Showing 6001 words to 9000 words out of 76958 words
Chapter 3 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf
'daure yace,
You need something???
Murmushi tasaki harsaida dimple 'dinta suka lotsa ahankali ta qaraso gurinsa ta 'duqa ahankali
tayi kissing lips 'dinsa tace,
No I was just looking at the man who stole away my heart,,
Lumshe ido yayi sbd qamshinta daya ha'du Dana shower creams 'dinsa ya cika toilet 'din Yana
kallon tsakiyar idanuwanta yace,
And who was that man?
Wani shu'umin murmushin tasaki tareda zura hannunta cikin ruwan dayake cikin ta shafosa tana
cewa,
Are you sure you want to know him?
Jawota yayi cikin ruwa Yana cewa,
0 percent sure.
Dariya ta qyalqyale dashi tana sbd cakulkulin daya Fara yimata Nan suka Fara wasa cikin
ruwan suna ta6e ta6ensu tuni ya manta da wata gajiya suka cigaba da sha'aninsu harsuka
gama sukayo wankan tare suka fito.
Shine namiji Amma fatarsa ma tafi Tata glowing duk kuwa da itama qarshe gurin kashewa
jikinta kudi da bawa kanta hutu.
Cikin qananan Kaya marasa nauyi suka fito
Shi black trouser da white transparent shirt sai designer slippers 'din channel dake qafafunsa
farare qal kamar Bai ta6a taka qasaba.
Ita kuwa wata loose half gown tasaka Dan dama Bata rasa Kaya room 'dinsa..
Tana Maqale a gefensa suka fito suna tana dariyar yanda idanuwansa sukai laushi sbd yunwa
dayakeji.
Sufyaan ne kawai a palon gurin dining area yanata faman ha'da tea.
Kallonsu yayi tareda barin abinda yakeyi cikin farin ciki yace,
Thank God you are hia guys yunwa is killing someone hia.
Kallon dawood tayi tana cewa,
Yeah baby Let's go somewhere and have dinner that silly idiot yau batayi aiki ba wai she's not
feeling well..
Maska ne yafito room dinsa ya qaraso Yana cewa,
Muje nima yunwar nakeji.
'daki sufyaan yakoma ya 'doro black shirt kan farar singlet dinsa yafito.
A Lamborghini car din maska suka fita dukkaninsu
Wani babban restaurant sukaje kowa yabada order abinda zaici suna gamawa suka dawo gida
bayan maska yayi order sabbin tsadaddun kwalaben wine 'dinsa sbd shikadai ne cikinsu baya
neman Mata saidai shi alcoholic ne kowa yayi hanyar room 'dinsa itama dai kamar lokuta da
dama ranar agurinsa ta kwana batareda takoma apartment dinta dake gefen nasu ba.
*******
Tunda tazauna qofar 'dakin tasake kwantarda kanta kan gwiwowinta tayi shiru tana kallon sama
yanda gagarumin hadari ya ha'du iska na kadawa.
Kamar daga sama Salim yaron dasuke bara tareda Bilal ya rugo yazo gabanta Yana haki cikin
tashin hankali yace,
NUR Bilal mota ta takesa Kuma......
Bai qarasaba ta miqe tsaye tareda Kama hannunsa ta matsar dashi daga qofar 'dakin sbd kar
baabaa yaji cikin sanyin murya tace,
Mekake cewa?
Duk da Yana yaro kuma yake cikin tsananin tashin hankali Saida yayi mamakin ganin yanayinta
sam Babu razana ko firgici saidai idanuwanta dasuka ka'da lokaci 'daya bawai Dan Bata shiga
firgici ko tashin hankalinba ita haka Allah yayita baya bayyana saidai zuciyarta tayita 'dawainiya
da dakon wahalar tashin hankalin da firgicin.
Da saurinta fice gidan hartana hadawa da gudu ta qarasa gurinda ta tararda anyi cincirindo
ansa Bilal din agaba anata masa fita sbd Wanda ya ka'desa ya gudu.
Rungumosa tayi jikinta da sauri hawayen idanuwanta suka sauko ta 'dago kanta ta kalli
mutanen gurin murya na rawa tace,
Dan Allah ku taimakeni ku kaimu asibiti.....
Watsewa taga mutanen sunfarayi sbd maganar taimako data ambata
Jikinta ne ya'dau rawa tasake rungume Bilal 'din hawaye naci gaba da tsinke Mata.
Maigadin companin dasuke ne yaqaraso da sauri Yana salati akidime yace,
NUR maza kamosa mukaisa chemist tunda ba qarfin zuwa asibiti.
