Showing 30001 words to 33000 words out of 75972 words

Chapter 11 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Amnoor   

19 Aug 2025

6013

America wajen karatun ta suna soyaya da wani dan banban mai kudine a kasar sanan mawaki ne suna tsaka da soyayar su ta samu ciki ya nuna sam baya son ciki shi baya son yaya domin yaya suna batawa mutun rayuwar sa suna tsufar da mutun da wuri su subarwa da mutun mama sanan mai gaba daya su hanashi shanawa tun tana kiyawa har ta yarda suka je aka zubar mata da cikin karshe ma aka juyar mata da mahaifa ba'afi wata daya da yi mata aikin ba yayi tafiya Paris wajen wani wasa a hanyarsa ta dawowa jirgin su yayi hatsari shi kansa kadai aka samu
Firgigit ta dawo hayacinta dalilin bubuga bayanta da irfan yayi
Ya ce : awatif lafiya kike kuka? KO bakya son haihuwa ne ke?

Awatif tayi Saurin girgiza kanta sanan ta tataro nutsuwarta ta ce: honey haihuwa mutuwa rayuwa aure duka lokaci ne ina matukar son yaya a kulun ina rokon allah da ya bani yaya masu albarka da hasken idaniyata wato kai aman har yanzu KO batan wata ban taba yi ba ta fashe da kuka
Ya rungumeta yana shafa kanta alamar tayi shiru a hankali ya ce : kar ki fadi haka Awatif muci gaba da adu'a insha allahu allah zai jikanmu ya bamu yayan mu masu kyau mu tarbiyantar da abinmu sanan idan ma Afane ce kadai kwaina a duniya na godewa allah allah ya bar min ita

Awatif tayi murmushi ta ce : amin ya allah , suna tsaka da hirar su cikin nutsuwa suka ji gamgamgam ana buga kofa ba KO sasautawa
Irfan ya ce chuit bodyguard

Awatif ta ja tsaki ta ce bodyguard nosence

Bugun da take ya zaburo ya zira doguwar jalabiyarsa ya bude kofar
Yana budewa Raisa ta rukumkume shi tana ihu gaba daya ta kanainaye shi taki barinsa ya numfasa da kyar ya samu ya cirata daga jikisa ya ce mata meye ke mahaucaciya meye na ce ki fada mini meye kuma kike yi min ihu tsakar dare
Tana rusa kuka ta ce masa AFANE AFANE CE TA MUTU AFANE TA MUTU








My Dear your comments and appeciations are important thereforπŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½92245338πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½πŸ‘‚πŸ½
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kada 🐊🐊 ta ruwa ce 🌧🌧🌧🌧🌧
Na sajida



38

Tsakanin sa da allah yake buga bal din itama ta dage tana tarewa aman sai saka mata yake domin ya fita tsayi ya fita iyawa sanan karfin ma ba daya ba ita kuwa Afane daga an saka musu sai tayi ta dariya tana tapi suna tsaka da wasan ta dauko bal din ta nufi πŸ€β›ΉπŸ»β€β™€ zata saka masa ya tare tayi tayi yaki sakin mata hanya ya gobshe ta ya anshe bal din haushin ganin zai kuma saka mata yasa ta fadi tana rusa ihu harda hawaye tana fadin kafarta da gudu Afane tayi wajenta tana mama sanu mamamana dena kuka cak ya tsaya ya juyo yana kalon ikon allah shi dai har harbinta yaga anyi bata yi kuka ba gabansa ya fadi ya ce KO dai ta karye ?
Da sauri ya nufota ai kuwa tana ganin hakan ta kara ihun kukan tana rike kafa yana isowa ya dagata yayi mata daukan jarirai ya nufi cikin gida da ita , haba raisa mai zatayi in ba ihu ba hade da dariya da kuka sai zilo take ita kuwa Afane tana rike da hanunta suna shiga ya shinfideta saman baban kujera ya fara tataba kafar tata yana tambayar ta ina ne ta karye

A ranta ta ce πŸ€”πŸ€” karyewa toh ga hanyar da zata rama ta KO mintsine shi da duka faratunan ta tana rintse ido tana ihu irin ciwo yayi ciwo har da cizo ta gala masa tana hawaye da Sauri yayi zumbur ya mike yana yarfe hanu sai ga Momy ta shigo da docter Mariam a bayanta tana zuwa Raisa kuwa ta ce sam bata san zancen a duba kafar ba akayi lalabar duniya takiya ai Irfan ya cire takalman sa ya daneta ya ririke hanayenta

docter Mariam ta duduba ta ta ce no ba karaya sai dai KO jin zafi don haka sai anyi radio an gani

Irfan ya cikata ya ce kin duba da kyau kuwa? KO dai a bakin nata ne ta bige kinga fa taki yin shiru

Lurar da docter Mariam tayi kukan na Raisa da biyune yasa ta ce suje da Irfan ta bashi magani Wanda zai rage mata zafin
Suna fita ta mike suka bushe da dariya ita da momy Ma ta ce walahi ba'a isa ba haka kawai ayi kokarin ganin an tayarwa da dana hankali?

