Showing 66001 words to 69000 words out of 75972 words

Chapter 23 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Amnoor   

19 Aug 2025

5990

su hakan yasa momy tayi dabara ake hada musu da madara , masha allah madarar kuwa ta karbe su yanzu su momy basu da aiki sai rainon bebys ita da hajiya khadija ita dai Ma tana kula da abincinsu tana murnar irin yanda yaren suke da farin jini , Fareed dai bashi da kuka Fadel ne mai shegen kuka kuma su duka sai suka dauko farin dadynsu


Sunkai minti ashirin suna zaune da bebys a hanunsu Irfan ne da Awatif sai wasa suke yiwa yaran
Raisa na hango gaban miroir sai tsantsara kwaliya take sai da ta gama ta dauko man lebe ta shafa ta mike ta dauki wasu arnan kananan kaya ta zira wandon irin wandunan nan ne masu lafewa a jiki ta dauko riga itama blue ta saka rigar iya tsatsonta ta tsaya bata sauka ba sanan wandan harda zaga zaga gareshi daga kasa daidai inda ya rike yayi dam a jikinta sai zuba kanshi take ta daure gashinta a tsakiya da blue din ribom dan karami gashin ya baje yayi maseefar kyau ta juya ta kara juyawa cikinta tamkar ba bebys suka Konta a cikinsa ba domin sam bata sha kunu kuma ta samu wata riga da Ilham ta kawo mata ta daure cikin hakan ya sa ya koma ya konta bai zama rusheshen nan ba ta dauko wani takalmi baki mai igiya ta saka bata rufe kanta ba ta fito

Tana fitowa ta hango General da matarsa suna ta yiwa yayanta wasa tayi murmushi a ranta ta ce " daga yau nima zan fara ramawa



To fa shin mai raisa take nufi da zata fara ramawa? Oh ni ma ina son sani ku buyo ni mรป leko๐Ÿ˜ณ
[14/12 17:35] Sage: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_




76

Irfan ya ce " mai kike nufi da bakya so? Meye bakya son?

Raisa ta kara hade rai ta ce " bana so ka tabani please

Irfan ya ce " saboda mai fa?

Raisa ta kawar da kanta ta ce " bana ra'ayi

Wani haushi ya tirnike Irfan ya ce " sai mai dan ban taba ki ba , allah ya sa ba ke kadai ce da ni ba

Raisa ta daga kafada , ya mike da Fareed a hanunsa yayi waje fuskar nan tamkar an aiko masa da sakon mutuwa Raisa ta bushe da dariya ta shiga shating da wayarta

Yana fita ya kama hanyar gidansa da Fareed a hanunsa ran nan nasa a matukar bace , Momy da fitowarta kenan daga kicin da kula a hanunta ta ce " General ina zuwa da yaron?

Irfan ya juyo ya kali momy ya ce " wajenki zan kai shi momy ya mika mata shi ta amsa tana kalon yanayinsa ta ce " lafiya?

Ya kawar da kansa ya ce " ba komai

Momy ta ce " to , yayi gaba har yana buge Babar kujerar dakin , momy tayi wajen Raisa tana zuwa ta tarar da ita sai dariya take shekawa ta ce " to mai aka samu haka?

Raisa ta ce " my momy ba komai

Momy tayi murmushi tana girgiza kanta a ranta ta ce " uhum ke ba komai shi ba komai to allah ya sanyaya muku


Irfan yana shiga ya tarar da Awatif konce saman babar kujera sai gursheken kuka take cikin sasarfa ya isa ya dagota ya ce " haba My awatif mai yayi zafi haka? Haba kiyi hakuri mana kinga gobe sai ki dena zaginta ki rike girman ki komai sai ya tafi daidai

Awatif ta dago jajayen idanuwanta muryarta har ta shake ta ce " aman kana kalo fa tayi min gorin haihuwa kuma kai ka fada mata yanda ka sameni ne?

Irfan ya ce " ni fa ba sakaran namiji bane da zan dauki zancen ki da nata na ringa hada ku kinji KO

Awatif ta ce " kuma fada zakayi min bayan ta walakantar da ni?

