Showing 1 words to 3000 words out of 76958 words

Chapter 1 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf

04 Jun 2025

5546

Compiled By Umar Dalha Funtua.


*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_

_for you surayyahms_




*1*
Bismillahir-rahmanirraheem.





_*NUR D.S specialist hsptl first floor acade building anyerinxs strt porthcrt 23 December...*_

Da wani irin speed motar ambulance 'din specialist 'din tashigo harabar building 'din asibitin
manyan Mercedes Benz 3600mz2018 black biyu na bayan ambulance din ko kyakkyawan
parking basuyiba sukai saurin fitowa Babu Wanda hankalinsa ke jikinsa sbd tsananin tashin
hankalin dake cikin zukatansu na ganin Wanda kowannensu baya iya kwatanta rayuwa
babushi...

Arikice suka qaraso jikin ambulance din daidai lokacinda nurses maza da mata tareda doctors
kusan biyar sukayo kan motar aka fito dashi cikin gaggawa akayi ciki dashi tun a hanya ake
'daura Masa ruwa da jini sbd tun acikin ambulance andaura Masa cannula tareda Fara basa
injections na jinin daya zubar sosai ta bakinsa..,
Cikin tashin hankalin dayafi na likitoci da nurses 'din asibitin ganin babban likitansu Kuma Mai
asibitin cikin wannan mummunan yanayin suke bin bayansu har aka iso bakin private aminity
emergency suka shige dashi aka rufo qofar Dr ayub ne yasamu damar 'dan waiwayowa cikin
gaggawa da son kwantar musu da hankali yace,
Sorry ma'am you will have to wait hia and please calm your self insha Allah he'll be fine we'll do
our all best just pray for him,,

Ya juya ya shige tareda wasu nurses biyu dasuka zo shigewa da gudu 'daukeda wasu kayan
theatre..

Baya tayi cikin tsananin tashin hankali tareda fashewa da wani irin kuka sufyaan dake gefenta

yayi saurin tarota cikin qarfin Hali ya bude bakinsa daqyar yasamu ya iya furta,

Please mum just pray for him..

Wani sabon kukan tasaki tareda rintse ido tana cewa,

Ya Allah ka kawowa 'dana sauqi da sassaucin wannan masifa,
Wannan wace irin qaddarace Mai wuyar cinyewa.....

Rufe Mata Baki sufyaan 'din yayi da sauri Yana kallonta da idanuwansa dasuka ka'da sukai jajir
tsabar tashin hankali...

Juyawa yayi ahankali ya kalli gefensa daidai isowar jass arikice ko gani sosai bayayi tsabar
tashin hankali Yana isowa ya tsaya cak ganin irin tashin hankali dake tattareda kowannensu,

Fuskar sufyaan ya kalla yaga hawaye sun cika jajayen idanuwansa Nan take yaji gwiwowinsa
sun Gaza 'daukarsa ya zube kan kujerar dake kusadashi tareda rufe fuskarsa da tafukan
hannayensa hawaye na tsinke Masa Masu zafi da ciwo.

Sunkuyar dakai sufyaan 'din yayi ganin halinda jass yashiga zuciyarsa na qara nauyi.,

Hawayen dayake dannewane suka gangaro Masa lokacinda ya 'dago kansa ya 'dora
idanuwansa kanta tana zaune Nana na zaune gefenta ta riqo dukkanin hannuwanta biyu tanata
qoqarin ganin ta kwantar Mata da hankali cikin hawaye da tsananin tashin hankali ganin kamar
zarewa 'yar uwar Tata zatayi sbd tunda abin yafaru ko motsin kirki batayiba bare hawaye saidai
jajir da idanuwanta sukai Sam ita tafiso taganta tayi kuka yafi sauqi akan wannan halin dataga
tashiga..