Momy ta ce shi da yake cin zalinta kin hana shi ne? Beby madallah kinyi min daidai

Suna tsaka da dariya Raisa tana nuna yanda ta mintsine shi sai gashi ya shigo kamar an wurgo shi

Raisa ta zaro ido ta dora hanu a kai ta ce wayo na shiga uku momyna kasheni zaya yi kafin tayi shiru ya nufota πŸ™†πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ












Happy juma'at
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: *DUK KARYAR KADA..🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*
*NA SAJIDA*



39

Gaba daya ta tsure tayi zaton zai daketa ne sai da ya iso ya zauna ya dade shiru bai ce komai ba a ransa yana ayana lalelale fa yarinyar nan sai ya koya mata hankali idan ba haka ba ta raina shi da yawa sai wajen karfe shida suka koma bangaren su yau zuwan Awatif ne ta saka an jere komai a mazauninsa karfe takwas suka halara wajen cin abinci yau Afane tayi baci da wuri tuni Raisa ta shinfideta su uku ne kawai ke cin abincin Awatif ta sha doguwar Riga mai budaden gaba rabin kirjinta duk a waje gashi sai kamshi take zubawa raisa ma doguwar rigar ce a jikinta kamar ta mai takaba ta kawo wata hula ta kindima kamar kurma abincinta kawai take ci fama take ta bar wajen tun kafin tayi laifi

Awatif ta matso a hankali ta dora hanunta a saman cinyar general ta fara wani salo tana yi masa tafiyar tsutsa sarai ya so ya basar don ya nuna mata yana fushi fa da ita aman abin ya gagareshi ya dago dara daran idanuwan sa da suka canza launi zuwa ja ya sauke su a kanta rabin breast dinta dake waje ya kuma dauke masa hankali bai san sanda ya cafkota ba Ya shiga kissing
Raisa da ta kai cokalin abinci bakinta tayi sauri zubar da shi cikin plat din har tana kokarin amayar da Wanda ta ci , wanan abin yayi matukar kular da Awatif ta zaro ido ta ce darling kaga fa kamar taga kashi mu take tofarwa da yawu

Raisa ta kwalalo ido waje ta ce : ke anti Awatif ki rufa min asiri ni wly ba ku nake kyankyami ba bakin ku nake kyankyami

Awatif ta ce yar rainin hankali bakin namu meye a cikinsa da zakiyi kyyankyamin sa? Ke ba'ayi kyankyamin naki bakin ba sai namu zakiyi kyankyami ke da kike soja?

Raisa ta zaro idanuwanta waje ta ce kai wanan ai da mijinki kike ni fa ba kazamar soja bace ni ai Anti Awatif ni bodyguard ce muna Wanda muna da tsafta bama son raini bama hade haden baki da gardawa sanan muna tsare yayayan baba da rai

Awatif ta ja wani uban tsaki ta ce ke banza ni ba antinki bace sanan ni ba zaki daukeni yar iska ba domin da mijina nayi iskanci ni bana kwana da mazan da ba nawa ba koda kuwa nayi daren aiki sanan da kike cewa ke ba kazama bace dubiki ki ganki banza kucaka duk Wanda ya taban mijina wly sai inda karfina ya kare ta juya wajen Irfan Wanda yake cin abincin sa yana dan kalon su kamar ya samu talabijin (dan duniya ) ta ce : my heart ina jiranka plz bazan kuma kara second daya wajen nan ba

