Showing 60001 words to 63000 words out of 76958 words

Chapter 21 - Dawood Book Complete writing by Mamuhge.pdf

04 Jun 2025

5548

hanya tafara samuwa nan gurin yafara
sakewa yasamu hanya ya dauki hanyar gidansu da gudu,

yana isa su sufyaan na harabar gidan sunata faman kiransa,

yanayin shigowarsa da parking dinsa yatabbatar musu da babu lafiya nufarsa sukayi kowanne
na qoqarin tambayarsa amma baimasan sunayiba saidai ya nufi flat dinsu ahargitse ya dudduba
koina bata nan yafito harabar gidan yana qoqarin sake fita jass ya riqesa cikin daga murya
yace,
wai bakajine,menene yake faruwa ka kasa fadamana duk kasa hankalinmu yatashi?

kallonsu yayi da jajayen idanuwansa wani irin zafi na tasowa daga zuciyarsa yace,

akaro na biyu aleeya tasake shiga tsakanina da farin cikina sbd jikina nabani NUR barina zatayi
sbd aleeya,,,,,aleeya itace babbar matsalata arayuwa kaji yanda take yiwa matata ihu kuwa,she
even slapt her bayan tasan she's pregnant and now nur left sbd gudun 6acin ran aleeya ya
zanyi da rayuwatane? bansan meyasa tunfarko ba nafara soyayya now i'm stuck wit this two best friends zance ko
sisters.

dafe goshinsa yayi yana sakejin ciwo cikin ransa,
ganin kamar yana buqatar taimakonsune yasa suka dunguma yawon duk wani motopark da

stations nemanta amma babuta babu mai kamada ita nan hankali ya qara tashi mum tun tana
daurewa kasawa tayi ta miqe ta fita nema itama sbd harga allah tasamo danta ya daidaitu
daqyar bata fatar akoma inda aka fito,
ta yarda tabi sai layla.


har dare suna abu daya amma babu alamar zaa ganta,
hankalinsu bai qara tashiba saida sukaga dawood na neman shiga wani hali babban abinda
yafi jijjiga duniyarsa shine sabon sonta da dansa ko yarsa dake cikinta,

duk yanda sukaso dawowa gida har gobe qiyayi haka suka raba tsakiyar dare suna nema shiga
tashin hankali,

asubar fari dole suka dawo gida jiran kira daga stations dinda suka bayarda reports reports,

duk yanda mum taso ko ruwan coffee yasha yakasa sha gashi har wani jiri jiri yake gani daqyar
yayi sallar asuba ya sulale yaqara ficewa basu saniba.





duk yanda taso bawa zuciyarta dangana da rarrashi saitaji takasa sbd mutane biyune data fifita
qaunarsu fiyeda komai suka taru suka karya zuciyarta da yardarta akansu,
tanason dawood so mai tsanani data za6i zaman rayuwar qunci agidansa sbd sonsa kuma ta
shirya hakan har qarshen rayuwarta saidai duk sonda take masa tafison laylanta fiyedashi
meyasa layla taza6i 6oye mata komai?
zata iya bawa layla jininta da qodarta bare abinda takeso amma suka za6i baqanta mata fiyeda
fada mata komai tun farko,

dafe zuciyarta tayi tana cigaba da rero kukanta sbd qunci da zafi takeji sosai cikin ranta idan har
haka ake sadaukarwa to itakam tata batazo mata a dadiba don kuwa nata
cutatarwane,ancuceta anbarta tana jinyar banza abanxa.

tun tana kukan da qarfi harta koma ta lafe saidai hawaye,

abba daya dawo yana fada sosai akan sunbarosa asibiti batareda anyi abinda akaje yiba cikin
sanyin murya da fargabar yanda zai dauki zancen ta zayyane masa komai,

shiru yayi yana jujjuya zancen cikin zuciyarsa kafin yasake ajiyar zuciya yakalli ammy cikin
sanyin murya yace,

wannan alamari tabbas qaddarane sbd matar mutum hausawa sunxe kabarinsa ce saidai duk

muduka amatsayinmu na iyaye munyi kuskure musamman keda kike uwa mace kuma kinsan
komai amma kika qyale,
datun farko kin fadamin koda baki fadawa aleeyarba saimu samu mafitarda zata 6ulle bakamar
irin wannanba,

