Showing 21001 words to 24000 words out of 76958 words

Chapter 8 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

5617

Layla tasamu miji farin ciki
sosai yayi saidai baitambayi komai akansaba yace abari saiya dawo Dan next week zasu dawo.

Da daddare daqyar tasamu yabarta ta waya sbd Dan yanda ya narke mata sosai ita har
mamakinsa take sbd da gani mum dinsa ta 6atasa da gata kamar yaro ga yanda ya iya narke
Mata akan saitayi masa firar soyayya yaji Dadi shi bai iyaba shi tasa kalar soyayyar ta Ido ce
Dan kuwa idan ya zuba Matasu wani lokacin ko motsi Bata iyayi Kuma ba ruwansa da duk
Wanda ke guri zuba Matasu yake ga idanuwan badai kashe jiki da rikita mutum ba.

Daqyar tasamu ya haqura ta kashe wayar tareda danna Kiran aleeya.

Cikin sa'a tashiga.

Tana dauka kusan atare suka saki ajiyar zuciya kowanne bakinsa da magana.

Cikin farin ciki aleeya tace,

Oh my...my layla I missed you so much na matsu nadawo I have alot to tell wlh.

Murmushi Mai sauti tayi tana cewa,

Dagajin muryarki kina cikin farin ciki is there anything I shud know.

Dariyar Jin Dadi tayi tareda gyara kwanciyarta a gadon bedroom 'din mum data dawo da kwana
Nan sbd kawai hotonsa dake 'dakin ta shafi hoton tana lumshe Ido tace,

Inasonsa Layla,,,,
Ina tsananin sonsa infact ban ta6a son wani da tsanani hakaba kamarsa....

Lumshe idanu Layla tayi sbd fuskar dawood 'dinta data Fado Mata a Ido.

Cikeda Taya 'yar uwarta murna tace,

And waye wannan dayakeson birkita zuciyar aleeyana.

Mi'amor..... layla zuciyata takamu da tsananin sonsa dahar nakejin kamar bazan iya rayuwaba
idan na rasashi,
Wani lokacin Kuma jikina na sanyi idan nayi tunanin qila bazai Soni ba Wanda wlh Layla bazan
iya cirewa zuciyata sonshiba....ta qarasa zancen muryarta na karyewa.


Sanyi itama laylar jikinta yayi cikin sanyi tace,

Bazaki ta6a rashiba insha Allah Zaki samesa sbd kome yakeji dashi nasan kema kin Kai duk
inda cikakkiyar mace Mai aji da gata takai.

No Layla Baki sanshiba,,I'm nothing compares to gata,kudi,ilimi,class,kyau da wayewar dayake
dasu kawai kimin addua Allah yabani shi ina sonsa Layla.

Ganin halinda aleeyar tashiga yasa tafasa fa'da Mata maganar dawood datai niya saitayita
rarrashinta da Bata qwarin gwiwa.

Tunowa datayi laylar nada abun fada Mata yasa ta saki muryarta ta nuna ba damuwa tace,

Ehemm inajin naki bayanin sbd daga yanayin murmushinki 'dazu I sense sumthing fishy.

Qoqarin buge zancen tayi da cewa,

It's nothing kawai....

No no no karmu Fara haka kawai ki fadamin inason naji Are we inlove?"""ta tambaya tana
dariya.


Rintse idanu laylar tayi da sauri kamar aleeyar na tareda ita cikin sanyi tace,


He is very nice and kind.

Wat??? Malamin makaranta ne hala?

Bude Ido tayi tace,

Aa.

To ina nakejin he is nice and kind inason naji kince he is very hot and cute.

Dariya suka sake dukkansu layla tace,

Idan akan hot ne zan ce Miki he is not hot but fire gaba 'daya.

Ihun murna aleeya tasaki tana cewa,

Wayyo na matsu nadawo mu ha'du Amma kafin Nan inason gaisawa dashi gobe.

Ok ok insha Allah.

Shiru aleeya tayi cikin sanyi tace,

Layla kinasonsa sosai ko?

Lumshe idanu tayi cikin sanyin murya itama tace,

Banta6a tunanin arayuwata zanso namiji hakaba aleeya,
Da farko naso na yaqi zuciyta akan sonsa duk da bansa daliliba Amma bansamu kuzarin yin
hakanba,
Sonsa yariga yazamo wani babban 6angare ajikina.

