Showing 9001 words to 12000 words out of 76958 words

Chapter 4 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

5644

karki zubomin dau'da Kinga kima tafi bana bada sadaka nima nema nake.

Matsawa baya tayi murya asanyaye ta miqo kudinta tace,

Siya zanyi harda koko.

Wani mugun kallo ta watsa Mata kafin ta fizgi kudin ta zuba Mata kosan 'dari kokon 'dari a Leda
baqa.

Kar6a tayi tareda tsayawa jiran canji.

Harara ta watso Mata tace,

Meye Kuma?

Canji zakiba.....

Canjin me Kuma ai kosan 'dari ne kokon'dari jeki Kisha saikin ture.

Girgixa Kai tayi tace,

Banason na duka.

Rufe Ido Mai kosan tayi ta koreta cikin rashin mutunci kafin taci gaba da aikinta tana masifa ita
kadai.

Komawa tayi takaiwa Bilal sosai yasha itakuma kadan Tasha Dan karya qare anjima su rasa ta
'daure sauran a Leda.

Ranar haka suka wuni cikin gurin Saida yamma tabasa sauran Kokon ya shanye tareda sauran
paracetamol din daya rage musu ita saidai ta kwana hakanan.

Washe gari tunda safe saiga Mai shagon yayi musu korar wulaqanci kamar zai dakesu sbd kai
Masa labari da'akayi sadaka yallah zasu mayar da shagonsa gida.

Suna fitowa suka hau titi suna gararanba harsuka Kai wani gurin siyayya sukaga mabarata da
musakai zazzaune suna jiran duk Wanda ya fito ya Basu sadaka.

Ba 6ata lokaci Bilal yaja hannunta Bata musaba sukaje sukabi sahu Dan dama ko ruwa Babu
acikinsu Bilal yayi kukan harya gaji yasawa kansa dauriya.

Tunda suka zauna ko acikin mabaratan sun fita daban sbd tsananin bushewar dasukayi ga
dau'da da mataccin kaya hakadai suka zauna jiran tsammani.

Tunda suka zauna kusan so hu'du ana bada sadakar kudi sai mutanen su rabe abinsu ko kallo
Basu ishesu.

Hawaye ta sharce tareda cewa Bilal yatashi sutafi wani gurin.

Qin tashi yayi saima matsawa daya qarayi kusa da qofar super market din daidai kuwa fitowar
wani saurayi tareda yarinya kimanin shekarun Layla.

Da sauri Bilal ya matsa gurinsa yace,

Munajin yunwa nida yayata Dan Allah kabamu abinda zamuci tun jiya muke jinta.

Kallon Bilal din yayi ganin yanda bakinsa ke bushe yasa ya yarda da zancensa yaciro 'dari biyar

yabashi.

Saboda murya ko godiya baiyiba yayi gurin Layla da gudu yace,

Nur tashi muje munsamu.

Girgixa Kai saurayin yayi ita kuwa Layla ta qurawa Ido tanajin wani irin so da qaunar Layla na
shigarta..
Tun ranar farko data Fara 'dora idonta akan Layla ranar dasukaje gurin faduwar ginin da
abbanta takejin wannan connection,
Tun ranar takasa cireta cikin ranta.

Harsuka shiga mota sukabar gurin Bata daina kallontaba harsaida suka 6ace.

Sukuwa barin gurin sukayi cikin farin ciki Dan kuwa ko ita Layla yau saidata nuna farin cikin
samun kudin.

Shinkafa da wake da manja suka siya ta 'dari biyu sukaci suka qoshi daga Nan suka cigaba da
bulayinsu har dare yayi suka la6e gefen wata islamiya suka kwanta da zazza6i dukkansu suka
kwana Amma gari na wayewa suka bazama bara bawai don sundaina jinsaba saidan ba
amfanin kwanciyar Dan korarsu ma akayi tun Basu tashiba.
Koko suka siya da qosai sukasha daganan suka koma super market din jiya suka zauna.

Ranar Kam ba sa'a har Isha Basu samu komaiba jiki ba qwari suka koma inda suka kwana jiya
suka kwanta bayan sun siya alalar hamsin sun raba sunci.

Tsawon sati uku da rasuwar baabansu Babu wani sauyi ko taimako saima ta6ar6arewa da
rayuwarsu tayi Dan zuwa yanxu duk inda suka samu kwana sukeyi hartakai idan sunga kangon
gida murya sukeyi dare yayi su kwanta gari ya waye suyi gurin bara..

