Showing 9001 words to 12000 words out of 75972 words

Chapter 4 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Advertisement

Amnoor   

19 Aug 2025

6049

Wace sukayi shiga iri daya har ma da zoben alkawari a hanun su ta ni sa tayi ajiyar zuciya ita kadai ta ce mafarki karya mafarki shirme mafarki tatsuniya aman duk da hakan ta kasa komawa bacin sai tashi tayi ta shiga gyara takalmin ta Wanda zata yi sabkon zuwa wajen aiki .............
Love u
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kado🐊🐊ta ruwa ce🌧🌧 na sajida😘😘
🐊🐊🐊🐊🐊🐊🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊
13
Godiya mai tarin yawa zuwa gareki antina Anti Jamila allah ya barmin ke
Jinjina ga masoyiyata Ouseina 😘


Konci tashi ba wuya yau har sauran kwana biyu familyn Mr president zasu daga zuwa kasa mai tsarki sai shiri suke duk da ba wasu kaya zasu dauka ba domin anyi musu tanadin kayan da zasu saka a can sanan yau suke tarbar bakin su wato Prince Imran da Samir idan kaga Ilham sai shige da fice take tana dan shirye shiryen ta ita kuwa Raisa sai baci take shekawa domin sun yi aiki mai tsauri na tsaron general wajen wani meeting da ya samu halartar manya manyan sojoji na kasashe daban daban,

Bangaren masu abinci Ma na tsaye bisa kafafuwan ta tana fadin ga yanda za'ayi ga yanda za'ayi domin tarbar baki,

Ilham ce zaune tana ta tayar da Raisa wace take ta baci tana tura bakinta irin an dametan nan da dan magagin baci take furta oh plz ilyta ki je palo ganinan zuwa
Ta ce aa wly tashi tashi ba inda zanje tashi kiyi wanka mu tafi abinda nasan halinki sarai tashi mana ta karasa tana kara bubuga bayan ta
Raisa ta mike ta fada toilette ta sakarwa kanta ruwa tayi bruch ta fito ta saka dogon wando irin damemen nan wanda daga kasan ma ya matse kafafuwan sanan daga wajen guwoyin kamar bera yayi wasa da wajen kalar blue ne ta dauko rigar ta kalar ash ta saka ita ba matsatsa bace budada ce ta dauko bindigar ta karama wace take kasan filon ta ta duba da kyau taga babu risq in ta dana kanta ko da an zauneta, ta dauko belt dinta ta daura ta daureta tsap a jikinta ta ja rigar ta ta rufe ta dauko lotion dinta ta dan shafa ta cukuikuya gashin kanta ta saka hular ta blue sai wani takalmi kato (chimberlake) ta saka ta daura igiyoyin sa ta juyo tayi gaba tana fadin muje Ilham tayi murmushi tana raya a ranta za'a sha fama gidan sarauta suna fitowa Ilham ta shige yiwa iyayen salamar zasu shige saloon ita kuwa tayi gaba abinta

Ansha gyaran gashi masha allah aman sai mita Raisa take an shafa mata mai a kai a hakan dai aka zanawa Ilham kunshi aman fir Raisa taki a zana mata itama dole sai haka suka baro saloon din suna tafe suna labari suna dariya har suka ISO gida

Wajajen karfe biyar baki suka iso gidan Mr president sun gaishe da iyayen sukayi gidan irfane gaba dayansu domin su sami nutsuwa kafin suje ga sahibansu
Tun da suka zauna suke labarai inda wayar irfane ke ta faman tsuwa aman KO kalo bata isheshi ba domin ya san mai kiran

Samir ya dauko wayar sa ya danawa Ilham kira ta daga cikin kwarkwasa tana iyayi shima sai wani kara narkewa yake irfane ya ja tsaki yana fadin an girma ana cin kasa
Imran yayi dariya yana fadin son Kenan
Irfane ya ce broth wai dan allah mai zakaci da yarinyar nan bakar nan mai kama da aljana
Imran yace soyaya yana wani kashe ido guda yana cije leben sa
Irfane yace sakarci dai a bodyguard akoy taushi ne (kuji fa da taushin na damun ka ne irfane? Inji Matar manya)
Imran yace hhhhh a sukumbiya akoy nutsuwane?
Irfane ya kai masa duka domin ya san Awatif yake cewa sukumbiya ya kauce yana kyalkyata dariya