Jin zancen nason sasu wani yanayin mutuwar jiki yasa aleeya tace,

Hmmnn harna Fara Jin kishinsa zai ragemin fili azuciyarki.

Fa'duwa gabanta yayi da qarfi Jin maganar aleeyar duk da acikin wasa tayita.

Ahankali tace,

Aleeya har abada Babu Wanda zai ta6a babban matsayin dakike dashi azuciyata,
Matsayinki a zuciyata yafi qarfin duk wani matsayi da kike tunanin kinadashi agurina,
Karki hada kanki dashi sbd shi zuciyata yakama ke kuwa jini da ruhi.

Hakan na nufin Bazaki iya rayuwa Babu zuciyaba da jini da ruhi.

Murmushi tayi kawai suka kashe wayoyinsu kowanne jiki ba qwari.


Ana saura kwana uku su aleeya su dawo yasamu Kiran gaggawa daga new Jersey Nan
hankalinsa yayi matuqar tashi Dan Kai tsaye yace ba yanxu zai dawoba ganin da gaske yake
yasa maska Kiran Layla ya fahimtar da ita Dole ana buqatar dawood din gashi yace bazaizo ba
and sunfi kowa sanin idan yace NO Babu Wanda ya Isa ya canzasa ko waye.
Damuwa da fargaba Mai qarfice tashigeta lokacinda maska yayi Mata bayani Dan dawood din
baifada mataba.

Acikin dare kasa daurewa tayi sbd fargaba kafin safe idanuwanta sun kumbura bawai Dan
kukaba sai Dan rashin barci da tunanin daya sakar Mata ciwon kai.

Yana sauke idanuwa akanta yaji hankalinsa yayi mummunan tashi coffee ma da ammy tabasa
kasa Sha yayi ya aje Yana zuba Mata ido alamar son sanin abinda ke damunta.

Zama tayi tareda kallonsa duk saitaji taqara rikicewa.

Miqewa Yayi yatsaya akanta tareda sake tsareta da Ido.

Kasa daurewa tayi ta dago ta kallesa cikin sanyi tace,

Maska yakirani.

Sai alokacin ya lumshe Ido Amma cikin 'dan 6acin Rai da takaicin maskan daya fada mata.
Maganar komawarsa.

Zama yayi tareda sakin ajiyar zuciya idanuwansa akanta cikin maqoshi yace,

Ba yanzu zan tafiba saisu mum sun dawo next month inason suzo gurinsu ammy sai abani ke
dake nakeson komawa.

Kallonsa tayi idanuwanta na qara ka'dawa tace,

Zaka iya komawa kafin next month din saika dawo maska yace your career is at stake idan
baka komaba so please kaje if not for your self me.

Girgixa Mata Kai yayi Yana tamke fuska.

Rikice Masa tayi sosai saidata ha'da da hwaye Yana ganin hawayenta jikinsa yadauki tsananin
rawa baitaba shiga tashin hankali ba arayuwarsa kamar yau dayaga hawayenta danji yayi
kamar qwaqwalwarsa zata buga..
Da gudu ya amince akan zaije dagacan zai wuce Miami gurinsu mum saisu dawo tare.

Jinya yadawo yi sbd zazza6in daya rufeta daga ranar.

Cikin qanqanin lokaci tayi wani iri musamman rama ta rashin cin isashen abinci.

Ammy har tausaya musu take itama duk saita shiga damuwa ganin yanda duk ta 'daga
Hankalinta shikuma suk ya susuce yakasa nutsuwa Dan Shima ramar yayi sosai sbd Sam hutu
ya qaurace Masa ko agurin bacci wani lokacin har qarfe goma Sha 'daya Yana gidan Yana
kwantar Mata da hankali duk da Shima kullum saisu jass sun kwanatar masa yake samun qarfin
gwiwa.


Ana gobe zai tafi ranar ko Nana saidatayi hawayen tausayin Layla sbd kwana tayi da wani irin
mugun zazza6i Amma da safe Yana Ganinta yaso rikice musu Dole ta daure tabawa kanta
qwarin gwiwa daqyar ya yarda takaisa airport bayan yabawa ammy da Nana kyautar maqudan
kudi Masu.
Suna Isa aka kira jirginsa
Riqe hannunta yayi yanason yayi magana yakasa sai kawai yakai hannun bakinsa yayi kissing
ya fito da sauri ya wuce Dan zai iya fasawa kowane lokaci.