Lumshe idanuwansa dasukai jajir yayi cikin tsananin tausayin _*ALEEYA*_ tabbas dukkaninsu
suna cikin wani Hali Amma tafisu Dan kuwa ita qunci da Sauyin rayuwa tuni ya Dade da
wargaza komai nata,
Ta Dade dayin bankwana da farin ciki,
Babu wani 'digon farin ciki dayayi saura arayuwarta,
Qunci,damuwa,kuka,ciwo,zafi dakuma baqin ciki sune kadai sukeda cikakken mulkin mallaka
arayuwarta yanxu kokuma yace arayuwar dukkaninsu dankuwa dukkaninsu sun Jima da manta
yanda yanayin farin ciki ko annashuwa suke,

A dah daza'ace akwai ranarda zasuji wata damuwa bare baqin ciki da bazai tsaya sauraroba
Dan bazai yarda ba sbd dukiya, kyau,ilimi, wayewa,gata,dakuma ingantacciyar rayuwar holewa
dusukeda ita a hannunsu Ashe komai na juyawa,,

Har ayanxu Basu rasa komaiba Amma komai yazama kamar babushi sbd babu farin ciki ko
kwanciyar hankalin Jin dadin kenan dukiyar da kyawun,da ilimin da gatan da wayewar basuda

wani amfani ayanxu arayuwarsu,
*_DAWOOD_* wani 6angare ne arayuwarsu dazasu iya kwatanta rayuwa babusaba,..

Hannu yakai ahankali ya dafa kafadun jass tareda jinjina Masa Kai alamar rarrashi 'dayan
hannun nasa na riqedana mum sbd har lokacin wani irin kuka take Mai tattareda
danasani,nadama da uwa uba fargabar rasa tilon 'danta,farin cikinta.

Zaman jigum jigum sukayi cikin matsuwa da fargaba har tsawon awa 'daya kafin doctors suka
Fara fitowa har lokacin mum hawayenta Basu tsayaba idanuwanta sun kumbura matuqa ko
gani sosai batayi fuskarta tayi jajir kasancewarta Fara sosai.

Sam Batada qarfin motsawa lokacinda doctor Jeremy da Dr Aqeel suka qaraso gabansu
Ganin tana neman shiga wani sabon halin ne sufyaan yasake riqeta Yana rarrashinta
Saidai jass ne ya miqe tsaye jikinsa na'dan rawa sbd sam Shima tamkar mace yake baida irin
dauriyar Nan sosai a irin haka.

Kallonsu yayi da jajayen idanuwansa murya na rawa yace,

How is h,,,kasa qarasawa yayi sbd kukan dayaso kubce Masa yayi shiru Yana goge fuskarsa da
handkachief..

Dafasa Dr Aqeel yayi cikin damuwar Shima yace,

Kuci gaba da addua shine kadai abinda zamu iya cewa,
Kaida sufyaan are doctors kunsan irin yanda abubuwan ke juyawa so please just keep on
praying for him sbd he really needs it...

Kallon mum sukayi cikin sanyin murya sukace,

We're really sorry Mrs assiddeeq addua shine the best thing now... Allah yakawo sauqi muna
fata..

Juyawa sukayi suka wuce jiki sanyaye cikeda tausayin familys din.

Zuru dukkaninsu sukayi kamar Babu Mai Rai suna kallo aka fito dashi aka Kai wani special
room sukayi rubuce rubuce da sauran formalities 'din kafin dukkaninsu suka fice.

Itace tafara miqewa Nana na riqeda ita sbd Bata iya tsayawa da kanta sbd jiri da ciwon dayake
damunta for some years now sukaga room din.

Bakin gadon ta qarasa zuciyarta na wani irin bugawa,zafi da ciwon zuciyarta na shekaru na
ninkuwa,
Kuka takeso tayi Amma takasa Wanda hakan yasa idanuwan sukai wata irin jemewa Babu

kyawun ganin sbd komawar dasukai kamar na tsufa.

Qura Masa idanuwa tayi zuciyarta na nauyi sbd ganin yanda ciwo ya mayardashi,
Kyakkyawane ajin qarshe kasancewarsa halfcas Amma gabaki 'daya kamaninsa sun canza,
Fuskarsa ta rame tareda wani irin duhu musamman gurin gurbin idanuwansa sai bakinsa dayayi
baqi ya bushe kamar yayi shekara goma baisha ruwaba..

