Showing 33001 words to 36000 words out of 75972 words

Chapter 12 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Advertisement

Amnoor   

19 Aug 2025

6065

dora hanun sa saman hanunta ya " sanu my bodyguard ya a wajen Mata (Fatma) uwa a wajen yata sanan ya lumshe ido ya bude ya ce .........




๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ92245338๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoorโœ๐Ÿฝ: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_

_Hohohohohohoho Sisto_
*Sajida Yar mutan Zinder*
Up
Up
Up
*Tabbas duk karyar kada ta ruwa ce da ruwa sunkare tata ta kare, Sisto Ashe haka wannan Littafin yayi sugar baki sanarmin ba, gaskiya kin cuceni da nayi jinkirin karantawa Amma na yafemiki saboda dadinsa da naji*

_Littafin nan fah yazomin na daban Wallahi haka kuma salon cikin sa dole ne ko na jinjina miki Abisa namijin kokarin da kikayi_

*J Confiance a tw ma chรฉrie muje zuwa aci gaba da gashi ina biye dake Wallahi, Amma plzz kizan yimana typing dayawa*

*Amnoor taki me kaunarki๐Ÿ˜˜*
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoorโœ๐Ÿฝ: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_




42

Ya ce: sanan abin soyuwa da mahaifiyata da kuma mahaifina allah ya tashi kafadar ki a hankali ya mana mata kis a goshinta ya tsurawa bakinta idanu ya fada tinanin ranar da yayi mata duren abin bakinsa shi kadai yayi murmushi ya dora yan yatsu biyu yana zagaywa a saman lebenta firgigit kamar Wanda aka mintsine shi ya sauke hanun ya dake ya juya ya bar dakin ya nufi na Afane yana shiga ya rintse idanuwan sa a hankali ya bude ya isa bakin gadon duk anbi an dadaura mata na'ura a jikinta hancinta harda bakinta ga karin ruwa a hanunta ya lumshe ido

Ya ce " i'm sorry bebyn dadynta i'm sorry bebyn mamamarta insha allah zaki sami lafiya dady zaiyi tayi miki adu'a kinji sanan ki tashi zan kawo miki yaran kuyi ta wasan da su kinji i promis beby zan kawo miki kuma na yarda bodyguard ta bani abincin a bakina zanci aman fa idan kika tashi my Afane; ya dan tsagaita yana ajiyar zuciya ya kali sama ya ce "" ya allah ka bani ikon zubar da hawaye KO naji sasaucin wanan azabar" kwarai ya yarda cewar kuka ma rahama ne sanan baiwa ce ,


Ya mike jiki a sabule ya fito ya shaidawa su momy da sauki



Washe gari
Bayan sallar isha'i da misalin karfe tara na dare *Raisa* ta farka daga bacin da ta kwana da wuni tana yi , dishi dishi ta fara gani sai daga baya ta fara gani ras idanuwanta ta sauke kan karin ruwan dake hanunta ta zaro ido ta tashi da kyar ta zauna tana zama hoton abinda ya faru ya fado mata a ranta , gabanta ya yanke ya fadi da dan razana ta furta "" *Afane* my *Afane* "" ta saka hanu ta zare karin ruwan dake hanunta ta ziro kafafuwanta ba KO takalmi a kafarta ta kama hanya ta bude dakin da take ta fito sai da ta ware murya tun karfinta ta furta *AFANE* !

Irfan ya bude dakin da suka yada zango suka fito a tare har rige rige suke suka iso inda take tsaye fuska tuni ta wanke da ruwan hawaye suna isowa ta kama hanun Momy domin ita ta fara isowa wajenta
Ta ce"Momy ina Afane ne

Momy ta ce " Raisa Afane bata mutu ba don haka ki kontar da hankalinki ki dena kuka kinji

Raisa ta kara damke hanunta ta ce" a nuna min inda take

Irfan ya matso ya kama hanun nata ya nufi dakin da Afane ke konce suna shiga ta saki hanunta ta isa wajen gadon Afane ta fashe da kuka har tana karkarwa ganin zata baro masa aiki ta saka momy tayi ta fada ya sa ya karasa a hankali wajenta ya kamo hanunta ya dagota daga tsugunin da tayi yana dagota ta rukunkume shi tana fadin Yaya irfan wa ya yiwa yarinyata haka? Ni ce KO? Domin ni na hada mata abincinta da hanuna a ina ta samu poison? Don allah kayi min rai ka fada min zata tashi ne?

