Showing 48001 words to 51000 words out of 76958 words
Chapter 17 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf
ma nan take hawan jininta yatashi akai
gaggawar kwantarda ita sbd kartayi kwalapsin,
bilal kuwa tsayawa yayi cak gaban gadon ammy idanuwansa jajir jijiyoyin kansa har wani motsi
sukeyi tsabar tashin hankali sam kwaqwalwarsa takasa daukar cewa 'yar uwarsa ta tafi tabarsa.
sulalewa mum tayi takoma gida afusace ta banka qofar dakin sarah tareda fusgota ta jehota
waje tareda watso mata kayanta tace,
duk wata masifa data afkomin nida yayana kece,
nayi baqin ciki da dana sanin kawoki gidana,
kin tarwatsa rayuwar yayana,
na hana yarona farin ciki ina kallo rayuwarsa ta ta6ar6are sbd ke,
yanxu kinzo kinyi qoqarin kashemin taheer inaji ina gani na maqalawa wata sbd kar laifin
yashafeni gashi ta rasa ranta ta rasu ta sanadinki amma bazan iya fadaba sbd dole nima saina
fuskanci sharia dan haka tun kafin kowa yasani kitashi kibarmin gidana bana buqatar sake
ganinki inason gyara abubuwan dana lalata da kaina.
muqewa sarah tayi tana kallon bayan mum din ido a waje,
juyawa mum tayi tayi ido biyu da dad tsaye idanuwansada fuskarsa qunshe da tsananin 6acin
rai,
mummunan faduwa gabanta yayi wani mugun zufa ya karyo mata tadaga qafa zata matso ya
daga mata hannu da ido jajir,
sarah na ganin haka ta sulale takwashi kayanta tabar gidan.
cikin wata irin murya mai tsananin sanyi yace,
faraah kanki kika cuta,
dasaka hannunki cikin lalacewar danki,
dasaka hannunki cikin mutuwar yar mutane,
bazan miki komaiba sbd haryanxu duniya bataimiki darasin daya kamata saidai nizan dauke
'dana mutafiyarmu bazaki sake ganinmuba insha allah dawood ma zan dawo na daukesa sbd
yanxu matarsa na buqatarsa na rashin yar uwarta datayi.
matsowa tayi da gudu ta zube gabansa tareda riqo qafafuwansa tasaki wani irin kuka mai qarfi
ya zame qafafuwansa ya wuce ya tattaro duk wasu takardu da abubuwan buqatarsa dana
taheer yafice tabisa har jikin mita tana kukan tashin hankali amma ko kallonta baiyiba yawuce
da gudu yabar gidan.
yana isa asibiti cikin qanqanin lokaci yasaki kudi sosai nan take suka samu flight aka saka
taheer suka tafiyarsu bataredama taheer din ya farfadoba.
#mamuhgee.
vote and follow pls.
_*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_
*32*
NOT EDITED
bayanta baffa dahiru yabi da kallo yana jinjina alamarin kafin ya nufi dakinsa ya zauna yana
sake nazarin alamarin,
baifitoba sai maraice yayi alwala shidasu dawood suka wuce masallaci har lokacin sosai
dawood yake cikin yanayi na jin zafin abinda laylar ke shirin yi duk da dai yasauki alqawarin
kobataso saiya aureta yagaji da wannan azabar datake gana masa arayuwa.
amasallaci bayan sallar magriba baffa yasamu mal liman yayi masa bayani akan rasuwar mijinta
dakuma auren dasukeson adaura,
dogon naxari mal liman yayi kafin ya nisa yakalli baffa dasu dawood din yace,
tabbas zata iya aurensa tunda wancan qaninsa din kunce yarasu saidai dole sai bayan tagama
takaba...
shiru baffa yayi na seconds kafin ya dago murya a tausashe yace,
eh to babu wani abu na aure daya ta6a shiga tsakaninsu hasalima basuyi rayuwar irinta zaman
aureba kuma kafin rasuwarsa yabata sakinta ahannunta.
sake gyada kai mal liman yayi yasake cewa,
eh to zasu iya aure amma idan son samune zaifi subari zuwa gaba kamar......
katsesa sufyaan yayi dafara zayyano masa komai daga farko zuwa qarshe.,
mal liman yayi shiru tareda qurawa dawood ido yana jinjina kai yace,
sannu dauda.
kallonsa kawai dawood yayi da lazy eyes dinsa shidai fatarsa kawai ace zaa daura auren.
