Showing 72001 words to 75000 words out of 75972 words

Chapter 25 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Amnoor   

19 Aug 2025

5985

" kawai kalar abincin nan ne sai naga tamkar tsutsa a jikinsa

Ilham ta saki baki ta kamo hanun Raisa ta tsareta da ido

Raisa ta ce " meye ?

Ilham ta ce " are u pregnant?

Raisa ta bushe da dariya tana tsaka da dariya sai naga ta dora hanu a kanta ta ce " na shiga uku wayo Allahna muje gida muje ta kuna motar ta figeta a guje , Irfan ya mike ya juya da Sauri bodyguard dinsa suka bude masa motar ya ce subi bayan motar madame , suka ce " OK sir suna Sara masa


Tafiya suke sai da suka ISO daidai wata Babar pharmacie suka tsaya Raisa ta sauko suka shiga suka sayo test na pregnant shi dai Irfan yana hangensu a ransa yana tunanin waye ba lafiya kuma? Suka daga suka nufi gida , suna zuwa da gudu Raisa tayi sama tayi dakinta ta shige bayi da gaba daya abubuwan gwajin ita kuwa Ilham ta zauna tana gumtse dariyarta daidai nan Irfan ya shigo ran nan nasa a hade tamkar hadarin gabas ya zabgawa Ilham harara ta mike da Sauri har tana tuntube ta fita a dakin

A hankali ya tura bayin ya shiga ya tarar da Raisa ta jera yan kananuwan robobin dake cikin abin gwajin ta cire doguwar rigarta tana famar cire pant dinta ta hangoshi ta miroir ta zaro ido shi kuwa ya nufota ya daga hanunsa ๐Ÿ™†๐Ÿ™†๐Ÿ™†๐Ÿ™†








To fa shin Raisa ciki ne da ita ga yara da wata uku? Irfan zai daki Raisa ne na ta FITA bada izininsa bรข? Wai shin meye dalilin fushin Irfan ga Raisa ne? ๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž
[14/12 17:36] Sage: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_




81

Mahaifiya , Mamana Allah ya kara girma na gode sosai da irin yanda kika fahimci rubutuna da yanda kika bani kwarin gwuiwa Allah ubangiji yasa ki gama da duniya lafiya , ina rokon Allah ya sa iyayenmu su gama da duniya lafiya sanan yasa aljana ce makomar su




Ci gaban labari


*Masarauta*

Hajiya bilkisu ce zaune tana duba agogon hanunta sai dan murmushi take yi jakadiya ta shigo ta duka ta gama kirarinta ta ce " uwargijiyata an gama komai sanan motocin yarima sun iso

Hajiya bilkisu ta sakarwa jakadiya murmushin da bata taba yi mata ba ta ce " to a kara gyara wajen cin abincin nasa kinsan yarima da abinci sai yaci yake hutawa , tana tsaka da maganar sai gasu sun shigo da mai martaba da kansa sai murmushin murnar ganin dansa duk da yana tunanin irin amsar da zai baiwa Hajiya bilkisu na daura auran Imran da yar kasar indiya suna shigowa Imran ya kali mahaifiyarsa wata soyayarta ta mamaye masa zuciyarsa ya saki murmushi ya isa da sauri yana kokarin dukawa dan ya gaisheta da Sauri ta dagoshi ta rungume shi tana shafa kansa a hankali tace " son my lovely son

Imran cikin yar kwalarsa ya ce " my mum i love you

Da kyar ya saketa sai kalonsa take tana kara taba fuskarsa shi dai mai martaba yana gefe saman babar kujera yana kalonsu , chrishna ta matsa a hankali ta zugunna ta taba yatsun Hajiya bilkisu irin yanda sukeyi din nan taki dagawa Hajiya Bilkisu tayi Sakai tana kalon wani sabon lamari

Imran ya ce " momna ki saka mata albarka kinsan a can sai an saka musu albarka suke dagawa

Hajiya bilkisu ta ce " su suwa?

Imran ya dan Sosa kansa ya waiga ya kali dadynsa yana nufin yayi magana , dady ya Mike tsaye ya ce matarsa ce

Hajiya Bilkisu tayi wata irin waigowa ta ce " what? Matarsa? Wata irin matarsa? Wa ya aura masa ita? Bazai yiwu ba wly bazan yarda ba , haka kawai kayi gagawar sakinta KO nayi maka baki , bayan na zaba maka matar zaka zo min da wanan aljanar?

