Showing 69001 words to 72000 words out of 75972 words

Chapter 24 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Advertisement

Amnoor   

19 Aug 2025

6088

ta kama igiyar nan ta fara zurawa na dora hanu a saman kaina ni ba nayi ihu ba su momy su farka Raisa ta harbeni hakan yasa da Sauri na bi bayanta ,

Nan da nan sai ga Raisa ta sauko kasa , su jony na gani masu tsaron bayan dakinta na da , nan da nan suka Sara mata

Jony ya ce " oga lafiya ?

Raisa ta ce " yau ka fara ganina na bi ta nan ne?

Jony ya ce " sorry oga sorry ,

Raisa ta kawar da kanta ta ce " zan je wajen General ne da asuba zasu fito nemana sai ku fada musu

Su jony suka Sara mata suna fadin " OK OK

Raisa ta juya ta sa kai sai bangaren gidan Irfan tana shiga ta kewaya har zata taka matatakalar falon ta ja ta tsaya domin sai a lokacin tsoron kar aje yana tare da matarsa ya fado mata tayi shiru tana kalon kasa sai ji tayi an rungumeta ta baya ta juyo da Sauri tayi arba da Irfan

Tayi ajiyar zuciya ta ce " har ka bani tsoro

Irfan yayi murmushi ya ce " my bodyguard da tsoro no sojata ban Santa da tsoro ba

Raisa tayi murmushi ya saka yatsarsa a inda ya loba kuncinta ya ce " ina son wanan abin

Raisa ta ce " ina zaka je haka ?

Ya ce " zuwa ne zanyi na ganku KO ta windows ne domin naga fushin ba zai fishe ni ba

Raisa tayi murmushi ta ce " nima nazo na ganka ne tunda lafiyarka lau bara na koma

Irfan ya zaro ido ya ce " ai walahi a biyoki da yaranki ya dagata cimak yayi cikin dakin da ita , yana shiga direct yayi dakinsa da ita bai direta KO ina ba sai saman bed ita dai Raisa banda faduwar gaba ba abinda take yi domin bazata taba mantawa da Azabar da ta sha da farko ba hakan yasa taki yi masa gardama ta bashi hadin kai dari bisa dari ganin haka yasa na fito da gudu na bar musu dakin ( asuba alkhairi Raisa )


Ba su su farka ba sai karfe takwas domin bacin kansa basu samu yinsa ba sai karfe hudu , Irfan ya mike tsaye ya tsurawa Raisa idanuwa tausayinta ya kama shi da wata tsantsar kaunarsa duk irin wahalar da take ji bai hanata yin juriya ba har ya gama abinda yake yi
A hankali ya daukota cimak sai a nan ta bude idanuwanta ta sauke su saman fuskarsa tayi Saurin rintse su Irfan yayi murmushi ya ce " i love you


Cikin nutsuwa sukayi wanka suka gabatar da sallah

Raisa ta kali Irfan ta ce " my Being yau fa aiki zanje

Irfan ya ce " aiki? Shin zaki iya aiki ?

Raisa ta ce " kasan fa an yi min hakuri sosai domin tun kafin cikin yaran nan ya tsufa nake gida idan da ance ciki ne da ni yanzu fa na dade da haihuwa kuma lafiyata lau dan haka kawai mu fice office oga

Irfan yayi murmushi ya ja hanunta ya ce " to beby na kara kadan KO?

Raisa ta ce " mai zaka kara?

Irfan ya Kane mata ido daya yana nuna mata , ai da gudu ta mike tayi waje ya biyota suna ta kyalkyatar dariya suna fitowa Awatif ta fito itama cikin shirinta na zuwa wajen aiki Irfan ya ce " My Awatif tare min ita please

Awatif tayi galala tana kalonsu ta buga tsaki ta dauki Jakarta tayi gaba KO gaisawa bata tsaya sunyi da mijin nata ba , haka suka gama guje gujensu suka shirya suka fito don zuwa office
Suna fitiwo sojan dake tsaye a wajen kofarsu ya ce " General Ma'am tazo ta ce idan ka fito a fada maka tana kiranka

Raisa ta zaro ido ta ce " na shiga ukuna ni Raisa

Irfan ya kama hanunta ya jata sukayi bangaren su momy , suna shiga momy ta rurumi kofin robar dake gefenta Wanda ta gama aiki da shi ta cilo musu , gaba dayansu suka duke kasa Irfan ya fara dagowa ya isa gaban momy itama ta iso duk suka kama kunayensu suna fadin sowie momy

Momy ta ce " wato ke Raisa bakya kishin kanki KO? Du irin rashin mutuncin da yaron nan ya shuka miki shine dan rashin zuciya ki tashi ki bisa gidansa ke mai danyen jego KO?

