da ciwone suka gangaro mata ganin yanda laylar takoma,
mezata gani haka layla takoma kamar wanda tayi shekara goma tana jinya,


LAYLAHH'''''ta furta muryarta na wata irin rawa,

kamar amafarki taji muryar aleeyar ta dago kai ahankali ta dorawa fuskar aleeyar ta sake
dubawa dakyau taga itace
sai kawai ta sunkuyar dakai ahankali hawayen datafi shekaru dason yinsu sai yau suka ciko
idanuwanta amma basu saukoba sai rawa da jikinta yafara dauka,

qarasowa ahankali aleeya tayi tareda zama kusada ita tayi irin zamanta suna fuskantar juna
cikin rawar murya aleeya tace,

i miss you like hell my laylah.

rintse ido layla tayi sai kawai kuka ya qwace mata suka rungume juna da sauri kowannensu na
sakin kukan daya jima baiyi irinsaba raheenat dake qofa takoma palo tasanardasu taheer nan
suka sauke wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya atare tareda roqon allah yasa iyakacin wahalar
kenan.
little aleeya kuwa murna takeyi yau zatabi mummy aleeyarta sutafi.


kuka sukai sosai saida suka gamsarda zukatansu kafin suka saki juna aleeya ta miqa mata
hannu tace,

lets go home.

kallonta layla tayi da jajayen udanuwanta zatai magana aleeya ta katseta da cewa,

wlh har abada babu dawood cikin zuciyata yanxu,
komai ya isa hakanan namiki alqawarin inganta rayuwata matuqar zakimin alqawarin kulada
dawood harya samu cikakkiyar lafiyarsa,
nabar dawood nikuma kimin alqawarin kinbarmin little aleeyah.

gangarowa hawayenta sukayi murya a shaqe tace,

aleeya takice har abada kece uwarta saidai nima babu abinda zanyi arayuwar dawoo....

baki gaji da ganinmu cikin wannan halinba kenan tun farko arayuwa taurin kankine yake jawo
mana matsala dan haka daga yanxu kingama yanke kowane hukunci idanhar nice aleeyarki
nice zan yanke hukunci daga yanxu,
and we are goin back home today.

tana fada ta miqe zuciyarta na daci sbd taurin kan layla yafara zama wani abin..
riqota layla tayi da sauri tareda goge hawayenta tace,

karkiyi fushi dani aleeyah konan gaba dan allah.

dawowa tayi ta rungumeta tana cewa,

har abada bazan qaraba insha allah idan har bazaki qara 6oyemin komaiba.

bazan qaraba i promise.

daqyar suka lallashi juna ta riqota suka sauko qasa bilal na ganin yar uwarsa kasa hkr yayi
yataso da sauri suka rungume juna cikin tsananin qauna da kewar junansu.

taheer daqyar ta iya kallonsa suka gaisa qasa qasa sbd ko kallonsa takasayi.

duk yanda raheenat taso su kwana kasawa sukayi abincima daqyar suka samu cusawa suka
juya da layla da little aleeya sbd amatse suke dasuga sun kai nur din gaban gadon dawood.

suna sauka airport direct asibiti suka nufa jikin layla nan take yafara rawa idanuwanta suka
canxa ahankali aleeya ta riqo hannunta tareda girgixa mata kai tana sakar mata murmushin
bata qwarin gwiwa gwara suyi facing komai once and for all kowa ya huta.
#mamuhgee


vote and follow.

[2/5, 8:18 PM] 0mmr Farouk: _*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_




*40*
Not edited.




Bilal ne yabudewa aleeya qofar motar taheer kuwa ya budewa layla suka fito kusan atare har
lokacin jikin layla rawa yakeyi saidai tana qoqarin 6oyewa dan nunawa aleeya she is ok duk da
kallo daya zakai mata ka gano bata cikin cikakkiyar nutsuwarta sbd bugawarda qirjinta keyi da
qarfi,
hannunta aleeya ta riqo tareda janta suka shiga,
tun daga nesa mum ta hangosu takasa yarda da abinda idanuwanta ke gane mata ta ta6a
sufyaan dake kusada ita ta nuna masa murya na rawa tace,

NURRR,

miqewa sukayi dukkaninsu atare shida mum sbd jass na ciki yana cirewa dawood din jinin
daaka daura masa ya qare,

karaf idanuwan mum suka sauka kan little aleeya dake hannun taheer daya dauketa,

murza idanuwanta tayi cikin wani irin yanayi da shauqi kobaa fada mataba tasan wannan
jinintace gudan jinin sweetboy dinta wata irin murna da hawaye tafara lokaci daya da sauri ta
kar6eta daga hannun taheer ta qanqame jikinta kota kan laylar bata farabiba saidai sufyaan ne
yayita yiwa allah godia idanuwansa na cikowa da hawayen farin cikin samun cikar burin dawood
dinsu,

Nana kuwa rungume layla tayi tana hawayen farin ciki sbd ita kanta tasan tana tsananin qaunar
layla har cikin ranta,

daqyar mum tabari sufyaan ya kar6i little tareda rungumeta dakyau wata irin qaunarta mai
tsanani na shigarsa don kuwa jiyakeyi kamar gudan jininsace aka haifo koba komai suma sun
zama dadys daga yanxu,,,alhamdulillah ya allah''''''ya furta ahankali tareda sakarwa little din
murmushi yana cewa,
welcom dadys princess mai iyaye da yawa.

