Showing 45001 words to 48000 words out of 75972 words

Chapter 16 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Amnoor   

19 Aug 2025

6011

naman naka na ka'ida Dadynka kuwa ai kasan tun da safe ya fita aman ya ce zaku hadu a can so bara na karowa yata sakonta

Tana tafiya ya dawo kusa da ita ya ce " walahi idan kika yarda kika yi min wani zancen shirme a nan sai a fasa tafiyar da Afane

Jin hakan ya sa tayi shiru tana fiki fiki da ido ya dan guntse dariyarsa a ransa ya ce oh yarinta

Bayan sun gama yin salama da kowa baba mai rainon Afane ta fito ansha sabuwar atamfa sai watsa hakora take da yar jakarta a hanu ta yiwa su momy salama , momy ta kara damka mata amanar yarta , har sun shiga mota gaba dayansu GENERAL ya sauko rike da wata farar takarda a ninninke a hanunsa ya matsa kusa da Ma ya damka mata ya hada da hanayenta yana kalonta yayi murmushi ya ce *MA* Thank you allah ya biyaki da aljanar firdaus

Ma tayi alamar rashin fahimta ta ce " yarona godiyar me kake yi min sanan wanan takardar ta meye?

Irfan ya girgiza kai ya ce " bazance miki komai ba aman ki sani a kulum ina yi miki fatan alkhairi yayi murmushi ya ci gaba " karfe goma bayan mun daga ki damkawa momy takardar nan ta karanta domin idan kika bata yanzu tafiyar zata iya fasuwa ne plz kiyi min alkawarin sai mun daga zaki bata

Ma gaba daya ta shiga rudani duk ya Sakata a duhu harma ta fara jin tsoron tafiyar tasu aman kuma ya kanainaiyeta ya hana ta yi masa tambayoyin dake fatar bakinta da kyar ta samu ta ce """" nayi maka alkawari sai karfe goma zan bata takardar ka kula da kanka allah ya kare min kai


Ya ce " amin Ma sanan kiyi min adu'a domin na tafi neman soyaya yana gama fadar haka ya juya da Sauri ya shige motar , yana daga musu hanu


Ma ta juyo tayi arba da Momy Wace ta miko mata hanu kan ta bata takarda


Shin me GENERAL ya rubuta a takardar sa? Sanan aikin meye general zai je yi a Malesia , ? Soyayar wa GeNERal zashi nema? Kumuje domin samun amsoshin tambayar mu








92245228
[7/7 19:18] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_



54

Karfe tara da minti ashirin Kenan Hajiya sajida ta saka Fatima gaba tana ta girgiza kafarta irin tana tunanin ya zatayi ta kwace takardar nan domin tayi fuskar tayi lalabar aman fir tace alkawari bazai cita ba


Momy ta ce " Fatima sauran minti har arba'in fa plz ki bude min naga abinda yaron nan ya rubuta na roke ki

Ma ta girgiza kai ta ce " sowie momy

Momy ta kara cika tana batsewa kamar ta kife Fatima , ita kuwa Hajiya khadija sai dariya take yiwa Momy tana fadin Sajida gaugawa haifar da nawa take

Momy ta ce " kinsan fa halin dan nan naku dan abun uwan nana ne

Ma ta kama baki tace " Dana dan albarka ne

Wasa wasa har momy ta dawo kasa ta zauna dirshan tana irga duk second din da zai gifta gani takeyi yau lokacin ma baya tafiya


Karfe goma daidai Ma ta mikawa Momy takardar har hanunta na karkarwa ta Mike tsaye ta bude takardar ta fara karantawa kamar haka


*Asalamu alaikum ya ku iyayena fatan na barku lafiya?* *Na rubuta muku wanan sako domin maganar tayi min nauyi a gaban ku*
*ina mai neman gafarar ku domin na yiwa yar uwata rukon sakainar kashi ban san cewa tresor ne a tatare da ni ba* *Ma kin malaka min kwan ki daya a duniya duk irin kaunar da kike yi min ban riketa da amana ba na kasance mai son kaina da yawa ki gafarceni*
*Momy uwa mai albarka please ki sanya mini albarkarki domin na tafi neman soyayar yarki ne ba aiki zanje yi ba*
*Sai laifina na gaba my mom ND my Ma duk da nasan sam bai dace na falasa wanan abin ba aman hakan na nufin in kara wanke Raisa ne a wajen ku dalilina kuwa shine kowa yana yi mata kalon wace ta dade da zubar da mutuncinta a waje ba hakan yasa har ni kaina naki karbarta da wuri a matsayin mata ba aman a shekaran jiya na yarda cewar ba shigar mutun ke nufin a yanke masa hukunci ba a karshe dai ina mai shaida muku my Raisa ta kawo mutuncinta thank you ina bukatar adu'arku ma'asalam*