Irfan ya lumshe idanuwansa ya jawota jikinsa ya rungume a hankali ya lalubi bakin ya fara kissing nan da nan ya fara fita hayacinsa ina ganin haka na kara gaba ๐Ÿ’ƒ



Bayan sati uku

Duk irin walakancin da Raisa ke shekawa Irfan da matarsa daga yayi zuciya ya fita kawai daga yayi nesa da ita shikenan ya kama tunane tunane har sai ya dawo gidan da niyar yazo ganin yayansa , kuma KO a gaban waye idan dai Raisa ta fice ta gabansa sai ya tsayar da abinda yake ya bita da kalon tsantsar so da sha'awa, ita kuwa duk shigar da zaiyi bata yarda ya kuma tarar da ita da kayan da ya barta ga tafiya tana tafe tana yanga tamkar karta dena tafiyar ,


Dawowarsa Kenan daga office da kayan sojojinsa a jikinsa da bakin glass , jijiyoyin hanunsa sunyi birde birde , daga kan da zaiyi ya hango wani dan uwansu Kabir dan cousin din Dady ne yana taka matatakalar da zata sada shi da baban falon gidan , gabansa ne ya fadi domin ya sani sarai yanzu Raisa tana falo da su momy gata da dan karan saka kananan kaya , ya furta chuiiiit tun karfinsa ya bude motar KO rufeta bai tsaya yi ba ya kama hawa mamatakalar da gudu nan da nan sai gashi ya haye aman ina tuni kabir ya tura ya shiga

Irfan ya ce " oh go ya kara gudunsa nan da nan sai gashi ya tura kofar madubin ba tare da ya Dana an zo an bude masa ba , yana shiga duk suka mike da alamar tsoro a fuskokin su domin duk da kwananan yana dawowa gida da wuri ranar da ba aiki aman bai taba shigowa da gudu haka ba ga yanda jijiyoyin jikinsa suka mimike, ya nufi wajen Raisa bai ma tsaya sauraron abinda Momy ke fada ba ya dauki Raisa cimak yayi dakin momy da ita


Raisa cikin inda INda ta ce " General lafiya?

Momy da ta biyo bayansa ta shiga bubuga dakin tun karfinta ta ce " Kai yaron nan ka bude mana kofa mana , lafiya?

Irfan da ya dire Raisa saman bed ya juyo a hankali ya ISO daidai kofar ya bude sai ganin su momy yayi sunyi cirkoy cirkoy da jariran a hanayansu yanayin yanda momy ke muzurai ya bashi dariya aman sanin idan ya dara zata kwada masa mari ne ya saka yayi shiru

Murya kasa kasa ya ce " momy ba komai

Momy ta dunkula hanunta ta nuna masa ta ce " gidanku da kai da ba komai din , kaji yaro da rashin kunya? Wani ne ya biyoka?

Irfan ya ce " wani kuma ya biyo ni momy kuma na kawo muku shi ? Ai sai dai nayi jeji da shi

Momy ta harzuka ta ce " to dan gidanku gudun meye kake ?

Irfan ya fito ya ce " my momy tsakani da Allah yarinyar nan ana kalonta da wanan shigar baza'a tsawatar mata ba KO wani gardi ya shigo ya tarar da ita a haka?


Momy ta shiga tafa hanu tana salalami ta ce ::::::::::::::::::::::::







๐Ÿธ
[14/12 17:36] Sage: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_





77

Momy ta ce : yaron nan Allah ya shirye ka haba Irfan ba sai kasaka hawan jini ya kama mutun ba ? Kuma wly kar ka dakar min ya

Irfan ya ce : aa momy bazan dakar miki ya ba

Ma tayi gaba tana dariyar tsoratar da suka yi Ashe ma ba wani abu bane ta yiwa Allah godiya ashe zata ga ranar da Irfan zai nunawa Raisa so? Komai idan kayi hakuri zaka ci ribar sa ,

Momy ta juya da Fadel a hanunta tana jijiga shi tana ta mitar Irfan na son ya hadata da hawan jini , tana tafiya Irfan ya koma dakin na momy inda ya tarar da Raisa zaune sai kikifta ido take a hankali ya matsa kusa da ita ya zauna

Raisa ta dago idanuwanta ta sauke su a fuskar Irfan sosai tayi missing din mijinta horon nasa da take fadin tana yi har ita kanta take horawa ta kawar da kanta

Ta kuma dagowa suka kuma hada ido hudu da shi ta ce " GENERAL tamkar kishi nake hangowa a idanuwanka, shin shima yana cikin basajar ne?

Irfan ya lumshe idanuwan sa ya kamo hanayen Raisa ya dora daidai zuciyar sa , bugun zuciyar tasa da sauri da sauri ne ya ce " kin san tunda nake a rayuwata zuciyata idan naji tana buga min da sauri da Sauri to abin da ta gani ta buga min haka ba karamin abu bane , Raisa kinsan mai yasa bana son kalonki cikin ido KO ke ki tsare ni da ifanuwanki?