Tsawon lokacin Basu ta6a ko wanka ba kayansu tuni suka qarasa yayyagewa Nan take suka
zama kamar wasu aljanu,
Yawon dasuke yini sunayi ko mashin ne saiyaso hutu bare 'dan Adam gashi bamai takalmi
acikinsu daga bayane Bilal ya tsinto musu wasu fasashi a bola idan yasa yau gobe ita tasa.,
Duk wahalarsu ba kullum suke samuba ko sunyi barar.

Tafe suke Bilal na Bata labarin yanda suke bara dah kafin baabaa ya rasu ta kallesa tace,

Bilal to meyasa yanxu bama samun sadaka.

Ko dacan fa gidaje muke zuwa muyi bara ko mu zubar musu da shara kafin abamu koya kwana
munaci.

Qarasawa bakin wani babban mall sukayi tana cewa,

Yaudai Allah yasa musamu da wuri muje mu nemi gurin kwana karmuyi irin na jiya duhu yayi
bamu samu gurin kwanciyaba Dole muka kwana gefen bola nidai tsoron bola nakeji banaso
muna kwana anan.

Zama sukayi Bilal ya aje matacciyar robar daya samo musu ta bara dacin abinci.

Har kusan magriba Basu samu komaiba sai wani guntun biscuit da wata yarinya ta jefar gurin
rigima ta fito gurin da uwayenta.

Kallonsa tayi cikin sanyin murya tace,

Bilal muje ko gurin kwanciya mu nema kar duhu yayi.

Sabon garari suka soma na neman gurin kwanan yau Amma duk inda suka Fara qoqarin zama
da gudu ake korosu gashi yau akwai hadari sosai daga ita harshi tsoron walqiya da tsawa suke
shiyasa duk jikinsu yayi sanyi.

Basu ankaraba aka Fara yayyagi saikuwa ruwa Mai qarfi da gudu suka raku6e qarqashin wata
bishiya duk da ba wani ruwa take karewa ba Amma haka suka fake tareda qanqame juna.

Ruwa Mai qarfi akayi sosai sai tsakiyar dare ya tsagaita daqyar taja Bilal suka ra6e gefen
shagunan gurin sbd rawar sanyin dayakeyi ko motsi yakasa.

Suna raku6ewa gurin itama ta dunqule jikinta na jijjiga sosai.

Ana fitowa sallar asuba gari na Fara haske takalli Bilal dake baccin wahala tace,

Bilal tashi muje karsuxo su dakemu kaga sunce duk suka sake ganinmu Nan saisun Mana
duka.

Da qyar yatashi zaune takamashi suka miqe sukabar gurin tana riqeda hannunsa.

Doguwar tafiya sukayi ya sulale qasa ya zaune gefen wata babbar makaranta ya lashi
busasshen makinsa daqyar yace,

Nagaji mu huta nan.

Zama tayi kusadashi tareda qurawa makarantar Ido.

Baccin wahala ne yasake daukar Bilal ta qura Masa Ido sai kawai ta fashe da kuka tana tunanin

badai haka zasuyita rayuwaba harsu girma su mutu.,,
Ahankali tace gwara mota ta ka'demu tare mu mutu tare mu huta.

Suna gurin har qarfe biyu hayaniyar tashin 'yan makarantar ne yatadashi ya tashi zaune yana
kallon gate din  makarantar yace,

Nur zanje na roqesu abinci idan sun rage.

Bai rufe bakiba wasu 'yan Mata uku suka fito suna dariya da manyan school bags dinsu goye.

Cikin sauri yace,

Dan Allah ku bamu sadaka muci abinci..

Wani mugun kallo suka watsa mishi atare Layla na ganin haka ta taso ta riqo hannunsa
batareda ta kallesuba.

Harsun juya 'dayar taciro nera goma tace,

Kar6i.

Da sauri Bilal ya juyo gurin kar6a ya ta6a hannunta wani wawan Mari ta sharara Masa cikin
tsananin Jin zafi ya tureta harsaidata fadi yace,

Allah ya isa muguwa..

Zaro Ido sukayi dukkaninsu cikin hasala ta miqe tareda rufesa da shuri da sauri Layla ta
rungumesa ta Kare
Qara quluwa tayi tasa qafa takaiwa laylar mugu bugu a goshi Nan take goshin ya fashe hannu
ta qara dagawa zata Kai Mata Mari aka riqe hannunta.