Ahankali ta furta,
*_DAWOOD.._*

Jitayi zuciyarta ta amsa Amon sunansa data Kira
Nan take jikinta yafara karkarwa zuciyarta na neman rasa Jan numashi.

Da sauri Nana dake gefe tana kuka ahankali kamar ranta zai fita sbd tausayi abubuwan dake
faruwa tsawon shekaru,,,,
Kowa na rayuwar farin ciki da Jin Dadi Amma cikin shekaru biyar kacal komai ya lalace,
Farin ciki yazamo tarihi arayuwarsu kuka da ciwo sune kawai ke qara wanxuwa a tsakaninsu.

Ahankali mum tashigo 'dakin jass na riqeda ita sbd sufyaan na bayansu..

Kallo 'daya zakayiwa mum tabaka tsananin tausayi sbd yanda ta jeme cikin qanqanin lokaci
tsufa yafara taso Mata duk kuwa da tsufan ne tayba,
Gabaki 'daya itama tayi duhu ga wata irin rama..bazaka kalleta kace itace Madame faraah ba
the famous Mrs assiddeeq Damien da kullum ake bugawa a cover din fashion magazine ba sbd
kasancewarta CEO na all the fashion empire na Miami,
Kyau,hutu,gayu,burgewa tareda 'dinbin dukiya uwa uba bazakai Mata kallon babbar macenda ta
aje babban the youngest multibillonaire doctor *_DAWOOD ASSIDDEEQ DAUDA_* ba
dasukaci lokacinsu Wanda haryanxu ba'asamu madadinsa ba shida friends dinsa Amma yau
duk Babu wannan sbd tun farko basusan qaddarar da Allah ya tanadar musu agaba.
Tsit dukkaninsu sukayi kowa da ka'dadden idanuwansa yake kallon dawood din dake tsakanin
Rai ko mutuwa sbd baimasan waye akansaba.

Sunjima ahaka kafin nurses biyu suka shigo tareda Dr shuan Lee Chinese ne cikin girmawa
yace suyi excusing nasu.

Jiki a mace suka fito sufyaan da jass mota suka koma sbd ganin yanda jass ke buqatar air
dinda zaiyi kuka son ransa Shima sufyaan kukan yakeson yi Amma nauyin dayake ji zuciyarsa
yaqi Bari yayi kukan..

Cikin sheshekar kuka jass yace,

Yaan bansan yazan kwantanta rayuwa Babu ku ba acikinta,

Banda kowa saiku,kaima bakada kowa saimu,
Munajin dadin rayuwarmu and then everythings change,,,mun rasa maska Wanda rashinsa ya
jijjiga duniyarmu da haryau Bata dawo daidaiba and now dawood...

Rintse ido sufyaan yayi da sauri tareda rungume jass 'din sbd kukan daya saki har cikin ransa
yakejinsa sbd qaunace ta junansu da Allah yasaka musu ajininsu su hudu 
*_DAWOOD,SUFYAAN, JASSPER,HAYDAR MASKA..._*

Jass yakasance Mai raunin cikinsu shiyasa koyaushe sukafi tausayinsa..

Kuka yake sosai Wanda duk dauriyar sufyaan saidayayi kukan Shima suka rungume juna suna
kuka zuciyoyinsu ka karye.

Tana fitowa room din ahankali ta nufi gurin receiption ta lalubi kujera ta zauna...

'dago idanuwa tayi ahankali ta 'dora kan babban farin glass dake 'daukeda sunan asibitin tana
qanqame jikinta dakeson Fara karkarwa aduk lokacinda taga wani Abu daya danganci.....

Dafata taji anyi ta sake cusa canta cikin qafafunta sbd yanda taji hannun daya dafata Yana rawa
yasa tasan kowaye...

Zama kusada ita mum 'din tayi tareda qura Mata idanuwa...