tabbas daura musu aure bai haramta ba dama dai nasone subari tayi kwana biyu kamar zaifi
amma tunda abun hakane gobe takasance alhamis jibi ranar jumaa insha allah da safe sai a
daura auren,allah yasa hakan shine mafi alkhairi arayuwarsu duka.
amin sukace dukkaninsu dawood najin wani sanyi da kasala na shigarsa sbd yasan babban
burin rayuwarsa ne zai cika idan NUR dinsa tazamo matarsa,
godiya sukai masa sosai kafin suka miqe,
basu koma gidaba saida sukai sallar isha suna komawa suka shige daki duk da zuciyarsa a
tsananin takure takedason ganinta amma hakanan ya daure sbd yasan idan ya matse mata
zatacene bazatai aurenba gwara yabata space har yasamu adaura auren,
yanaji inna halima nayiwa baffa complain taqi fitowa har lokacin kuka takeyi yayi zuru tareda
mayarda dukkanin hankalinsa kan qofar dakin datake,
sufyaan dake qoqarin sanardashi maganarsu saraah ganin hankalinsa baya jikinsa yasa yabari
harsai bayan auren idan hankalinsu yadan kwanta.
da tsakar dare kasa kwanciya yayi sbd yana jiyo ajiyar zuciyarta alamun idanunta biyu sam
bayada sukuni na jiki dana zuciya sbd rashin sanin halinda take ciki.
har asuba yana zaune ko gyangyadawa baiyiba sbd ita.,
suna fita sallar asuba itama tafito daqyar sbd ko gani batayi sosai sbd kumburin idanuwanta na
kuka,
alwala tayi takoma ta tayarda sallah a zaunema tayi sallar sbd wani irin mugun jiri da zazza6i
mai zafi dayake cinta,
tana gamawa ta dunqule gurin tana kakkarwa tareda wani irin wahalallen nishi.
hankalin inna halima ne yafara tashi ganin halinda take nan tazauna jiran dawowarsu baffa basu
dawoba saida gari yayi haske sosai.
maganin zazza6i baffa yabayawa innar abata shima bayason matse mata dankarma ta tayarda
maganar rashin son auren,
dawood ma ganin zai iya rasa nutsuwarsa yasa sufyaan jansa suka fita bayan gidan,
zama sukayi bakin wani dutsi ya rufe idanuwansa ahankali tareda jinginarda kansa jikin ice
zuciyarsa na qara rasa sukunin halinda nur din ke ciki,
tabbas NUR itace rayuwarsa,farin cikinsa,baqin cikinsa,qaddararsa dakuma burinsa aduniya.
dafasa sufyaan yayi ahankali tareda tausasa murya yace,
idan andaura auren ya kake tunanin zamu fuskanci su mum?
bude idanuwansa yayi dasukai jajir ya qurawa qasa ido kafin ya dago cikin takaici yace,
idan na aureta she's mine,
my responsibility,
my future,
rayuwar danayi abaya cikin mummunan yanayi yasa na qara daukan wani life lesson so na
shirya gyara rayuwana ta hanyar shimfida sabuwar rayuwa dan haka ba ruwana dasu mum or
wata aleeya can,am gonna take her somewhere,where we can start a very happy married life
sai bayan wani lokaci zamu dawo idan sunga dama su kar6emu idan sunga dama su gujemu.
jinjina kai sufyaan yayi tareda cewa,
ina bayanka lets start a new life afterall jass yakusa cika shakarunsa biyu yafito....
yes saura sati biyu yacikasu inaga wannan wata damace da allah yasake bamu mu shimfida
kyakkyawar rayuwa mai tsafta.
murmushi suka saki dukkaninsu sai alokacin yaji dan sauqin abunda yakeji.
suna gurin baffa yazo wucewa gona sufyaan ya miqe yabisa dawood kuwa gida yakoma
yashige daki ya kwanta yana kallon sama tareda lumshe idanu yana tunanin abubuwa da dama.
sufyaan kuwa saida sukayi nisa sosai yakalli baffa yace,
baffa inason shiga inda zansamu harkar banki maana wayayyen guri haka.
tsayawa yayi tareda juyowa gefen sufyaan din yace,
mezakayi dabazaka bari sai bayan daura aurenba?
gyara tsayuwarsa yayi yace,
inason nine zanbiya kudin sadakin abokina sbd wannan shine burin maska harya rasu shine
yayi alqawarin biyawa dawood sadakin aurensa matuqar da NUR ne ayanxu dabaya raye
inason dauke wannan nauyin.