To,,,tace tana miqewa jiki na rawa ta kamasa ganin takasa iya 'daukarsa yasa ya kar6esa sukai
hanyar chemist 'din dake gefen titin da sauri daidai lokacin ruwa Masu qarfin gaske da iska Mai
qarfi suka taso Nan jamaa suka Fara gudu kowa na neman mafaka Musamman ganin yanayin
qarfin iskan.
Gabanta ne yayi mummunan fa'duwa tunawa tayida duk ana iska da ruwa irin haka fitowa suke
daga ginin harsai angama ruwan sbd gujewa faduwar ginin Dan tuni dama want gefe yafara
rugujewa.
Kallon Bilal da'akewa allurori ana dressing inda yaji ciwuwuka tayi tareda miqewa jikinta na
rawa tayi hanyar fita
Damqo hannunta dahiru Mai gadi yayi cikin fada yace,
Bakida hankaline Zaki fita cikin wannan ruwa da iskan Masu qarfi ya kukaji da neman na
abincima bare na ciwon mahaifinki gana bilalu yanzu sannan kina qoqarin samawa kanki wani...
Qwacewa tayi hawayen idanuwanta na qara gudu tace,
Baabaa nacan nasan cikin gidan Nan Babu Mai fiddasa zuwa zanyi na fito dashi.
Ke dalla yiwa mutane shiru idanma kin fiddosa wani gurin gareki na kaisa yanzu cikin wainnan
ruwan Kuma.......
Zuwan Raheenatu hankali tashe tana ihun kukan daya mugun ka'da kayan cikinta tayi gurinta
jikinta na wani irin mazari ko magana takasa yi sbd tashin hankali da hannu ta tambayi
Raheenatun jikinta na tsananta rawa.
Cikin tsananin kuka tana nuna hanyar waje tace,
Gini ya Fado Kuma....Kuma....
Wani wawan turi tayi Mata cikin tsananin tashin hankali ta fice da mugun gudu
Hankali tashe dahiru da sauran jamaar chemist din sukabi bayanta dahiru nakiran sunanta..
Sam ko gani sosai batayi sbd tsananin qarfin ruwan Amma Sam ko ruwan bataji duk inda
tasamu jefa qafarta takeyi..
#Mamuhgee
#vote
#comment
#follow
#and share
[12/31, 10:50 AM] +234 706 677 7871: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*5*
Tana Isa Bata tsaya tunanin komaiba tafara qoqarin kutsawa ciki mutanen dake gurin suka
rirriqeta suna cewa Batada hankaline tana ganin gini na zubewa zatashiga...
Qwacewa tayi cikin tsananin kuka tana Kiran baabanta jikinta ba inda baya rawa..
Cikin zafin nama dahiru ya damqota tareda riqeta da qarfi
Ihu take da kuka sosai tanason qwacewa Amma ba qaramin riqo yayi mataba Dan kuwa
ayanda take ba cikin hayyacinta ba idan aka saketa zata iya shiga ginin Wanda tuni ya qarasa
rugujewa....
Ihu tasaki Mai qarfi ganin yanda gaba daya ya qarasa rugujewa kamar ba'ataba dogon giniba
agurin.,,
Arikice dahiru ya girgixata Yana Kiran sunanta cikin tsoro da tashin hankali sbd ganin kamar
Bata numfashin..
Layla... Layla..ke tashi karki mutu ahannuna..innalillahi
Arikice Raheenatu tafara jijjigata tana Kiran sunanta cikin tsananin kuka Amma Sam ba alamar
tanada sauran numfashi...
Cicci6arta sukayi suka koma gefe sbd ruwan saman ya 'dauke mutane sun qara taruwa agurin
ana kallon yanda ginin ya zube...
Kallon Raheenatu yayi cikin tsoro yace,
Ke kamata muje chemist idan Bata tashiba to tafiyata zanyi wlh ba ruwana.
Cikin tsananin kuka ta Mike suka kamata suna Isa chemist din hamisu Mai chemist na ganinta
yace,
Aa wannan tafi qarfin chemist asibitin zakuje Dan da alama kamar bugawar zuciya ne kamarma
ta Dade da mutuwa..
Ehhh,,, dahiru yafada cikin tsananin tashin hankali da tsoro Yana zaro jajayen idanuwansa
Nan Take jikinsa yadau rawa ya kalli Raheenatu Yana cewa,
Nayi iya yina saiki 'dora Kuma wlh ka sunana yafito ciki.
Ficewa yayi jiki na rawa Yana sharce gumi duk da sanyin ruwan da aka gama.