*GENERAL IRFAN*


Momy tayi tsai sai yanzu zancen da ta saurara a kofar dakinsa ya fado mata domin ita mantawa tayi sam da zancen ta shiga kai kawo inda Hajiya khadija take furta alhamdulilah alhamdulilah kai allah abin godiya allah mun gode maka ,
Ita kuwa Fatima sai kawai ta kawar da kanta a ranta tana tasbihi ga allah subahanahu wata'ala sanan maganar mijinta ta fado mata a ranta inda wani lokaci ta ce masa " Pa ka dena dora yarinyar nan a irin halayar maza ina gudun wata rana muji kunya

Yayi murmushi ya ce " idan dai irin kunyar da nake tunani ce kike nufi to ki saka a ranki allah bazai taba bari hakan ta faru da mu ba domin kuwa ayar allah ce abinda kayi yar wani za'ayiwa taka , ni dai ba yar Wanda nayiwa bansan iyayena ba kema kuwa hakance dan haka muyiwa yarmu adu'ar allah ya kare mana ita

Ma tayi murmushi ta ce " allah ya Kare mana ita Pa


Momy dake kai kawo wata irin murna take ji a ranta harma hakoranta ta kasa rufewa ta juyo ta ce " yaron nan akoy dan abinda ba'a fadi ba to dan ubansa ranar da fir yaki yarda na daukota yasan abinda ya aikata KO? To aman oh my god kardai oh my god da Sauri ta dauko waya ta dana number Ilham

Ilham dake kicin ta daga ta ce " hello momy

Momy ta ce " ke fada min gaskiya a gidan ki ya aikata abin kunya KO?

Ilham ta ce " wa?

Momy ta ce " ke irfan nake nufi

Ilham ta bushe da dariya tana fadin yar taki tayi baranbaramar KO?

Momy ta ce " au da bakiyi niyar fada min ba dan ashatar ki wa kike so ya fada min?

Ilham ta ce " to momy nace miki me ? Momy yanzu ba gashi ba ta fada miki yar rigimar? Yanzu tana ina?

Momy ta ce" ban sani ba ta datse Kiran tana ta banbami su dai kowa yayi shiru da abinda yake sakawa a cikin ransa

Momy ta ce " to yanzu da ya tafi da ita karfa ya je ya ilata min yarinya

Hajiya khadija ta ce " momyn yara kiyi musu adu'a mana

Ta turo baki tana ta buga number su aman bata shiga ( sowie momy😁)



Yan matan dake rabon jus da kula da pasinger jirgin suka fara sanarwar a daura belt domin nan da minti biyar jirgi zai sauka a kasar indiya

Raisa ta dago kanta ta kali General ta ce" General ba Malesia zamu tafi ba?

General ya ce " no an canja kasar , yaci gaba da dadana wayarsa

Ta turo baki a ranta ta ce" aman an ma raina ni ai sai a sanar da ni KO?

Shi dai kawai yana ganin bakinta na motsawa ya danyi murmushi a ransa ya ce" allah kadai ya san mai take sakawa a cikin ranta allah dai ya sa ba mugunta ake shiryawa GENERAL ba


Jirgin na sauka wata tsaleliyar mota kirar ruwan toka a pake mutumin dake ciki bakin fata ne abin mamaki yana hausa ya sarawa general sanan ya bude musu mota suka shiga gaba daya suka nufi tamkamemen gidan Elhaj Muhammad Ibrahim
Baba ta bude baki hayam tana kalo tace " dan nan ni kuwa har yanzu a cikin duniya muke

Raisa ta bushe da dariya ta ce " baba a duniya muke mana

Shi dai awai kalonta yake yanda take dariya abin na mugun birgeshi ya danyi murmushi ji yake kamar ya saka hanunsa a kuncinta Ashe Imran idan tana dariya haka ne yake ji har yake taba kuncinta? Yaja tsaki a ransa ya ce " shege yana taba matar mutane(to kaji masu mata manya)

Bayan sun sauka sun ci sun sha wani kuku ya shigo ya ce " oga an gama gyaran komai

Irfan ya ce " ohk harda na madame KO?