Irfan da gaba daya ya dan daburce ya ce " ke ai da sauki fa zata samu sauki suna tsaka da zancen zata samu sauki sai ga Ilham ta shigo Raisa na ganinta ta je da gudu ta fada jikinta suka kusan zubewa domin Ilham da dan cikinta na wata biyar da Sauri Irfan ya tare sanan ya dauki Raisa cimak yayi dakin da aka kontar da ita tana kukan ita fa yar ta ya yi mata wata uwar tsawa sanan tayi shiru ta hadiye kukan nata


Konci tashi sai da Afane tati kwana shida sanan ta fita daga comma yanzu kam alhamdulilah yan uwa na nesa da na kusa duk sun zo sun ga marar lafiya

Zuwan bara'atu Kenan ita da mijinta da kuma yarta anisah suna zama suka gaisar da su Momy Bara'atu ta ce momy wani daki ne Afane din take?

Momy ta ce" ku fara gaisar da Raisa ga dakunta can no21 sai ku dawo ku shiga na Afane

Bara'atu ta Mike ba musu ta shiga dakin na Raisa tana shiga ta tarar da Raisa na kalon sama tana ta tinanin yarta , Bara'atu ta tafa hanayenta ta ce hawayen kin cin galabane kike? To ta allah ba taki ba azaluma kin so ki kashe masa kwonsa daya a duniya dan ke juya ce tuni bin maza ya bata miki mahaifa bazaki haihu ba shine kike kukan baki samu kin kasheta ba , idan su kin gama da su ni kinyi karya yarinya sanan mu zuba ni da ke shege ka fasa tayi kwafa ta juya ta bar dakin
Tana fita Ilham dake Saurin ta gama alwalah ta fito ta tsayar da wanan cin mutuncin da Bara'atu ke shukawa Raisa ta fito da Sauri tazo ta rungume Raisa Wace ta hade kanta da guiwarta tana rusa kukan wanan walakancin

Raisa ta ce: Ilham yaushe zan iya cutar da yarinyar da nake ji a can cikin raina? Wly ba ni ba ce sanan da take cewa na kasa haihuwa to ni mai gamina da haihuwar ma? Mai yaya irfan zaiyi da namiji irin sa? Ta kuma fashewa da wani kukan


Ilham ta ce tabas sai mun basu mamaki gaba dayansu sister kafin Samir ya dawo daga tafiyar da yayi sai kin zama son kowa sai kin zama tauraruwa bi'izinilah sanan allah sai ya nunawa anti Bara'atu shi ke sawa ayi kuma ayi

Ita dai kukanta take tun karfinta




Bayan sati biyu
Zaune suke a falon momy Afane na saman cinyar Raisa tana ta jan jelar gashin raisa ita ala dole sai tayi mata kitso

Ilham ta fito ta shirya ta ce..........






Muje zuwa masu karatu


[20/7 23:47] ~Amnoor๐Ÿ‘ฏ๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€: [3/7 14:52] Sajida: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_


43

Ilham ta fito cikin shirinta na doguwar abaya ta nade kanta cikin bakin dan kwali dan cikinta ya fito das da shi ta saka takalminta marar tsayi tana saukowa ta tarar da Raisa inda ta barta
Ilham ta ce: madame ya haka baki shirya ba?


Raisa ta ce : shirin mai kuma? Kawai mรป je ni fa wly na tsani wanan abin haka kawai ni fa bazan iya ba walahi dan momy ta ce don naji dadin jikina aman ba dan wani can zan canza yanayin rayuwata ba , ta murguda baki

Ilham tayi murmushi ta ce" naji tashi mu tafi

Raisa ta mike ta kama hanun Afane wace aka saka mata dan wando baki da rigarsa (rainon soja) suka fito itama dogon wandon ne a jikinta da farar riga da takalmi silifas fari sai hula ita dai Ilham tana son tayi magana tana tsoron tafiyar ta fasu shi yasa tayi shiru da bakinta


Gaban baban boutique na Hajiya Khadija suka yi parking suka shiga Raisa ta nemi waje ta zauna ta shiga dadana wayarta ita kuwa Ilham ita da Afane suka shiga zabar kaya na gani na fada tun daga shada lesh, abaya, lifaya, materiel, atamfa, kala kala ta dawo wajen takalma manya manyan masu tsini class ta zabi kaloli masu kyau, ta koma layin sarka da dan kune duk da na lefenta komai bata taba ba ta zabo masu kyau tana zuwa ta tarar bata wajen zaman can ta hangota wajen kananan kaya
Tayi murmushi ta zauna tana maida nunfashin gajiyar da tayi