Yana fita ta kwantarda kanta kan sitarin mota hawaye Masu zafi suka gangaro mata kafin taja
motar daqyar tabar airport din.
#mamuhgee

VOTE
COMMENT.
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*16*
*_All thanks to Allah gameda qauna da masoya ke nunamin nida rubutuna,_*
*_Gskia bansan dawood yasamu kar6uwa da wuri hakaba sai yanxu so thank you all for the
love.....mamuh loves you more._*




*_This page goes to members na zauren biebie Isa,,,Layla Nur and aleeya na godia..._*






Tana dawowa daga airport ta kwanta Nan danan zazza6i Mai qarfi ya sake kwantada ita kuka
takeso tayi kota samu sauqin abunda takeso a qirji da zuciyarta Amma yaqi zuwa saima wani
irin yaji da idanuwanta ke Mata na Jan dasukai.

Hankalin ammy tashi yayi sosai nan tafara rarrashinta tana Bata Baki sbd kobata fadaba tasan
ciwon na rafiyar dawood ne.

Ita gabaki 'daya ma alamarin tsoro yafara Bata wannan wace irin soyayya ce tun ba'aje koinaba
tafada cikin ranta cikeda tausayin laylar.

Cikin kwana biyu ta canxa sosai duk da tana qoqarin ganin ta sake sbd kullum sai sun raba
dare suna waya hardar yanxu dabasa kusa narke Mata yake kamar zaiyi kuka itama wani
lokacin da hawaye suke rabuwa ta wayar gashi tunda yaje suka daina video call sbd yace akwai
wadda bayaso taganta Koda mistake ne datace waye Bai Mata qarya ba yace Mata ex-girlfriend
dinsa sbd hakan na 'daya daga cikin qualities dinsa shi baya qarya baya 6oyo.

Ranar daya fada Mata Saida yabawasu maska tausayi sbd shiru tayi taqi magana jiki na rawa
yakashe ya danna Mata video call

Hawaye yagani fuskarta suna tsiyaya Nan yahau kawo zance kala kala cikin tashin hankalin
ganin hawayenta saidataga kamar zai sawa kansa ciwon Kai gurin qoqarin lallashin ta goge
fuska tareda sakin siririn murmushi tace,

Ok Ya isa haka you need to rest ji hancinka yanda yayi ja alamar you're having a headache..I'm
ok.

Lalla6asa tayi suka gama wayar tana ajewa ya lumshe lazy eyes dinsa zuciyarsa na tunano
Masa saraah sbd itace baya fatar Koda wasa tasan maganar Nur bare taganta sbd yasan hw
stupid and crazy she is zata iyayin komai and that he can't dare to take.




****
Duk wata shaquwa da aminci tashiga tsakanin taheer da aleeya sbd arayuwarsa baida friends
ko 'daya Bai ma ta6a yinsu ba yayansa shine abokinsa idan Yana gari sbd akwai soyayya da
shaquwa sosai atsakaninsu sai yanzu daya samu aleeya yakejinta sosai cikin ransa amatsayin
aminiya daya yarda da ita.
Mum kuwa duk da'din duniya ya isheta data gano irin soyayya Mai qarfi da aleeya kewa mi'amor
'dinta sbd duk duniya ba abinda take tsananin so da qauna kamar ka nuna kanason mi'amor
dinta.

Uwa uba data Kira CJ ta bugi cikinsa taji abban aleeyar ba laifi he's very rich and famous Dan
haka tasan mi'amor dinta his in-laws will be Rich and famous kamarsu just the way datakeson
abubuwan sukasance Dan babban burinta shine yanda suka mallaki billions of dollars suke
billionaires duk wainda zasu zama in-laws dinsuma su zamo.
Tuni ta qara sakewa aleeya tana qara nuna Mata qauna da kulawa na musamman tareda qara
koya Mata abubuwan fashion sbd tanason matar 'dan nata tazamo like no other.

Aikuwa tuni aleeya taqara tsundumawa cikin soyayyatar mi'amor 'din mum din Dan tuni mum ta
nuna goyan baya dari bisa dari Dan harma so take tafi aleeyar zaqewa Dan tuni tafara yiwa
dawood 'din maganar aure Dan taji ra'ayinsa aikuwa ga mamakinta Kai tsaye yace Mata ya
shirya kowane lokaci zai iyayin aure sbd bayason adauki time yanama son zuwa dama yafada
musu aure yakeson yi.

