Showing 51001 words to 54000 words out of 75972 words

Chapter 18 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Amnoor   

19 Aug 2025

6014

suma dan wuya momy tayi rungumeta tana rusa kuka wiwi tamkar ance mata Dady ya mutu

Dady da ransa ya gama bace ya nuna Irfan da yatsa yace" ashe baka da mutunci? Ashe kai butulune? Ashe baka san darajar aure bâ? Sanan baka san darajar maraya bâ? Kai zaka bata min aikin ladan da nake son tsira da shi? Ashe kai mahaukacine? Irfan tir tir da zuciyarka sam ba zuciyar musulmai bace irfan bakayi hali mai kyau ba , ai sai kace min kai Muhammad auren nan fa daka daura min bana so sai kaga idan har ban raba ba , aman ka rasa wanan kokarin ma sai dai ka kashe min yar amana? To walahi baka isa ba ina jiran takardar sakinta ka rubuto ka kawo min tun kafin na tsine maka sanan na rufeka banza marar imani ya juya ya ce " Hajiya Sajida tashi muje kamata mu tafi


Momy ta tashi ta kama Raisa Wace kanta yake mugun juya mata hajijiya tamkar zata kife ta juyo ta kali irfan Wanda yake binsu da kalo ya kasa furta komai ta zabga masa harara muryarta na rawa tace" bakayi min adalciba sanan baka yiwa kanka adalciba, bazan furta maka muguwar kalma ba na barka da dadynka tunda kake bai taba neman alfarma wajenka ba sai wanan Karin aman ka watsa masa kasa a ido yau yayi fushi da kai abinda bai taba yi ba , ni kuwa nayi hawaye dalilin halayarka allah ya shiryeka Irfan

Irfan hankalinsa ya tashi , yayiyayi kuka yazo ina ya mike ya kama kafar dady , dady ya buge hanunsa yayi gaba abinsa , momy ma ta kewaye shi ta ficewarta ,
Irfan ya kuma mikewa da niyar ya bisu sai ji kake Jim ya yanke kiki ya fadi kasa sumame










To fa shin irfan zai samu lafiya bayan ana kokarin rabashi da macen da ya fara so a rayuwarsa ga kuma fushin iyayensa da fir suke fushi da shi? Shin zai saki Raisa ne KO kuwa Elhaj Muhammad Ibrahim sai rufe shi ne? Wai ya wajen Raisa zata iya jure rashinsa bayan ta kamu da sonsa ? Kumuje 😲😲😲😲92245338😲😲😲😲😲😲😲
[20/7 12:59] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_




62


Raisa ta dago kanta idanuwanta suka sauka saman idanuwan Irfan Wanda suka rikide kalar ja tamkar an watsa masa barkono gabanta ya fadi ganin Irfan ya zaro bindigar dake jikinsa ya saita kan Imran , bata san sanda tayi kukan kura ta fada saman kansa ta damke bindigar suka shiga kokowar sai ya harbe Imran ita kuwa ta dane allah ya bata sa'a ta jefar da bindigar ya juya da Sauri ya dauki wayar sa lokacin tuni jami'an tsaro sun zo suna tambayar KO lafiya suna famar kama shi

Irfan ya bude bakinsa zaiyi magana aman ina ba hali domin inda indar sa tayi mugun tashi gaba daya jikinsa rawa yake ya juya cikin motar ya fitar da takarda da biro ya hau rubutu kamar haka da turanci *Mustapha maza ka dauki wayata ka kirayi yusuf su shirya zamu koma Nigeria yau yau din nan* ya mikawa Mustapha Wanda ya tsaya kwatantawa jami'an tsaron cewar ba komai bane ya nuna musu carte dinsa ta shedar KO shi waye sanan suka watse aman suka ja Imran don kar General ya kashe shi,

Da gudu Mustapha ya dauko wayar ya danawa su yusuf din kira ya fada musu umarnin General nan da nan kuwa suka fara haduwa don komawa Nigeria inda shi kuwa ya tsaida adaidaita ya nufi masaukinsu don ya taho da baba tsohuwa


Irfan ya juyo inda Raisa take yashe tunda ya jefar da ita ya tako cikin karkarwar jiki ya dauki Affane ya juya ya nufi mota , ganin hakanan ya saka Raisa ta tashi da gudu itama ta shige motar gabanta sai faduwa yake ta rasa gane me ke faruwa ne?


