Showing 51001 words to 54000 words out of 76958 words
Chapter 18 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf
kanta bakin gado idanuwanta alumshe.
qura mata ido yayi tsawon mintuna kafin ya qaraso ahankali tareda aje mata abincin gabanta
cikin wata irin sanyin murya yace,
kici abinci ga kuma kayanki nan na dauko miki.
bude jajayen idanuwanta tayi takallesa tanason yin magana takasa sai kawai ta miqe ta zauna
bakin gadon batareda tasake dagowa ta kallesaba,
kasa hkr yayi ya zauna bakin gadon kusada ita sosai tayi saurin miqewa zuciyarta na bugawa
da sauri ya riqo hannunta tareda dawo daita ta fado masa ya zaunar da ita kan qafafunsa ya
riqeta gam,
kasa motsi tayi sai kawai hawaye suka 6alle mata tafara fitarda kuka mai qaramin sauti sbd ba
qaramin riqoyayi mataba,
jin kukan nata na shigarsa sosai yasa ya sassauta mata riqon tareda dago fuskarta yana kallon
hawayenta murya a tausashe yace,
please NUR kukan ya isa haka,
tun shekaran jiya kike kuka har yanxu zaki jawa kanki ciwon kai nayi miki alqawarin komai zaizo
da sauqi insha allah so please nur kina axabtardani da wannan kukan.
tsananta kukan tayi harda shesheka ya shigarda ita ahankali cikin jikinsa ya rungumeta tareda
sakin wata kasalalliyar ajiyar zuciya,
saidatayi kukan har baya fita sai ajiyar zuciya kawai takeyi yana shafa bayanta ahankali alamar
rarrashi hartayi shiru kafin ya miqar da ita yaja hannunta har toilet ya hada mata ruwan wanka
masu 'dumi ya bude sabon brush yasaka mata toothpst yasaka mata cikin hannu kafin yafito
yaja mata qofa,
ahankali ta daga kai takalli fuskarta ta mirror taga yanda kamanninta suka canza sbd kuka kafin
tafara brush din ahankali tana qoqarin daidaita kanta da bawa kanta nitsuwa da qarfin hali kafin
ta fuskanci aleeya sbd tasan tariga tazamo butulu agun aleeyarta.
wanka tayi sosai kafin ta dauro towel ta fito cikin saa baya dakin yafice.
ko mai bata shafaba ta bude akwatinta ta dauko doguwar riga mara hannu kawai tasaka takoma
ta zauna tareda 'daukar ruwa kawai tasha sbd batajin zata iyacin komai.
anayin sallar isha ta miqe tayi ta koma gado ta kwanta tareda rufe idanuwanta ahankali tana
tunanin hindasu aleeya suke ciki ayanxu dan tasan sunacan suna nemanta.
cikin daren komai na tafiyarsu ya kammalu suka harhada komai nasu gari na wayewa sukaje
gidan mamyn maska sukai mata bankwana tareda yimata bayanin komai tareda aje mata
kudade masu yawa
dazasu tafi tareda ita suka dawo sbd tace tanason ganin nur,
lokacinda tashiga dakinta da sallama azaune tasameta bakin gado tayi wanka ta canza kaya
zuwa doguwar riga black.
tanaganin mamyn ta sunkuyar dakai tareda zamewa qasa ta gaidata cikin sanyin murya.
amsawa tayi tareda sakar mata murmushi tana kallon dawood daya zubawa laylar ido.
fita sukayi ta gyara zama sosai tafara yiwa laylar nasihar yarda da qaddara ta rungumi mijinta
sbd aure dai anriga andaura gwara su tsaya su fuskanci yanda zasu gyara gaba da abunda zai
biyo baya,
sanyi jikinta yaqara yi duk dadai babu mai karkare butulcin datayiwa aleeya.
lokacinda mamyn zata tafi tabata kyautar yankunnayen zinari da turaren datazo mata dashi
kar6a tayi tareda godiya hawaye na zubo mata,
bayan tafiyar mamy lokacin tafiyarsu yayi yashigo dakin ya tsaya daga bakin qofa tareda zuba
hannayensa duka biyun cikin aljihun wandonsa yace tafito,
tasowa tayi ahankali tazo gabansa ta tsaya tareda kallonsa ta dauke kai cikin dasashiyar murya
tace,
muje gida dan allah karmu tafi koina.....