Elhaj Abdurahaman ya hade fuska ya nunata da yatsarsa guda ya fara magana cikin kakausar murya ya ce " Ke Bilkisu ni ubansa ni na daura masa aure da yarinyarnan domin suna son juna , ban lamunce miki ki ringa hantararsu KO muguwar magana KO kice ya saketa idan har kika aikata haka bazan taba yafe miki ba , kuma karki manta a matsayin baiwa kike na yanta ki na aureki duk dan Adam dan Adam ne ba Wanda yafi wani a wajen Allah sai Wanda yafi tsoronsa dan haka ki fita a idona ki bar yaro ya raya aurensa KO na saba miki , KO ki zaba Imran ya saki matarsa nima na sakeki

Su duka suka dora hanu a saman kansu da Sauri Imran ya karasa ya tsuguna gaban dadynsa ya ce" tuba muke ranka ya dade tuba muke ayiwa mahaifiyata hakuri tuba take Allah ya huci ran mahaifina


Mai martaba ya shafa kansa ya ce " Allah yayi maka albarka tashi kuje kai da matarka ku tafi gidanku Allah ya baku zaman lafiya , ba yanda ya iya haka ya mike ya kama hanun chrishna Wace ta zamto tamkar kurma tana kalonsu ita dai bata san mai suke cewa ba , aman ita ta gane cewar akoy abinda yake faruwa ta juya ta bi mijinta a ranta tana cewa koma meye oho tunda mijinta yana sonta



Wasa wasa mai martaba ya kasa ya tsare ya hanata yiwa Imran magana kai ita ta samu ta Ganshi ma ya gagara , gashi sam mai martaba ya fita a harkarta KO gaisuwarta tasan dan yana tsoron hakin musulunci ne yake amsawa , duk tabi tayi wani duhu ta fice a hayacinta burinta kawai su sasanta

Yau da sasafe ta samu bayan mai martaba ya shiga fada ta fito cikin banda kama gudun kar a fada masa zata fita ya hana ta samu ta fice a kafa sai da tayi tafiya sosai ta samu ta tsayar da adaidaita sahu ta shige tayi masa kwatancen gidan yarima ya kama hanya da ita yana tafe yana zuba mata labarin ai sarki mahaifin yaron da yaron akoy kirki , matarsa ce mutuniyar banza ita kuwa ba kowa ba domin baiwace ya wanketa ya aureta tazo tana raina masu yanci , ya dan juyo yace " baki sani ba baba ai yarima shi ya birge ya auro yar indiya idan yaso ta hadiye zuciya ta mutu sarki ya auro yar daraja domin wanan kai ba yar gidan girma bace

Hajiya bilkisu jikinta yayi wani irin sanyi tunda mai martaba yayi mata tuni da KO wacece ita gaba daya rayuwarta ta dawo mata sabuwa bata da aiki sai tunane tunane shin ya akayi ta koma haka? Hawaye ya ziro mata zuciyarta ta bata amsar giyar mulki da kuma zugar kawaye bata san har sun ISO ba sai da mai adaidaitar ya ce " to hajiya ki kawo kudin

Sai a lokacin ta tina cewar haka fa ta fito sai wayarta gabanta ya fadi ta ce " dan dakata na shiga na karbo maka

Dan adaidaitar ya ce " au munafurtata zakiyi da KO kudin mashin din bakida shine kika shigar min? To wly bazan yarda ba kawai ki bani kudina hajiya eh haka kawai rashin tausayi?

Hajiya bilkisu ta kali wayar hanunta a kala zatayi dubu dari biyu ta dago ta kali mai adidaitar da ya tsareta tamkar tayi sata da Sauri ta Mika masa tana cewa karbi karka tara min jama'a ni

Mai adidaita hanu na karkarwa ya karbi waya yana jujuyata yana zaro idanuwansa ya ce " kai wanan a ina kika samu karbi abinki ke da Allah bazan karbi abin SATA ba aje a kamani ke da Allahnki , ta wurga mata wayar yayi gaba abinsa , haka ta duka ta dauke tana ta jiri domin duk sai taga garin yayi mata wani irin girma ta juya ta nufi get din gidan danta tana isa masu tsaron kofar wato dogarawan kofar suka ce sam idan bata cire abin fuskarta ba bazata shiga ba domin su dai ba'a fada musu za'ayi bakuwa ba