Raisa ta bushe da dariya ta ce hahaha su my heart manya to kice masa ur huhu mana hhhhhhhhh taci gaba da dariyarta tana kwaso abinci zata kai bakinta ta ga General yana kalonta gabanta ya yanke ya fadi itafa har ga allah tana mantawa ma da yana waje sai ta gama rashin kunyarta ta gansa ba shiri ta zurmo kasa ta kama kujerar da yake zaune tace kayi min rai yanda allah yayi maka ka rufan asiri ka taimakeni ka ceci rayuwa ta kar ka rama mugunta da mugunta domin ba kyau allah ya hana ka sani ni yarinya ce wly yarinta ce ke rudata har na gayawa matarka magana bazan kuma ba na rantse da allah daya ma kuwa
Tun da ta fara magana shi dai bai ce mata komai ba yana sauraronta kuma yana ta taunar abunda ya saka a bakinsa ganin bai tankata ba ya sa ta tashi harda kakabe rigarta wajen tsugunwan da tayi ta kara gyara daurin dan kwalinta ta juya zata koma dakinta sai ji tayi yayi caraf da hanun nata ya juyota ta zaro ido ta bude baki zata zunduma ihu sai ji tayi an juba mata wani Abu a bakin ta zapi rau abin sanan da abin miya miya a jikinsa ya gumtse mata baki ya matse mata hanci ai bata san lokacin da ta hadiye masar da ya tauna a bakinsa da yawunsa da komai a jikin tako yi aniyar amayarwa ya kuma riketa da hanun sa daya da dayan hanun ya dauko jus ya gumtsa a bakinsa ya kuma jan gashinta da karfi ta kuma bude bakin don yin kuka ya kara zube mata jus din gaba daya sai da ta hade shi tas sanan ya dauko bakin ruwa ya bata ya kara matse mata hanci sai da ta shanye tas ya ruko wuyanta ya jata jikin garu ya hade bakinsa da nata yayi kissing dinta son ransa sanan ya cikata ta fadi yagob a kasa tana maida numfashi yana kadangare

Ya ce kinji fa abinda take ji a bakin nawa shi yasa take sonsa aman tunda kema kina so gaban nan zaki rinka shan yawun kazamin soja , ya kuma yin murmushi ya ce night maman Afane zanje na baiwa Awatif abinda yafi wanan KO kina so?

Cikin Sauri ta girgiza kai tana matsar kwallah yayi gaba abinsa ta bishi da kalo ta Mike tayi bayinta da gudu tana kakarin amai







92245338πŸ€·πŸ»β€β™€
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_β™»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_


41
Gaisuwa mai tarin yawa zuwa gareki masoyiya *Amnoor* allah ya bar zumunci





Ci gaban
Ji yayi kamar kunan sa baya ji da kyau wani irin karfi ne yazo masa ya cirata yana kalon ta kamar sabuwar halita
Ya ce" ke Raisa KO dai mafarkine kika yi?

Raisa da har yanzu idanuwanta suke rufe sunyi hulu hulu sai karkarwa take ta yi kokari ganin ya cikata ya jayota da karfi ya rungumeta tun karfi a jikinsa yana fadin no plz no kuma can ya cikata da gudu yayi dakin da Afane take yana zuwa ya tarar da ita duk kunfa ce a bakinta da hacinta sanan idanuwanta a kafe tana kalon sama ga jikinta kamar ba jini da gudu ya sureta yayi cikin banban gida da ita Raisa da awatif na biye da shi yana shiga ya tarar da matan gidan na zaune suna kalo da gudu ya kaita tsakiyar su ya ajiye idanuwan nan nasa sunyi jajajir shi baiyi kuka ba shi baiyi magana ba shi baiyi dariya ba

Momy ta zabura ta dafe kirjinta ta kuma dora hanayenta biyu saman kanta ta silale kasa

Hajiya khadija ta furta inalilahi wa'ina ilaihi raj'une da kudu ta fita ta nufi baban asibitin gidan domin sam ta manta da wata aba wai ita waya a yau gani take zuwa da kanta yafi sakon waya


Irfan sai kai kawo yake idan kayi masa kalo daya bazaka so ka kara kalonsa ba Awatif kuwa na zaune ta rafka tagumi hanu biyu biyu ; momy tun da ta silale take kalon wajen da Raisa ke rungume da Afane tana rusa kukan da baya fitowa tsananin muryarta ta disashe sam bata fita hawaye wani na korar wani sai surutai take tana kara kankame Afane a jikinta shigowar likitoci harda kayan aikinsu da gudu suka banbare Afane daga jikin Raisa Docter Mariam ta saka abin nan na jin nunfashin mutun KO bugun zuciyarsa ta kontar da Afane ta cire mata rigar jikinta ta dora saman kirjinta wajen wuyanta tayi kasa kasa wajen zuciyarta ta dora ta dade tana sauraro can ta zabura ta ce muje dakin tiyata muje

Irfan ya ce " docter ta mutu KO?