Raisa ta ce " momy bana jego fa

Momy ta zaro ido Irfan ya dan mintsineta ta ce " auuuuch my Being ka dena mintsinina mai nayi maka

Irfan ya rufe bakinsa ya ce " shikenan ta faru ta kare

Momy ta ce " ku yiwa Allah ku tashi ku bani waje yara ne Allah ya raya su bayin Allah inda Allah ya taimake su daman nonon sai anga dama ake basu basu da wata rigima lokacin da kuka ga dama a basu ku fitar min da gani

Irfan ya Mike ya kama hanun Raisa yana fadin Allah dai ya huci zuciyar momy

Raisa ta daga murya tana fadin love you momy , love you Ma , love you my Afane , love you mama ( hajiya khadija )

Afane da yau bata damu da fitar iyayen nata ba ita dai tana wajen kaninta ta ce " love you mamamana ND papapapana

Yau Irfan da kansa ya tuka su zuwa office din cikin wata mahaukaciyar mota baka mai shegen kyau su duka sun sha bakin glass suna isa ya fito ya budewa Raisa motar sanan ya mika mata hanu ta ziro kafarta ta mana masa kiss a kunci, kowa mamaki yake suna mamakin wai General ne ya budewa bodyguard mota lale , jama'a sai kara yi musu sanu da zuwa suke da kuma tambayar bebys ,



Konci tashi yara har sunyi wata biyu masha allah sun kara girma domin sosai momy ke kula da duk wani abu nasu , su Raisa idan suka tafi office basa dawowa sai karfe shida na yama , kafin ta tafi tana basu su sha sosai sanan idan suka dawo ta basu har safe ,yara kam basa cikin matsi haka dadynsu yana samun kulawa wajen matansa duk da har yanzu Awatif na fushi da shi ,

Yau tunda karfe goma Momy ke kira ta ce ai fadel ne yaki shan madarar yau gashinan yana ta kuka ,

Irfan ya ce " gasunan zuwa yanzu insha Allah

Tafiyar minti ashirin suka yi saï gasu sun ISO , suna isowa sukayi gidan su domin a tunanin su yaran suna gidan ba'a kaisu can banban gidan ba , suna shiga Raisa ta ga basa nan ta ce bara tayi kira da numberta na etisalat a kawo su Irfan ya ce "ohk beby

Tana shiga Irfan ya zauna saman banban kujera idanuwansa suka sauka saman bras din Awatif , ya mika hanu ya dauko yana fadin aa mai ya kawo wanan nan ? Kafin ya rufe bakinsa yaga fitowar Lili tana ta sheka dariya zigidir haihuwar uwarta kuma daga dakinsa sai ga Awatif ta biyota itama tana ta dariyar tana fadin Wace ka fara kamawa ita ce ta karshe , sai ga wani garjejen kato nasara mai Jan kune ya fito shima zigidir yana fadin to ganinan zuwa duk ku shirya , jin faduwar glass ya saka suka juyo a tatare mai zasu gani *IRFAN* ne tsaye yana kalon su ya salam na furta domin tunda nake a film a fili a novel nasha gani KO jin idan ran mutun ya baci yanda yake aman wanan ya gyasa gane gane na

Irfan ya daga yatsarsa guda ya nuna su nan da nan inda indarsa ta tashi ya shiga buga kafa a kasa yana so Dole sai magana ta fito aman ina hakan ya sa ya juya wajen katuwar TV din dake makale jikin bango ya gigibota ya juyo ya nufo su














Ganin haka ya anaci ta kare kafin na zama shaidar kisa 💃💃

[14/12 17:36] Sage: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_






80
Zaune take ita kadai ta daga kanta sama tana tunanin yanda zata yi Irfan ya saurareta ita bata ma san mai tayi masa ba yau kwana uku kenan da rabuwarsa da matarsa aman fir yaki nemanta tana gani zai fito ya dauki yayansa yayi musu kis a goshi idan ta fito sai ya dan kaleta yayi gaba abinsa , ta rasa gane kanta ta rasa ina zata dosa taji sanyi ita tambayar da take yiwa kanta meye laifinta a ciki ? KO ita ta raba shi ne da matarsa da zai yi mata fushi?

Affane ta shigo da gudu ta ce " mamamamana ki zo ga maman beby karama tazo (Ilham)

Raisa ta dago kanta da Sauri ta ce " OK beby muje , ta Mike ta kama hanun Affane suka fito , suna fitowa tayi banban falo dan tasan suna can taje suka gaisa da su momy ,

Momy ta ce " wai kinci abinci kuwa?