maganar gskia naji zafi matuqa kuma wlh banga laifin aleeyaba sbd an cutatar da ita ta hanyar
6oye mata alhalin idan itace nasan tabbas bazata 6oyeba abu mafi zafima shine ace ansaketa
ranar da aka kaita kuma tsabar cin fuska da zarafi ace tacigaba da zama tana yimasa bautar
kula dashi baya gidan giya baya club sannan duk da haka qarshe ace sunyi aure wani gurin duk
baa nememuba saida taji maganar ciki shin a ma'auni na hankali mezaisa ran mutum bazai
6aciba kokuwa so ake tayita hadiyar ciwo da qunci ita kadai bayan duk wanda ta jima tana diba,

shin idan ta cancanci haka daga dawood wannan fine babu matsala amma agurin yar uwarta
datakeso fiyeda komai dan nasan tabbas dazaa bawa aleeya zabin ta hakura da iyayenta
tabarwa layla zata iya bakomaine yasata hakaba face 6oyewarda akai mata ana tunanin bazata
iya hakura dashiba kuma wlh kowane dan adam akayiwa haka zaiji zafi,
agaskia banji dadiba kwata kwata sbd ancutatarda aleeya kuma kece silar komai sbd idan ita
layla tayi tunanin wannance mafita saiki lurarda ita ba wannance mafitarba ki dage ki jajirce ki
nuna mata kece uwa,

karki dubi kasancewarta marainiya kice bazaki takurataba ki nuna mata abinda ya cancanta sbd
wannan babban kuskurene ace bazaa iya rufe ido ayiwa maraya fadaba sbd gudun 6acin ransa
gashi inda komai yazo yanxu,
nikaina amatsayina na mahaifi nayi babban sakaci amma insha allah yanxu zan tsaya tsayin
daka kan iyalina,

ayanxu kam tunda alamura sun lalace zan danne 6acin raina adaidaita komai tukuna sbs
bazanso kan yayana ya rabeba idan komai ya daidaita nasan abinyi.

yana gama fadar haka ya miqe yashige toilet ransa ba dadi ko kadan sbd sosai ransa yayi 6aci
amma kasancewarsa babba dole ya danne 6acin ransa sbd samun alamuran su daidaitu dan
idan ya nuna 6acin ransa aleeya zatafi qara hawa.

ajiyar zuciya ammy tasake cikin tsananin sanyin jiki da damuwa tareda fargabar halinda aleeya
da laylan suke ciki yanxu,
tabbas tayi kuskure amma insha allah angama daga yanxu bazata taba barin wata 6araka sake
shigowa tsakanin yayantaba.


tsakar dare ammy tashigo dakin ahankalin tareda lalubar wutar dakin ta kunna batai mamakin
ganin aleeyar zaune daram tsakiyar gadoba tayi zuru tareda nisa ciki tunani idanuwanta sunyi
wani irin mugun ja da kumburi fuskartama gabaki daya tayi jajir sbd kuka,

qarasowa tayi ahankali ta zauna bakin gadon jikinta amatuqar sanyaye da tausayin aleeyar sbd
tasan ko aje adawo aleeyarce zata cutu,

hannu takai ahankali ta dafo kanta tareda kiran sunanta murya a shaqe,

dagowa aleeyar tayi takalli ammy tareda amsawa daqyar,

aleeya ni uwace datayi babban kuskure ina fatar zaki yafemin harma da layla..

rufe ido tayi ahankali hawayen ciki suka gangaro tasaki wani wahalallen murmushi mai ciwo
tace,

ammy bana fushi daku saidai dolene zanji zafi da ciwon abinda akayimin,

kina tunanin zanta6a daina qaunar NUR?
qaunarta acikin jinina take ko kadan bazan iya daina qaunartaba sbd qaunace daga allah
tsakanina da ita saidai nakasa gane meyasa tayi tunanin nibazan iya hkr da dawood ba ta za6i
cutatarda rayuwar mutane da dama,
shin ammy kinkuwasan zafi da 'dacin dana dandana aranar dana tare aranar aka sakeni
meyasa duk mutanen danake so sunkasa fahimtar irin soyayya da qauna danake musu,,,

sharce hawaye ammy tayi sbd tsananin tausayin 'yarta ganin yanda har lokacin tana qaunar
layla da zuciya 'daya,


kuka tasake mara sauti tana cewa,

ammy nice da hannuna na mari laylana,
laylana nada ciki maimakon nayi farin ciki amma nice na mareta da kaina wannan wace irin
qaddarace,
meyasa suka za6i farin cikinsu akan na masu qaunarsu shin meye laifina dan inayi musu qauna
mai zurfi?