Ya ce " yes sir

Ya ce " ohk

Bayan sun gama cin abincin ta mike ta nufi dakin da akace nan ne dakinta tana shiga taga wata irin fitila tamkar walkiya ta haske mata ido nan da nan sai duhu idanuwanta basa ganin komai ta shiga lalube sai ji tayi mutun ya rikota ya rada mata a kunanta it's me my angel kar ki tsorata

Ya jawota a hankali kanta a saman kirjinsa yana tafiya da ita sai da ya isa har tsakiyar dakin sai ga haske ya gauraye dakin


Ta bude idanuwanta da kyau gabanta ya fadi domin wata irin duniya ta tsinci kanta a ciki ta kara waro idanuwanta tana kara kalon dakin kamar idan ana celebrate din aure KO birthday wajen sai walkiya yake da wasu yan bulbul kamar diamants suna ta haskawa da wasu irin balanbalan na zuciya suna fitowa suna bacewa wata music ta fara tashi cikin taushi Raisa ta lumshe idanuwanta ta juyo dan ta yiwa irfan tambayar nan kuwa inane???? Sai ganin mutun tayi yayi irin gurfanen da a film idan mutun zai tambayi mace zata aure shi ? Ta kwalalo idanuwanta kafin tayi magana ya rigayeta


Ya ce""""""""""""::::"""""""""""::::"""😳









92245338
[9/7 08:11] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_




55

Raisa tayi sakakai da baki tana kalon sabon salon kiran sallah da kusur

Irfan ya dago kansa idanuwansa suka zama wasu shanyayu kamar mai jin barci stil hanun Raisa na cikin nasa
Ya ce ""

*FOR THE FIRST TIME IN MY LIFE I FALL IN LOVE WITH AN UNEXPECTED PERSON*, *IT COMES OUT OF MY HEART AND INVADES MY BODY* , *IT STIFLES ME EVERY TIME YOU ARE AWAY FROM ME* , *I ASK YOU TO BELIEVE ME*; *I TELL YOU WHAT DISTURB ME LOVES GIVE ME THE CHANCE TO TEACH YOU TO LOVE ME* *MY BODYGUARD*


Raisa ta kuma kwalalo idanuwanta tana kalon sa a hankali ta duko ta rada masa " GENERAL shin ana kalon mu ne? Mun shiga basajar ne?

Irfan ya girgiza mata kai alamar aa

Ta kuma zaro ido ta dora hanunta a wuyansa tana tabawa domin ita kawai gani take irfan bashi da lafiya ne ,

Irfan ya ce " Raisa lafiyata lau

Ta kuma zaro ido ta zama tamkar tababiya kawai sai ta bushe da dariya ta fizge hanunta tayi bayabaya luuuu ta fada Saman makeken bed din da aka shinfida masa farar dara stil bata dena dariyar ba tana lumshe idanuwanta

Irfan ya lura da bata dauki abin da mahinmanci ba hakan ya sa ya taso ya zo kusa da ita ya kuma ruko hanayenta ya ce " Raisa shin baki yarda cewar yes nine Irfan nake yi miki wanan batu bâ? Shin bazaki karbi tayina ba?

Raisa ta dago kanta sanan cik kamar an tsayar da dariyar tata ta Mike ta shiga cire kayan jikinta sai da yayi sauran daga ita sai bras da pant ta matsa kusa da shi ta ce "" GENERAL IRFAN ka sani Ni Raisa ba mahaukaciya bace sanan ba sakara bace nasan ciwon kaina sarai kawai dai ina nunawa ni din bansan ciwon kaina ba ,
Raisa a wajenka ba komai bace face *BODYGUARD* sam soyaya da kai da RAISA bata da dadin ji domin kai tsabtatace ne , kai mai hali na kirki ne, kai baban mutun ne, sanan kai fari ne , tayi murmushi mai ciwo ta ce" shin mai zaka so a jikin gardi kamar kai? Meye abin so a jikin bakar mace? Mai zakayi da bodyguard karamar yarinya? Waima na tambayeka yaushe ka fara son Bodyguard ne ? Ta ce " oh na tuna ranar da kayi raping din bodyguard KO? Oh idan kuwa hakane ba son bodyguard kake yi ba , no kana sha'awarta ne duk da Nasan a maleji ne don matarka bata nan aman karka damu ni tamkar baiwarka nake domin ni bodyguard ce sanan Wace aka daura maka jarabar da aka hadaka da ita so ta cire bras din ta ce yau ba sai kayi raping dina ba kana iya bi a sanu KO tun karfi zan jure domin aikina Kenan


Irfan ya kauda kansa duk irin jarabar sa yau baya son KO kalonta a haka ne domin shi fa ita yake so ba wai jikinta ba taya ma zatayi tinanin wai dan jikinta yake sonta ? Wai shin yaushe ma ta iya fitsara haka? Wata zuciyar tace masa ah Malan kai da ka zubar da girman ka harma ka duka mata ai Dole ta raina ka kawai ka shareta tunda dai son nata ba kasheka zaiyi ba ai ba kanka farau ba rasa abinda ake so ,