Tunda jirgi ya tashi gum kake ji ba mai magana baba tsohuwa tana ta al'ajabin allah yayi dawowar su Nigeria bayan har ta fida rai sai dai tana tsoron dawowar tasu domin da alama iyayen gidan nata ransu a bace yake

Shi kuwa Irfan yana gudun yin magana ne a gaban yaransa ji yake tamkar ya rintse ido ya gansa a Gida domin yarinyarnan ta bashi amsa shin wa take so? Har yanzu tana son Imran ne? Shi bai isa namijin da zata soshi ne? Yana son sanin ina zuciyarta ta dosa ? Shi kadai sai huci yake

Ita kuwa tana tunanin lale lale général ya fiya son kansa da yawa inba son kaiba taya kai ka dauko mace tazo gida ta zauna a matsayin karuwar ka , karuwarka mana domin ba Wanda ya aura maka ita ni ina ji ina gani ba dare ba rana kulun ta allah kana tare da ita a daki guda bansan mai kuke aikatawa ba hasalima KO a gabana kana rungumarta KO a gaban baba tsohuwa ne ban taba ce maka ufan ba sai ni da ba'a haliceni da zuciya ba KO? Aman yau dan na hadu da tsohon mijina ina mamakin ganinsa har ka daga hanu ka mareni? To walahi bazan yarda ba allah ya kaimu gidan lafiya tunda dai Ma tace bata yafe min ba idan na bude bakina na cewa su momy su raba auren nan to ni zan bar muku gidan ku nayi tafiyata Afane ce na rinka lekawa School dinsu ina ganinta Ma kuwa na rinka kiranta a waya tunda ta dena sona


Karfe biyar na yama jirginsu ya sauka a birnin Abuja suna saukowa Irfan ya amshi ky din motar da za'a kaisu , kowa mamaki yake General zaiyi tuki?

Suna shiga bai tsaya an saka kayansu ba kawai ya figi motar sai da baba tsohuwa ta gwara kanta da madubin motar ta kuwa ce " Annabi Muhammadou ka ceceni ni gambo yaron nan karka kasheni dan allah


Irfan yayi banza da ita shi dai burinsa ya ganshi a cikin gida, duka duka tafiyar minti ashirin sukayi sai gasu a Gidan Mr Président sojojin dake tsaro duk suka Mike suna Sara masa shi KO ta kansu bai bi ba yana yin parking da motar ya bude gefen da Raisa take zaune ya damko hanunta kiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆











😘
[20/7 12:59] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_



59

Ina Mika gaisuwata zuwa ga Maman yusrah allah ya jikan baba

Ina jinjina ga duk mai suna *IBRAHIM* ba na biyunka

*Exclusive writers's forum* love you


Ci gaban labari
Irfan ya dauko abincin a saman dan karamin teburi 🍱 ya nufi dakin nata yana turawa ya hangeta saman kafet ta dukunkune a hankali ya karasa ya ajiye abincin ya Mika hanu ya dan taba wuyan ta , ta tashi tana kalonsa da marayun idanuwanta masu kama da kamar Wace zata rusa kuka

Murya kasa kasa yace"" ga abincinki Raisa

Raisa ta dan juya kanta a hankali ta ce " no na koshi GENERAL

Bai kulata ba ya bude kular ya dauki plat guda ya zuba dan abincin sai miyarta cuscus ya gyara zamansa ita dai tana binsa da idanuwa ya dauko a cokali ya kai bakinsa ya tauna ya hade har yana tande baki ya dago sukayi ido hudu da shi yayi murmushi har hakoransa suka bayana RAISA tayi kuri tana kalonsa , daman haka murmushi yake yi masa kyau? Kai aman gaskiya IRFAN allah yayi masa kyau sosai

Irfan ya ce " kinga naci bai yi min komai ba walahi bazan yi empoisonner ki ba so ki bude bakinki kawai na ciyar dake KO kuma na dura miki kuma na kwana a nan

Raisa ta zaro idanuwanta a cikin ranta tace tap wanan ai shine fin karfi to aman ina ruwansa da cin abincina? Ni fa bana son shishigi

Irfan yayi tsai yana kalon lebenta yanda ta fara motsa shi da alama tana zancen zucin ne yayi murmushi yace bismillah madame

Ba yanda ta iya domin itama yunwar na mugun damunta hakan yasa ta mayar da hankalinta taci abincinta shi kuwa ya sakata a gaba kamar TV yana lure da dukan motsinta da yanayinta komai nata kawai birgeshi yake ( da baya ba )

Sai da ta gama ya dauka ya dora saman teburin ya juyo yana kalonta , a jikinta taji cewar fa ya tsura mata idanuwa hakan yasa ta dago kanta suka hada ido hudu a hankali


ya ce *I LOVE YOU*


Saï da gaban Raisa ya fadi muryarta na dan karkarwa tace *Bazan taba yarda ba*

Ya duko ya mana mata kis a kuncinta ya ce *BELIEVE ME MY ANGEL*

Raisa tayi murmushi ta ce *NEVER MY HUSBAND*

Sai da ya kaleta da kyau yace " Kenan kin yarda i'm ur husband?