Kallon Nur din tayi cikin sabon kuka tace,
Kiyi hakuri Layla nima bansan ya zanyi Miki ba Dan banida wata taimako Kuma.
Miqewa tayi ta fice batareda tabari hamisu Mai chemist ya luraba.
Wani mugun ashar ya sako lokacinda yagama sallamar wani yaga sun gudu sun bar Masa
gawa
Ai nantake 'yan hanjinsa suka ka'da Bai tsaya wata wata ba jiki na rawa ya zagayo yasa qarfi ya
cicci6eta ya lalla6a yakaita gefen gininsu daya zube sbd duhun magrib yariga yagabato yadawo
ya cicci6i Bilal yakai gefenta ya aje yadawowarsa ya rufe chemist dinsa yayi gida.
Babu Wanda yakuma kawosu arai sai tsakar dare guraren qarfe uku suka farfado kusan atare
sbd sanyin asuba daya sawo Kai dakuma sanyin ruwan da'akayi.
Daqyar ta iya lalabawa ta tashi zaune ta bude idanuwanta da sauri ta rufe sbd ganin a inda
suke yashe kan hanya kusada bola.
Da hannu ta lalabo Bilal dake kukan azabar ciwo ahankali ta rungumesa tareda sakin qaramin
kuka ahankali tana kiran sunan mahaifinsu,
Sun zama marayu basuda uwa basuda uba basuda kowa dazasu gani ko sukira nasu
Tun adaren da mahaifinsu ya rasu sun Fara shiga garari tunda gasu da kwana gefen bola.
Jin kukan azabar da Bilal keyi yasata bude ido ta sake qanqamesa tana basa haquri Dan kuwa
raunika ne sosai a jikinsa duk saiya qara 'daga Mata hankali ta birkice.,
Daqyar taga lokacin sallar asuba yayi anyi gari ya 'dan Fara haske takamasa daqyar suka 'dan
matsa daga kusada bolar ta samo wani jikakken kwali ta shimfida Masa ta kwantar dashi.
Rawar sanyi yakeyi sosai ta rasa ya zatayi cikin hawaye ta kalli lifayarta data gama tsufa da
faffashewa tasa hannu ya farketa biyu ta lullu6esa sauran ta 'dan budeta ta rufe jikinta Wanda
Bata rufe dukaba saima taqara fitowa datayi a sadaka yallah dinta.
Koda gari yayi haske sosai jama'a kowa nata harkokin gabansa Babu Wanda ko kallo suka
ishesa gashi har lokacin Bilal sosai yake cikin azabar ciwukan jikinsa ga zazzafan zazza6in
dake cinta.
Daqyar ta miqe ta kamasa suka qara matsawa daidai bakin ginin ta kwantar dashi duk da
daqyar take iya daukarsa.
Zama tayi kusadashi tareda cusa Kai cikin qafafunta tanason tayi kukan Amma yaqi zuwa ga
mutane suna 'dan taruwa sake kallon ginin dakyau cikin haske.
Ahankali taga su Raheenatu da iyayensu suna zuwa suna zaunawa kusadasu kan kace me
gurin ya 'dan cika da mutane mabarata da musakai.
Raheenatu ce cikin Jin nauyi da tausayinta ta matso murya a sanyaye tace,
Ya jikin Bilal?
Kallonta kawai tayi da jajayen idanuwanta sbd ko magana batajin zata iya.
Allah yajiqan baabaa,,,tasake cewa tana kallon ginin.
Sake rintse ido laylar tayi Jin abinda Raheenatun tafafa ko Amin din takasa cewa.
Kaf gurin Raheenatu ce kawai ta iya yimusu mgn ta miqe takoma gurin Yan uwanta.
Shiru tayi jikinta na 'dan rawar zazza6in dake tsananin cinta.
Ido dahiru yayita warewa harya hangota raku6e gefe kunya yadanji ya Sosa Kai tareda fuskewa
ya nufi gurin tareda 'dan yaqe Baki yace,
Layla ya jikinki Dana bilalun?
Sake cusa kanta tayi tsakiyar qafafunta batareda tace komaiba.
Kingane ki kwantarda hankalinki insha Allah zaku samu mafita wannan taruwar dakikaga
wainnan munafukan sunyi na zuwan Alhaji Mai companin ne sbd zaizo yayi ta'aziyar abinda
yafaru yakuma taimakawa wainda suke zaune suje su nemi wani gurin Kinga ke zakufi kowa
kaso Mai tsoka tunda ke mahaifinku ya rasa ransa qila abin Nan zai biya...um um mema ake
cewa sunan abun idan za'a biya....ummm yauwa diyya..Kinga daganan saina taimaka muku
nasamo muku gurin zama da.....