Raisa ta girgiza kanta ya ce " abinda yasa shine idan muka hada idanuwa da ke sai naji zuciyata tamkar zata faso kirjina ta fito , tun lokacin aurena da Mahaifiyar Affane zeinab a ranar diner da kika zo da wando da riga a jikinki wa'inda Pa ya saya miki su masu kyau sai kika kai aka yayaga miki su a ranar muka hada ido hudu da ke gabana ya yanke ya fadi hanayena har karkarwa suke na fadawa Zeinab tun daga ranar idan nace mata ni har yanzu na kasa gane shi so din nan da ake fadi sai naga Zeinab tayi murmushi ta ce " tabas kana so , sai dai a yanzu koyayar abinda zuciyar taka ke so ta rinjayi soyayar ta , ni kuwa sai nayi dariya na ce " wanan ai shirme take , RAISA kina tune ranar da kika fara zuwa office dina a matsayin bodyguard dina kika tarar da ni ina shan giya?

Raisa ta gyada kanta tana kalonsa

Ya kuma yin murmushi ya ce " to a ranar Dady yayi kirana ya ce min ga amanarsa nan zaki zo ki zama bodyguard dina domin bai yarda kije cikin wasu mazan ba gwara dan uwanki

Na ce " dady please kar ka hadani aiki da ita , mace ce kuma kasan sarai yanayin aikina akoy hatsari sosai

Dady ya ce min " Irfan ka sani wanan yarinyar amana ce a wajena sanan ta fiye min kai don haka idan kana neman faranta min rai to ka rungumi yarinyar nan , jin haka yasa na ce OK insha allah , kuma kinsan wani Abu ? Ba komai ne yasa na nuna kin amincewa ta da zama waje daya da ke sai tsoron faduwar gaban da take riskata a duk lokacin da muka hada ido

Raisa tayi saki tana kalon sa ta ce " to aman mai yasa kake hantara ta ? Mai yasa kake tsayar da ni ba aikin komai zanyi maka ba nayi ta tsayuwa har lokacin tashinka? Mai yasa baka taba yi min murmushi ba ? Mai yasa na zamto tamkar makiyiyarka?

Irafan ya rufe mata baki ya ce " My Raisa abinda yasa nake tsayar da ke ba da wani dalili ba shi ne ina son na gano ne menene yasa nake tsoron idanuwanki domin ni a lokacin har cewa nayi KO dai ke aljana ce , idan kina cikin aikin ki ni kawai kalonki nake don na gane meye ya banbanta ki da sauran mutane ? Abinda ya fara bani mamaki sai ranar da kike magana da sergent din nan mai tsaron bangaren office dina naji wata irin tsanar sa da wani irin haushin ki tun kafin a daura mana aure
Kuma abinda ya kara bani mamaki sai da dady ya fada min ya aura min ke na kasa yi masa musu duk da wani sashe na zuciyata na ingiza ni da kawai na nuna bana so , aman son abin yafi rashin son sa yawa , sai na dangata hakan da kawai ina son yiwa Dady biyaya ne kuma bana son Ma tayi kuka

Raisa tayi murmushi ta ce " GENERAL mai yasa baka son yawan yin magana ne?

Irfan ya ce " haka Allah ya halice ni aman a gaban ki har mamaki nake idan na fara zuba sam bana gajiya

Raisa tayi murmushi ta sada idanuwanta kasa stil hanunta cikin na Irfan ta ce " General Kenan har yanzu idanuwan nawa baka son gani ?

Ya dago fuskarta ya ce kaleni

A nitse ta dago tana kalonsa , ya ce " a yanzu na gane cewar nima soyayace ta kama min zuciya ba wai idanuwanki kadai ne ke hargitsa min tunanina no ke gaba dayanki ne ke daukar hankalina kaunar ki ce ke rikitani a da ban gane ba ga kuma kunyar ni da girmana da shekaruna na tile a wajen kanwata aman daga baya na gane cewar sai fa da ke zanyi

Raisa ta juya idanuwanta ta ce " kana nufin a yanzu ka yarda kowa ma ya gane cewar kana son bodyguard baka yarinya ?

Irfan ya jawota jikinsa ya lumshe idanuwansa ya ce " tabas ni Irfan na yarfa Cewar *Duk KARYAR KADA TA RUWA CE*

Raisa ta kara rungume shi a hankali ta furta *I LOVE YOU*

Irfan ya dagota da Sauri ya ce " Really?

