Showing 63001 words to 66000 words out of 75972 words

Chapter 22 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Advertisement

Amnoor   

19 Aug 2025

6145

saman table sai dai su zauna a falo a saman kafet su ci domin kujerar bata daukar Raisa duk kafafuwanta sun dan fara kumbura haihuwa baifi sati biyu ba abinda yayi saura ,


Fitowarta kenan daga dakinta tana takawa a hankali , Afane da baba tsohuwa suna shinfida babar ledar da suke cin abinci a sama gudun kar su bata kafet din , Afane ta hangi mamamarta ta fito ta aje robar mai dauke da cokula ta tafi ta kamo hanun mamarta tana fadin mamamana sanu

Raisa tayi murmushi tana jin dadin yanda Afane shekara Hudu da yan watani aman takeda hankali da tausayin mutane , ta ce " sanu bebyna

Bayan ta zauna ta mimike kafafuwan ta Afane ta ce " mamamana ni bari muje da baba na amso abina

Raisa ta ce beby abincin fa ?

Afane ta ce" mamamana ai naci fa bana jin yunwa s na dawo kafin Raisa ta kuma yin wata maganar har ta fita da gudu

Bata jima da zama ba sai ga masoyan sun fito suna makale da juna

Suna Zama Awatif ta bushe da dariya ta ce " wai an zama shara

Raisa ta kaleta ta watsar bata tankata ba , ta bude plat dinta guda ta zuba abincinta kaya guda ta ja ta fara ci


Irfan ya kali Awatif ya ce " wifyna take

Awatif ta juyo kawai sai ya hade bakinsa da nata yana Kissing dinta tun karfin sa itama ta biye masa ,
Raisa da tunda ya furta wifynsa ta dago kanta ta sauke idanuwanta a kansu har yanzu tana kalon su , cikinta ne yayi wata irin murdawa tamkar ana cakuda hanjin cikinta , tayi Saurin sakin cokalin dake hanunta ta fara kokarin tashi tsaye , cikin ya kuma juya mata ta damki babar kujerar dake kusa da ita, ta rufe idanuwanta ruf lebenta na karkarwa ta shiga takawa cikin karfin hali tana nufar dakinta,

Irfan da tunda ta saki cokali ya cika Awatif yana kalon yanayinta ya mike a hankali ya nufota
Cikin karaji ta furta " kar ka tabani !





Love uโค



72

Cikin karaji raisa ta ce kar ka tabani kar ka saki ka tabani kaji KO?

Irfan ya dan dakata yana kalon yanda ta hada gumi ya kara matsaya yana cewa " Raisa please mana bakya ganin kamar baki da lafiya?

Raisa ta ce " Au kama ce ma KO? Kamace ma, to bara kaji ni da ba haka ba nake , kazo ka dirkan ciki dan na sawaya shine zaka wani juya min baya to sai me ni ka sake.....kafin ta karasa maganar ta cikin ya kuma murda mata ta dafe cikin nata da rufe idanuwanta ta kwala kara da gudu irfan ya riketa ta kuwa damke fuskarsa da faratunan ta ta ce " wayo cikina, wayo hanjina zai cire wayo kafata zata cire bayana zai rabe biyu,

Irfan ya ce " sanu Raisa sanu bebyna

Raisa cikin ihun kuka ta kai masa duka a kirjinsa ta ce " ni ba bebynka bace Allah ya tsareni ,an gaya maka bani da zuciya ne ? Kazo kana rungumar Matarka a gabana na tsaneka Irfan

Yayi Saurin rufe mata baki ya ce " i'm sorry

Raisa ta rushe da kukan zafi ganin zata sumar masa yasa ya cicibeta gaba dayanta ya nufi kofa da ita, shi dai docter ta ce masa a gaban nan ma zata kai kwana goma KO ta huce kafin ta haihu , kuma gashi yanzu tana ihun cikinta da bayanta , gabansa ya fadi yana tune likacin haihuwar mamar Afane haka ta ringa cewa har ta mutu nan da nan tsoro ya shige shi da gudu gudu sojawa na binsa don ganin kamar ba lafiya wasu kuwa suka nufi fadawa Matan mr president domin alamar kamar haihuwa ce

Suna shiga aka tare aka dorata saman gado aka turata sai cikin dakin haihuwa Irfan na rike da hanunta yana ta share mata gumi, KO kiftawa baya son yi gudun kar ta mutu ta barshi, ita kuwa daga ciwon ya dan lafa sai jikinta ya saka ta shiga ajiyar zuciya , suna tsaka da haka sai ga Momy a fujajan ta shigo dakin , tana shigowa ciwon na kara tashi Raisa ta kankame gadon ta rufe idanuwanta sai ga hawaye shar suna bin kuncinta lebenta kuwa duk tabi ta cije da hakoran ta , momy ta ISO da sauri tana shafa kanta tana aikin sanu sai da tayi kamar minti biyar sanan ya saka mata
Yana bari kuma sai ajiyar zuciya