girgiza mata kai yayi kafin yace,
zamu tafine yanxu sbd kar masu nemanki su kamaki yanxu zuwa gaba idan angano gskiya
zamu dawo so please karkice bazakiba i promise to bring you back idan lokacin hakan yayi.
shiya jawo akwatinta tariqo handbag dinta suka fito kamar yanda suka zo daga qauyensu baffa
haka suka nufi airport sune abaya sufyaan agaba har suka isa ba 6ata lokaci jirginsu ya daga.
tunda suka shiga jirgi yana riqe riqedq hannunta akai akai yakan juyo ya kalleta har wani irin
wahalallen barci data manta rabonta dashi ya dauketa a kafadarsa.
sai dare sosai suka isa direct gidansu suka nufa nan kowa yayi hanyar dakinsa.
kasa zama tayi ganin daki daya zata zauna dashi ganin yanda takasa sukuni yasa ya riqo
hannunta ya zaunar da ita bakin gado tareda sakar mata wani qayataccen murmushi yana
kallon face dinta yace,
sweethrt relax ok,,,ba anan zamuyita zamaba zamu dan kwana biyune anan kafin jass yafito
zamu tattara mukoma wani gurin ne acan zamu fara sabuwar rayuwa.
zame hannunta tayi tareda jinjina masa kai ya miqe yashige toilet.
wanka yayo wanda yasaka masa wata irin nutsuwa yafito daureda towel iya qugu ta dauke kai
tareda miqewa ta shige toilet dindaya fito.
#mamuhgee
vote and comments pls.
*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*34*
NOT EDITED
Tsayawa tayi cikin toilet din tana qoqarin saita numfashinta kafin tayi wanka tareda dauro alwala
ta fito,
akan daddumar sallah tagansa atsanake ta shirya cikin doguwar riga fara mara nauyi ta zura
hijab tazo gefensa ta tayarda sallah.
tana gamawa yasata miqewa sukai nafilar godewa allah daya cika musu burinsu.
sosai yayiwa allah godiya tareda yiwa maska,taheer da jass addua sosai kafin ya miqe yafice
dakin.
a palo ya tararda sufyaan tayi musu order abinci yashiga kicin ya dauko qaramin tray da spoons
bayan ya dauraye ya jera mata tafeda ruwa da drink mai sanyi ya koma dakin.
zaune take har lokacin kan sallayar saidai idanuwanta dake lumshe.
ajiye tray din yayi tareda zama kusada ita yana sakin wani sahirtaccen murmushi,
bude mata abincin yayi chips ne da kidney souce sai chicken shawarma.
kallon abincin tayi ta kallesa tareda girgiza masa kai ahankali.
shima girgiza mata kai yayi yana smiling harsaida dimple dinsa ya lotsa ya matsoda ita jikinsa
sosai ya debo da fork yakai bakinta tareda kafeta da idonsa.
budewa tayi dole ta kar6a yasakar mata qayataccen smile tareda matsoda bakinsa kunnenta
cikin rada yace,
thaz my beautiful bride.
wani kallo ta watsa masa ya daga mata gira daya yace,
yes baby...
rasa abinyi tayi sai kawai tayi kamar bata jisaba yaci gaba da bata abincin tanaci,
sosai tayi mamakin yanda taci abinci sbd rabon dataci wani abincin kirki harta manta sai yau ga
wani irin bacci datakeji.
ahankali tace,
ya isa haka na koshi.
daukar glass cup din ruwa yayi yabata tasha tana kallon fuskarsa dake fidda wani irin annuri na
farin cikinda zuciyarsa ke ciki.
chips din kawai yaci shima kadan sai cocumber mix dayasha ya kwashe kayan yayi waje dasu.
koda yadawo tana zaune still yashiga toilet yayo brush da sauran aladunsa daya saba kafin ya
kwanta yafito ya sanya dogon wando fari qal mai laushi da rigarsa mai budadden gaba ya juyo
ya kalleta yaga yanda ta juyar dakai daga gefensa,
murmushi yasaki yana mamakin abubuwan datake masa yanxu wanda da ba haka take
masaba akwai sakewa sosai tsakaninsu ada amma ko yanxu zaiyi qoqarin dawo da hakan,
matsowa yayi ba zato taji ya miqar da ita tayi saurin kallonsa ya hura mata iska cikin idon yana
cewa,
kina buqatar hutu my love dan haka zamu kwanta da wuri.