share hawaye aleeyar tayi tareda zamewa ta kwanta jikin ammy murya na rawa tacigaba da
cewa,

har cikin raina bana buqatar layla ayanxu ina buqatar zuciyata tasamu sarari tukuna sbd ganinta
yanxu naqarawa ciwukan zuciyata zafi.

shafa kanta ammy tayi cikin muryar banhkr tace,

aleeya ki yarda babu wata qauna ko soyayya aduniyarnan datafiki agurin layla,

layla namiki qauna irin wadda kike mata sbd tun asali komai datayi tayine sbd taza6i rabuwa da
wanda take tsananin so sbd ke,
ta za6i yarda da auren qaninsa sbd ta haramtawa kanta wanda takeso duk sbd kene,
wannan cikin na jikinta isharane sbd allah yayi da akwai rabo atsakaninsu koda aure kobabu
aure dole zaa samesa tunda allah ya qaddara to maixai hana mu taru mu rungumi qaddarar
gabaki daya.

shiru tayi tareda rufe idanuwanta ahankali zuciyarta na qara nauyi.

ammy anan ta kwana gurinta tana qara fahimrarda ita kuskuren dasuka taru suduka suka tafka.





baidawo gidaba saida su jass suka fita nemansa hankali ba kwanceba,
koda suka dawo gida wahala da yunwa tafara zabgesa wuni guda,
mum kuwa tayi jimamin tayi kukan zuci acikin kwana na uku tuni kukan fili yafara bayyanar mata
sbd masifar data hangowa kanta kan 'danta,

duk iya nema da bincike anyi babu nur babu labarinta tun abu na sauqi sauqi haryayi zafi abba
dakansa yafara nasa aikin sawa nemanta hankali tashe
ammy ma kam rashin hankali yadawo sabo ganindai ta tabbata ba'aga laylaba ta 6ata,

duk yanda aleeya takaiga daurewa abin cinta yake cikin ranta da jikinta sbd wata irin rama da
lafiya data fara qaurace mata babu layla ga dawood kwance sosai babu lafiya,

bilal kam kallo daya zakayi masa kasan baya cikin kwanciyar hankalin 6atan yar uwarsa ga
aleeya ma dayake gani yana rage kewar layla batada walwala kwata kwata yanxu kullum tana
daki,

cikin sati biyu alamari yayi tsanani kullum cikin yiwa dawood allurar bacci ake har taso fara ta6a
masa qwaqwalwa suka daina yimasa aikuwa nan take ciwo yadawo sabo babban abinda yafi
daga musu hankali shine mugun ciwon cikin dayakeyi sosai nan suka duqufa bincike suka gano
giyar dayayishace abaya ta ta6a masa qoda nan suka duqufa magani amma kamar basayi,
sannu ahankali damuwa da quncin dasuka fito yafara dawowa kamar da,
mum duk ita inda tashin hankali yakai tana ciki tayi kuka har idanuwanta sun rikide
lokacinda abun yayi tsanani hankalinsu jass yatashi suka sanarda dad da taheer halinda ake
ciki nan take dad ya shiryo zuwa yazo duk yanda mum taso yaqi bari tagansa yayi iya
kwanakinsa suka wuceda dawood din sbd aikin dazai masa acan.

bayan tafiyarsu kullum ammy agidan take wuni itada nana suna rage mata damuwa,

aleeya sosai take jinyar kanta amma haka ta daure tashirya taje gurin mum din aranar data
dawo gida tayi kuka sbd ganin ko yanxu rayuwar mutane da dama na neman lalacewa ta
sanadin rashin layla to idan wancan karon laifin layla ne yanxu nawaye?


anyi masa aiki cikin nasara saidai sosai yadaga musu hankali gida yakeso su koma kar layla
tadawo bayanan,

hakanan suka tattaro suka dawo dashi aka dora jinyar anan,
sannu ahankali ciwo ke cinsa babu abinda yake fata ayanxu irin mutuwa sbd yatabbarda
soyayyar layla itace ajalinsa,
zafi da ciwo mara sassauci yakeji cikin zuciyarsa matuqa,babu abinda yakeson gani irin laylarsa
sbd duk inda take ayanxu ta haife cikin dake jikinta da wata daya,

rufe idanuwansa yayi ahankali yabudesu ciki azabar ciwo wasu irin hawaye masu dumi suka
gangaro masa tabbas nur itace rayuwarsa.