Irfan ya kare yi mata kalo kawai sai hoton mamar Afane daidai tana fitar rai ya fado masa , ya rufe idanuwan sa jikinsa ya kwashi karkarwa ya mike da Sauri ya fita yana fitowa ya hadu da dady dady ya jawo hanayensa ya ce " son mai ya sameta ne ? Ai kuwa haihuwar da saura tunda momynka ta fada min sai nan da 2weeks KO?

Irfan ya rukunkume Dady kawai sai ji yayi wani abu mai gumi yana sauka a wuyansa , ya samu da kyar ya dago shi mai zai gani , hawaye a fuskar GENERAL , Dady ya ce " kai ta mutu ne?

Irfan ya girgiza kansa da kyar ya samu ya ce " dady bana so na rasata , dan allah ayi mata tiyata a fitar da bebyn kar ya kasheta, dady ina sonta fiye da kaina

A hankali dady ya shiga share masa hawaye yana bashi magana, suna tsaka da tataunawa sai ga momy ta fito da gudu tana kugin docter , Irfan ya cika dady ya koma dakin yana zuwa ya tarar ciwon ne wanan Karin harda kuka take , kusan tatare suka isa shi da likitocin mata Aka dakatar da momy a waje ita da dady

Docter Mariam ta ce " General ka dan bamu guri KO?

Irfan ya gala mata harara ya ce " ba inda zanje salon na matsa ciwon ya karu KO?

Raisa ta kwala wani karan tana fadin " wayo mutuwa zanyi

Irfan ya kara damke hanunta ya ce ba zaki mutu ba beby ba zaki mutu ba

Docter Mariam ta gama kimtsawa haka nurses din suma su biyu docter ta dan lalatsa cikin ta ce " Madame ki nisa tun karfi kinji? Ki nisa iya karfinki

Raisa ta kasa nishi , irfan ya kara rike hanunta ya ce " beby kalani mu nisa tare kinji please ki taimaka min mu nisa tare

Raisa cikin galabaita ta ce " bazan iya ba , idan na nisa hanjina zai fito

Irfan ya ce " no bazai fito ba beby kinga idan nima na nisa ai baya fitowa , ya kuwa takarkare yayi nishi tamkar shi yake nakudar

Raisa ta zabga mishi harara ta ce " walah idan ka kuma yi min nitsi sai na kutuhe ka , yo kaine mai cikin bรข?

Docter Mariam da nurse dai suna shan dariyar wanan couple abin abin tausayi sanan gwanin dariya, wai shi ke yin nishin

Tana tsaka da fadan ya dena yi mata nishi ai laifinsa ne kawai sai ji tayi wani nishi ya taho da kansa tamkar an matso shi ta shake wuyan Irfan da yakushi da cizo da komai Docter Mariam ta samu ta zaro beby boy ta mikawa nurse aishe ,

Docter ta laluba ta ce da wani

Raisa da irfan a tare suka ce " da wani ๐Ÿ˜ณ suna zaro ido ,nan da nan shima ya kankama sai ga wani beby boy din

Cikin murna Docter ta yanke cibi ta gyara komai Irfan na tsaye harda shi ake gyare gyaren aka shiryata tsaf ta fito fes da ita su momy kuwa suna can wajen bebys aka turota saman gado akayi dakin hutu da ita

Bayan a gyara ko'ina dakin sai kanshi yake sai ga su Momy sun shigo

Momy mai zata yi banda dariya da ta karewa general kalo , general dan gayu yau a naira biyar ma bazaka dauke shi ba

Shima dariyar yake ya ce " momy a je a kawomin kayana na canja please





๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณto fa zaman jego ba za'ayi?????๐Ÿ˜†๐Ÿ˜†
[14/12 17:35] Sage: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_


73

Jinjina gareki masoyiya *MAMAN MANAL* na sadaukar miki da wanan bbin Allah ya bar kauna


Ci gaban labari
Momy tayi dariya da beby daya a hanunta ta dady Wanda shima sai murmushi yake yana kara tasbihi ga rabbil izati da wanan kyauta mai matukar albarka yaya biyu lokaci guda kuma duk maza ne kuma jikokinsa kai yana kara godewa Allah da ya hada wanan aure yau wai gashi Raisa ce har da yaya