Raisa tayi murmushi ta daga kanta
Ya ce please ki kara fadi

Raisa ta rufe idanuwanta ta ce " i love you

Irfan ya ce dan Allah ki kaleni cikin ido ki fada min dan Allah

Raisa ta samu da kyar ta hada idanuwanta da shi cikin wata irin murya Wace ita kanta bata san tana da ita ba ta ce " *BEBY you know, you are the air that i breathe life that's in me, Beby you know , you are all that i need you give me everything, each time i see you my heart starts to pound, you'r all i need, you give me eveything, make me complete, ta hade hanayenta ta ce please love me*

Irfan da ya sandare yana kalonta ji yayi tamkar ba a duniyar ba yake da haka yake shi so din nan ya jawota da karfi jikinsa ya shiga kissing dinta tana mayar masa fadi yake i love you , i love you my wife itama tana fadin i love you my GENERAL , irafn ya kama bale mabalin rigarsa nima na bala da gudu tun kafin a bala aiki a gabana momy ta bala mu








๐Ÿ˜ƒ love u๐Ÿ˜ƒ
[14/12 17:36] Sage: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_




78

Gaba daya Irfan nema yake ya zarce gona da iri Raisa tayi gagawar dakatar da shi ta hanyar fadin " my Being stop stop please

Irfan ya dago shanyayun idanuwansa ya ce " please my life ki barni mana ki tuna fa shekara guda harda yan kwanaki rabona da ke fa please

Raisa ta kara rike shi ta ce " please kaga fa a inda muke kuma ni da nake wankan jego

Irfan yayi murmushi ya ce " Madame kin manta tun washe garin suna na tarar da ke kina sallah har nayi tambaya Momy ta ce wai ai ana sallah idan ana jego tamkar wani yaro karami

Raisa tayi dariya tana mayar masa da botiran rigarsa ta ce " my Being i love you so much aman bazan yarda a nan ba

Irfan ya marairaice ya ce" to mu tafiyarmu gidanmu dan Allah beby

Raisa ta zaro ido ta ce " tap hahhh momy ta yankani kake so?

Irfan ya ce wanan fa ba fadar Allah bace taya ina bukatar matata kawai a hana ni wly idan bakizo gareni ba zan iya mutuwa kar kice ban fada miki ba ,

Raisa tayi shiru tana kalonsa a ranta tace kai Irfan ba kunya , aman a fili ta ce " please an kusa gamawa fa

Irfan ya hada rai ya ce " ni dai na fada miki kuma karki fito a haka sai wanan garjejen ya bar gidan nan ya mike yayi gaba , Raisa ta bishi da kalo tana mamakin halayar Irfan fushi fa yayi ta mike tana canza kayanta ita kadai tana ta mita


Wasawasa har dare yayi Irfan bai shigo yaga yara da Raisa ba , sam Raisa ta rasa sukuninta tsoronta daya kar aje ya mutun , kuma abinda ya fada ya tsaye mata a ranta da yace ai ba ibada bane ,

Momy ta kaleta ta ce " bebyn momy yau baza'a konta ba da wuri?

Raisa tace " Em am em Momy bara naje na konta

Momy ta ce " lafiyarki kuwa?

Raisa ta ce " ba komai momyna tana kokarin kakaro murmushi , momy tayi gaba tana gyarawa yaran konciyarsu a saman dan gadansu

Karfe daya daidai gaba daya kowa yana sheka bacinsa banda Raisa da ta rage hasken waya tana ta Kiran number Irfan aman baya dagawa tayi tayi shiru sam baci ya gagari idanuwanta hankalinta ya kasa konci a hankali ta dan haska Momy taga tayi nisa a bacinta hakan yasa ta sauko a hankali ta dauki takalmanta a hanu ta fito
Cikin sanda ta ratsa har ta isa dakinta ta tura tare da bismillah ta shiga ta dauki peper da biro tayi rubutu a farar takarda ta aje a nan saman bed din , ta tsuguna kasan bed din nata ta jawo jakarta wace ta bari a nan ta wajen aiki ta bude ta ciro igiya mai karfe a jiki ta zira takalmanta daman kayan baci ne a jikinta riga da wando ta daure gashin kanta ta saka hula ta rataya karfen a jikin windows ta bude windows din kawai sai ji nayi tayi wani fito fiiiifit na zaro idanuwa ina tunanin wai mai Raisa take nufi ne? Kafin na gama tunanina sai gani nayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login