cikin 'doki da zumudin farin ciki Nana ta matso zata kar6eta ahannunsa hannuwansu suka hadu
wani irin tsigar jiki yaji da sauri ya dago ya kalleta itama kallonsa tayi tareda sunkuyar dakai ta
kar6i little din ta juya yabi bayanta da kallo kafin ya kalli tsigar jikinsa data tashi,

rungume layla mum tayi takasa mgn sai hkr take bata tana roqonta karta sake barinsu,

jijjiga kai tayi tana share hawayenta babu wadda takeson gani yanxu kamar ammynsu tasan
itama tana cikin hali na tausayi da damuwa,

bilal dake faman waya dasu ammy yanata yimusu bayani ta kalla tanason cewa yabata ammy
amma tanajin nauyin ammyn sbd sai yanxu dataga halinda kowa ke ciki tayi nadamar dcision
dinta,

ahankali aleeya ta miqe ta shige dakinda dawood din yake daidai shikuma ya juyo ganin waye
yashigo,

cikin idanuwan juna idanunsu suka sauka ta dauke kanta tana kallon dawood din cikin farin
cikinta daya kasa 6oyuwa afuskarta,

qura mata blue eyes dinsa yayi akaro na farko dayaga murmushi kan fuskarta jiyayi kuzarinsa
na ragewa ya juyarda kai cikeda mamakin abinda yasata farin ciki suna cikin wannan halin,

cikin wata irin murya tace,

kanasaran zai farfado nan kusa i mean yaushe kuke sakaran farkawarsa?

dan juyowa yayi ya kalleta yace,

anytime soon tunda jinin yagama shiga.

juyawa tayi tafice batareda taqara wata maganarba wannan ne karo na farko da magana
doguwa irin wannan tashiga tsakaninsu.

tana fitowa takalli layla dake sharewa mum hawaye tariqo hannunta tareda miqar da ita tace,

nida mum munyi namu now its your turn zaki kulada mijinki mukuma zamu koma gida muyi
jinyar kanmu.....

katseta mum tayi da cewa,

no aleeya ina zata iya jinyarsa itama fama takeyi da kanta..

murmushi aleeya tayi tana cigaba dajan layla zuwa dakin tace,

mum na tabbatarda ciwon laylana ya warke alokacinda muka hadu da juna abinda ya rage
aciwon dr dawood zai qarasa warkar dashi.

kallonta layla tayi da sauri saikawai taji kunya da nauyin zancen meyasa tabari sonda takeyiwa
dawood ya bayyana har haka aleeya tagane.

sake tura qofar tayi ahankali wannan karon jass yana juyowa da little yafaracin karo yaquramata
ido kafin yayi mgn idanuwansa suka sauka kan nur da sauri yamaida kallonsa kan little aleeya
kafin yakalli aleeya dake kallonsa ta gyada masa kai cikin murmushin farin ciki tace,

yes she's our little princess my little....

rintse idanuwansa yayi kafin ya zube qasa yayiwa allah sujjada hawayen tsananin farin ciki
mara musali suka gangaro masa yataso da sauri ya dauke little sama yana jera mata kisses a
goshi da fadar,

yes i'm a father now nima inada 'ya yanxu,,,,

murmushi aleeya tayi tana kallon yanda yake nunawa aleeya wata irin qauna kamar zai
hadiyeta yace,

nine zanzama real dad naki sweethrt kowa ya hakura nixa'abarwa....

matsowa aleeya tayi gabansa tareda 'dan tamke fuska ta miqa masa hannu alamar yaba ita
tace,

sorry dr amma she's my already so.......

dariyar daya manta rabon dayayi yayi tareda saurin ficewa dakin sbd tunowa dayayi akwai
patien da sauri tabi bayansa tana cewa,

ji wannan dan qarfin halin.


tunda suka shigo idanuwanta suka sauka kansa tayi saurin dafa gado sbd wani irin mummunan
jiri daya 'dibeta,

rawa jikinta yakejyi sosai da qyar ta qarasa bakin godon ta zube qabansa tareda sakin wani irin
kuka mai ciwo ahankali,

tabbas bazata ta6a yafewa kantaba tunda tasaka dawood cikin wannan masifar tayi tunanin

rashinta zaisa ya dangana ya rungumi aleeya amatsayin abokiyar rayuwa amma ga abinda
hakan ya jawo,
tabbas koyaushe bin ra'ayinta ba alkhairi bane daga yanxu tadaina bin tunaninta sbd kullum
shiyake kaisu ga masifu irin haka,


daqyar ta iya tsaida kukanta ta dago tareda qurawa fuskarsa ido ta lumshe idanuwa ahankali
tanajin tsananin tausayinsa nabin jijiyoyinta duk yanda take tunanin cirewa ko danne soyayyar
dawood azuciyarta wannan abune dabazai ta6a yiyuwa agaretaba duk kuwa baqar wuyar
datake sha gurin gwada yin hakan,
hannunta ta dago ahankali yana rawa ta doro kan nasa dake kan cikinsa tasaki wata irin
wahalalliyar ajiyar xuciya kafin takai kanta ahankali ta kwantar gefen guskarsa numfashinta na
fita zuwa cikin kunnensa.




awaje kuwa abu soyayi yazamarwa jass da aleeya fada qarshe dai dole yabata sbd gida dazasu
dukkaninsu shida sufyaan ne kawai zaa bari a asibitin sbd kar dawood ya farfado babusu akusa
dan sunasaka ran farkawarsa koyaushe sbd jinin daaka saka masa.
#mamuhgee


vote and follow.
[2/5, 8:18 PM] 0mmr Farouk: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*41*
Not edited.

suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login