Har ya mike ya juya zai bar dakin sai kuma ya dawo inda take zaune ya zuba mata ido a ransa ya ce muguwa, a fili kuwa ya duka ya kwaso kayanta inda ta jefar ya rufa mata rigar ya ce " bakiyi karya ba tabas jikinki da na kusanta shekaran jiya shi ya kara mini kaunarki a raina, bakiyi karya ba ni din ba karamin mutun bane sai dai ki sani da dan jikinki ne zan dawo na duka miki kinyi kadan domin a daren nan ina iya auren biyu ku cike hudu manyan manyan mata sai dai matsalar na rigai na kamu da sonki aman fa hakan ba shi zai baki damar ki walakantani ba so madame ayi baci lafiya I LOVE YOU😉

Ya juya ya FITA

Raisa ta rufe idanuwanta ta lula tinani



Toh fa
[9/7 08:12] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_


56
Salam masu karatu ina neman afuwarku ta kwana hudu da zanyi bana typing because zan fara wata jarabawa ne ranar talata so ina bukatar adu'arku daga mai yar uwarku SAJIDA thx


Raisa tayi konce tana tinane tinane ta ce: duk tsahon soyayata da Imran bai taba kissing dina ba yayi hakuri sosai duk irin shigar da nake yi a gabansa , sai yanzu kai ka taso min da wani wasan fina finai? General bana sonka KO kadan bazan taba sonka ba tun ina yarinya KO ganina kayi sai ka tofar da yawu dan tsabar tsana aman wai yau ka tashi ka ce min kana sona? Lolz bazan taba yarda da soyayarka ta karya ba ta lumshe idanuwanta yau KO wankan ma bazata iya yi ba kawai tayi adu'a sai barci

General dake zaune a falon gidan idanuwansa saman TV shi so yake ya nuna fa rashin karbar soyayar shi da Raisa taki yi bai dameshi ba , aman ina gangar jikinsa take nan aman ruhinsa ya tafi t
[20/7 23:48] ~Amnoor👯🤸🏻‍♀: [20/7 12:58] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_


56
Salam masu karatu ina neman afuwarku ta kwana hudu da zanyi bana typing because zan fara wata jarabawa ne ranar talata so ina bukatar adu'arku daga mai yar uwarku SAJIDA thx


Raisa tayi konce tana tinane tinane ta ce: duk tsahon soyayata da Imran bai taba kissing dina ba yayi hakuri sosai duk irin shigar da nake yi a gabansa , sai yanzu kai ka taso min da wani wasan fina finai? General bana sonka KO kadan bazan taba sonka ba tun ina yarinya KO ganina kayi sai ka tofar da yawu dan tsabar tsana aman wai yau ka tashi ka ce min kana sona? Lolz bazan taba yarda da soyayarka ta karya ba ta lumshe idanuwanta yau KO wankan ma bazata iya yi ba kawai tayi adu'a sai barci

General dake zaune a falon gidan idanuwansa saman TV shi so yake ya nuna fa rashin karbar soyayar shi da Raisa taki yi bai dameshi ba , aman ina gangar jikinsa take nan aman ruhinsa ya tafi tinanin yanda zai karkato mace mai ra'ayin kanta gareshi , can dai yayi wani tinani sai kawai yayi murmushi

Da safe karfe takwas sun halara suna karyawa yana matukar son halinta na duk abinda akayi mata idan kaga fuskarta kamar ba'a taba yi ba tana cin abincinta tana ciyar da Afane ,, ya kuma cewa a ransa sanan duk fushin da take yi da shi bai shafar Afane yayi murmushi a fili ya ce " Ma sak

Raisa ta dan dago ta kaleshi jin ya ambaci sunan Ma sai taga abincinsa yake ci sai ta basar ta mayar da kanta kan abincinta


Bayan sun gama cin abinci su Raisa suna zaune falo suna kalon cartoon harda baba tsohuwa irfan ya shigo yana zabga kamshi ya zauna

Da Sauri Raisa ta fada dakinta ta saka kayanta na bodyguard aman a nan bakake ne ba kalar na sojoji bane ta dauko yar karamar bindigarta ta daure daga ciki kafin ta dora bakar rigarta ba KO huta kawai ta dauko bakin glas dinta ta fito ta shiga yiwa yarta wayon fita

Irfan ya kaleta galala ya ce:: fita zakiyi?

Raisa ta ce " ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login