Raisa ta ce " eh naci momy

Ma ta ce " wai mai ke damunku ne ku biyun nan?

Momy ta ce " kema kya fada nayi nayi su fada min aman sun kiya to ba sai mu saka mu zubawa sarautar Allah ido ba ?
Daidai nan Irfan ya fito cikin wata dakakiyar shada ruwan ash ya dora hula sai zuba wani uban kanshi yake aman fuskarnan ba alamar ya taba murmushi , ya zauna saman kujerar dake kusa da dan gadon su Fareed ya shiga gaishe da iyayensa , Raisa ta kare masa kalo wani haushi ya ziyarceta , ita fa ba kwondon shara bace da zai zamto tamkar yana kyankyamin ganinta , ai saki daya ya yiwa matarsa yaje ya maidota mana , sai mai ta mike ta nufi dakinta na da KO kalon yaran bata tsaya yi ba yau , Irfan ya dago idanuwansa ya bita da kalo har ya dan mike zai bi bayanta sai kuma ya koma ya zauna tare da dafe kansa yana maimaita inalilahi dan ya samu saukin zuciyarsa a cikin ransa ya furta i miss you my Life My Raisa ,

Su momy dai ba Wanda ya tanka masa domin ba ruwansu idan sun gama munafurcin nasu sa shirya

Yana fita Ilham ta kali momy da alamar tambaya ta ce " lafiyarsu kuwa momy?

Momy ta ce " aa tunda akayi sakin nan suke haka mai yiwuwa basu so aka rabasu da ita ba

Ma ta ce " um momy kinsan yau da safe da na tsare shi yaci abinci na tambaye shi wai fushin fa ? Cewa yayi shi da barinsa akayi ya koda dan kakarya musu kafa ne sanan ya yiwa mai fuska biyun nan saki uku da ya dan huce a irin abinda suka yi masa shi yanzu tsoron lamarin mata yake

Momy ta ce " kaji hauka shine zaya ringa yi mana fushi a cikin gida

Ilham tayi murmushi ta ce " ai manyan sai a slow bara na dubo yar uwa rabin jiki soja matar soja , tamike tayi dakin Raisa tana shiga ta tarar bata tsakar dakin da alama tana bayi , ta nemi guri ta zauna , bata jima da zama ba sai ga Raisa ta fito daga wanka da tawul a jikinta ta kali Ilham ta ce " madame kin shigo

Ilham ta karewa Raisa kalo ta ce " soja wai lafiyarki kuwa ?

Raisa ta ce " ina zanyi lafiya bakya ganin matsalar da muke ciki

Ilham ta ce " no gani nake kin kara wani fari na lafiya ne kuwa?

Raisa tayi shiru gabanta na faduwa a ranta tace" tabas yau sai nayi test na ga mai ke damuna domin ina ganin sauyawata sosai a fili ta ce " ina zuwa haka?

Ilham ta ce ' ni fa biyowa nayi mû tafi wajen zanen sunan Mufida yar gidan gwamna Habubakar kinsan sun zo sunan su Fareed fa

Raisa ta ce " ba itace mai kanwar nan da ta tsare GENERAL da idanuwa ba lokacin da ake yi mana hotuna?

Ilham ta bushe da dariya ta ce ' eh ita fa Ashe baki manta ta ba

Raisa ta ce " hum bara na shirya mu tafi

Ilham ta ce " aman baki tambayi Yaya ba fa kar yazo ya dakeni a banza kinsan halinsa

Raisa tayi wani malalacin murmushi ta ce " ai zanyi masa message , a ranta tace shi da ya fice ya yi min salama ne? ( to ikon Allah Raisa mijin? )

Ba karamin lokaci ba Raisa ta bata wajen tsantsara kwaliya ta dauko kalar ruwan ash da Irfan ya saka anyi mata doguwar riga da ita har kasa ba'a yi wani aiki da yawa a jiki ba aman aikin tsarare ne ta saka bras da pant ruwan ash sababi ta zira rigarta ta dauko wata dankareriyar sarkarta ta zinari ta saka da abin hanu da zobe ta mikawa Ilham dan kwalin ta daura mata waouh Ba karamin kyau Raisa tayi ba sai haskawa take ta dauko dan karamin mayafinta gudun kar Ma ta hanata fita a haka kalar ja mai dan haske domin Zubin zaren kalar jan ne sai takalmi mai uban tsini ta daura a kafarta Ilham dai sai da ta raina kwaliyarta duk da irin yanda ta Kure adakarta itama sarkar zinariyarne a wuyanta aman duk irin farinta da kyanta da jikinta na manyan mata gani take Raisa ta gyasa ta (lolz)

Haka suka fito Raisa ta matsa ta shiga tsakiyar yaranta ta watsa musu selfi ba karamin kyau suka yi ba domin su dukansu a kimtse suke tamkar za'a FITA anguwa da su ,

Momy ta ce " oh yata masha Allah wajen sunan zaku tafi ko?

