Showing 33001 words to 36000 words out of 76958 words

Chapter 12 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

5604

cewa kuwa?

Qwarai kuwa maganar dr dawood da Nur din dayakeso..

Kallonta mum tasakeyi sbd jin sunan yarinyar abakinta ya tabbatarma da tasanta da gske.

Kifada zamu Baki ku'di iya adadin dabazaki iya kashewa ba.

Murmushi tasaki tace,

Nida nake hangen injimin ku'din gaba 'daya Mai zanyi da Wainda zakuban??
'danki nakeso taheer.

Wani irin mugun kallo mum ta watsa Mata baqin ciki da takaici na taso tace,

'dana yafi qarfinki kifada wani abun bayan wannan.

Inada asali cikakke Dan haka nafi sadaka ayalla da ba'asan asalintaba ita meyasa baifi
qarfintaba.?

Kidaina sako wannan sbd itama bawai tasamesa bane zanyi lokacinta idan muka gama da
matsalar dawood tukuna.

Kar6e zancen saraah tayi da saurin cewa,

Mum ki amince kawai da buqatarta Dan musamu Musan abinda mukeson sani afterall Naga
wannan 'din dazai aura ba sonta kikeba.

Shiru mum tayi cikin tunani sbd har abada bazata ta6a Bari 'yayanta su auri wainnan biyun dake
gabantaba Dan kuwa data Bari taheer 'dinta ya auri wannan ba gara tabari ya auri Laylanba
tayita gana Mata wulaqanci da azaba tasan zata 'dauka akan tasa ya auri wannan da zata iya
korota daga gidan wata Rana..
Murmushin Dole tasaki tana cewa,

Shinkenan tunda kince haka na amince zansa ya aureki Amma da sharadin sai bayan aurensu
na yanzu Kuma sai kunyi narasar raba 'yayana dasu Kuma ba.....

Sallamar Nanace tasa mum 'din yin shiru tareda sakin yaqe
Nana tace,

Ammy na magana.

Ok ganinan muje.

Bin Nana tayi tana watsawa gefensu wani mugun kallon qyama.

Bayanta sukabi da kallo saraah harda qaramin tsaki kafin ta juyo ta kalli siyama up and down
tace,

Zan fada Miki gaskia wannan matar qarya take Miki bazata ta6a barin ki auri 'dantaba zatayi
amfani dakene kamar yanda take tunanin tanayi Dani batasan Nice zanyi amfani da itaba Dan
haka just name any price zan biyaki kifadamin komai gameda yarinyar.

Kallon saraah 'din tayi koba komai maqiyin maqiyinka abokinka ne koba komai mace ' dayace
suke Hari kuma dole dama wasu ayukan datake planning Saida cash gashi saraah nadasu Dan
haka komai zaizo musu asauqi dan haka ta matsa jikin qofa tasaka key tareda dawowa ta
zayyanewa saraah komai ta 'dora da cewa, garaje ba naki bane kibini kiga yanda asannu zamu tarwatsa rayuwarta da duk wani munafukin
dake binta idan mun gama dasu saimu koma kan yanda zamu samu mazajen burinmu.

Wani irin murmushin Jin Dadi saraah tasaki tana jinjina shawarar siyama aranta Dan kuwa
siyama itace irin mutanen datakeso arayuwarta wainda zasu iyayin komai dansu samu abinda
sukeso at long last tasamu qawar dasuke ra'ayi guda.

Zama tayi bakin gadon dakin tana cewa,

Zan nunawa mrs Damien kuskuren data tafka na tunanin zata yaudareni sbd bayan zuwana
Nan gidan ayau na fahimci komai wato itakeson dawood ya auri aleeya nikuma tayi amfani Dani
gurin rabasa da wadda yakeso hmmm dukkaninsu saisunyi danasanin cin amanata harshi
dawood 'din su maska kuwa saina hargitsa rayuwarsu 'daya bayan 'daya Susan wa suka taru

suka hainta,
Mum kuwa bamu Bari tasan Layla bace sbd zata iya canza ra'ayi idan dataga 'danta na Shirin
mutuwa
Baqin cikina 'daya Dole zan hkr Ina kallo dawood yafara auren wata kafin Ni.