murmushi baffa yayi yace,
to ai dan wannan ba matsala bane ni zan biya....
aa baffa kaine kazamo kamar kawu ga nur kuma kaine zaka bada aurenta baikamata ace
sadakinta yafito daga garekaba nine nayi niyya kuma nine zanbiya insha allah.
to tunda kanaso hamisu rakasa kuje gonar mal jamilu kugani idan motar akori kurarsa bata
wuce gariba saiku bisa yawuce daku idan zai dawo yadawo daku.
juyawa sukayi suka wuce shima ya qarasa gonarsu dake kusada rafi.
cikin saa suna zuwa suka tararda yadauki kayan miya zai wuce suka fada yawuce dasu atakure
bama kamar sufyaan dabai ta6a shiga irin wannan motarba da duk qarfece ba guri mai laushi
ko kadan ko gurin zaman duk ya cinye sosai yakecin duwawu amma haka yadaure sukaita
gurxawa.
tafiya mai nisa sosai sukayi kamar bazata qareba daqyar suka iso wani dan gari ba laifi yanada
cika sosai dakuma abubuwan zamani kamarsu bankuna biyu da yar babbar kasuwa da babbar
tashar motoci harda babbar asibitinsu gasu da wuta koina.
bai tsaya bata lokaciba yashiga banki bayan dogon turanci daqyar ya iya cire kudi masu yawa
ta slip yafito suka shiga kasuwar daqyar ya iya shigarta aka kaisa wani babban shagon saida
kaya daqyar yasamu shaddodin dubu ashirin ashirin yasiya guda biyu agurin aka dinka musu
shida dawood ba aiki ba komai kawai babbar riga hudu yace ayi musu ta ishesu tunda ana
daurawa zasu wuce.
gasassun kaji dakaton na drinks yasiya da takalmi sai dogayen riguna guda biyu daya siyowa
nur.
daganan lafiyayyar matarda bataji jikiba golf yayi musu shata tamayardasu da sharadin acan
mai motar zai kwana washe gari bayan daurin aure zai fito dasu qauyen abuja zai kaisu.
sai bayan magriba suka iso nan ya miqawa inna halima kayan nur dakuma kajin sai baffa
babbar riga daya hamisu daya shima daya sai ango daya.
dawood baiyi wani mamakiba sbd shidai amatse yake da gobe tayi adaura auren su wuce.
lokacinda inna halima takai mata kayan kar6a kawai tayi ta ajiye sbd tuni kuka ya qaurace mata
tayi zuru zuru ko iya bude ido sosai batayi.
daren yau dinma daga ita harshi babu wanda yayi bacci uwa uba abinda yake tsananin cinsa
shine yinin ranar gaba 'daya basu ga junaba ba qaramar azabtuwa da dauriya yayiba.
ana kiran asuba yasaki wata irin ajiyar zuciya shiya riga kowa fitowa yayi alwala kafin suka fito
sukai alwalar suka nufi masallaci baki daya.
kamar koyaushe saida gari yayi haske suka dawo suna shigowa gidan cikin sa'a idanuwansa
suka sauka akanta lokacinda take qoqarin aje butar data fito bayi.
sunkuyar dakai tayi daqyar dasashiyar muryarta dake rawa ta fito asanyaye ta gaida baffa dake
gaba.
amsawa yayi cikeda farin ciki kafin yq wuce sufyaan dake bayansa fuska asake yace,
gud morning.
'daga masa kai kawai tayi tareda juyawa da sauri zata bar gurin yakasa haquri ya riqo hannunta
ta tsaya cak numfashinta na futa da sauri sauri.
matsowa taji yanayi ta janye hannnunta da sauri tareda shigewa daki ta dafe qirjinta sbd
bugawar dayake.
kallo yabi qofar dakin da shanyayun idanuwansa dasuka galabaita dasonta kafin ya wuce dakin
dasuke shima.
sauran kajin jiya sufyaan yaci shukuwa bakinsa wata irin bushewa yayi yawunsa suka qafe
babu abinda ke gabansa dayafi yaga andaura auren,
baida wata nutsuwa ko sukuni ayanzu saiyaga nur tazama tasa.
wanka yayi yamayarda kayansa da aka wanke jikinsa wani irin sanyi yayi sosai daqyar sufyaan
ya taimaka masa yasaka babbar rigarsa sbd bai iya sakata ba.
koda baffa yafito yace su fito nan jikinta ya tsananta rawa tanason yin kukan amma takasa haka
ta rarrafo ta fito ta tsaya gaban baffa ta sunkuyar dakai sbd idanuwanta dasukai jajir zatayi
magana dawood dake gefen baffa yadawo gabanta tareda kafeta da lazy eyes dinsa murya
amatuqar sanyaye yace,
zakice bakyson adaura miki aure danine sbd kema kinga na zama abun qyama ko?