Ta ce " eh Nasan da wanan tun ranar da IMRAN ya sakeni dady ya daura maka ,

Ya ce " yes dady ai ya iya zaben miji ne

Raisa tace " dady bai san mai ya zaba ba domin shi bai san halayar yaron Ma ba

Yayi murmushi ya ce " koma dai meye halayar yaron Ma ya kamu da soyayar yar gidan MOMY

Raisa tayi dariya tace" ya kamu dai da soyayar wani Abu


Ganin bazata yarda da soyayar tasa ba ya juya a cikin ransa yana fadin ai KO shekara zamuyi a garin nan sai dai muyi wly sai kin soni ( ikon allah ?


Konci tashi wasa wasa satin su Irfan Uku a kasar indiya kuma kulum ta allah sai irfan ya kunsa mata takaici shi da marry domin baya tashi jayo Merry jikinsa sai yaga Raisa yana kule da dukan motsinta da dukan abinda take aikatawa a cikin gidan sanan abin haushi yanzu ta koyi boye fushinta sam bata nuna masa sai dai ta shiga daki ta shan kukanta ta wanke idanuwanta ta fito hakan na cutar da shi


Nigeria

Momy ce zaune ta saka Mr president gaba tana ta rigimar kawai a kira mata yaron nan taji lafiyar yarta


Elhaj Muhammad ya nisa ya ce" momyn yara na fada miki lafiyarta lau wai yama za'ayi su fita da mijinta kuma kice a maidota?

Momy ta ce " aa ni so nake nasan inda suke


Elhaj Muhammad ya Mike sai da ya kusan shiga bayi ya juyo yace suna *INDIYA* yayi shigewarsa ya barta wangalau da baki tana mamakin irin rainin hankalin Irfan (sowie momy irfan fa ya fada?

Haka ta dangana a cikin ranta tayi ta adu'ar allah dai ya hada kansu sanan allah yasa karya wulakanta mata Raisa

















Love u all
[20/7 12:59] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_





60

Raisa ce zaune gaban madubi ta kai minti ashirin tana gyare gyaren jikinta taba nan goge can shafa wanan caje wanan tana shirin fitar da zasuyi ita da Irfan da merry da Afane suna shirin tafiya restaurant daga nan su fice boutique suyi sayaya

Raisa ta ja tsaki ita kadai tace " ai wly yau nima sai nayi adon nan badan ban iya bane ba fa kawai dai don a zatona aiki ya kawomu tunda sha'aninka ya kawoka ai nima sai na dan cashe yau har sati hudu a garin da ba namu ba kuma fir ka hana mu ganin iyayen mu itama matar taka KO irin ka nemeta a waya haka kawai salon cin mutunci ? To da na zauna bakin cikin ku ya kasheni gwara nima na dan cashen
Ta gama kwaliyarta ta mike ta bude babar akwatin ta domin bata juye kayan cikin werdrob ba duk a ganinta zasu koma da kowani lokaci, ta shiga dadagawa tana watsa su a kasa domin babu atamfa KO lesh ko yadi daga wando da riga sai doguwar riga sai sket da riga hakahaka dai ta rasa wane zata dauka kawai sai ta dana kiran baba thohuwa tana zuwa ta dauko riga da wando rigar ja wando baki ta Mika mata tace" Baba ki sakawa beby wanan duk bamu zo da kayan hausa ba gashi kuma zamu fita

Baba ta amsa tace" to yarnan an fara sanin saka kayan hausa , allah dai yasa ki tsani na turawa

Raisa ta ce " ba amin ba baba

Baba ta fita tana dariya a ranta tana adu'ar allah ya shirya tsakanin yarinyar nan da Irfan domin yarinyar akoy shiga rai