Manyan jeeb jeeb dinda suka doso gurin yasashi miqewa da sauri Yana gyara fuskarsa zuwa
kalar tausayi ya nufesu jiki na rawa haryana tuntube
Sauran mutanen dake cikin gurin kuwa tuni suka Fara fuskar kalar tausayi wasu harda kuka
wasu kuwa kwantawa sukayi ana musu fifita da sannu.
Motocin na tsayawa tuni Yan press yo caaa suka rufesa da tambaya daidai lokacinda drivernsa
yabude Masa ya fito motar.
Tambayoyi sukai tayi Masa Yana amsasu cikin nuna jimami da tausayawarsa ga alamarin.
Ahankali take kallon mutanen cikin tausayawa ta cikin glass din motar batareda tafitoba,
Rintse idanuwanta tayi sbd yanda gabanta ke tsanan faduwa duk lokacinda idanuwanta suka
sauka kan 'daya daga cikin mutanen...
Qura Mata ido tayi zuciyarta na ingizata ga zuwa gurinta..
Saurin 'dauke Kai tayi numfashinta na fita da sauri.
Tunda yazo dukkaninsu suka Fara rawar jiki har lokacin Bata 'dogo kantaba saima qarfi da
zazza6inta yaqara.
Ahankali yafara binsu 'daya bayan 'daya Yana Basu kudi Masu yawan gaske suna wucewa
haryazo kanta.
Kallonsu yayi cikeda tausayawa itada qanin nata ganin qarancin shekarunsu sosai.
Cikin jimami dahiru dake gefe ya matso daga gefen securities din Alhajin yace,
Alhaji wainnan sune marayun 'yayan Wanda yarasa ransa.
Sanyi jikinsa yayi yasake kallonsu kafin yakalli PA dinsa yace,
Aminu ayi gaggawar Ciro gawarsa.
Ok sir,,,yace tareda Ciro wayarsa Yana danna Kira tareda komawa gefe.
Kallonsu yasakeyi cikin taushin murya yace,
Layla kamar yanda dahiru yafada sunanta.
Kasa 'dagowa tayi saima sake cusa kanta datayi cikin qafafunta tana kuka ahankali Jin gawar
baabaansu daza'a Ciro sbd tana kwatanta irin azabar dayasha kafin ransa yafita lokacinda ginin
yafado Masa.
Cikin qanqanin lokaci motocin aiki sukazo aka Ciro gawar saidai duk Wanda ke gurin Saida
imani da sanyin jiki suka kamasa sbd ganin yanayin gawar abin babu kyawun gani saidai
adduar Allah yaji qansa.
Kukanta yaqara tsananta sanyin jikinsu musamman qananun shekarunta daga ita har qaninta.
Basubar gurinba harsaida akayi jana'izarsa Nan Alhajin yaciro dubu 'dari yabawa dahiru yace
yakula dasu sbd cewa dayayi zai kaisu gurin innarsa ta riqe.
Suna barin gurin ya miqo Mata kudin cikin farin ciki da zumudi yace,
Ungo riqemin zuwa anjima idan zani gida zan kar6a sbd karna fita dasu yanxu a yankemin
aljihu.
Kar6a tayi batareda ta 'dagoba ta tura qarqashin kwalinda Bilal ke kwance Allah ya taimakesu
ba Rana.
Agurin suka yini sai magriba Bilal ya farfado ta zaunar dashi jikinta na rawa
Kallo 'daya tayi Masa taji jikinta yaqarayin sanyi sbd ciwo da yunwa data hango qarara nacinsa.
Ita kanta ciwo da yunwar na cinta Amma Batada yanda zatayi.
Kuka yasake daqyar yabude Baki yace,
Yunwa nakeji Kuma inajin ciwo Layla kisamomin magani da abinci kona cikin bolane Ni zanci.
Kukansa yayi tsanani daga Mata hankali rashin sanin abinyi yasa itama tasa kuka tana
rarrashinsa amma kamar tana qara Masa ciwone Dan har wani irin rawa jikinsa keyi.
Tunawa tayi da kudin da'aka basu ta 'daga kwalin taciro kudin ta zari 'daya ta mayar tareda
miqewa tace,
Zan dawo yanxu kaji.
Da sauri ta juya ta nufi Mai abincin kusada chemist din hamisu tasiyo Masa shinkafa da ruwa ta
kar6o Masa magani gurin hamisu ta dawo da gudu.