Raisa haka kawai taji tana sha'awar daukan kananan kaya da dogayan riguna hakan yasa ta zabi masu kyan gaske harda na baci , haka ta zagaya wajen na yara ta kwasowa yarta kalolin kayan zamani masu masifar kyau

Bayan sun gama aka gama irga komai don a tantance abinda suka dauka domin hajiya khadija ta ce kar a amshi kudinsu KO nawa zasu dauka

Daga nan ma dreba ya zarce da su shagon isma'il telan manya suka zube masa gaba daya kayan Ilham ta zage ta zabi dinkuna kalakala wasun sai ma an aika anyi aikin su a dubai kuma duk abinda aka dinkawa Raisa sai an dinkawa yarta daidai da atamfa sai an fitar da nata

Ilham ta ce" yaushe zaka bani su ina sonsu da wuri wuri fa

Ya ce " insha allah hajiya za'a gama nan da sati guda gaba dayansu

Ta biya shi makudan kudi yana ta godiya suka fito suka je gidan gyara suka samu hajiya zahra mai gidan ce Ilham ta fada mata tana son Wace zata koyawa sister dinta kwaliya , da yanga , da yanda ake tafiya da manyan takalma,

Hajiya zahra tayi murmushi ta ce" kin zo inda za'a share kukan ki aman itama yar Mr president ce?

Ilham ta ce " matar general Irfan ce

Hajiya zahra ta zaro ido ta ce " lale dole a bata kulawa so yanzu aikin nan da ni kaina za'a yi shi ni zan kula da koya mata kwaliya da magana idan yaso sister halys ta koya mata tafiya da heels insha allah soja zata zamo soja mai yanga

Suka yi dariya gaba dayan su Hajiya zahra ta ce" so gobe zamu fara aikin mu zamu dauki sati guda muna yi don haka a bamu takardar shiga gidan naku kar muje a hanamu

Ilham tayi murmushi ta ciro wasu kati uku a Jakarta ta saka hanu suma kowace ta saka hanu ta basu suka huce gida Raisa sai mita take



Washe gari

Tun da safe karfe takwas suka zo suke zaune Raisa na sheka barcin ta
Wanan shigan Ilham na hudu Kenan tana dubawa KO ta farka, ta fito tana kirkirar murmushi sai ga Fatima ta fito zata je su gaisa da baki
Ta ce"" ina Raisar ne?

Ilham ta ce wly Ma tana baci

Fatima ta ce" au shine kika kyale mutane zaune suna jiranta? Kai allah ya shirya ta tashi fuuuuu tayi dakin Raisa

Tana shiga Raisa ta fito daga wanka ta ce" to yar mulki saka kayanki muje

Raisa ta cuno baki ta ce" Ma morning kinga fa yarinyata bata farka ba kar aje ta farka bana nan

Ma ta ce" idan ta farkan zanyi mata wanka na kawo miki ita

Raisa ta ce to, domin tasan idan ta tsaya musu Ma zata iya marinta ne haka ta kama hanyar dakin baki ta tarar da su suna zazaune suna tadi , ta mimika musu hanu suka gagaisa


Hajiya zahra ta ce...............








92

24 53
38
[3/7 14:53] Sajida: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_


44

Hajiya zahra ta ce " to madame yau zamu fara gyara plz ki bamu hadin kai mu samu aikin mu yayi kyau


Raisa ta ce" uhum

Ilham ta ce" insha allah

Zahra ta fara aikinta gaban banban madubi ita kuwa Halys ta dauko wani irin takalmi mai shegen tsini ta daurawa Raisa a kafarta fakar ta dauru da kyau har wani zapi zapi take yi mata haka dai ta daure bata ce komai ba
Sai da Zahra tayi ta nuna mata yanda ake gyara idanuwa yanda zata caje gashin idanuwanta domin tace ita fa bata son zana gira sam bazata zana ba hakan ya sa zahra ta dage wajen fitar da ainahin kyan idanuwan ta sai da ta gama aisha ta harhada mata sabulai masu masifar kanshi mai kontar da hankali da na wanka da na wanke hamata da kuma Wanda idan tana ra'ayi zata shafa a fuskarta kafin ta shiga wanka sai ta wanke yana kara sulbin fata , Aisha ta shafa mata harda hanayanta ita dai da idanuwa take binsu sanan tana daukan abinda suka koya mata tana tsananin mamakin su kuwa a ina suka koya?