Wani irin dadine yaqara kama mum din cikin zumudi tace,

Ok my love saikazo sbd nima banason ka qara wani lokaci ba auren.

Kai tsaye tafadawa taheer da aleeya yanda tayi dashi cewar ya shirya yin aure.

Da daddare takira cj tafada Masa abinda ke faruwa nason juna da dawood da aleeya keyi sosai
yayi mamaki sbd yasan Sam dawood baida niyar aure ayanzu sai zuwa gaba qila Amma Kuma
daya Kira dawood ya tambayesa shiyace zaiyi aure yanxu Kai tsaye yace Masa eh qilama
Nanda 3 months.
Aje waya dad din yayi cikeda mamaki Amma Kuma tuna yaji daga bakin dawood din ai
shinkenan abin farin cikinsune.

Ba 6ata lokaci washe gari dasuka gama saka hannu akan partnership nasu dad yayiwa Abba
bayanin abinda ke faruwa sosai abban yaji Dadi ranar dasuka dawo Miami da kansa ya tambayi
aleeya ba kunya tace eh tanason dawood din.

Ranar murna da farin ciki gurin mum harda wata special dinner sukai having dukkaninsu Abba
ma farin cikinsa baya 6oyuwa wannan tafiyar tasu tayi Masa Dadi sosai sbd komai anyisa cikin
nasara ga zumunci zai qullu.

Ranar kosu ammy da Layla da aka bugo aka sanar dasu angama komai dasun dawo za'a bawa
itama saurayin Layla dama ya Aiko baza'a Bata lokaciba za'ai bikinsu sbd mum dake ganin idan
aka tsaya jan time za'a iya samun matsala.

Farin ciki ranar gurin Layla da ammy kamar me ranar kusan raba dare sukayi suna waya da
aleeya da zumudi da farin ciki yasa takasa sukuni gashi tun adaren mum tabawa wani babban
fashion empire aikin dinko musu wasu irin dogayen rigunan dazasu saka agurin bikinsu har
agama.
Tun tana waya da aleeya kiransa ke shigowa wayarta tana gani tasaki murmushi tun tana
fahimtar Mai aleeya ke fada harta daina dukkanin hankalinta yakoma kansa Kuma takasa cewa
aleeyar Yana kiranta tana kallo yaita Kira ba qaqqautawa aleeyar da kanta ta gano hankalin
laylar baya tareda ita ta kashe wayar tana murmushin farin ciki jitake ta matso tahadu da
dawood din Kota samu sassaucin sonsa dake neman rabata da nutsuwarta.


Aleeya na kashewa kiransa na sake shigowa tana 'dauka taji lokacinda ya sauke wani irin
kasalallen numfashi tareda cewa,

NUR ahankali kamar Mara lafiya.

Ajiyar zuciya itama ta sauke batareda ta amsaba sukayi shiru dukkansu.

Miskilancinsa ne ya motsa yau Dan haka haka sukai shiru Kati na tafiya abanza tsawon lokaci
kafin taji Yana sauke numfashi ahankali alamar yayi bacci.

Murmushi tasaki tareda kashe wayar ta aje sbd ta saba da hakan idan Jan ajinsa ya motsa sai
kawai yakira Yana sauraron numfashinta haryayi bacci.

Kwantawa itama tayi tareda lumshe Ido tana sake girmama abubuwan datakeji gameda dawood
din.




Washe gari da sabon farin ciki suka tashi sbd ranar su aleeya zasu sauka da kanta tayiwa
aleeya wani qaramin chocolate cake da samosas yan kadan.

Ita kadai taje daukarsu suna ganin juna suka rungume cikin farin ciki ba tsalle tsalle ba ihu
ahankali tace,

I missed you so very much my love.

Cikin farin ciki aleeya tace,

I missed you more sweetheart.

Sakin aleeya tayi tareda kallon Abba tana murmushi tace,

Abba welcome.

Thank you layla,,hp mun sameku lafiya?

Lafiya qlau abba munyi kewarku sosai.

Hmmm kewa ai sai Bilal sbd kullum saiyi kaman zaiyi min kuka awaya wai munqi dawowa.

Murmushi tayi suka nufi mota bayan ansake booking flights din dazai wuce dasu Abba da ammy
yau da yamma.