Aleeya""""""tafada tana kallon cikin idon wadda ta riqe Mata hannu sbd batasaran ganintaba
gurin zuwa daukarta.

Sake Mata hannu aleeyar tayi tareda juyowa ta kalli Layla dasuke kuka antaru anata kallonsu.

Hannu ta miqawa laylar.

Miqewa tayi tareda riqo Bilal suka juya zasu wucewarsu aleeya tayi saurin riqeta murya na rawa
tace,

Zan taimakeku.

Atare itada Bilal suka qurawa aleeyar Ido sbd yaushe Rana ta farko da wani yace zai taimakesu
duk kuwa gwagwarmaya da gararin dasukayi.
#mamuhgee




                *VOTE*
            *COMMENT*
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*7*
'daure fuska siyama tayi sosai tana kallon aleeya tace,

Wat do you think you're doing aleeya?

Abinda Yakamata nayi tun ranar farko banyi shi zanyi yanxu.

'dari biyu siyama ta Ciro cikin school bag dinta ta jefawasu Layla tareda Jan hannun aleeya
tace,

Let's go zuciyana tafara tashi da warin dau'darsu.

Fizgewa tayi cikin 'daga murya tace,

Dasu zan tafi so gwara ki dauki 'dari biyunki zatai Miki amfani gurin Hawa taxi kar kafin mukai
warin dau'darsu yasaki amaye kayan cikinki..

Wat?,,,,siyamar ta fada tareda matsowa gabanta tana rage murya tace,

Karma kifara tunanin 'daukar wainnan sadaka yallah din Dan haka salin alin kibasu sadakar
dazaki Basu mutafi coz wannan abin dakikeyima you're disgracing your self.

Hannu ta qara miqawa Layla akaro na biyu laylar taqara qanqame Bilal har lokacin kuka sukeyi.

Tsaki siyama taji cikin tsawa tace,

Kubar Nan shegu matsiyata.

Miqewa sukayi aleeya ta damqo hannun Layla tareda kallonta Ido cikin Ido tace,

Zan taimakeku zaku bini?

Qura Mata ido Layla tayi akaro na farko,
Sake tambayarta aleeya tayi tana kallonta tace eh zasu bita.

Murmushin farin ciki tasaki tareda qara riqe hannun laylar suka nufi mota batareda taqara
waiwayar siyama ba ta sakasu mota tacewa driver sutafi.

Wani mugun huci siyama ta furzar tana cewa,

Allah yasa wannan taimakon yazamo muguwar qaddarar rayuwarku ta har abada,
Ina muku baqin bakin Allah yasa wannan shegiyar sadaka yallar tazamo babban bala'in dazai
wargaza rayuwarku gabaki 'daya atare...

Idan ita Bata zamo muguwar qaddararki ba Toni zanzamo muku muguwar gobarar dazata qone
farin cikinku da rayuwarku duka.

Tunda suka shiga motar tayi shiru tana kallon Layla itakuwa Bilal daketa farin ciki ta qurawa ido
yaune karo na farko dasuka ta6a shiga mota arayuwarsu.

Babban gidan dasuka shiga yasa ta qanqame hannun Bilal harsuka fito motar.

Kallonta aleeya tasakeyi tareda qara riqo hannunta suka nufi cikin palon gidan.

Ammy da abbanta na zaune apalon suna magana tashigo da sallama hannunta na riqe qam da
hannun Layla dake biyeda ita kamar raqumi da akala.

Tsaye ammy ta miqe tana kallonsu Layla dasukafi Mata Kama da mahaukata arikice tace,

Aleeya suwaye wainnan?

Ahankali tasaki hannun Layla ta matso gaban abbanta ta durqusa murya a sanyaye tace,

Abba ina qaunarta tun ranar farko Dana ganta ranar da mahaifinsu ya rasu mukaje Dan Allah
Abba ka taimakesu.,

Kallonta yayi cikin kulawa ya tayarda ita ya jawota kusadashi yace,

Aleeya ai nabasu taimako tun.....

Girgixa Kai tayi tace,

Abba sonake kazama uba agaresu inason sudawo Nan taredamu ingantacciyar rayuwar dakake
bani nakeso kabasu.

Kallonsu Laylar ammy tayi taga yanda sukayi wani iri kalar tausayi saitaji jikinta yayi sanyi Nan
take wata zuciyar ta ingizata data kar6esu matsayin 'yaya kodan 'yarsu qwaya 'daya tal data
nuna son hakan.