tari yayi ahankali mum tamiqa masa tissue yarufe baki yana tarin yana dago tissuen ahankali
yaga jini ya lumshe idanuwansa daqyar cikin azaba tareda 6oye tissuen kar mum ko su jass
sugani,

hankalinsu baqaramin tashi yayiba ranarda yaringa kwararo aman jini nan suka kwashesa sukai
asibitinsu,
lokacinda sukaga result din bincikensu akansa kuka sosai jass yazauna yanayi sufyaan na
qoqarin danne nasa gurin lallashinsa sbd sun sadaqar da shima rasashi zasuyi kamar yanda
suka rasa maska tabbas dasun tabbata marayu idan babu maska babu dawood.


tsawon wata hudu da dawowarsu babu siyama babu dalilinta ga ummanta ta daga musu hankali
da koke koken nemanta nan hankalin ammy yasake tashi ga abba sosai hankalinsa ke tashe
gurin ganin ansamo inda layla take kusan shekara kenan babu labari,

tareda abba ayau suka sauka porthrct direct headquatr suka nufa gurin jin bayaninda akakirashi
akansa cewar antsinci gawar wata mata da jariri sabo.

wata mummunar sarawa kan aleeya yayi tayi saurin jada baya tana qoqarin zubewa daidai
kawowarsa shima ya iso hankali tashe jin kiranda akai musu kan case din nur.

fado masa tayi idanuwanta na qoqarin rufewa jikinta nason saki,

riqeta yayi dakyau tareda cewa abasa ruwa masu dan sanyi,

miqo masa abba yayi jikinsa na rawa,

kadan ya zuba mata amma ko alamar motsi babu atareda ita nan abba ya rude suka kwasa
asibiti hankali tashe,

bayansu yabi da kallo ahankali tareda kallon qaramin gyalan doguwar rigar dake jikinta da
akabari ajikinsa,

nauyi yaji azuciyarsa akaro na farko daya ta6ajin hakan ya dafa zuciyarsa ahankali tareda
qurawa gyalen ido yana sauraron abinda ake fada masa kan gawar daaka tsinta,

shiro yayi cikin tsananin tashin hankali yafito yanufi gida yana tsoron fadar zancen kar dawood
yaji gashi tun jiya yana asibiti jikin yatashi sosai cikin dare,
yana isa asibiti kallon sufyaan dake daurawa dawood jini yayi ya girgiza kai idanuwansa na
cikowa da hawaye.

lokacinda ta farfado kuka takesonyi amma yaqi zuwa tsabar tashin hankali da firgicin datake
ciki.
zaidai jajir da idanuwanta sukai lokacinda abba zaije dubo gawar saidai yakaita gurin mum dan
harlokacin bata dawo daidaiba,

kallo daya sukaiwa juna itada mum suka tausayawa kansu nana datuni aka barwa mum ita ita
tayita fama dasu ko ruwa daqyar sukesha har abba yakira yasanardasu ba gawar nu bace,

washe gari aka dawo da dawood gida ana shigowa dashi palon idanuwanta acikin na jass suka
fara sauka kusan atare suka dauke fuska kowanne babu walwala,
shikuwa dawood baisan wayene akansaba harlokacin,

ganin halinda yake ciki yasake girgixa kwanyarta tayi kuka adaren da ita da mum ba'asan mai
rarrashin waniba bare da tsakiyar dare abin yataso yayita aman jini tuni suka fitarda rai akansa
banda kukansu su duka nabu abinda kd tashi,

sannu ahankali yafara gane wainda ke kansa nan aleeya tayi masa alqawarin nemo masa nur
da kanta takawo masa da wannan alqawarin suka dan fara sabawa itace ke kulada cinsa da
maganinsa,

ahaka harsuka sake shekara babu nur duk wata rayuwarta ayanxu ta tattarane gurin kula dashi,
bata iya barci kullum kwana take azaune,
mum ma ahankali tafara ciwo nan abubuwa suka taru sukai mata yawa musamman yanxu da
ciwon dawood yake sake gangarawa dan yanxu kam yafi wata akwance ko motsi bayayi tun
ranarda ya kwana yana aman jini,

kallonta ammy tayi cikin hawaye tana cewa,

aleeya mukoma gida kiyi jinya wlh kema bakida lafiya ji yanda kika kashe rayuwarki gurin jinya.

share hawayenta tayi da dogayen yatsunta dasuka rame murya a sanyaye tace,

ko ayanxu na mutu nasan wannan danakeyi shi ake kira sadaukarwa babu cutatarwa babu
6oyo da zuciya daya nakeyi kuma wlh komai danakeyi inayine damin layla bazan ta6a bari
abinda takeso ya wulaqantaba,
ni layla da dawood sune tawa qaddarar.