cire mata hijabin jikinta yayi yajata zuwa toilet tayo brush kafin ta fito ya ciro mata rigar bacci
mai dan kauri da laushi ya miqa mata.
toilet takoma ta sanyo tana fitowa yajata gaban mirror ya fesa mata turare tareda tattara mata
dogon gashinta ya daure mata yajata bakin gado ta zauna ya dauki qafafuwanta ya dora akai
tareda kwantar mata dakanta kan pillow ahankali yana kallon fuskarta datayi fayau.
saidaya fita yaje gurin sufyaan sun dan jima suna magana kafin yadawo lokacin hartayi bacci
cikin yar kwanciyar hankali dan tadauka acan zai kwana kamar abuja.
kashe wuta yayi tareda qarasowa ya kwanta gefenta tareda ja musu bargo ya juyo gefen
fuskarta ya qurawa face dinta ido cikin farin ciki mara misali harsaida wasu irin hawayen farin
ciki suka ciko idanuwansa baisan wani irin so zuciyarsa keyiwa nur ba.
hannunta ya lalabo ya danqe cikin nasa ahaka bacci ya daukesa cikin nutsuwa,
itace tafara tashi da safe ahankali ta bude itanuwanta sai akan fuskarsa dake daf da tata suna
fuskantar juna,
lumshe idanuwa tayi tareda sake budesu ta sake dora masa,
tsimin sonsa taji yana taso mata idanuwanta suka ciko da ruwa tabbas tasan har abada bazata
raba zuciyarta da sonsaba,
sonsa acikin jininta yake bazata iya rayuwa lafiyayya babushiba itakadai tasan axabar datasha
wancan karon data rasashi...
ajiyar zuciya ta sake ahankali ta zare hannunta daga nasa ta sauko ta shiga toilet,
alwala da brush tayo tana fitowa tagansa zaune yana jiran fitowarta,
alwala yayo shima yazo yayi sallah suna gamawa ta miqe zata zauna bakin gado tajisa bayanta
ta tsaya cak batareda tajuyoba,
zare mata hijabin yayi ahankali tareda rungumota ta baya ya xuro kansa ta wuyanta ahankali
yabata wani lafiyayyan kiss a gefen fuska murya qasa qasa yace,
gud morning my angel.
kasa magana tayi sai juyowa tayi ta kallesa tareda daga masa kai,
murmushi yasaki tareda janta suka koma gado ya kwanta tareda dora kansa aqafafuwanta yana
kallon fuskarta hannunta ya riqo yana cewa,
youre my happines love bazakiyimin magana ko so daya bane?
shiru sukayi dukkansu ahaka bacci yasake daukarsu,
basu tashiba sai ten yana tashi wanka yayi ya fice sbd sam ya manta zasu fita yau tunda safe
da sufyaan.
saidayayi mata ordern breakfast ya aje mata adakin kafin yayi kissing lips dinta ahankali yafice.
yana futa ta bude idanuwanta zuciyarta wata irin nutsuwa take samu alhalin ita tana qoqarin
hana hakan sbd ganin butulci ne da cin amanar aleeyarta.
wanka tayi ta sanya straight skirt black da dark blue shaking material riga mai dogon hannu,
zama tayi ahankali taci abincin kadan tareda miqewa ta fitar dashi takai dining anan taga kicin
sai kawai ta shige tasaka sauran fridge saitaga fridge din akashe yayi qura komaima gashinan
atsare saidai qura koina na kicin da palon.
zuwa tayi tasawa qofar shigowa lock tadawo tagyara kicin din tsaf ta goge komai ta wanke na
wankewa tadawo palo nanma saidata goge komai ta kakkabe ta share tayi mopping ta kunna ac
ac da tareda room spray data gani jere cikin wata qaramar showcase dake dining area
yawancima duk sunyi expire sbd dadewa amma it make sense duk da hakanan, lock din qofar ta cire sbd karsu dawo su bude yaqi
bedroom dinsu takoma ta gyare tsaf tareda wanke toilet tana gamawa dole ta sake wani
wankan tana fitowa ba zato tagansa zaune kan couch yana saka laptop dinsa charge.