Shiru Abba yayi ganin tafara hawaye yace,

Shikenan yanxu dai zasu zauna kafin gaba zansan abinyi.

Rungumesa tayi tareda cewa,

Thank you Abba.

Ammy miqewa tayi ta miqawa Bilal hannu tace,

Zoka fadamin sunanka.

Ahankali yakalli Layla kafin ya matsa kadan yace,

Bilal.

Jin tsami da warin dasuke tashi ajikinsu yasa tayi saurin Kiran shafa'atu Mai aiki tace taje dasu
tayi musu wanka.

Harsunbi bayanta aleeya tayi saurin riqo hannun Layla tareda sakar Mata murmushi tace,

You're my responsibility from now on so I will be the one to clean you up..

Sunkuyar dakai layla tayi sbd batasan abinda aleeyar tafada ba saidai binta datayi har cikin
qaton lafiyayyan room dinta dayaji adon komai blue and white Bilal kuwa shafa tatafi dashi
danyi Masa wanka.

Kallon Abba ammy tayi bayan tafiyarsu tace,

Allah zai biyaka for this kaida 'yarka sbd tun farko haka Yakamata kayi kodan ita babbar dake
mace.

Sauke numfashi yayi ahankali yace,

Tunda aleeya na qaunarsu I have no other option but to Join the Q,

Insha Allah zan kwatanta Basu kyakkyawar rayuwa.

Allah yatamu riqo tace tana kallon qofar dasukabi.

Kayan jikinta tasata cirewa tareda miqa Mata blue towel 'dinta daqyar ta tube ta 'daura tana
cewa,

Ina Bilal.

Murmushi aleeya tasake tana tattara tsumman kayanta data cire tana cewa,

Anje yimasa wanka ki kwantarda hankalinki kinji.

Toilet suka shiga tsoro da mamakin gurin Yakamata Amma miskilancinta yasa hakan Bai fitoba
Aleeya tajata bakin shower tun ba'afara wanke kaiba ruwan datti suka Fara zuba Nan take towel
ya canxa kala sbd dama qin cirewa tayi.

Mamaki da tsoro dau'dar dake fita ta Bata Amma hakanan takejin Bata qyamarta tasa shampoo
tayita wanke Mata Kai harsaida ta qararda kusan robar shampoo 'din.

Sabulu da soso ta damqa Mata a hannu tareda juya tafice daga toilet din.

Jiki asanyaye tayi wankan tafito daure da sabon babban towel 'dinda aleeyar ta nuna mata
arataye.

Tasowa tayi tajawota ta zaunar gaban mirror tana goge Mata jiqaqqen gashinta tana kallonta ta
cikin mirror fuskarta 'daukeda murmushi tace,

Haryanxu Baki fadamin sunanki ba nadaiji na qaninki 'dazu saura naki.

Kallonta Layla tayi kafin ta sauke Kai ahankali tace,

LAYLA Amma baabana nakirana da NUR.

Murmushi aleeya tasaki tareda dawowa gabanta ta riqo hannunta tace,

Ni Baki tambayi sunanaba.

Ahankali tace,

Naji dazu anfada.

Ok kifada naji da bakinki.

Ahankali ta "dago takalli aleeyar tace,

Aleeya.

Miqewa tayi tana Jin farin cikin daga yanzu tasamu 'yar uwa Kuma qawa bazata qara komai ita
kadaiba.

Kayanta ta 'dauko gown black da sabon pant da vest tabata tana cewa saka Bari nakawo Mana
abinci.

Ficewa tayi taje kicin da kanta ta 'debo musu abinci a plate 'daya takawo tareda robar coke biyu.

Kallon abincin Layla tayi ta ha'diye wani tsinkakken yawu kafin ta 'dauke Kai tana wasa da
sarqar hannunta.

Aje abincin tayi tana kallon sarqar da Laylar ke wasa da ita tace,

Sauko ga abinci.

Kallon abincin tasakeyi kafin asanyaye tace,

Tareda Bilal zanci.

Karki damu Shima gashican za'a saka Masa nasa.

Miqewa tsaye tayi tana qara sanyaya muryarta tace,

Dan Allah inaso naci taredashi munsaba bamaci dabam.

Okay okay Bari nakirashi sai yazo kuci wannan Ni naci nawa dabam.

Da sauri taje takirawosa suna shigowa da gudu yayo gurin layla Yana cewa,

Layla dubi kayan da'aka sakamin Masu kyau Kinga harda takalmi aka bani kumafa harda wanka
akamin kema ji anbaki Kaya Masu kyau Dan Allah Layla karmu tafi muyita zama anan harmu
gir......