shuru ammy tayi tana fidda qaramin sautin kuka ahankali sbd gabaki daya aleeyar ta canxa
tamafi wanda ke jinyar lalacewa sbd abin ita a zuciyarta yake cinta.
wannan wace irin soyayyace allah ya jarabci aleeyar da ita akan dawood da layla.

kuka sosai ammy tayi na tausayin yarta haka takoma sbd aleeyar taqi yarda tabita,

bayan tafiyar ammy mum tayi sabon kuka dan tabbas gskia ta fada aleeyar na buqatar kulawa
fiyeda ita sbd ita kanta tana hango qunci da tsananin ciwon zuci da aleeyar ke fama dashi.

aranar da suka dawo gida da dawood tazauna takallesa taga yanda ciwo yamayar dashi sai
aranar tasamu kuka yazo mata tun bayan tsawon lokaci,

bude idanuwansa yayi daqyar tareda lumshesu cikin azabar ciwo yace,

thank you aleeya.

giegiza masa kai tayi cikin tsananin kuka ko mgn bata iyayi,

sake bude baki yayi daqyar yace,

duk ranarda kikaga nur da abinda ta haifa nabaki amanarsu and pls forgive me aleeyaaa'''''ya
qarasa fada cikin wata irin azaba tareda fara tari

tsananta kukanta yayi kamar zata shide,

mum ce tashigo ta tarardasu ahaka arikice ta qaraso ganin jini fiyeda na kullum salati tasaki mai
qarfi jikinta na rawa nan aleeya ta dago tana ganinsa tafuta cikin tsananin firgici daidai isowarsu
sufyaan da kwalayen drip drip suna ganin yanda yaks suka watsarda komai aka kwashesa suka
koma asibiti cikin sabon tashin hankali.

****
DAWOWA LBR

zama taji anyi kusada ita shiyasata dauke jajaye idonta dagakan sunan asibitin ta sunkuyar
dakai qasa,

anty aleeya'''''taji ankira sunanta murya na rawa,

kobata dagoba tasan muryar bilal ne sai kawai ta share hawayen dasuka sauko mata ta dago
ahankali,

taheer tagani tsaye bayan bilal yana kallonta cikin tsananin tausayawa sbd tabbas ta jarabtu,

kama hannunta bilal yayi yana kallon tsakiyar red swollen eyes dinta yasaka mata takarda cikin
hannunta yace,

anty aleeya hawaye da damuwar danake gani cikin idanuwanki har abada bazasu barni na
zauna cikin sukuniba,
layla da dawood ne farin cikinki tuntuni nayi alqawarin dawo miki da farin cikinki,
ban nemo laylaba sbd tana yar uwata na nemotane sbd ke.

kallonsa tayi da sauri idanuwanta na cikowa yace,

layla itace warakar dawood insha allah ke kuma warakarsa da ganinta itace taki ina fatan komai
yazo qarshe.

kallon takardar tayi hawayenta na saukowa kafin tadago tasake kallon bilal din da sauri ta fada
jikinsa tareda sakin wani irin kuka.

saidatayi kamar bazata bariba kafin ya miqar da ita tashiga dakin dawood taquara masa
zuciyarta na karaya tsawon lokaci ta sake kallon takardar hannunta ta juya ahankali ta fuce
tareda sake waiwayarsa.

tan fitowa sukaci karo da jass zaishigo kallon juna sukayi kowanne ya wuce,

kallonta taheer yayi yace,

muje nizan kaiki lets finish this today insha allah.

gyada masa kai tayi hawaye na gangaro mata suka wuce kosu mum basu saniba.
#mamuhgee

vote and follow.
_*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_




*_This page is for you AUFANA thank you for the love,love you too_*💋




*39*
not edited.




bilal ne riqeda hannunta har cikin motar taheer suka zauna baya still hannunta na riqeda nasa
sosai takejin rashin sukuni a zuciyarta,
lumshe jajayen idanuwanta tayi tabude cikeda abubuwa da yawa ciki hardajin zafin yanda
koyaushe layla tafi shaawar barinsu batareda taqara laakari da halinda zasu shigaba shin
meyasa kullum kukanta da damuwarta akan layla ne,
ada kam fushi tayi sbd abinda sukayi amma ayanxu ne zata dauki matakin gaske

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login