Cikeda murmushin farin ciki itama siyama ta jawo doguwar Riga ta zura tasamu wadda zata
tayata aiwatar da aikinta cikin sauqi....
Hmmmnnnn Layla tashin hankalinki ya qarato kekuma aleeya saikinyi danasanin fifita bare
akaina.
#mamuhgee
#vote
#comment.
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*24*
NOT EDITED.




Rama tayi sosai tareda firgicewa duk da tana iya qoqarinta gurin ganin ta danne abunda ke
damunta sbd gudun damuwarda aleeya da ammy zasu shiga saidai dauriya kawai takeyi gashi
bikin sai qaratowa yakeyi,

nana ce kawai tasan halinda take ciki sbd duk lokacinda taji wani abu na taso mata dakinta take
zuwa musamman yanxu da kuka ya daina zuwar mata saidai qirjinta gayi mata wani irin nauyi
sosai takeson kukan yazo mata kotasamu sauqin abunda takeji a qirjinta,

biki kuwa kusan dukkanin wani buri na ammy da nasu akan bikin aurensu ya kau sbd kusan
dukkaninsu su uku din babu mai wata doguwar walwala sbd kowa da damuwarda yake fama da
ita saidai kowa qoqarin 6oyewa dan uwansa yake kada yasashi damuwa.

6angaren siyama da sarah kuwa duniya sabuwa sbd wani aminci dasuka qulla da juna ko
yaushe suna tare wani lokacin ma can gidansu mum take kwana gurin sarah
koda mum ta tambayesu maganar Nur kai tsaye suka nuna mata tabari sai andaura aurensu
dawood tukuna idan ba hakaba sukaiwa NUR wani abu dawood yaji kafin daurin aure zai iya
fasawa kenan basu samu yanda sukesoba.

ba wani dogon nazari ta amince da hakan tanaso ayi auren tukuna suci mata uwar NUR

itakuma tayi musu korar wulaqanci daga gidanta kenan komai yatafi a yanda takeso,
wani irin murmushi tayi ta fice daga room din,

bayanta sukabi da kallo
sarah ta dauki ipad dinta tana cigaba da abinda takeyi tace,

wlh saina mayar da rayuwar mrs damien abun kwatance batasan akan danta saina aika kaf
zuriarta lahiraba stupid woman.

murmushi siyama tayi batareda tace qalaba sbd so dadama tana mamakin yanda rayuwar
sarah takeba samsam batada tarbiya ita haryanxu tama kasa gane musulmace ko muna
musulmi sbd bata ta6a ganin tayi sallah ba ga yanayin shigarta wani lokacin ko rufe kanta
batayi suke fita shiga ko wace iri yi takeyi dan taga tanada kyawu ne qila.
duk inda hankalin mum yake yatashi daurewa kawai takeyi kullum saita kira maska taji ko sun
iso sbd daqyar suka yarda zasuzo tareda dawood din.

yana gama waya da mum ya kalli inda dawood din ke kwance sun daura masa drip daqyar ya
yarda sbd ko miqewa yayi jiri ke dibarsa,
babban tashin hankalinsu shine ramar dayake tafara basu tsoro gashi yanxu ko aiki baya zuwa
koyaje baya zama gashi hakan na neman lalata carier dinsa gaba daya sbd so biyu yana
samun matsala gurin aiki danma duka biyun allah ya taimaka tareda jass suke aikin.

ruwan na qarewa yasamu qarfi ajikinsa ya tashi zaune tareda kallonsu da idanuwansa dasuka
canxa sosai,
sanyi jikinsa yayi ganin yanda komai ya canxa musu rabonda suyi fira suyi dariya tunda yarasa
Nur,
barinsa gida adamawa yakoma yafi sati biyu yana gararin nemanta harya kwanta ciwo maska
yaje yadaukesa suka dawo new jrsey
duk iya qoqarinsu na ganin abun bai ta6ashi ba sosai sunyi amma sam babu nasara saima
lalacewa dakomai ke qarayi,

washe gari tun kafin su fito yayi wanka ya fice zuwa office dan ganin ya qoqarta sbd ganin
yanda rayuwarsu tafara duqushewa sbd tasa,

cikin rashin sa'a yana isa ya tararda wata emergency theatre da farko yaso yaqi shiga sbd sam
baya tunanin zai iya saikuma ya daure yashiga yana qoqarin daidaita nutsuwarsa,

sabon tashin hankaline ya riski su maska lokacinda wani dr bk yakirasu ya sanardasu dr
dawood yashiga theatre,

arikice hankali tashe suka iso su duka ukun kowanne na addua da fatar kar asamu matsala sbd
wannan shine karo na qarshe da idan yaqara samun matsala carier 'dinsa zata lalace gaba