'dagowa tayi ahankali takallesa sai takasa magana sufyaan na ganin haka yayi saurin cewa,
baffa muje su malam nacan najira .
wucewa sukayi kowanne na gyara babbar rigarsa shikuwa saidaya qara kallon fuskarta dake
sunkuye kafin ya wuce.
suna futa ta shige daki tareda qanqame jikinta dake wata irin rawa wace irin masiface zata
sameta yau ta auren mijin aleeyarta.
sukam suna isa dama tuni sukawai jamaa ke jira sbd anyi sanarwa daurin auren bayan sallar
asuba nan aka fara sufyaan yafito da sadaki naira dubu hamsin nan take aka gabatarda daurin
auren aka shafa fatiha.
#mamuhgee
vote and follow.
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*33*
NOT EDITED.
wasu irin hawayene suka ciko idanuwansa dasuka qanqance sbd yunwa da wahala dakuma
fargaba,
kallon mutanen dake miqa masa hannu yake kamar wani wawa sbd tsanananin mamaki da farin
cikin daya kasa gasgatawa yau NUR tazama tasa da sauri ya miqe yayiwa allah sujjada yatashi
tareda rungume sufyaan daketa faman washe baki farin cikinsa baya misaltuwa.
saida aka gama komai mutane suka watse suka sakeyiwa mal liman da baffa godiya sosai nan
sufyaan yayiwa mal liman babbar kyautar kudi sosai sukai masa bankwana suka wuce sbd so
suke su isa abuja da wuri,
gida suka nufa ahanya ya zare babbar rigar tareda zuba hannunsa a aljihu murmushi yake saki
yana tafiya kwata kwata hankalinsa baya taredasu sufyaan da baffa shi wata duniyar tunanin
dayake dabam,
sufyaan na lure dashi yasaki murmushin farin ciki yana girgiza kai tareda cigaba dayiwa baffa
bayanin wucewa zasuyi yanxu.
kudinda yatanadar masa tun jiya ya ciro yabasa cikin girmamawa yace,
insha allah dakomai ya gama daidaituwa zasu sake dawowa sukawo gaisuwa.
godiya kawai baffan yayi tareda cewa,
bakomai allah dai yakawo fahimta acikin alamarin cikin sauqi.
amin''''sufyaan yace yana kallon gefen dawood da wani irin annuri ke fita fuskarsa baimasan
mesuke cewaba.
suna isa gida cikin tsananin farin ciki inna halima tayi musu allah sanya alkhairi sufyaan ne
kawai ya amsa dawood hankalinsa nakan qofar dakin datake yasan kuka takeyi kobaa fadaba.
ko dakuna basu shigaba sukace wucewa zasuyi,
inna halima tashiga dakin datake takalleta taga har lokacin ko wanka batayiba tana zaune
yanda take tundazu harlokacin jikinta bai daina rawaba.
dafata inna tayi tareda yimata yar qaramar nasiha ta dagota daqyar suka fito tana fitowa
idanuwanta suka sauka cikin nasa ta sunkuyar dakanta tareda dagawa baffa dake mata
magana kai.
'yar nasiha baffan yayi mata tareda bawa dawood amanarta suka fito,
motarda sufyaan ya dauko musu tun jiya shata har qofar gidan ta qaraso suka shiga suka wuce
hawayenta na saukowa ahankali na fargabar abunda zasuje sutarar.
sufyaan ne agaba itada dawood din abaya tunda tashiga ta juyar dakai gefe tareda rufe
idanuwanta ahankali sbd ko jinsa zaune gefenta tsananta bugun zuciyarta yake bare ta iya
kallon gefensa.
qura mata idanuwansa dasukayi laushi yayi cikeda wani irin farin ciki shikadai yasan irin
rayuwar dayake musu tunanin shimfidawa kafin sudawo sbd bazai ta6a gangancin bari suje
gida yanxuba a 6angale masa auren dako kwana daya baiyiba aduniya dan yasan sarai hakan
zata iya faruwa takowane 6angare na mum dinsa kona su aleeya.