Docter Mariam ta ce General a yanzu bazan ce eh ba zance aa ba domin kayan aikin mu ba anan ba so mu je tun kafin mu rasata
Gaba dayansu suka dugunzuma suka yi asibitin gidan suna isa akayi dakin tiyata da ita su kuwa suka zazauna can dai Fatima ta dauro alwala ta kawo baba tabarma da tapi ta shinfida ta koma ta kwaso carbi ta kawo ta mimikawa kowa ganin hakan ya basu kwarin gwuiwa Momy da Hajiya khadija suka dauro alwalar suka shiga jan carbi

Shi kuwa irfan har yanzu ya rasa a duniya yake KO a lahira yanda zuciyar sa take azalzalar sa sun kusa awa daya sai ga docter Mariam ta fito daga dakin tiyatar a tare suka mike suka nufota kafin su karasa sai ji sukayi yim faduwar mutun a tare suka juyo *Raisa* ce konce kunfa ta hanci ta baki tana zubo mata ai basu tsaya tambayar Afane ba Haka docter Mariam ta koma da gudu likitoci suka fito da gado aka dorata aka turata cikin dakin tiyatar itama suka rufu a kanta

Irfan ya hada hanayensa biyu ya dunkule ya naushi dayan Momy ta fashe da kuka tana fadin inalilahi wa'ina ilaihi raj'un tun karfinta gaba dayan su sun rikice banda Fatima da ta kabarta sallah take ta aikin nafiloli

Momy ta ce irfan dan allah kayi kuka kar ka hadiyi zuciyarka dan allah ka rufa mana asiri kayi kuka , Kai kayi kuka dan ubanka kaji KO ta shiga marin sa ita dole sai yayi kuka kar yaje ya hadiyi zuciya ya mutu shima , da kyar Hajiya Khadija ta samu ta kwaceshi shi kuwa gaba dayansa ya zama wani ja da idanuwan da kalar fatar tasa sai suka zama kala daya banda huci ba abinda yake yi ya rasa ina tinanin sa ya tafi ,






Bayan minti talatin Docter Mariam ta fito ta karaso wajen su su duka sunyi shiru suna jiran jin kalmar bakinta kowa tsoro yake ya tambaya ita kuwa taki yin magana
Can momy ta ce " wai zaki fadama ne sun mutu KO?

Docter Mariam ta ce" no da ransu basu mutu ba

Gaba daya suka furta alhamdulilah

Taci gaba da fadin sai dai akoy matsala wato su dukan su sun sha wani poison ne ita Afane yayi saurin cin mata ita kuwa Raisa a hankali ya shigeta yanzu dai ita Raisa mun samu ta farfado mun yi mata alurar baci da kuma magungunan da zasuyi Saurin cin karfin poison din , ita kuwa Afane tana cikin comma so muna bukatar adu'ar ku mun Sakata a dakin observation domin mu lura da yanayin lumfashinta da kuma idan abin na raguwa KO yana karuwa so insha allah su duka zasu samu sauki cikin ikon allah


Irfan ya ce " poison wani irin poison , a ina suka samu poison ?

Docter Mariam ta ce allah masani sai Wanda ya basu don haka a kula da masu shiga suna fita wajen su a kula sosai


Fatima ta ce" docter daman shi haka yake da saurin kayarwa?

Docter ta ce" yes ma'am ai allah ne ya taimaka aka gano matsalar da wuri da ba'a gano ta ba da abin zai fi haka domin akoy Wanda pak daya zaya yiwa mutun sai dai wani ba shiba


Momy ta ce " lale kuwa KO ubanwa wa ya saka musu abin nan allah ya toni asirin sa walahi talahi bazan taba yafe masa ba

Shi dai irfan tun da yaji cewar kila wa kala yarsa zata rayu ya yiwa allah godiya sanan yayi shiru ya tsunduma titanin cin abincin su na jiya Raisa da Afane a plat guda suka ci abinci suna ta dariyar su ya lumshe ido ya ce " wanene yake kokarin ganin ya kawar min da fitilar gidana, da nishadin rayuwata mai sakani nishadi?


Ya ce" docter bayan mu kar a bar kowa ya shiga wajen su

Docter Mariam ta ce " OK insha allah general yanzu mutun daya yana iya shiga don ya kara kontar muku da hankali idan yaso sai a barsu magani yayi aikinsa

Momy ta tsurawa Irfan ido tana kalon sa a ranta ta ce hum yaro yaro ne har yanzu bai yarda da zuciyar sa ba a fili kuwa ta ce " bara na shiga na gani


Murya kasa kasa ya ce " plz momy ki barni na je na gani

Tayi dan murmushi ta ce jeka toh

Yana shiga ya jayo kujera ya zauna bakin gadon ya tsura mata ido tabas yau ya kara yarda da irin son da Raisa ke yiwa Afane tamkar ita ta haifeta da cikinta a hankali ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login