'daya,

cikin sauri jass yaje yayi shirin theatre saidai kafin ya gama aka fitoda dawood akayi emergency
dashi sbd yana cikin aiki ya yanke jiki ya fa'di,

sufyaan ne yashiga dubasa cikin gaggawa shida nurses,
ruwa da allurai ya daura masa nan take kafin yafa sakawa ayimasa runnin wasu test.

koda ya kar6i results din yaduba zama yayi a kujerar office 'dinsa inda aka dawo da dawood din
tareda miqawa jass yana cewa,

sake dubamin.

kar6a yayi yana kallon yanayin face dinsa kafin ya maida kallonsa ga result din,

rashin hutune da damuwa sosai datayi masa yawa sai ciwon qirji abunda ya 'daure kusu kai
sosai tareda basu tsoro shine yaushe dawood 'din yafara shan alcohol.

shiru maska idanuwansa sunji jajir dan kuwa baya buri ko fatar wani masoyinsa yafara shan
giya sbd illarta shima tazame masa kamar wata qaddarane yakasa daina shanta duk da kuwa
yanason yadaina amma yakasa,
basu ta6a luraba ko tunanin dawood yafara shaba saidai ga dukkan alamu lafiyarsa da jikinsa
basu qar6etaba tunda gashi tafara masa illa da wuri saidai ya tabbatarda duk akan matsakarsa
ne rabasa dashanta kuwa zaifi musu sauqine idan suka samu inda Nur take dan haka suka hau
shiri kai tsaye dan tahowa saigashi mum takira akan suzo bikin yana qaratowa.
aranar dazasu taho nigeria sosai jikinsa yaso tsanani saidai sufyaan yayi masa wasu allurai na
bacci suka taho dashi ahaka.

ranar dazasu iso aranar su mum suka dawo abuja daga adamawa kuma aranar su dad da
taheer suka dawo atare,

kallo daya dad yayi masa hankalinsa yayi mummunan tashi nan maska ya kwantar masa da
hankali yace bawani abu bane alcohol yakesha a yan kwanakin shine ta tabasa amma daya
kwana biyu aba masa allurai yana samun isashen bacci batareda yashataba zai warware insha
allah.
tom kawai dad din yace badan hankalinsa ya kwantaba saidan kasancewar yasan su maskan
qwararin likitocine dabaida haufi akansu koba komai yasan yanda sukeji da abokin nasu,

mum kuwa duk yanda taso daurewa kasawa tayi ganin cikin qanqanin lokaci yafara canzawa
sbd rama da wani 'dan duhu dayayi sannan ace dawood 'dinta nason zama mashayi sbd
mace,,danko baa fadaba tasan sbd nur ne,itakam tanason ganin wannan nur 'din yanxu kodan

taga abinda yasa danta ke neman illata lafiyarsa akan sonta.

bacci yake sosai sbd allurar da akai masa saidai bazaka kallesa kace baccin hutune yakeyiba
sbd fuskarsa data rame zata nuna baccin wahala da dolene yakeyi,

kwanansu 'daya da dawowa kenan amma harlokacin bai farkaba sbd qarfinta,
ajiyar zuciya maska ya sauke zuciyarsa ba dadi a karye lokacinda yafama kallon dawood 'din,

jass dake zare masa drip ya kalla yana dafe goshinsa tareda furzar da numfashi mai zafi murya
amace yace,

yau zanje adamawa inason ganin matarda mum zata aurawa dawood we need to talk kafin
daga baya akwai wanda zan sanya ya nemo mana nur cikin garin na tabbatarda zai nemota duk
inda take insha allah kafin nan zanfara biyawa kaduna gurin mamyna.

wani irin sanyi jikin jass yayi yakalli maska cikin sanyin murya yace,

zanbika muje tare inason zan gaisa da mamy nima.

ajiyar zuciya ya sauke ahankali kafin ya girgiza masa kai yace,

kabari idan nadawo zamuje gaba 'dayanmu kamar yanda muka saba zuwa mu gaidata,
yanxu dawood na buqatarku atare dashi fiyeda komai,

juyowa yayi yasake qurawa dawood 'din ido saikawai yaji hawaye sun taru a idanuwansa yayi
saurin dauke kai tareda kallon jass da jikinsa yaqara sanyi da wata irin murya yace,

jass promise me zaka kulada dawood da sufyaan kafin nadawo,

'daga masa kai yayi kawai batareda yasaniba sbd shima yayi nisa sosai cikin tunani,

rungumesa maska yayi yana cewa,

see you soon.