Raisa ta ce " eh momy please bani ky din sabuwar motar nan da ita zamu tafi

Momy tayi dariya ta ce " yata manya , Ma ta girgiza kai tana murmushin itama ta ce " ai su kishi ya kawo kansa inda ba'a iya ba

Raisa ta ce " Ma ai kishin zamani ki saka zinari na saka ne ki hau mota na hau mai kudin jirgi dan uban yarinya

Ma ta dauki mayafinta ta wurgawa Raisa tana fadin au rashin kunyar taku ta sojoji ce zaki yi min ? Raisa idan baki dena zagi a gabana ba nayi miki alkawarin hakoranki a hanuwanki insha Allah

Raisa ta Mike tana dariya ta manawa Affane kis a goshi da kunci suka amshi ky din , su momy suka yi musu adu'a suka yi gaba abinsu

Tafiya suke suna hira cikin nishadi Ilham ta ce " rabin jiki mai zamu kai mata ne ?

Raisa ta ce " gaskiya bazamu iya wata sayaya kafin mu isa ai munyi maraice kawai chek yayi

Ilham tayi murmushi ta ce " kyayi ki gama domin shi yaya bai damu da su ba KO kadan

Raisa ta daga kafadunta ta ce " a yiwa gawa duka dan mai rai yaji tsoro , daidai nan sukayi parking

Ba mata ba har mazan dake kasan shikokin cikin gidan suna hirarsu sai da suka zubawa motarnan ido ,

Irfan na hango yana dadana waya , elhaj kabir dake kusan sa ya cewa angon jegon " yawa minister kaga motar da nake fada maka ai mutumina motarnan ba yanda banyi ba da kudina da komai aman cewa suka yi aa sai dai nayi hakuri nan da shekara biyu za'a gama ta jama'a domin yanzu kwaya ashirin ce suka kera kuma ta mutane ashirin ce sai sun gama yayinta za'a bugo mana mu takaru

Minista auwal ya ce " dan Allah to wanene a cikinta ?

Elhaj kabir ya ce " koma wanene mai fada aji ne kai madubinta fa baya fashewa kuma daga ciki tamkar kana cikin wani palais ne , Irfan dake dana wayarsa ya Buda profil din matarsa yana famar budewa bishiyoyin wajen suka saka sabis din bashida karfi sai kuma maganar da Elhaj kabir yakeyi ta dan dauki hankalinsa domin shi dai tamkar motarsa yake bayani a kanta domin harda Mr president aka kerawa guda shi kuwa ya baiwa GENERAL domin shi ire ire harakokin nan basu dame shi ba ,

Daidai lokacin da GENERAL ya dago kansa daidai nan su Raisa suka fito daga cikin motar ita da Ilham tamkar wasu gimbiyoyi Raisa ta rufe motar ta dauko wayarta da ky din a hanunta dan mayafin da ta dauko ta rike shi a hanunta shima , Ilham ma wayarta ce a hanunta sai wata yar pocht mai shegen kyau sai murmushi suke suna tafa hanu , wani Abu yaji ya hadiye bai shirya ba

Minister auwal ya ce " au matar Oga GENERAl ce Ashe da kanwarsa matar docter Samir

Elhaj kabir ya juyo ya kali Irfan ya ce " gaske Ashe manyan ne a ciki

Irfan yayi kicin kicin da rai yana fadin zaku ci ubanku ne a cikin ransa , ya ce to wai da izinin wa ta fito? Kuma ba baban mayafi kuma tayi duka wanan adon kuma tazo tana murmushi har ana kalonta , yau sai ta fada min daga inda suke haka , ya dan saki fuskarsa ya ce " itace maman twins

Mutanen wajen sai mamaki suke aman ba Wanda ya furta gudun rigimar Irfan yanzu zai bige mutun kuma ba yanda ya iya da shi

Suna shiga daidai an fido wani kalar abinci na larabawa ne talotalo ne ake dafawa a laulaye shi da doguwar maka suna dakin mai jegon sun gama yi mata barka sun ajiye mata check ina faman lekowa dan gani nawa aka rubuta mata saï ga abincin an shigo da shi Raisa na kai dubanta taji tamkar an yamutsa mata hanjinta ta ce " oh no ta mike da Sauri tayi waje ,Ilham na kiranta aman ina ita dai fama take ta ganta a waje sai da suka shiga motar ta saki ajiyar zuciya

Ilham ta ce " Raisa lafiya kuwa?

Raisa ta ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login