Bayan salar isha Hajia Sajida da kanta ke shirya er tata tana fadin bebyna kar ki manta fa banda ihu banda kokowa banda daga murya kinji plz bebyna ki nutsu plz ita dai sai gyada kai take domin hankalin ta gaba daya yana wajen Afane ne idan ta farka bata ganta ba akoy rigima Momy ta ciro mata wasu materiel kalar ja mai ratsin baki dan ubansu sun sha dinkin doguwar riga har kasa daga saman ta matse daga bakin kugun ta bude har kasa da hanun ta iya guwar hanu ta kuma dauko dan kune karami baki sai takalmi baki mai dan tsini ta bata ta saka ita kuwa ta daura mata dan kwali saman gashin da yasha gyara ( wato makaranta da ba a gabana aka shirya Raisa ba da sai na rantse ba ita bace domin ta hadu iya haduwa) Momy ta ce kinyi kyau beby tayi dariya tace momy bara na tarda su tun dazu ilham take yi min test
Cikin takunta na sauri ta fito tana waka tana ta juyi har dan kwalin ya fado daga kan nata ta dauko tana mitar dama ya za'a daurawa mutun wanan katon abin to yanzu ya zatayi ta daura shi ai kuwa ta karasa warwareshi gaba daya ta daga zata daura Ilham ta kuma kiaranta sai kawai tayi daurin ba tare da ta tsara shi ba tayi gaba abin ta ta shigo falon da suke zaune tana shigowa Ilham ta mike ta shiga tafa hanu domin daurin kamar indon kauye ta..........
+22792245338
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kado🐊🐊 ta ruwa ce🌧🌧na sajida😘😘
🐊🐊🐊🐊🐊🐊🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊
14
Masha allah anyi sunan yayata Binta mun samu ya Hafsat allah ya raya mana cikin adinin musulunci



Dariyar da Ilham ta bushe da ita shi ya tinzura Raisa ta hade girar sama da ta kasa ta turo baki ta galawa Ilham harara sanan mai gaba daya ma ta cire dan kwalin tayi jifa da shi Samir yayi Saurin tarewa yana fadin haba kawass karki jiwa tawan ciwo mana tayi kwafa ta tunkari Imran Wanda yayi sumar zaune yana kalon irin baiwar gashin da allah ya yiwa Raisar sa yayi murmushi shi kam yana son mace mai gashi sosai duk munin ta kuwa shi baya gani a haka ta isa ta zauna tana zama ta Mika hanu ta dauki tufar dake ajiye Wace zulumi ya hane shi ya ci ta kai bakin ta ta shiga ci shi dai kawai kalon ta yake yana tsananin mamakin irin wanan halaya ta Raisa tana gama cinye na hanun nata ta kuma mika hanu sai a lokacin ta tino nasihar Momy tayi saurin ajewa ta shiga kokarin nutsuwa yayi murmushi ya ce bebyna ina son ki ina son tsarin rayuwar ki sosai
Tayi murmushi tana kalonsa ita kadai take rayawa a ranta to wai shi so din nan ya ake a ji shi ne meye ma so din ? Shin irin wanda take yiwa su Ma (Fatima) ne? Ta kuma yin murmushin shi kuwa kawai kalonta yake yana ganin tana ta aikin murmushi gaba daya kumatunta sai sun lotsa ya kai yatsar sa a hankali ya saka a dan ramin na kuncin ta
Wani wawan tsaki suka jiyo a tsakiyar kansu da suka juya a tare Irfan ne tsaye da Afane a hanun sa tana ta ihun mamarta tun da ta farka ya miko mata ita yana yatsinar fuska kamar zai taba kashi ya juya ya dauko dan kwalin da ta jefi Ilham da shi ya juyo ya mika mata yana wani kakauda kai ya furta ki koyi daure kanki gaban yarinyata kar ta koyi mumunar dabi'ar ki cikin faduwar gaba ta daura dan kwalin tana dan juya kanta
Imran abin ya bata masa rai saΓ― yake ganin wanan ai walakancine ita kuwa KO a ranta domin ta saba da irin hakan
A haka ya juya yana takun sa mai cike da kasaita ya bar wajen inda gaba dayan su suka raka shi da ido