'daga masa kai yayi ahankali tareda cewa,

safe journey friend.

har mota yarakasa daidai isowar sufyaan daga gidan maska inda dawood yayi zama dama
acan suka sauka jass ne kawai atareda dawood anan gidansu mum.

rungume juna sukayi batareda sunyi maganaba tsawon lokaci kafin suka saki juna ya wuce

yana qara maimaita musu su kula da dawood sosai karsu bari yacigaba dashan alcohol.

murmushin qarfin hali sufyaan yasaki tareda jinjina kai har maskan ya fice daga gidan cikin
motarsa sbd da mota zaiyi tafiyar kaduna daga kaduna zai hau jirgi ya wuce adamawa.

koda ya isa kaduna mamynsa batanan tayi tafiya zuwa wani taron gidan marayu sbd batasan
ayau zai baro abuja ba,

bedroom dinta yashiga ya zauna tsawon lokaci kafin ya miqe yafito tareda barwa masu aikinta
saqon dayazo mata dashi yafasa kwana ya wuce sbd itama bayau zata dawoba,

airport ya wuce cikin saa yasamu ticket yawuce.

kaida kawo mum keyi cikin tsakiyar bedroom ranta ajagule,
saraah dake kwance tana shopping ta cikin waya ta 'dago tana kallonta sbd yanda kaida kawon
yafara damunta cikin ko inkula tace,

wani abu nadamunki ne mum?

rai a6ace ta juyo tace,

dama yazaayi narasa damuwa ina tareda mara amfani kamarki.

aje ipad din hannunta tayi tareda daure fuska tana kallon mum din.

yes mana sbd gashican maska yakama hanyar adamawa zai nemo nur dakansa kuma kinsan
daya samota wlh babu abinda zai hana aurenta da dawood koba komai nafara gajiya da
wannan balain.

shiru sarahh tayi cikin tunanin dole takira siyama duk yanda zaayi ayi kar abari maska yaga nur
ko gidanma kar abari ya isa kota halin qaqane.
#mamuhgee
vote
comment.
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*25*
NOT EDITED

koda ya isa adamawa ko hotel 'din dazai kwana bai isaba saida yanufi gidansu aleeya,

bai wani sha wahalaba ya isa gidan saidai cikin rashin sa'a mai gadi yasanar dashi suna lagos
acan sukefin zama,

dafe goshinsa yayi cikeda damuwa kafin yayiwa maigadin godia ya wuce,

hotel room yakama yayi salloli tareda ordern ruwan lipton da black coffee sbd hakanan yakejin
baya iyacin abinci mai nauyi.

shiru yayi tareda qurawa ruwan lipton din ido wannan shine karo na farko dabaiyi ordern giyaba
tun girmansa,
yau kuwa sam baya shaawar shanta sbd tunda yaga result din dawood yafara shanta yaji ya
tsaneta sbd yasan zataiwa amininsa illa dan haka koda zai hanasa shanta saiya fara raba
kansa da shanta wannan alqawarine ya dauka bazai qara shantaba insha allah,

kur6a biyu yayiwa lipton din ya ajiye sbd kwata kwata bayada apatite,

wayarsa ya 'daga yakira wanda yakeson gani yace yazo yasamesa a hotel,
cikin qanqanin lokaci wani babban saurayi ya iso yayi knocking room din yabude masa ya
shigo,

cikin girmamawa yace,

dr barka da isowa nigeria,

murmushin qarfin hali maskan yasaki tareda cewa,

thank you sambo,aiki zan baka kuma koma meyene inason samun aikina ta kammalu zuwa
gobe zan biya ten times na amount din aiki.

washe baki sambo yayi yana kar6ar wayar maskan dayake nuna masa hoton Nur,

bude bluetooth dinsa yayi yatura hoton cikin wayarsa tareda miqawa maska wayarsa yana sake
kallon hoton yace,

dr wannan aikin anriga angamasa kafin safe insha allah sbd yau komai dare saina gano komai
gameda ita,

daga masa kai kawai yayi tareda miqa masa envelope,

kar6a yayi ya fice yana kiran wanda zaifara tayasa aikin.