Rungume ammy aleeya tayi tana cewa,

Ammyna nayi kewarki.

Muma munyi kewar hayaniyarki.

Dariya sukayi dukkansu Nan suka shige bedroom dinsu sukabar ammy da Abba a palon.

Tubewa aleeya tayi tayo wani wanka tasaka jeans da white vest tayi sallah suka fito Palo Nan

sukaci abinci gabaki 'dayansu har zuwa qarfe biyar suka Kai su ammy airport suka wuce
sukuma suka dawo.


Da daddare kusan kwana sukayi fira kafin suka kwanta sbd gobe Dole zasu Fara zuwa school
danma anfara lectures tun last week.

Tunda sassafe kafin layla ta tashi sbd zumudin son ganin dawood din Layla aleeya ta tashi ta
'dauki keys na flat 'din dawood din da layla tace yabar Mata sbd bazai dadeba zai dawo.


Tana shiga babban palon tayi arba da makeken hoton maska daya qara qawata palon yayi kyau
harya gaji sbd he is looking so hot a hoton Dan a beach yayi hoton da kayan Shan iska ajikinsa
dasuka qara fitarda kyawu da hutun fatarsa.

Wow,,,he is damn hot and cute"""tafada tana dariyar taya laylarta farin ciki.


Saidata qare Masa kallo ta juya ta fice tareda rufe flat din tana komawa ta fada toilet tayi wanka
tana fitowa Layla na tashi itama tashiga tayo wankan suka shirya coke da cake Layla taci
itakuma Tasha golden morn suka wuce school.


Ahanyarsu ta zuwa aleeya ke driving layla kuwa massages din dawood take replying sai wani
irin sahirtaccen murmushi takeyi sbd yanda duk ya 'daga hankalinsa zai dawo tana lalla6atasa
akan yabari yadawo Taredasu dad dinsa sbd koyazo shikadai su anan bazasu bashi aureba
Saida iyayensa.
Kallonta aleeya tayi tace,

Naga hotonsa 'dazu you two will make the best perfect couples.

Kallonta Layla tayi tace,

Kingansa da gske?

Yes dazu kina bacci naga hotonsa.

Murmushi layla tasaki tana sake kallon hotonsa dasukai tare dake wayarta aranta tace,

Dama I know my aleeya zatace kayi.

Suna Isa school suka shiga kowa yayi gurin lectures dinsa sbd Layla medicine takeyi aleeya

Kuma law.



Ahankali suka Fara nisa akaratunsu sbd exams ma suke rubutawa kuma zuwa lokacin tuni aka
yanke shawarar tsayarda ranar bikinsu danma antsaya jiran dawood din Layla yazo da iyayensa
sukuma su dad 'dinsa daya tuntubesu da maganar yaushe zasu koma Nigeria sukace sai next
month sbd sukuma anasu tsarin so suke sai su aleeya sungama exams saisuxo ayi komai
gabaki 'daya.


Ranar dasuka gama exams washe gari suka wuce Lagos sukuma su mum aranar suka sauka
Abuja dawood kuwa sai washe gari zai sauka daga baya su sufyaan zasu biyosa sbd kar
saraah tayi zargin wani Abu.


Ranar dasuka dawo tun a airport suke mamaki da tsokanar Bilal ganin yanda lokaci 'daya Yana
Shirin zama saurayi Dan harma ya kusa kamosu a tsawo.

Ranar gidan cikin farin ciki da nishadi suke komai sbd gida ya kammale.

Ana saura biyu su mum zasuzo Lagos ammy tabugawa anty Nana tafada mata maganar neman
aurensu aleeya daza'azo atsayar da date.

Siyama na zaune Koda ummanta ke waya da ammy taji duk abinda aka fada ta ta6e Baki tana
cewa,

Duka dukafa Basu Dade dafara University ba shine za'ayi musu aure.

Numfashi umman tasake kafin tace,

Ba Dole suyi musu auren da wuriba kinaji tace bazaa dauki lokaciba za'ayi sbd aurene za'ayi na
yayan billionaires sbd mazajen ko wacce ba'ama qasarnan suke zauneba.

Wani kallo siyama tayiwa umman tana juya zancen cikin ranta kafin tace,

Wai harda ita sadaka yallan ba'a qasarnan zatai aureba.?

Saikuma kiyi tunda ke kin kasa tsaida ruwan Ido ki tsayar gashi harkin gama degree

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login