doguwar tafiya sukayi babu wanda yayi magana acikinsu basu iso abuja ba sai yamma sosai
nan sufyaan yayiwa drivern magana kai tsaye ya nufi gidan maska dasu.
lokacinda suka isa gidan sosai taji habkalinta yatashi ta kalli dawood din da sauri ganin yaciro
mukullin gidan inda suke aje spares cikin wata flower dake qofar shiga,
daure fuska yayi nantake yakoma dawood dinsa sbd karma tasamu fuskar jeho masa wani
zancen,
ganin yanayin fuskarsa yasa ta sunkuyar dakai tareda rufe ido hawayen ciki suka sauko ta
share ahankali,
suna shiga sufyaan yayi saurin shigewa bedroom daya yabarsu apalon.
kallonta yayi yaga yanda ta tsaya batada alamar motsawa ya matso ahankali yakamo hannunta
yakaita har tsakiyar 'dayan bedroom din ya juyo yafito yakoma wanda sufyaan yake sbd duka
gidan is two bedrooms flat ne,
tu6ewa yayi ya kwaso kayan daya cire yaje yazuba dusbin yadawo yashiga wanka,
kwanciya yayi cikin ruwan dumin tareda lumshe idanuwansa yasaki ajiyar zuciya ahankali wani
irin kwanciyar hankali na shigarsa,
ya jima acikin toilet din yana dumama jikinsa tareda yin wankan daya jima baiyi irinsaba kafin ya
fito daureda towel iya qugunsa.
yana fitowa ya tsaya gaban mirror tareda shiryawa cikin three quater black da black shirt mai
hula yayi sallah yana idarwa ya kalli sufyaan daya fito wanka yace zashi gida yadawo.
dayake basu sallami drivern ba sai gobe tukuna saiya shiga motar suka fuce,
nesa da gidansu yasa drivern ya tsaya yajawo hular rigarsa yarufe rabin fuskarsa ya isa qofar
gidan ahankali cikin saa babu kowa sai maigadi,
maigadi na ganinsa ya miqe da sauri cikin sauri ya girgiza masa alamar karyayi magana ya
matso kusadashi sosai yace,
akwai mutane sosai aciki gidan?
bakowa yallabai alhaji yayi tafiya hajiyama bata dade da fitaba zuwa asibiti can gurin haj aleeya
daaka kwantar kwana biyu yanxu sbd rasuwar mai dakin taheer.
wat yace da dan qarfi kafin yayi saurin yin qasa da murya yace,
kana haukane zakace nur ta mutu,,,get lost and karka fadawa kowa nazo komai rintsi.
cikin sauri yashiga gidan direct part din mum yafara zuwa yashiga dakinta yafara duddubawa
baiga komai na nur ba yafito yashiga dayan dakin cikin sa'a yaci karo da handbag akan gadon
dakin da sauri ya bude yana dubawa cikin saa yaga passport dinta bai tsaya cire komaiba
yadauki jakar tareda akwatinta dayagani aje tun dawowarsu bata budesaba yasan ba shakka
tatace,
maigadi yabawa yakai masa mota da sauri shikuma ya nufi part dinsa ya dauki passport dinsa
dana sufyaan tareda wasu kayansa da laptop da duk wasu mahimman takardunsa da komai
nasa mai mahimmanci ya fito.
saidaya qara gargadar maigadi tareda basa wasu kudi masu dan kauri daya tsinto a dakinsa
suna barin gurin mum da Nana nadawowa daga asibiti sbd har lokacin anrasa gane kan aleeya
ciwo take sosai anyi qarin ruwa da maganguna har anfara gajiya babu wani saiqi sbd ba
qaramin bugun zuciyarta da qwaqwalwarta batun rasuwar layla yayiba ga 6angare guda annemi
gawarta acikin motar baaganiba.
yana isa gidan yazauna palo tareda kallon sufyaan dake zaune palon yana waya da lndline ta
gidan,
waya yake da wanda zaiyi musu komai so suke kamai rintsi gobe su wuce.
yana gamawa order daya bayar daga pizza kitchen ta iso ya bude qofa ya karbo tareda ajiye
nasu ya miqawa dawood na layla.
kar6a yayi tareda jan akwatinta ya nufi dakin,
knocking yayi ahankali ya tsaya jiran ta bude.
tsawon mintuna bata budeba yasake knocking tareda tura qofar ahankali yashiga tareda turo
qofar,
zaune take qasa kan daddumar sallah ta kwantarda