washe gari qarfe goma sambo yagama hado masa duk wani tarihi akan nur har asalin inda tayi
zaman bara kafin mahaifinta ya rasu da address dinsu na lagos.

lokacinda yakawowa maska bayanin da wasu sabbin hotunanta datake tareda aleeya a
instagram,

shiru yayi tareda qurawa hoton ido zuciyarsa cike fal da farin ciki mara misaltuwa sbd
yasamowa abokinsa farin cikinsa,

bai tsaya 6ata lokaciba ya harhada ya wuce airport ko takardun bayanan bai kar6a ba ya wuce
sbd matsuwar yaje yaga nur da aleeya suyi magana atare,


tunda yakama hanyar airport yake kiransu jass amma babu wanda wayarsa ke shiga,

sukuwa sunacan hankali amatuqar tashe sbd jikin dawood aya rikice musu amai kawai yake
shararawa mum tayi kuka har idanuwanta sunfara kumbura amma duk da haka batajin zata bari
a 'daga bikin gwara ayi matarsa tayi jinyarsa idanma wata qasar za'a fitar dashi,


ganin yakasa samunsu saiya yanke shawarar kiran numbern nur da sambo yabasa,

qaramin tsaki yasaki lokacinda yaji wayar bata zuwa,
shiru yayi tsawon lokaci kafin ya yanke shawarar kiran numbern aleeya yafara fadamata komai
ta waya kafin ya iso,

numbernta da duka cikin binciken sambone aka samo yakira,


zaune take bakin gado ta tallafe kanta dake tsananin ciwo tayi zurfi cikin tunani,

ringing din wayar dake kusada itane yasa tadan juyo ahankali takalli wayar tareda lumshe
idanuwanta dasukai jajir ahankali tasake ajiyar zuciya tareda dauke kai sbd hoton dawood ne
kwance akan screen din wayar ta aleeya,

sake kira akayi ta miqe da sauri tabar 'dakin batareda tasake kallon wayarba.

tana fita siyama dake toilet na fitowa hararar wayar tayi tareda jan qaramin tsaki tana wucewa,

cak ta tsaya tareda dawowa da sauri ta duba numbern kamar wadda sarah ta turo mata ta

tsohon 'dan iskan dakeson yiwa aikinsu shishigi,

wayarta taciro da sauri taduba numbern taga tabbas itace
kiran nasake shigowa ta 'dauka da sauri tareda daidaita muryarta tace,

hello

ajiyar zuciya yasake ahanakali tareda amsa sallamarta cikin qwarin gwiwa yace,

aleeya madibo please?

ahankali itama tace,

yes waye?

khaleefa maska aboki kuma 'dan uwan dr dawood,
inason maganane dake akan keda 'yar uwarki nur sbd samowa kanmu mafita gabaki daya,

wani yawu siyama ta hadiye mai daci na tsanarsa sbd da allah baisa itace tadau wayarba kenan
haka zai lalata musu komai,
wlh zaiyayi danasanin wannan karanbanin bashibama duk wanda yayi shishigin ha'da wainnan
masoyan saiya biya da abinda yafi qarfinsa,

daidaita muryarta tasake yi cikin sanyi tace,

gskia ayanxu banason muyi wannan maganar agida sbd nur batasan nasan komaiba dama ina
neman mafita dan haka yanxu saidai muhadu wani guri muyi magana,

shiru yayi nadan lokaci kafin yace,

ok kibani address na.....

aaa kabani address na inda zan sameka ni zanzo.

ok idan na iso lagos zanmiki sendin room no na hotel dinda na sauka.


kashe wayar tayi tareda sakata silent ta tura cikin jakarta sbd karya turo address din wayar bata
hannunta,

shiryawa tayi tafito ta nufi 'dakin ammy ta tarardasu kamar koyaushe cikin kwanakin,

layla da zaune tana gyarawa ammy wardrobe amma sam hankalinta na wani guri,

aleeya kuwa tana qoqarin gusar da damuwartane ta hanyar qoqarin taya bilal wani aikin a
laptop amma itama hankalinta na wani gurin ammy kuwa waya takeyi na kayan datayo order na
aurensu itamadai daga sautin muryarta kana iya jiyo sanyi da samuwa aciki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login