Showing 57001 words to 60000 words out of 75972 words
Chapter 20 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt
zancen ta ce" Momy mai yake baki dariya ne ? Yaya shin baka jin mai take cewa? Ciki ne fa da ita kuma ta rude Kenan bata san bama KO na wanene? Shegiya mai bin maza ba ga irinta ba to ai sai ki nemi ubansa domin Awatif ta fada min yaya kaloma baki ishe shi ba
Ji kake dau Irfan ya dauke bara'atu da mari , sanan ya jayo Raisa yana goge mata hawayen dake shatata a idanuwanta ya damke hanunta don ta dena karkarwar da takeyi ya nuna Bara'atu da yatsarsa ya ce " ki guji sheganta min mata , ki guji zagin min mata domin yayarki ce , wanan cikin ya shafa cikin Raisa ya ce " nawa ne , cikina ne , raisata na dauke da cikina, kuma ina matukar murna da shi, ina murnar zai kasance tsatson abin sona, idan baki manta ba kwanakin baya muna hira ni da ke nake shaida miki ki kasance cikin matan da basa yanke hukunci saman abinda idanuwansu basu gani ba , tabas ni ne nan ishara domin naji kunya marar adadi a dalilin hukuncin da na yanke kan wanan baiwar allahn, sai da allah ya nuna min wanan ta fiye min mai yawo da dogon hijabi dan munafici, ki sani bara'atu Ina matukar son matata kuma cikiin jikinta nawane idan ma baki dena yi mata kalon abinda kike yi mata ba to mu biyu ne karuwan,
Yana gama yiwa bara'atu bayani ya juyo bagan raisa ya jata a hankali ya zaunar da ita saman gadon ya ce " idan da auranki kin san mai zai faru? Momynki zatayi murna ne, Ma dinki zatayi murna ne , dady zaiyi farin ciki ne , ni banma san yanda zan kwatanta miki irin adu'ar da zan rinka miki ba , sanan duniya zata taya mu murna ne, idan kin mutu za'a sakaki aljana ne so dena kuka karki saka rashin lafiyar ki ta dawo please
Raisa tayi shiru ta dan leka tana kalon su momy Wace har yanzu murmushi takeyi aman Ma ta FITA, ta juyo ta kara kalonsa stilll ita yake kalo , ta kuma kalon momy
Momy ta matso tana fadin su dan bata waje
Irfan yayi kalar tausayi ya ce " momy ☹
Momy ta ce " aa general kuje ka yiwa docter tukuicin albishir dinta ni kuma na gana da yata
Ba dan yaso ba dan Dole ya juya yana takawa a hankali yanayin jikinsa suka fito suka bar momy da Raisa kadai
Momy ta ce """"""""""'"'''""""""""""""""""""""""""
[20/7 12:52] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*
*NA*
_*SAJIDA*_
_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_
66
Momy ta shafa fuskar Raisa tana ta murmushi ta ce " allah yayi miki albarka yata allah ya raraba lafiya, aman beby in tambayeki mana
Raisa ta ce " to
Momy ta ce " wai idan kinje islamiya mai ake koya miki?
Raisa tayi shiru sanan ta ce " momy idan an gama karatu nayi hardana idan za'a fara wa'azi sai in tsere inje in kali su Pa a wajen aikinsu
Momy ta ce " kinyi ahlari da kawa'idi? To ya wajen salarki?
Raisa ta ce " tap kafin Pa ya rasu Ma kulun bata barina tana bibiyar salahna har sai da taga ina yi daidai , idan kuwa Malan ya kawo karar bana yin sauran litatafai bayan alkur'ani Ma tayi ta fada hardai na samu na fasa masa kai
Momy ta zaro ido ta ce " wa?
Raisa ta turo baki ta ce " Momy yo kulun fa sai ya saka Ma tayi ta fushi fa
Momy ta dan girgiza kai a ranta tace " haba ga dalilin da yasa yata ta rikice dan tana da ciki ( tunatarwa , iyaye mata da maza mu kula sosai wajen tarbiyar yayen mu idan mun kaisu makarantar islamiyar mu rinka bin didigin abinda suke aikatawa sanan mu dage da adu'a da kokarin mu har yayenmu su karanci duk wani litafi na adinin musulunci ko da basu hardace shi ba su san abinda ya kunsa domin KO wane da wajen sa , allah ya kama mana amin )
Momy ta ce " to beby kinga gudun karatun nan na sauran litatafai na musulunci su suka saka kike cikin duhu domin komai sai ka karance shi har zaka san inda ya nufa , dan haka idan allah ya baki lafiya Malan mu'azu zai rinka zuwa kuna karatu kinji?