Momy ta ce " Irfan baka daukin yaran ba fa

Irfan ya ce " momy sai nayi wanka na wanke wanan datin sai na daukesu don kar na goga musu datin nan ( to kaji )

Momy ta dan girgiza kai ta ce " uhum ka mayar da hankali kaje gida ka kimtsa sai ka dawo

Irfan ya ce " to ya dan duka ya manawa Raisa kis a goshi baya KO jin kunyar su dady yayi gaba abinsa


Asibitin nan da nan ya cika da jama'a ta ko'ina yan uwa da abokan arziki sai taya familyn Mr president murna ake domin duk wani mai ji da kansa ya tako wajen nan duk da ba Wanda yaga mai jegon da kuma bebyns suna can suna hutawa sai Ilham da Momy a dakin suna rike da yayan ba mai so ya ajiye idan ya dauka


Irfan yana shiga gidansa direct dakin Awatif ya nufa don yi mata albishir din karuwar da suka samu , yana shiga ya tarar da ita tana konce tana shat da wayar ta , da Sauri ya karbe wayar yana ta aikin murmushi ya ce " my Awatif albishirinki

Awatif cikin zakuwa ta amsa da goro fari kar

Ya ce " beby ta haihu ta haifo mana boys biyu

Awatif kwata kwata sai sunan beby ya shige mata ta ce " waye beby?

Irfan ya ce " Raisa mana

Awatif ta zaro ido ta ce " what? Kana nufin ita Raisar ce ta haihu har yaya biyu maza?

Irfan ya ce " yes

Awatif ta ce " kuma an duba da kyau duk da ransu kuwa?

Irfan ya ce " wanan wace irin magana ce haka Awatif?

Sai a sanan ta kula kar taje tayi ya ganeta ta ce " barka husby

Irfan yayi murmushi ya sauka yana fadin bara nayi wanka na koma

Yana shiga bayi Awatif ta rarumo wayarta ta danawa kawarta kira , tana dagawa ta rushe da kuka tun karfinta tana sanar mata cewar yarinyar nan ce ta haihu har yaya biyu maza

Da kyar Lili ta lalabeta ta ce tana nan tafe zasu dauki mataki nan da wata daya domin tayi tafiya kasar waje da niyar yin shekara guda ita da wani balarabe da suke harka tare ( ๐Ÿค” )

Awatif ta ce " ohk ina jiranki


Yana bude dakin da Raisa ke konce ya tarar ta farka tana zaune tana shafa cikinta , Irfan yayi murmushi ya matsa kusa da ita yana fadin beby kin farka ya jikin?

Raisa ta kakaro murmushin mugunta ta ce " da sauki dear

Ya dan kaleta ya matso ganin fuskata a sake ya hau saman bed din ya rungumeta ya ce " na gode bebyna na gode da wanan kyautar allah yayi miki albarka

Raisa ta talabo fuskar sa ta ce " no My me , ba ni zaka yiwa godiya ba , kawai ka godewa Allah domin shi ya bamu

Irfan yayi mamaki kwarai da abinda ta ce gashi tana kalonsa cikin ido wata kasala ta saukar masa ya matso a hankali zai hade bakinsa da nata sai gani suka yi an bude kofar su anti lailatu ne har sun iso ganin bebys da mamar su ,

Anti lailatu ta kali Irfan ta ce " Au har ta farka ba ?

Irfan ya ce " eh ta farka saukar yaushe?

Anti lailatu ta ce " saukar yanzu suna tsaka da gaisa sai ga su Ilham da bebys da Afane tana ta tsale tana dada fadin bebynsu ne har biyu bebys biyu mamamarta ta kawo mata

Ilham ta mikawa Irfan guda , nurse ta matso ta dorawa Raisa guda a cinyarta , Raisa tayi tsai tana kalon yaron ta kama yatsarsa tana kalo ta juya shi ta kuma juyo shi kawai sai ta bushe da dariya tana fadin " Afane wly yana motsi hahhh kuma idanuwansa a bude zo kiga

Su lailatu kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya domin kowa yayi tsai ne don yaga zata so yaran KO bazata so su ba ?

Haka sukayi ta jagular yayan wai dole sai sun yi dariya shi kuwa ya dage sai hotuna yake daukar su gwanin kyau , har suka fara kukan yinwa ta mikawa Ilham tana fadin a basu madara yinwa suke ji

Ilham ta kaleta ta ce " madara fa yo ta jikinki fa?