Kyakkyawar fuskarta dake 'dauke da kyawawan fararen idanuwanta ta tuno data kalleta yanzu
taga yanda komai nata ya zabge,

ALEEYA kyakkyawar budurwar datai tashen hutu, dukiya dakuma kyau uwa uba aji da burgewa
da barkwanci Amma qaddara da azabar SO sun juya rayuwarta harma sa kamanninta takoma
kamar wata goggo yakumbo wadda ayanxu take iya wata batareda tayi magana biyu zuwa
ukuba.
Hawayen tausayin aleeyar ne yanxu suka gangaro mata,
Idan 'danta nacikin wannan azavar ciwon tabbas aleeya nacikin makamancinsa Yana cinta cikin
Rai da ruhinta Wanda ciwon ciki tabbas yafi na bayyane duk da tasan dawood Kam sai wani
ikon Rabb,
To idan duk suna cikin wannan halin tasan akwai wadda tafisu Jin ra'dadi da azaba fiyeda komai
*_KINA INA NUR..._* shine kalmar data furta ahankali sabbin hawaye da 6alle Mata.

Jin furucin na mum yasa aleeya 'dagowa ahankali tasake qurawa sunan asibitin ido akaro na
farko bayan wasu shekaru da hawaye suka sauko idanuwanta..

Jitayi nantake hawaye sun 6alle Mata ba qaqqautawa
Lumshe idanuwanta tayi batareda tadamu da gogesu dan tanada tabbacin Babu wani sauqi ko

nauyi da kukan zai rage Mata na dangane da abinda takeji sbd wannan wani nauyine da Allah
ya 'dora Mata a zuciyarta Wanda sai ranar da numfashinta yabar jikinta zata samu sauqinsa.

A wahalce mum ta bude Baki tace,

Ina fatan samun sauqi da maslaha ga dukkanin damuwarmu,
Allah yabawa kowa ikon cinye jarabarsa domin kuwa dukkaninmu jarabarmu 'dayace idan Allah
ya 'dauke ran dawood,,,,,ta qarasa fa'da tana goge idanuwanta dasukai luhu luhu ko ganinsu
ba'ayi sosai sbd sun shige fuskar ta kumbura.

Batareda tayi maganaba tasake 'dagowa akaro na uku ta qurawa sunan specialist 'din ido....
*_NUR D.S SPECIALIST._*

Bazata manta yanda komai yasamo asaliba Wanda saidai takira hakan da mafari.....
##mamugee💋


#Vote
#comment
#share
#and follow...
[12/31, 10:49 AM] +234 706 677 7871: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_

_for you surayyahms_



*2*
Sake lumshe idanuwanta tayi wasu hawayen suka sake gangaro Mata Masu zafi Wanda zafinsu
tundaga tsakiyar zuciyarta ya fito....... 


Layestrt adamawa 22 April

Buzaye ne irin wainda ake cewa sadaka yallah sbd talauci da baqar dau'dar data Kama jikinsu
harta dafe su gashinsu da 'dan sauran hasken daya rage musu kawai zaka gani kasan buzaye
ne..

Zaune suke cikin wani kangon company dayayi shekaru ba'a qarasashi ba tsufa da alamu da
zubewa duk sun bayyana a ginin duk da ginine da'akayi na cement zalla Mai qarko da kyau.
Sam girmansa baya Basu tsoro dan kusan Hawa biyarne na ginin sudai rayuwarsu suke aciki
sbd basuda wani gurin zama idan ba Nan 'dinba Wanda basusan yazasuyi da rayuwarsuba idan

Mai companin ya nemi su tashiba.,

Ahankali dattijon dake kwance tsawon shekaru biyu ba lafiya ya bude idanuwansa daqyar ya
'dorasu akanta,,,

Zaune take kusadashi ta kwantarda kanta kan gwiwowinta ta qurawa qasa ido Wanda yasan
idan zasukai wata safiyar ahaka bazatai maganarda ta wuce biyu zuwa uku ba...baabaa
sannu,,,ya jikin,,,,kana buqatar wani Abu???? Wainnan sune kadai kalaman dayasan zata iya
furtawa kokuma yace kullum sune iya maganarta saikuwa idan tana yiwa qaninta qwaya 'daya
tal aduniya magana ko wasa Wanda shi baima ta6a ganin wasa irin nataba da Babu wata dariya
ko motsa jiki saidai murmushi kawai....