Masarautar elhaj abdurahaman

Ina bazai yiwu ba wanan ai kaskanci ne da neman zubdawa wanan masauratar mutunci da kima a idon mutane shin Imran ya rasa wa zaya aura sai namiji dan uwansa ah to namiji mana duba fa ki ga hoton yarinyar nan wanan ai kawai a dena ce mata mace a kireta da garzali in banda jaraba mai yake jan sa a jikin wanan murdadiyar yarinyar ya ce bata da sitira sai wando da riga da katon takalmiπŸ‘’πŸ‘’ kulun kugun ta daure da bindiga ita a kulun tana jiran a kawo mata hari ta tare? Wanan ai ba matar gidan sarauta bace wanan matar yare ce can wa'inda basa sallah ko in kokowa aman a gaskiya bazan lamunci irin wanan cin zarafi da walakantar da kai ba ai wly ko zanyi yawo tsirara ne KO da zan yaye Imran ne dole ya fasa auren wanan katon Hajia Bilkisu Kenan mahaifiyar prince Imran sai masefa take kan auren Imran Wanda a farko tayi amana da shi ta Nuna tana so domin a lokacin bata sans Raisa ba er Mr prΓ©sident bace sanan bata san cewa da BODYGUARD dan ta yake soyaya ba sai yanzu da aka tsayar da maganar aure inda ta tada kayar baya tace sam bata san zancen ba duk irin kawaicin sarki abdurahaman da irin son da yake yiwa matar sa uwar yayan sa wanan Karin kam yaki ya biya mata bukatar ta domin KO ba komai yana ganin darajar Muhammad Ibrahim yana na'am da wanan aure aman sam hajia Bilkisu ta ki ta maida hankalin ta ta goya masa baya su hadu su sha bikin cilon dan nasu hakan kuwa na mugun daga masa hankali baya son yaga matar sa abin kaunar sa tana bata ranta to dai yanzu haka tana maseefar nan ne a gaban kawar ta Zeinab Wace ta dage take ta tirata kan gaskiya wanan yarinyar bata dace da takamar sarauta ba to taya ma zata iya yarda a tsare ta ita mai tsare wani ?

Can ta nisa tace kawata barni da shi insha alahu idan ya dawo zan same shi na fada masa ra'ayina game da wanan shirmen auren ta ja tsaki ta mike domin amsa Kiran mijinta Sarki Abdurahaman


Tun karfe goma na dare suke zaune a airport suna jiran tashin jirgin su na karfe daya domin zuwa kasa mai tsarki
In matan ne kadai domin su iyayen a jirgin Mr presedent suka daga bazasu bi jirgin haya ba
Kowace ta sha abaya mai kyau tayi roling din kanta da mayafin abayar ita kuwa Raisa ta tufke kan nata yana tsohuwa sai pikipiki take da idanuwanta tana dauke da Afane Wace itama ta sha abayar tayi mugun kyau
Tana cikin kai kawo ta ga test da wata bakuwar lamba an rubuta ki kula da yarinyata tayi murmushi taki yin rply don kawai ta kular da shi ta kuwa samu domin sai tsaki yake ganin har yanzu yarinyar nan bata yi masa amsan message din sa ba ya ja tsaki ya dana kiran ta yana shirin ta dauka ya sauke mata kondon balaki

Daga dayan bangaren yaji ana cewa............

Taku har kulun er ku kanwar ku yayar ku er uwar ku er buzaye SAJIDA love u😘😘😘😘
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kada🐊ta ruwa ce🌧na SajidaπŸ“Έ
15
Daga dayan bangaren yaji ana cewa ki kular min da kanki bebyna kiyi mana adu'a sosai allah ya nuna mana ranar da zan kiraki matata ki kirani mijinki
Da gaya ta ce ina tsananin sonka my prince zanyi missing dinka a lot
Irfane ya zaro ido ya kurawa wayar ido kamar tana kalonsa yana ayana shi kadai ya san irin walakancin da zai yiwa Bodyguard lale yarinyar nan ta raina shi , sai cicije leben sa na kasa yake domin idan ransa ya bace sai leben sa na kasa yayi ta karkarwa yana cije shi yana lumshe ido dan yayi control din fushin sa da Sauri ya dane ya kashe kiran yana duba agogon hanun sa yayi tsaki domin sauran minti 13 jirgin su ya daga lokacin bazai ishe sa ba da yaje ya babala yarinyar nan ya nuna mata tsakanin aya da tsakuwa, yayi tsaki ya fada makeken gadon sa yana ajiyar zuciya

Raisa tayi murmushi ganin an kashe kiran ta kara gyarawa Afane konciyar ta har aka fara kiran sunaye alhazan da zasu daga a haka suka yi salama da Imran wanda yazo yi musu bankwana domin shi ba yanzu zai tafi ba

Masha allah allah ya sauke su lafiya inda suka tarar da masu tarban su suka dugunzuma banban gidan da sarki Khalid ya sauke iyalan Elhaj Muhammad Ibrahim

Isar sa kenan garin nasa (kantsΓ©) yana konce yana baci huta gajiya jakadiya ta kuma shigowa wanan shigar ta ce ta 6 har yanzu bai farka ba ta koma ta zube gaban Gimbiya Bilkisu tana fadin allah ya kara miki lafiya da tsahon rai har yanzu bai farka ba
Ta nisa ranta a jagule ta ce OK bayan an sha ruwa ai zan gan shi mutumin kawai

Jakadiya ta ce allah ya huci ran Gimbiya matar sarki allah ya sanyaya ranki duk wani bakin abu da zai tunkaro ki allah ya tarwatsa shi allah ya kara haskaka tauraruwar mata
Gimbiya bilkisu ta kada kai tana ta huci