Raisa ta ce " ohk momy insha allah
Momy tayi murmushi tace yawa yar momy yanzu ki kwonta ki huta , mai kike son ci?
Raisa tayi shiru tana tinani abin mamaki ta rasa mai ranta yake so duk irin yanda takeda kwadayi kawai sai ta tuna tana yarinya akoy shan rake da agwaluma taji kawai tana ra'ayin shan su ta kali momy ta ce " momyna agwaluma da rake nake sha'awar sha
Momy ta zaro ido ta ce " a me?
Raisa ta ce " agwaluma
Momy tayi tsai tace " tap ni kam ban san menene agwaluma ba aman bara naje na tambaya sai a kawo miki
Raisa ta ce " momy ni fa wly bana jin komai please muyi tafiyar mu gida
Momy ta ce " bara dai a dan jima bara ina zuwa, ta Mike ta FITA tana nanata agwaluma kar aje ta manta sunan domin momy sam babu ruwanta da ciyeciye gashi ba cikin gari suke ba ita kuwa a sunayen fruits KO légume bata san wani abu agwaluma ba ( haha momy agwaluma dadi tsami )
Bayan fitar momy irfan ya turo kofar a hankali ya shigo ya ya karaso wajen Raisa Wace ta dukar da kanta ya tsuguna daidai kafafuwanta ya dora hanunsa saman cikinta
Ya ce " yaushe cikin zai taso ki fara tafiya kina rike cikin naki kina fadin wash kama min nayi kwana da cikin
Raisa ta bushe da dariya tace " no walahi bazanyi irin na Ilham ba , sai da ta ce Ilham gaban ta ya fadi ta hade hanayenta biyu ta ce " please general ka taimaka karka fadawa Ilham wly zata rama abinda nake yi mata ne
Irfan ya ce " me kike yi mata?
Ta rufe idanuwanta tace ba komai
Ya ce ai sai kin fada min
Ta ce " daman da naga cikinta ya zama katoto ne nace wly sai momy ta kasheta idan ta gani kuma ta nemo mai shi dan kuwa my freind Samir ba dan iska bane
Irfan ya zaro ido ya ce " ke bazaki dena zagiba KO?
Raisa tace " ai sai da na ce maka bâ sai na fada maka ba ka nace
Irfan ya girgiza kansa still hanunsa dai a saman cikinta ya ce " raisa kinji fa yana fadin dady dady
Raisa ta rike baki ta ce " kai yaya kaji tsoron allah
Irfan yace " to Please kiyi shiru karki karasa ( hahaha)
Raisa ta marairaice ta ce " wly yinwa nake ji tun jiya da safe rabona da abinci
Irfan ya zaro ido ya ce " subahanalah mai kike son ci
Ta dan watsa hakora ta ce " agwaluma
General tace " meye kuma hakan?
Ta ce " muje na gwada maka inda ake siyarwa
Irfan ya ce " no ke da ba lafiya gareki ba ?
Tace " ai fa na warke sai dan jiri please mu tafi , kafin ta rufe bakinta sai ji suka yi an banko kofar ba KO salama awatif ce da wani karfe a hanun ta ta nufo Raisa ta daga😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳
92245338
[20/7 12:52] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*
*NA*
_*SAJIDA*_
_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_
67
Awatif ce ta banko kofar ta shigo ta nufo inda su irfan ke zaune da wani karfe a hanunta ta daga zata rafkawa Raisa allah yasa irfan ya tare ya sauka a hanunsa da sauri ya mike ya riketa gam ta fasa kara ta cakumeshi cikin karaji tace" ka barni, ka barni na halakata yar asara , Ashe aikinta Kenan? Shine daga ta gani kana kissing dina har tofar da yawu take Ashe munafukar so take itama ? Ashe sonka take?
Raisa ta mike ranta a bace tace" ke jahila marar tunani , to ubanwa ya fada miki sonsa nake ne? Ni ba wani sonsa da nake sai tausaya masa da nake, ki tambaye shi na taba furta masa kalmar so? Ki tambaye shi
Irfan ya ce " Raisa enaugh kinji? Ya ishe ki taya zakina bada bada da ni? Kar ki so nin sai mai? To ni ina sonki dan allah ki mutu idan baiyi miki ba, sai kace wani sa'anki ki saka baki gaba kina ikirarin bakya sona? Ke karki sonin ,
Awatif ta ce " ka cikani , please ka cikani , na koya mata hankali
Raisa ta tafa hanu ta ce " ka cikatan dan allah ka cikatan haba sai kace wata uwata?