Tsawon rayuwarsa Bai ta6a ganin rayuwa irinta 'yarsaba Dan kuwa ko acikin miskilan nata ya
wuce tunaninsa Wanda tun yanada lafiya yayita nema Mata magani atunaninsa Batada
cikakkiyar lapia ne sbd Sam arayuwarta Batada wani kuzari ko hayaniya,
Bata dariya sai murmushi Dan tunda ta diro duniya haryau data girma Bai ta6a ganin
dariyartaba kowama Bai ta6a ganiba sai dai murmushi Wanda Shima dacene duk da bazaka
kalli fuskarta kace a 'daure takeba.,,
Bazaka ta6a cewa ta tsaya ta kalleka so biyuba kallo 'daya takewa Abu ta sauke 'dauke Kai
wannan 'dabiarta ne Wanda cikin jininta yake,
Ta fannin magana kuwa duk Wanda zai zauna da ita sai hakuri sbd Sam Bata magana saita
Kama Dole Wanda ko dolen a gajarce zata baka amsa Wanda sanyin muryarma kawai ya Isa
yasa kaji ranka ya 6aci Dan zakai tunanin bataso amsama bane..

Talakawane sosai ko Kuma ace mabarata duk da tsawon shekaru biyu kenan rabonsu da bara
tunda ya kwanta ciwo rigis Wanda Sam basusan ciwon meneba sbd basuda kudin zuwa asibiti
abinci madai sai idan qaninta BILAL yabi sauran buzayen dasuke zaune tare bara yake samo
musu abinda zasuci wata Rana kuwa saisu yini su kwana Basu ciba sbd Sam ita tsoron mutane
take Sam Bata iya fita ko ina tun kafin mahaifiyarsu ta rasu a gidan gurin haihuwar bilal Wanda
itada baaban suka rainesa tun tanada shekaru takwas lokaacin harya girma yanxu yanada
shekaru bakwai Amma yafita kuzarin Nemo musu abinda zasuci sbd kasancewarsa
kyakkyawan yaro Mai shiga Rai Nanda Nan yasamo sadaka yakawo yakoma.

Sam shikansa wani lokacin yakan tambayeta ko Batada lpia sbd ganin kalar rayuwarta harya
Saba yagane haka Allah yayita ita.

Farace qal asalin buzuwar gske wadda ta ha'da da asalin kyakkyawar baqar fatar bahaushiyar
mahaifiyarta sbd baabansu ne kawai buzu mahaifiyarsu bahausar Wanda kyawunta ya ha'dune
na asalin buxu da mahaushe saidai tafi 'debo komai na buzayen.,,

Sam basuda wata suturar arziki Dan har gwara ita ta ha'da hardana mahaifiyarsu tana sawa,,,,

Kyawunta dayasa ake yawan kallonta yasa kullum jikinta a lullu6e yake har fuskarta da wata

tsohuwar lafayar mahaifiyarsu data Bari baqa Wanda Bata saniba kalar baqin ke qara fiddo da
asalin kyawunta duk da Rashi da yunwa sun 6oye fiyeda Rabin kyan.

Wata kyakkyawar sarqace ta asalin 'danyen baqin azurfa aqafarta wadda tun asali itace sadakin
mahaifiyarsu harta rasu tana qafarta bayan rasuwar ta ga'deta,
duk inda ta taka sai sautin sarqar ya fita Wanda hakan ke matuqar 'daukar hankalin wasu
mazan idan sunji
Sai wata sarqar a hannunta wainda Bata ta6a ciresu hakama Bata ta6a saka ranar ciresuba
saidai idan ta mutu itama acire Mata
A duk lokacinda tayi tafiya babansu yaji sautin kukan sarqar mahaifiyarsu yake tunawa sbd
komai Bata baroba na uwar tasu saima ninkawa datayi dankuwa uwarta harta rasu Bata ta6a
zaunawa tayi Masa kallon ko minti ukuba kullum daga to sai aa idan yayi magana.