Raisa ta kale ta ce " wani irin ta jikina ai da kunya na daga rigana gaban mutane na basu wanan abin ta nuna mamarta


Ilham ta kali Irfan Wanda yake kalon bakin Raisa tana magana , a ranta ta ce oh ikon Allah wai yayane zaune haka yana kalon bakin mace uhum

Ta ce " yaya gashi yinwa suke ji ta ajiye copin da ta gama dama mata kunu tayi gaba abinta

Irfan ya dauko bebyn ya kaleta kalar tausayi ya ce KO ni ma na fita idan kunya kike ji?

Raisa ta turo dan karamin bakinta , yayi murmushi ya zauna ya kama ya fitar da mamar ya gyara konciyar bebyn ya saka masa mamar a bakinsa ta rufe domin ana saka masa ya cafke ta janye da sauri tana fadin wly zafi bana so

Irfan da hanunsa ke karkarwa ya ce " sowie beby please dan yi hakuri kinji kar sabon bebyn suyi rashin lafiya kinji? Haka dai da lalaba ta shayar da yaran


Da yama aka basu salama Momy tayi ruwa tayi tsaki ta ce ai kawai gidanta za'a fice da su bazai yiwu a tafi da jarirai haka ba

Bรข yanda irfan ya iya haka suka fice gidan Momy a ransa ya ce " ai kuwa zan kauro ne nima
[14/12 17:35] Sage: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_



74

Shirye shiryen suna ake ta kowani bangare ba gidan Mr president kadai ba kai harta cikin garin ko'ina kabi zancen bodyguard ta haihu ake jama'a da dama sunyi mamakin yaushe ta reni cikin domin tun da cikin ya girma tayi zamanta a gida , wasu kuwa fadi suke aa abin mamaki idan ka gansu cikin TV bazaka taba cewa matarsa ce ba domin tana tsaye kikam a bayansa da bakin glas sanan bazaka taba lura da suna wata alama da zata nuna cewar matarsa ce ba , sun iya takun su
Wasu kuwa su ce ai an haifi zafi domin zafi da zafi ne suka hadu wato General ND bodyguard

Bangaren Raisa kulun sai ansha Daru da ita wajen wankan ruwan zafi ta kuwa takarkare ayi ta dirka kokowa da ita duk sai ta watsawa mai yi mata wankan domin idan aka BArta ita kadai ba yinsa zata yi ba , gashi haihuwar daya ma ya aka kare balatana biyu dole sai ta sha gashi karta danyace ( ๐Ÿ™Š )

Irfan kusan wunin a nan yake yi har hutu ya dauka a wajen aiki don ya ringa wuni wajen matarsa da kuma yayansa , haka Awatif tana kai zuciyarta nesa tazo ta wuni da su domin Lili ta fada mata ta nuna tana son yaren dan KO sun aikata wani abu kar a zarge su



Konci tashi har ranar suna ta zagayo a wanan rana naga jama'a ba kalar fatar da babu ba kalar mai mulkin da babu kowa ka gani wane ne KO dan wane , harda aban Imran ya halarta a wanan suna yaren sunci sunan Muhammad da Boureima sunan dady da Aban Raisa suka yi musu lakabi da Farid da Fadel

Cikin gidan suna canjin kayan da su Raisa suke yi baya faduwa kuma kowane ta saka sai kaga tamkar a jikinta aka dinka su wato suna matukar yi mata kyau takanas Ilham ta kirayi masu make up suka zo da niyar wuni duk kayan da zata saka sai an canja kalar kwaliya sanan a daura mata dan kwali sun sha hotuna harda yarinyarta da kakaninta na wajen uwa suna matukar murnar yanda Afane bata kukan rashin uwa domin suna hankalce da duk motsin da Raisa zata yi sai ta ce a duba mata bebynta fa gashi duk kayan da ta canja sai an kamo Afane an canja mata sanan su dauki hotuna itama daga anyi wani abu a wajen sai ta dawo ta ce mamamana kinga anyi kaza a aje idan na dariya su dara idan na haushi ne su ji haushi idan na gargadi ne ta gargadeta su dai basu da bakin godiya sai adu'a da suke yiwa Raisa allah ya taimaketa itama a rayuwarta

Kayan barka special daki guda ne aka ware tankamemen shi kar kaso kaga kayan sunan da ake budewa ana zubawa , gaskiya kayan ba kadan bane wasun harma yayan su girma baza'a saka musu ba koda kuwa a wuni za'a ringa canja musu kaya sau biyar biyar ne ( ๐Ÿ˜ )
Cikin konciyar hankali aka ci suna aka watse kowa ya kama gaban sa sai su anti lailatu suma a washe gari zasu fice garinsu




Konci tashi har su Raisa sunyi sati biyu da kwana uku yara sunyi bulbul da su domin ana hada musu da madara saboda tsotsa ne da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login