Irfan abin duniya ya ishe shi ya ce " duk Wace ta yarda ta kuma bude bakinta tayi min maganar rainin hankali walahi sai na hukuntata , ya hade rai stilll yana rike da Awatif Wace duk ta jike da gumi
Dakin yayi tsit sai ajiyar numfashin awatif ya dan cikata ai kamar jira take ta kuma hayayakowa zata kaiwa Raisa naushi
Ya tareta ya daga hanu ya wanka mata mari
Awatif ta ce " ka mareni? Ka mare ni saboda wanan bakar ? Ka mare ni ? Dalilin wanan shegiyar?
Irfan ya ce " ke ba shegiya bace da ubanta , kuma cikina ne jikinta
Awatif tayi dif tana kalonsa jikinta yayi wani irin sanyi ta dago kanta ta tsuwara Raisa ido bakinta na karkarwa ta ce " ciciki? Ciki kayi mata?
Irfan ya kauda kansa ya rasa amsar mai zai bata
Kawai sai ji sukayi ta kwala kara ta mimkyar sumamiya irfan ya zaro ido ya kali Raisa Wace itama shi take kalo
Ya ce " ta suma fa
Raisa ta daga kafadu irin bai shafeta ba
Ya zaro ido ya ce zo ki kama mini mu dorata saman bed
Raisa ta kuma zaro ido ta ce " ni na aura maka ita ne? Kawai ka kama abinka ta juya ta zira hanayenta a aljuhun wadonta ta kama hanyar tafiyarta cikin gidan Momy
Da kyar ya samu ya shinfideta yana sakin lunfashi ya dauko ruwa ya shafa mata a hankali, ya kuma shafa mata firgigit ta farka tana sakin nunfashi , ta kare masa kalo kawai sai ta fashe ta kuka wiwi tana yi yana kara riketa yana bata hakuri da kyar ya samu ya rarasheta ta dena kukan har sai sun je gida
Docter Mariam ta shigo dan ta kuma duba lafiyar Raisa da Irfan sai ta tarar suna zaune shi da awatif
Irfan ya ce " docter gida zanje na samu lafiya
Docter Mariam ta ce " general bazai yiyu ba har sai mun kuma dudubawa idan ba wata matsalar sai ka tafi domin rashin lafiyarka bata son tashin hankali KO bacin rai
Irfan ya yamutsa fuska ya mike yayi gaba abinsa yana fadin zan dawo domin yanzu akoy abinda yake gabanta
Ba yanda docter Mariam ta iya haka ta cire karin ruwan ta fitar da su a ranta tana al'ajabin auren Raisa da Irfan , sanan tana jiran ganin cikin Raisa ya fito idan har bata barar da shi ba a yanda take komai na maza ( ni ma ina tsoron hakan docter)
Falon momy
Zaune suke sai zancen cikin raisa suke kowa na al'ajabin hakan sai gata ta shigo tana isowa daidai babar kujera maimakun ta kewaya ta hau ta zauna kawai sai ta kama ta dira sai gata zaune tsakiyar Hajiya khadija da anty leilatu
Gaba dayansu suka kwashi salati Momy harda dora hanu a kai
Raisa ta zabura tana waiwaya bayanta domin ita tayi zaton KO irfan ne yazo ya daketa don taki kama masa matar sa su shinfida saman gado bayan tayi sumar karya ( kujifa raisa ana sumar karya ne daman? )
Momy ta kamota ta zaunar da ita su duka suka tsura mata ido
Anti leilatu ta bushe da dariya ta ce " to fa abin yazo ga gwanai kukan aure da salalami , yar momy da ciki
Raisa ta kaleta ta turo baki ta ce " momy wa ya fada mata? Ba kin gani ba shi yasa nace kar a fada musu yanzu zasu fara rama abinda nayi musu shi kuwa ba kyau rama Abu KO momy?