jawota yayi ya zaunar kan qafafunsa yana kallon face dinta har zuwa koina jikinta dake jiqe da
ruwan wanka.
shafo fuskarta yayi tareda sakar mata murmushi yace,
go and get ready sweethrt we are goin out.
tashi tayi shima ya shige toilet wanka,
doguwar riga ash tasaka mai buudewa sai gyalan rigar data yafa ta fesa turaran da mamy
tabata tasaka loafers tana zaune kanta aqasa ya shirya cikin wasu designers qananan kaya na
armani,
hannunta ya riqo suka fito apalo suka tararda sufyaan zaune yana aiki sosai a laptop sbd so
suke sugama hada komai nasu intime su bar qasar.
murya ba qwari ta gaisa da sufyaan kafin suka fice.
bude mata gaban lambogini dinsa yayi tashiga ya zagaya yashiga yatayar suka fice,
shopping din kayan sawa sukayi dana sauran abubuwan buqata kafin suka tsaya wani
restaurant sukai lunch duk da takasa sakewa sosai har lokacin,
sai yamma suka dawo gida suna dawowa lokacin sufyaan yafita nan sukai wanka ya zaunar da
ita tareda sata magana dole tun tana kauce masa dole tafara masa magana.
da daddare su uku sukai dinner a dining sbd dawood da sufyaan dakansu suka shiga kicin
sukai mata girki na musamman,
duk yanda taso daurewa saidatayi murmushi ganin yanda sukai jiga jiga gurin aikin.
ba laifi abincin yayi maana taci kuma ta yabawa sufyaan dawood saidai tabisa da wani irin
kallon daya kashe jikinsa ya riqo hannunta yayi kissing dinsa yace,
luv you NUR.
murmushi tasaki ahankali sbd ganin sufyaan na gurin,
sosai suka saki jiki sukaci abincin suna gamawa taso tattarawa suka hanata su biyun suka
tattara komai suka gyara gurin tana zaune sai dariya suke bata.
dole dawood ya riqeta saida sukai dan fira apalon tareda sufyaan suka ringa janta fira suna
qoqarin ganin tasake,
sunjima apalon kafin suka shige yauma bacci sukayi cikin kwanciyar hankali.
washe garima su sukai mata girki hardasu baking tayi dariyarsa sbd yanda flower tayi musu
kaca kaca waya dawood yabata yace tayi musu hotuna su ajewa jass,
sai dasuka gama sukaje wanka itakuma ta gyara gurin.
cikin qanqanin lokaci suka sauyata tafara sakewa dasu dan tuni tasaki jiki dasu musamman
dawood dababu ruwansu koina nuna mata soyayyarsa yake
shopping da gurare da dan dama duk suna futa ko gurin mum din jass zuwansu hudu ko ita
tafara sabawa da ita.
****
Aleeya kuwa sosai takejin jiki ganin babu wani sauqi yasa ammy da bilal sawa kansu juriya da
danganar rashin layla suka maida hankali gurin kula da aleeyar qarshe dai abba dauketa yayi
suka komawarsu lagos sbd ba qaramin zafi da takaicin rashin ganin dawood da dadynsa harma
da taheer yayiba agurin lalurar yarsaba da rasuwar yarsa dayaba,
suna dawowa haka aka dasa sabuwar jinya abu biyu kecinta shine rashin layla da rashin
dawood tarasa ta yanda zata sawa kanta danganar rashin daya daga cikinsuba,
mum kuwa sabon tashin hankali tashiga ranardasu ammy suka dauke aleeya sukabar garin tayi
kukan rashin kowa tareda ita nan tamayar da hankali gurin neman inda dawood yashige hankali
tashe.
sarah aranar data bar gidan ta isa airport ta sauka a lagos har lokacin bata cikin cikakkiyar
kwanciyar hankali a farkon layin gidan ta tsaya takira siyama a waya ta fito.
tana isa gabanta ta tsaya sarah ta bude baki zatayi magana ta dauketa da wani gigitaccen mari
axafafe tace,
sarah when people hav friends like you they dont need enemies in their lives...