Bayan fitar baba ta Mike ta dauki wando dogo har kasa baki mai santsi ta saka ta jawo rigarta ja itama ta dora a sama ta fitar da hula baka domin yanayin garin ta dora a saman kanta sanan ta zira kafafuwanta a wasu mahaukatan takalma jajaye masu shegen kyau sanan da dan tsayin su kadan , ta saka dan kune masu dan tsayi aman siraru ne ta kara goga man lebenta ta dauko riga baka ta sanyi wace zata dora a saman jan ta kuma dauko ta yarinyarta ita kuwa ja mai shegen kyau ta fito da takalman Afanne a hanayenta kafa ciki da sapa fara ta fito

Tana fitowa ta tarar da AFANne sai kokowa suke ita da dadynta taki tsayawa ya saka mata kayan , tun da yaji kanshin tirarenta ya dago kansa yana kalonta a ransa yace oh ina zataje a haka?

Raisa ta karaso ta karbi pant din a hanunsa ta ce " bebyna zo na saka miki mu tafi mu sayo beby barbie mai magana ,

Tana jin haka ta tafi da Sauri tana ta washe hakora ta fada saman cinyar Raisa ta saka mata kayanta ta dora mata ta saman tayi mugun kyau shi kuwa ya shagalta yana ta kalonta sai da Raisa ta ce " ina matarka mu fice

Ya kaleta galala yace"" ina zaki fice a haka?

Raisa ta kali kanta ta ce " su kadai muka kawo idan mun fitan sai na sayi abaya na dora

Irfan ya ce " ohk muje ita ta dade a mota

Raisa ta mike ta fice gaba ta dauki Afane domin yanzu bata da waya tun da ta shiga kasan panpo ruwa ya jikesu suka lalace


Shopmarly kriss

Banban boutique ne dake kasar indiya Wanda babu ne kawai babu tun daga kayan mata , maza, yara , manya, kayan wasa, kayan ado , babu ce kawai babu sai dai shegen tsada domin idan kaga mutun ya tsaya to baban mutun ne Merry sai murna take domin tunda uwarta ta haifeta bata taba tunanin zata shiga wanan boutique ba gaskiya tana murnar haduwarta da Mester love (to kaji master ashatarki)

Suna tsayawa Raisa ta bude ta fito da yarta a hanunta su kuwa su Irfan suka tsaya suna tataunawa bata san kan me suke magana ba ita dai tayi gaba abinta tana jin dan jiri na dan dibarta , tana tsakar tafiya takalmin Afane ya fadi ashe bai dauru da kyau ba ta duka ta dauka tana tafe tana daura mata sai ji tayi ta bangaji mutun wayar hanunsa ta fadi kasa suka duka tatare suka duka ita da niyar ta dauko masa tana fadin sorry shima da niyar ya dauko abinsa hanayensu suka hade da Sauri ya dago kansa yana kalonta itama bakinta na karkarwa ta nuna sa tace " *IMRAN*


Imran ma cikin Sauri ya ce *RAISA* my RAISA

Raisa tayi Saurin kalon gaba da baya tace " mai mai kake yi a India ? Kayi aure ?

Imran kawai kalon ikon allah yake yi Raisar sa ce ta zama haka tayi wani irin freich da ita fatar ta har wani sheki take yi gashi ta saka maskara a idanuwanta idon sai ya gama rikita shi ga bakinta yana shekin man leben da ta shafa ya lumshe idanuwan sa yace my Raisa

Ita kuwa mamakin ganinsa a nan da tayi ya saka ta matsa ta daga hanunta ta shafa gefen fuskarsa irin yanda suka saba kafin a daura musu aure ita duk dan ta gaskata cewar idan shi din ne shi yasa ta shafa gefen fuskarsa shi kuwa ya lumshe idanuwansa yana ajiyar zuciya sai ji sukayi Tau tau an dauke Imran da wani wawan mari Kafin Raisa ta Ankara sai ji tayi itama a kuncinta gaba daya komai ya tsaya mata ta saki afane tayi tsam wuta ta dauke mata sam ta dena jin komai idanta yayi mugun ja tayi tsaye tamkar gunki tana kalon Wanda ya zabga mata marin nan







Kakakarakaka shin waye ya mari Raisa da Imran? Shin za'a kyaleshi? Wai jama'a Raisa ta kurumce ne KO me? Shagali



92245338
[20/7 12:59] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_



65


Allah ya barmin ke my lovely *AMAL* this page's for you ❤❤


Labari
Gaba daya dakin suka tsurawa docter Mariam ido suna jiran albishir dinta

Ta mikawa General takardar tana fadin " congratulation Madame na da shigar cikin wata daya da kwana biyu ,

Momy ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login