Halys ta ce " to madame sai ni ki taso ki zo wajen kofar shigowa sanan ki dawo

Raisa ta zaro ido ๐Ÿ˜ณ waje ta ce " ban gane ba

Halys ta mike ta je daidai kofar shigowa falon sanan ta dawo

Raisa ta bushe da dariya har tana rike ciki ta ce " aman gaskiya lafiyar taki anti da sauki dai , aman in ba hakanan ba ina ni ina tafiya da wanan zungureren abin na kafata naje ina da shi ? Hahhh tap plz ki dena wanan bayanin

Su duka suka yi tsuru suna kalonta , ita kuwa Ilham sai gumtse dariyarta take kai Raisa akoy yar airs wai kice Anti kuma kice bata da lafiya?

Ganin fuskar Halys ba alamar wasa ta saka serius a ciki ya saka ta ciciba da kyar ta tashi tana yin taku na biyu ta fadi , ta kuma cicibawa da rike garu da komai ta samu ta isa daidai kofar ai kuma dawowar tayi zaune dirshan ta jawo duwaiwainta ta dawo tana washe hakura kamar gonar auduga๐Ÿ˜,


Halys ta mike ta suka koma suka dawo sunyi hakan ya kai sau shida Sanan ta saketa taje da kanta ta dawo harda tafa mata suka yi bravo๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘

Haka suka wuni kowace tana Nuna mata mahinmancin aikinta da kuma anfanin yin hakan a jikin mace , sosai ta yarda zata koya KO don itama ta rinka taku irin na mata

Suna komawa abinci kawai ta samu ta ci domin bata sallah ta yasu a nan ta shiga bacin gajiya , daidai wanan lokacin Irfan ya shigo gidan domin dawowarsa kenan daga wajen aiki yazo ya ga gudan jinin sa kafin yaje ya konta

Bayan ya gaisar da iyayensa Afane tayi baci a saman kujera yayi mamakin hakan a ransa ya ce KO ina uwar tata domin ya san indai tana nan bata barinta tayi baci ita kadai

Momy ta lura da yana dan waige waige ta ce" kai dauki Afane ka shinfide ta sanan ka dauki Raisar itama bacin ya dauketa ta gaji baiwar allah bazata iya zuwa dakin da kanta ba

Ilham ta dan zaro ido aman ba damar tayi magana

Ya mike ya dauki Afane ya nufi dakin Raisa na da ya shinfideta saman bed din ya cire mata kayan na jikinta ya saka mata riga marar nauyi sanan ya fito ya nufi wajen kapet inda a nan yaga Raisa ta dukunkune tana ta barci ya lura ita dai haka koncinta yake , ya dan duka ya dauketa cimak yayi dakinta da ita yana shinfideta ta rike rigarsa kagam cikin barci ita bata ma san tana yi ba
Yayi dan tsai sanan a hankali ya cire hanayenta yayi shiru yana son ya cire mata kayan ya canza mata wani shashe na zuciyarsa ya ce ka guji raini general ka kama girmanka (su girma manya) hakan yasa ya daidaita musu ac din ya musu kofa yana dawowa ya yiwa iyayensa sai da safe ,

Har ya kai kofa ya dawo ya ce " ke Ilham zo nan


Ilham ta tashi da sauri tana zuwa ta tsuguna ta ce " gani yaya


Fuska a daure ya ce " kije ki canzawa yarinyar nan Riga rigar dake jikinta ta matse bazata ji dadin baci ba


Ilham ta ce " Afane? Domin harga allah ita ta dauka Afane yake nufi

Ya watsa mata harara ya ce " AA uwar Afane nake nufi yar rainin hankali Afane din ce sai na saka ki canja mata kaya? Raiisa zaki canjawa ya ja tsaki yayi gaba

Ilham ta ce ikon allah sai kalo


Yau ya kama kwana na shida kenan ana gyaran Raisa masha allah idan kaga tana tafiya saman heels sai ka rantse ka ce ba ita bace sai dai sunyi sunyi su daidaita mata maganar abin yaci tura domin daga an fada mata ga yanda zata rinka yiwa general kawai sai ta bushe da dariya ta ce " abin wani banbarakwai kato a aljanah

Yau suke gama aikin su tun da safe Raisa tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login