Rufe Masa Baki tayi tana murmushin farin cikin ganin yanda yayi fes farin ciki da murna fal
ataredashi.

Abincin gabansu aleeya ta nuna Masa cikin dariyarsa tace,

Ga Kuma abinci Yana jiranka kaci saika ture.

Zaro Ido yayi yawunsa na katsewa ganin taliya da miyar kwai da namomi.,
Tunda suke Basu ta6acin taliya ba har gwara nama idan sallar layya tayi idan yaje yawon bara
ko aikin yakan samo tsokoki suci.

Zama yayi da sauri Yana jawo hannun layla Yana cewa,

Zo muci layla Kinga harda namafa.

Zama tayi ganin ganin aleeya ta fita Nan suka Fara cin abincin jikinsu har rawa yakeyi
dukkaninsu
Kallonta yayi cikin dariyar Jin Dadi yace,

Layla wlh abincin Nan Dadi Allah yasa su riqemu suce suna sonmu wlh idan suka koremu ba
inda zamu kuka zamuyatayi muqi tafiya..

Dariya tayi ahankali tana Kai lomar taliya bakinta tace,

Da ganifa sunada kirki bazasu koremu ba kumama aleeya nada kirki tana sonmu.....

Dariyar datake riqewace tun dazu data samesu sunata faman cin abincin  ta kubce Mata ta
qaraso tana cewa,

Bilal layla tafadi gskia ko kowa baya sonku ni ina sonku daga yanxu nima nazama yayarka.

Cikin Jin Dadi jikinsa haryana rawa yace,

Da gaske zamuyita zama anan bazamu qara kwana bola ko titi ba.

Hawayen tausayinsu suka ciko idanuwanta ta jawosa jikinta tace,

Name alqawari insha Allah bazaku qara rayuwa ako inaba sai taredamu.

Ahankali Layla ta 'dago murya a sanyaye tace,

Mungode.

Zaunawa tayi tareda saka hannunta a abincinsu tana cewa,

To nima aci Dani tunda daga yanxu nima Dani za'ariqa cin abincin.

Suna gamacin abincin ta sake jawosu suka nufi palon Abba suka qara gaishesa ahankali ya

riqa yimusu tambayoyi akan rayuwarsu Nan Bilal yayita fada Masa komai tin talauci da wahalar
dasukasha tun baabansu nada rai har zuwa yanxu itadai tana rakube gefe.

Cikeda tausayawa ammy tajawota tana cewa,

Sannu kinji Layla.

Kai ta 'daga ahankali tana wasada sarqar hannunta Wanda yake 'dabiarta.

Janta aleeya tayi suka koma 'dakinta shikuwa Bilal zagewa yayi yanata bawa Abba labari abban
na sauraronsa qaunar yaron nashigarsa sbd kewar yara qanana data shigesa gashi ba ranar
samunsu sbd bazai qara ta6a haihuwa ba.

Ammy kuwa dariya da tausayin labarin da Bilal din ke bayarwa kawai take sbd duk yakai
qarshen kalma saiyace Dan Allah su riqesu karsu koresu.

Mamaki da tausayine yakama aleeya lokacinda sukazo sallah taga yanda laylar keyi Sam ba
ilimi aciki suna gamawa ta juyo ta kalleta tareda gyara zama tanayi Mata gyara.

Ita kuwa sunkuyar dakai kawai tayi tana sauraronta.
#mamuhgee


                          VOTE
                     COMMENT
[1/1, 11:03 PM] +234 701 680 1465: _*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_




*8*
Lokaci yaja Ahankali tafara sabo da kowa na gidan Bilal kuwa ba ruwansa tuni yayi sabo da
kowa musamman Abba kamar dama Nan aka haifesa ammy kuwa Layla takeji matuqar ji da it's
duk da har lokacin takasa sakewa gabaki 'daya aleeya ce madai ta sake da ita sbd yanda take
matuqar ji da ita Wanda Dan Dole kowa keji da Layla agidan sbd aleeya.
Wata 'daya sukayi agidan suka tattara suka koma Lagos sbd can dama suke da zama hutu da
aiki sukazo yi duk da dai su Yan asalin Nan 'dinne.

Sosai su Layla sukayi mamakin ganin girma da kyawun gidansu nanan din Dan duk kyawun na
adamawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login