Showing 75001 words to 75972 words out of 75972 words

Chapter 26 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Amnoor   

19 Aug 2025

6005

sai soja )




A gurguje

Bayan shekara shida gaba daya duniya tayiwa Awatif da abanta zafi domin bayan sakin da aka yiwa Awatif abanta suna zuwa gida mahaifiyarta ta nuna sam ba'ayi daidai ba don mai dadyn Awatif zai bi bayan yarsa? Ai bincike yana da dadi hakan yasa suka samu mugun sabani har ya kai ga saki tsakanin mahaifiyar Awatif da mahaifinta , ta tatara ta koma gidan mahaifinta banban malamin islamiya , bayan rabuwarsa da matarsa rayuwa ta fara canjawa domin ba'a yi wata hudu ba aka zige shi daga gurbinsa na minister domin bincike ya nuna cewar nan da shekara biyar ya dauki kudin gwomnati wajen biliyan biyar ya batar ba ta hanyar ci gaban kasa ba hakan yasa aka tsige shi aka amshe kadarorinsa

Cikin tashin hankali ya nufi gidansa da niyar su tatara shi da yarsa da yan kudadansa da yake ajiyewa a gidansa su bar kasar , yana shigowa ya nufi dakin Awatif da Sauri tun kafin ya isa ya fara jin nishin mutane tamkar ana wani Abu , baiyi kasa da gwuiwa ba ya tura dakin ya shiga abinda ya hango ne ya saka ya kusa suma a tsaye da gudu ya nufesu ya shiga tafkarsu dukansu yake tun karfinsa su kuwa
Sun kasa amsar kansu domin sai da suka gama mayensu sanan suka tafka masha'ar su ( subahanalah ) cikin maye awatif ta mike ta rike hanunsa da yake tafkar Lili cikin zafin nama ya juyo ya hankadata ta gamu da garu karfen kofar ya caketa a kai nan ta silale bayan ta kwala ihu , ihunta yasa mahaifinta juyowa abinda ya gani ne yasa shi tsorata domin yarsa ta cikinsa ce konce jini yana tsartuwa ta kanta bakinta a dage idanuwanta har sun kakafe ya dora hanu a saman kansa yayi wajenta da gudu yana girgizata yana ihu daidai nan motar polisai ta shigo gidan domin an turo su kama shi don kuwa an dauki maganarsa wada ya taba hada hanu shi da elhaj mai mata aka kashe tsohon minister suna shigowa suka tarar da abinda yake faruwa , aka kwashi Awatif akayi asibiti da ita aman ina ta dade da mutuwq rai yayi halinsa , shi kuwa mahaifinta ya zauce sai tona kansa yake irin abubuwan da ya aikata ( ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu , Allah kasa mu cika da imani amin ) haka aka turbude Awatif sai hali sai sallah shi kuwa mahaifinta akayi prison da shi


Rayuwar Raisa Da irfan da yayansu rayuwace cike da son juna duk da yayan a gidan su momy suke aman hakan bai hana iyayen basu kulawa daidai gwargwado ba

Koda yaushe suna office idan suka dawo su kula da yayansu wataran gidan su momy ma suke kwana ba ruwansu , sosai Raisa ke yin kokari wajen ganin ta biyawa mijinta duk wani hakinsa a ko'ina yake bukatar hakan babu ruwansu hakan yasa ya kara kaunar matarsa Bodyguard dinsa


Dady ne zaune yana ta nishadi cikin jikokinsa , Raisa tana yanka fruits a gefe Momy tana yiwa hajiya khadija kitso manya a saman kanta Ma ta goya beby Ihsane mai wata uku da haihuwa ,

Wata yan mata naga tana saukowa da bakin glass a idanuwanta da katon takalmi na sojoji ta dadaure kafafuwanta da igiyoyi tana saukowa ta tsaya gaban Raisa da irfan ta Sara musu tana fadin GeNERAL an gama shirya komai muje

Raisa ta bushe da dariya ta ce " kai beby ba haka nake yi ba fa

Affane ta cire glass din tana dariya ta zauna tace" mamamana ina son na zama tamkar ke

Irfan ya ce " bebyn mamarta zaki zama tamkar momynki insha Allah

Ta Mike tace " yeah i love u dadd i love u mamamamana

Raisa tana dariya ta ce " i love you too bebyna

Elhaj Muhammad Ibrahim ya lumshe idanuwansa yana yiwa Allah godiya da ya bashi iyalai masu matukar kaunar junansu




ND, fin




Ina mai matukar farin cikin ganin karshen litafina *DuK karyar kada ta ruwa ce* tabas nayi litafin nan ne domin na nishadantar da masu karatu sanan fadakarwana a wanan litafi shine inayiwa iyayenlu Jan hankalin daurewa yaya gindi kan yanayin rayuwa idan Allah subahanahu wata'ala yayi ka mai arziki kar kayi anfani da wanan damar wajen sangartar da yaro , sai abu na gaba ina matukar alfahari da rayuwar Raisa domin ta kasance mace mai kwazo duk da irin yanda take mu'amala da maza hakan baisa ta zubar da darajar da Allah yayi mata ba hakan ya jawo kauna tsakaninta da mijinta irfan , ya ku yan matanmu mu sani daraja daya ce mu kama mutuncin mu don mu rabauta duniya da kiyama Allah yasa mu dace



Dole nayi jinjina ga Exclusive writers gaba dayanku kun zamto yan uwana na jini ina kara rokon Allah da ya barmu tare Sanan ya kara daukaka fadakarwarmu


Auntyna Amnoor yar uwata sanan malamata Allah ya kara kauna

Aunty queen jinjina gareki

Gaba daya mumber na Exclusive writer ina kara Mika gaisuwata Allah ya kara kauna tsakanin mu

Grup Andiya , mata masu aji, Aunty fauza grup , ina Mika gaisuwata Allah ya barmu tare

Dukan marubuta ina kara jinjina muku ina rokon Allah yasa aikin mu mai anfani ne , Allah ya hada kawunan mu yasa mu ci gaba da fadakarwa da kuma nishadantarwa cikin amana

Writers na gode ina cikin godiya na bina sau da kafa har muka ga karshen wanan litafi Allah yasa mû anfana da shi baki daya

*Ina neman gafarar duk Wanda na batawa domin duk dan Adam ajizi ne ma asalam daga mai kaunar ku yar mutan Niger SAJIDA*










Love 92245338 u









🤷🏻‍♀

BYE-BYE

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login