Ajiyar zuciya yasake ahankali cikeda tausayin 'yayan nasa Dan yasan idan ya rasu basuda
madafa wannan kullum shiyake 'daga Masa hankali sbd itama haryanzu yarinyace shekara
goma Sha biyar bazata iya fuskantar rayuwaba duk da baisan me rayuwa ta tanadar Mata
agaba ba..
Cikin tsananin sanyin murya yace,

*_NUR..._*

ahankali ta 'dago kanta ta kallesa da manyan fararen idanuwanta kafin ta 'dauke Kai ahankali
tace,

Baabaa kanason wani Abu ne?

Girgixa Kai yayi hawaye na taruwa cikin idanuwansa tana gani tasake lumshe ido tanajin wani
ra'dadi cikin ranta Amma batasan yazatayi ta nunaba ahankali batareda ta kallesaba tace,

Yi hakuri baabaa..

Rintse ido yayi hawayen ciki suka zubo
Wani irin 'daci da ra'dadin ciwo yakeji cikin ransa Amma Babu amfanin bayyanawa sbd babu
abinda bayyanawar zai amfana.

Shiru sukayi idanuwanta sukai jajir ta miqe ahanakali ta fito daga kangon office dinda suke
kirada 'daki.

Ahankali takoma defen qofar 'dakin ta zauna tana gani abokan zamansu suka dawo bara kusan
su hu'du kowacce da 'yayanta harma da mazajensu Amma mazan basanan 'dayar Kuma mijinta
ya rasu.

Tana ganinsu ta sunkuyar dakai ahankali tace,

Sannu da dawowa.

Ko kallonta basuyiba suka wuce suna bede abubuwan dasuka samo..

Lumshe idanuwanta tayi tanajin tausayin kanta na yanda Allah yayita Mara amfani kaman
yanda take fada kafin cikin sanyi tace,

Astagfirulla..




Babban gidane dayaji komai najin dadin rayuwa musamman Masu gadi da securities da'aka
zuba agidan,

Kwance take cikin lafiyayyan gadonta na cikin bedroom 'dinta dakomai na cikinsa yake blue sbd
shine kalar datafi so.,

Arazane ta tashi sbd mafarkin datayi Wanda inda sabo Yakamata ace tasaba sbd kusan kullum
saitayisa tunda tafara sanin kanta.

Dafe goshinta tayi kafin ta miqa hannu ta jawo hular kanta data cire tana goge zufa da'ita....

Meyasa kullum saitayi mafarkin suna kuka na fitar hankali harsuna Aman jini itada wata wadda
Bata ta6a ganin fuskartaba saidai yanda suke kukan atare yasa kullum takejin so 'da tausayin
koma wacece Yana shigarta....

ALEEYA....

Taji ankirata..
Da sauri ta juya ta kalli qofar ganin ammynta yasa tasaki ajiyar zuciya ahankali tareda saukowa
gadon ta nufi ammyn ahankali ta shige jikinta ta rungumeta batareda tace kamaiba.

Shiru ammyn tayi sbd tafara sabawa da wannan sabuwar 'dabiar ta aleeya duk da hakanan
takasa fa'da Mata mafarkinta na kullum datakeyi.

Cirota tayi daga jikinta tana kallonta tace,

Aleeya kina wasa da addua yanxu ko?

Girgixa Kai tayi cikin 'son yin Kuka tace,

Ammy wlh kullum inayi.

To naji duk da haka za'aiwa malam halilu magana ya qara dawowa baya a hisnulmuslim dinki..

Dariya tayi kafin tace,

Kai ammy baya Kuma inama laifin tsakiya.

Bayandai za'a dawo yanxu bama Shiba daddynki zai fice dubo tsohon building 'dinsa daya
kawosa garinnan inaso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login