Bayan an sha ruwa Imran ya shirya ya shiga bangaran mahaifiyar sa duk da dumbin fargabar abin da zaya tarar
Yana shiga ya bayin suka fara jero masa gaisuwa da kirari sanan suka yi layi suka bar dakin gaba dayan su wanan yana daya daga cikin tsarin wanan masarauta idan Imran ya ziyarci mahaifiyar sa KO mahaifinsa to kowa zaya tashi ya bar su su zanta
Cikin nutsuwa yake takawa yana karantar duk adu'ar da tazo bakin sa domin samun kwarin guiwar tunkarar mahaifiyar sa yana isawa ta zube ya dora kansa a saman cinyar ta yana ajiyar zuciya tsakanin da da uwa saΓ― allah duk sai ta nemi banbamin fadan nata ta rasa a hankali ta dora hanun ta saman kansa tace why prince? Why ? Me yasa zaka zabi wanan yarinyar ne me ka gani a tare da ita da yake rudar ka? Duk kalar macen da kake so zaka sameta kamamin daga nan naija har kasar maka kowace kalar fata sanan komin kyanta aman saΓ― ka tile a Bodyguard? Mace mai tsaron lafiyar namiji sadauki? Mace mai gaisawa da maza tayi cudanya da maza wani sa'in ta kwana waje daya da maza? Kasan da wani kalar namiji take mu'amala? Shin baka tsoron cututukan zamani?
Tun da ta fara wanan bayani ya rintse idanuwansa gaban sa ke luguden duka yana dan girgiza kansa yana ajiyar zuciya
A nitse ya ce: bani da kamar ki ya ke umana bani da wada ya kamo kafar ku ke da abana plz ki saka min albarka a aurena KO naga da kyau ki tausayawa yaron ki mai son farin cikin ki

Ranta ya gama baci ta ce................'''''

+227 92245338
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kada🐊🐊 ta ruwa ce 🌧🌧 na Sajida😘

16
Ranta ya gama baci har ta buda bakinta zata balbaleshi da fada sai kuma tayi wani tinani a ranta tayi dan murmushi ta dafa kansa tana cewa naji zanyi nazari
Ya dago yana murmushi ya ce love u mamana


Konci tashi ba wuya wajen allah yau sauran kwana biyu sallah kuma yau su Mr president suke isowa domin suyi sallah a kasa mai tsarki karfe biyar tuni suna masalaci suna ta ibada tsakanin su da su Hajiya Sajida sai dai a gaisa a koma masalaci a can suke yin sahur dinsu da Buda bakin su su Raisa an dukufa ana ta ibada inda aka bar afane da masu rainon ta sai dai su je su leko lafiyar ta su dawo

Yau ta kama lahadi yau baki ya bude salah sai karatu ake a baban masalacin sanan ana ta shagulgula anyi sallah lafiya iyalan Muhammad Ibrahim suna shirin haramar dagawa zuwa dubai su bada odar kalar gadajen amaren kuma suyi gida bayan dogon hutun azumi da suka sha,

Taku yake cikin kasaita ya shigo cikin falon inda hayaniyar irfane Ilham Raisa da kuma Nafissa an daurewa Ilham ido tana ta faman neman daya ta kama sai anyi magana idan taji inda mutun yake kafin ta karasa an canja waje
Raisa na dauke da Afane wando ne jikinta sakake da kadan ya huce guiwar ta sai bakar riga ita kuwa Afane er karamar riga ce fara mai karamin hanu sai dan underpants fari shima an daure mata kanta tubarkallah daga sun samu sun labe sai ta ce tata ai kuwa Ilham ta rarumi inda suke kafin ta ISO sun ruga wani wajen ana haka ne sun labe bayan kujera ta kusan hanyar fita sai afane tayi wata dariya harda tafa hanu da gudu Raisa ta Mike ido rude tayi hanyar fita shi kuwa yazo shigowa suka yi karo yayi saurin taro su kar su fadi domin baya tayi zata fadi kasa ya saka dayan hanun sa cikin zafin nama ya tarota da dayan hanun ya talabo bayan ya jayota ta fada kirjin sa ita da Afane din gaba daya
Raisa da ta lumshe ido tana shirin jin ta fadi kasa sai jin ta tayi a jikin mutun cikin razana ta bude idanuwanta ta zaro ido 😳 lokaci guda gaban su ya yanke ya fadi nan da nan ta kwashi karkarwa tana kokarin sakin Afane Wace ganin mahaifin ta ta shiga bangalar dariya
Sunyi kalon ido cikin ido na sakan biyar da Sauri ya tare Afane ya hade rai kamar hadarin gabas ya daga hanuπŸ‘ŠπŸ»πŸ‘ŠπŸ»πŸ‘ŠπŸ»πŸ‘ŠπŸ»πŸ‘ŠπŸ»





Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login