dafe fuska sarah tayi cikin tsananin baqin ciki da zafin marin ta dago tareda daga hannu zata
shaqo siyamar taji anriqe hannunta ta baya ta jiyo tagasu seeya kafin tayi wata maganar suka
rufe bakinta tareda matseta siyama ta watsa mata wani mugun kallo da idanuwanta dasuka
mugun kumbura sbd kuka tace,
zan nuna miki bana wasa da alqawari idan na dauka sbd alqawarine nayi duk wanda yata6a
taheer dina zaiyi dana sani,
zaki biya abinda kika aikata sarah sbd zan riqeki harsai ranarda taheer ya bayyan gareni cikin
qoashin lafiyarsa,,,seeya kuje da ita ku aje cikin baqar azaba kuyita hutawa da ita harsai lokaci
yayi damacan sauran wani ce babu komai ajikinta.
hawayen baqin ciki da tsorone suka gangarowa sarah tafara fixge fixgen qwacewa amma sun
toshe mata baki tareda turata mota suka wuce da ita tana waiwayen siyama.
share hawaye siyama tayi cikin tsananin damuwa da rashin sukunin zuciya sbd tasan kwanciyar
hankali da sukuni sun dade dayiwa raguwarta qaura tun ranardata kashe maska.
satinsu biyu a new jarsey suka shirya cikeda murna da 'doki suka wuce tareda mrs smoak sbd
washe gari suke saka ran fitowar jass.
suna isa suka sauka a wani babban hotel mum din jass sam takasa sukuni sbd farin ciki
dukkaninsu suma cikin farin ciki suke harda shopping sukayo masa na kayan dazaisa da sauran
abubuwan dasukasan yanaso da buqata.
washe gari tun safe suka shirya qarfe bakwai a bakin prison tayi musu hannunta na cikin nasa.
qarfe goma aka fito dashi wani irin kuka mum dinsa tasaki tareda qarasawa da gudu ta
rungumesa yariqeta gam yana sakin ajiyar zuciya,
lokacinda suka rungume juna dasu dawood hawayen farin ciki suka ringa fitarwa dana baqin
cikin ganin yanda yakoma.
yana sauke ido kan nur yakalli dawood da sauri tareda sufyaan suka qara rungume juna cikin
farin ciki kafin suka dunguma zuwa masaukinsu.
har magunguna saida sufyaan ya rubuta aka kawo musu suka basa yayi wanka da gyaran
fuska tareda cikasa da abinci kala kala harsaida ya dakatardasu.
yana gamawa suka barsa ya kwanta baccin magungunan da suka basa.
bai tashiba sai tsakiyar dare yayi wanka yayo alwala yazo yayi sallah sosai sufyaan yayi
mamaki nan sabon farin ciki ya lullu6esa jass dinsu is now a muslim.
dawood ma dayaji da safe sosai yayi farin ciki mum dinsa kuwa kadaran kadahan bata damuba
sbd bazata iya hanasa abinda yakesoba.
godia yayiwa nur data kasance tareda abokinsu kwanansu biyu suka koma new jersey.
ranar dasuka dawo da kanta tayi musu dinner tareda mum din jass sbd har dare sosai tana
gidan.
da daddare shigarda ita jikinsa yayi sosai sukai bacci sbd zazza6in gajiyar kwana aiyukan
datayi yinin.
kwana biyu sukai suna bawa jass kulawa sosai tuni yafara dawowa yanda yake nan suka
qarasa abinda suke suka tattara suka sauka porthacort inda nan ne asalin sufyaan duk da
bashida kowa marayan allah ne mum da dad dinsa shikadai suka haifa kuma sun rasu tun yana
karatu.
babban gida ne sosai mai flat hudu kowanne flat palor ne da three bedroom aciki kowanne da
toilet dinsa sai kicin,
tun maska nada rai suka ginasa da niyyar zasu zauna ciki da matayensu wata rana
kowannensu da flat dinsa da sunansa jiki,
sufyaan da jass ana sufyaan din suka sauka sai dawood da matarsa anasa,
saida sukayi baccin gajiya kafin suka fita suka samo abinci kowa yaci nan suka zauna babu
6ata lokaci suka kira meetings da wainda zasu farayi musu aiki.
har tsakar dare sunayi sai dare sosai suka gama nan aka shigarda komai suka saka hannu
washe gari