Momy ta gyada kai ta ce " yar gidan momy bani hankalinki nan sauraran ni da kyau
Raisa ta nutsu tana kalon momy
Hi 😆
[20/7 12:52] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*
*NA*
_*SAJIDA*_
_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_
68
Momy ta ce " beby kinsan wani Abu, yanzu muka gama jajan wata baiwar allah da ta mutu da ciki
Raisa ta zaro ido ta ce " mai ya kasheta
Momy ta ce " kawai ciki ta samu akace tana da ciki kawai saï ta tashi tana ta tsale tana murna , kawai cikin ya fara zubar da jini aka kaita asibiti kafin a isa har ta mutu
Raisa ta sauko kasa a hankali har tana bismilah tace " momyna dan allah a cire min shi kar ya kasheni nima dan allah bana son barin yarinyata , idan na mutu wa zai kular min da ita? Wa zai rinka Goya min ita? Matar ubanta bata daukanta ku kuwa kun tsufa dan allah kar na mutu yanzu
Momy ta kauda kai ta galawa anti leilatu harara domin ta dage sai dariyarta take kwasa ita kuwa Ma takaicin duniya duk yabi ya isheta ta rasa Wace irin sakarar ya ce wanan sam bata da tsari bata san komai ba
Momy ta ce " beby ai Babar matsalar idan akace a cire shin domin kuwa gwara alburushin ku ta yiyu ya bar mutun ya dan kali masoyansa , to shi idan za'a cire miki ciki kawai KO harbawa bazaki yi ba zaki mutu, kuma kije kiyama allah ya hukunta ki
Raisa tayi wani tsuru kamar ruwa ya daki kaza ta ce " baza'a fitar da shi ba kawai a bar shi
Momy ta ce" yawa ai kuma ba barin nashi ba , kinga ko wajen aiki kika je karki yarda ayi kokowa da ke, karki yarda fada ya hadaki da wani , kar ki yarda ki rinka tsalake tsalake , sanan kar ki kuma biyowa ta windows domin kina iya barin cikin a baya shi Kenan kema sai ki mutu
Raisa ta daga hanunta kamar idan ana shara'a a kotu idan mutun zai rantse yanda yake daga hanunsa ta ce " insha allah duka bazan kuma ba
Momy tayi ajiyar zuciyar nasara sanan ta ce " KO je fa bebyna allah kare ki
Raisa ta ce amin , sanan ta Mike a hankali tana kokarin zaunawa saman kujera a hankali har tana bismillah daidai nan Irfan ya shigo yayi kasake yana kalon kuma wani savon salon
Momy tayi masa alamar kar ya tanka , ya kuwa kawar da kansa ya ce " am momy yarinyar nan wai gwaluma take so
Anti leilatu ta yi dariya tace " general agwaluma yake , kuma fa ba abinci bane , kamar tsamiya yake sai tsamin tsiya
Irfan ya kaleta ya ce " what ? Tsamiya fa kika ce? Ba ita bace tamarind?
Leilatu ta ce " eh itace
Ya kali momy ya ce " am momy kar a sayo mata ita a sayo mata wani abin domin ita tana iya lahanta bebyn dake cikin
Momy ta kama haba ta ce " to baba ka gama? Au ni zaka koyawa kar taci kaza kar taci kaza? Dan gidanku sai ta cin
Irfan ya juya ya kali Ma , da niya yayi ya ce taga Momy KO? Kawai sai ji yayi wani irin nauyin Ma.ya darsu a cikin ransa, hakan yasa ya juya kansa ya ce " Raisa taso muje na saka a dafa miki abinda kike so
Raisa ta zaro ido harda kara turo hular dake kanta gaba ta ce " an gaya maka bani da hankali? Bayan yanzu na gama yi maka musun bazan kama maka matarka ba mû dora saman bed kuma yanzu saï na tashi na bika salon ka dirki banza ba idanun momy KO? To bazan je ba
Momy ta ce " mai ya samu Awatif din?
Irfan ya dan Sosa kai ya ce " aa kawai ta dan buge ne
Raisa ta zaro ido ta ce " ka fadi gaskiya a rayuwa koda kuwa hakan,,,,,,, kafin ta karasa taji a buge mata baki tayi Saurin rike bakin tana fadin auchhhhhhh
Da Sauri irfan ya shiga dan hura mata iska a wajen ya ce " ba ga irinta ba tashi mû tafiyar mû allah ba zan dake ki ba
Jin ya rantse mata yasa ta Mike suka yi tafiyar su tun kafin Ma ta zubar mata da hakora
Bayan wata biyu da kwana takwas
Cikin raisa ya shiga wata na hudu Kenan idan ka ganta ta dan kara kiba kadan sai wani haske da fatarta take dada yi , cikinta ya dan tasa har tsoro yake bata , zama a hankali tashi a hankali gudun karta mutu, ta kowani bangare ana nan nan da ita , ga shegen shan agwaluma da cin tukeken tuwo, wanan kuwa momy kulun sai ta tuka da kanta gudun kar abinda ya faru da su ya kuma faruwa, idan suna zaune ita da yarta sai Afane ta ce " mamamana cikinki yana walkiya
Ita kuwa sai ta dauki wayarta suyi ta selfi
Ilham ta haihu har suna ya