Cak ta tsaya cikin tsananin tashin hankali jikinta na daukar rawa ganin Bilal cikin jini kwance
kamar matacce.
Watsi tayi da abincin tayo kansa da gudu tana jijjigasa tareda kiran sunansa..
Bilal meya sameka?..meye yayi maka haka wannan jinin.....
Daqyar Yana kuka yace,
Kudin dakika aje sukamin duka suka 'dauke duka sun gudu.
Wani irin kuka da ajiyar zuciyane sukazo mata lokaci 'daya kafin tayi magana dahiru yaqaraso
da saurinsa yace,
Yauwa Layla bani kudinnan Kuma kutashi muje..
Sunkuyar dakai tayi cikin kuka tace,
An dauke duka.
Harara ya watsa Mata tareda gyara tsayuwa yace,
Kinga banason baqin ciki nida zan taimaka muku banmuku baqin cikiba sai 'dan kudinda zan
qaru dasu shine zakumin baqin ciki Amma wlh bakida imani Layla...
'daga kwalin yayi ya zazzage baiga komaiba.
'dagowa tayi ahankali takallesa tace,
Wlh ansace sunema aukaiwa Bilal haka....
Ke dalla yimin shiru muguwa kawai Amma wlh kin cuceni Dan har bashi naci yanzu Koda
uwarwa kukeson nabiya,
To wlh kanku kukayiwa Dan saiku nemi gurin zuwa wlh ba inda zan kaiku tunda bakida Jin qai
da tausayi.
Juyawa yayi afusace kamar zai rusa kuka ya wuce Yana masifa.
#mamuhgee
VOTE
COMMENT.
[12/31, 10:50 AM] +234 706 677 7871: _*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_
*6*
Bayansa tabi da kallo harya 6acewa ganinsu ta Sunkuyar dakai hawayenta na qaruwa takalli
Bilal cikin hawaye tasake miqewa tareda komawa tasake siyo Masa abinci da sauran canjin
hannunta da ruwa tadawo ta 'dauki maganin dazu data siyo.
Tuni jikinsa ya rikice da zazza6i takamasa daqyar sbd itama qarfinta yayi qasa sosai ta tayar
dashi zaune ta basa abincin kadan yaci yasha magani ta 'daure sauran a Leda ta aje gefe
tasake lullu6esa tana Masa sannu ahankali.
Dare nafarayi zazza6insa yayi tsanani ga mage mage dasuka dinga Bata tsoro Dan wani irin
kuka sukeyi Mara dadi ta kalli bolar Nan tsoro yaqara rufeta ta miqe jiki na rawa ta tattarosa
daqyar ta Goya nauyinsa na rinjayarta haka tabar gurin tana tunananin gurin fakewa kafin
safiya.
Saidatayi nisa sosai da anguwar kafin taga wani qonannen shago bakin titi daga gani gobara
yayi ta qarasa ahankali ta saukesa tareda zubewa gefe tana fidda numfashi daqyar sbd yunwa
gajiya da zazza6in dake cinta.
A wahalce bacci ya daukesu su duka Bata farkaba sai da gari yayi haske tana bude ido taga
Bilal zaune Yana kallon waje.
Tashi tayi ahankali ta dawo kusadashi murya Bata fita sosai tace,
Kaji sauqi Bilal?
Eh yace Yana qoqarin bawa kansa qarfin jiki Dan haka bazatai musu ba Dole zasu Fara bara
danshi Sam bayada jimirin yunwa ko kadan.
Layla muje bara Kinga Ni yunwa nakeji wlh Kuma Kinga baabaa tuntini Yana cewa mu iya nema
da kanmu kintuna.
Kallonsa tayi da idanuwanta dasukai jajir sukai mugun nauyi sbd kuka taga yanda duk ya
kumbura fuskarsa da sauran jikinsa sbd kadewar da mota tai Masa dakuma dukan da akai
Masa ga raunikansa sunanan saima quda dake qoqarin hawa ta girgixa Kai zuciyarta na qara
karyewa tace,
Bazaka iya fita baraba kabari ga saurin naira 'dari biyu a hannuna zamuci wani abu da ita.
Miqewa tayi ta fita tana dudduba inda zata samo abinda zasuci.
Duk Wanda tabi ta gefensa saitaga ana kaucewa sbd kallo mahaukaciya da ake Mata.
Qosai taga wata Mata nayi gefen wani shago ta qarasa tun kafin tafadi qosai tazo siya matar ta
taso Mata cikin masifa tace,
Matsa daga can