Hankalinta ya tashi tasan idan ta bude tabas labari sai ya jewa mai martaba cewar itace aman kuma wata wahalar tafi wata hakan yasa ta yaye mayafin fuskarta , suna ganinta gaba daya suka zube suna kwasar gaisuwa , ina yau ba kanta bata tsaya yi musu gadara ba burinta tayi arba da gudan jininta , ta ratsasu tayi cikin gidan danta

Tana shiga ta tarar da shi da matarsa suna cin abinci sai murna suke suna raha ta dade tana kalonsu ta windows a hankali ta zagawa ta dana karaurawar dakin , chrishna ta aje plat din tace bara ta bude

Imaran ta mana mata kis ta taho ta bude dakin , tana budewa taga mamyn Imran tayi murmushi ta hade hanayenta ta ce " namaste ma

Hajiya bilkisu ta kakaro murmushin karfin hali sai ga Imran da Sauri ya ce " mum mum kece? Lafiya mom? Mai ke damun ki?

Hajiya bilkisu ta ratsa ta gefensu ta isa maimakun ta hau saman banbar kujera sai ta zauna kasa Imran ya biyota yayi Saurin zama itama chrishna ta zauna a kusa da shi tana bin mum da ido

Hajiya bilkisu ta nisa ta ce " tabas naga rayuwa ni Bikisu , sai yau na gama yarda cewar mutun shi ke jawa kansa mutunci da akasin haka , ni ban gyara gidan auren nawa ba , ni ban bar dana ya raya tasa rayuwar ba , ta dago ta dubi Imran ta ce " dana ka yafe ni

Da Sauri Imran ya dora kansa a saman cinyarta yace i love u mum i love u please ki manta wly ni banida sama da ke please ki yafe min nima please

Mum ta yasha kansa ta ce " na yafe maka son kumuje gurin mai martabar ( tofa daman yan magana suna cewa idan ka raina inda kake inda zaka ya rainaka duniyar Kenan Allah kasa mu dace )







Abuja

Irfan ya tako cikin bacin rai ya ISO ya daga hanunsa ya tura raisa jikin garun bayin ransa a matukar bace ya ce"










๐Ÿ˜•๐Ÿ˜•๐Ÿ˜•๐Ÿ˜•๐Ÿ˜•๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
[14/12 17:36] Sage: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_





82
Cikin hot voi ya ce " wa ya baki damar yin irin wanan adon ki tafi gaban mazan nan Raisa?

Ta kama da kyar ta kwace kanta ta rufe ido ta ce " mai hadina da kai GENERAL ? Mai nayi maka kake marmarin halakani? Dan na hana ka kashe matarka? KO don an raba ka da masoyiyarka ?

Irfan ya dafe kai ya ce " chiiiiiiiiit abinda kike tunani Kenan?

Raisa ta tare da sauri ta ce " eh hakan nake tunani kuma tunanina gaskiya ne , dan haka nima kasan kayi aut da ni domin banga ribar zamana a sunan mai miji ba , gwara na samu daidai ni

Cikin zafin nama ya hadeta da garun ya matseta gam yana huci ya ce " abinda nake gudu kenan har na dan daga miki kafa my Raisa you , you , you are mine " babu wani dan iskan da zai rabeki sai dai idan bayan raina ne , tsoron irin hakan yasa na zauna nayi dogon tinanin gyaran aikina da ke , bazai yiwu kina nesa da ni ba koda kuwa tafiya ce ta kamani dole muje tare , Raisa ki zamto jinin jikina idan na rintse idona na hararo wanan matar gabana yana kara faduwa ni banyi zina da matar wani ba , ni anayi da tawa matar , Dole na firgice dole na tsorata da lamarin mata i'm sorry Na-san ke ta dabance nasan a yanda na sameki duk irin gwagwarmayar da kike sha cikin maza na sani sarai aman duk da haka na tsorata , ya nisa ya sasauta mata rikon ya hade hanayensa guri biyu ya ce " i beg u wifey ki dena ambatar kalmar saki a gabana zuciyata na iya bugawa i beg u ,


Raisa jikinta yayi sanyi Kenan dai kishi ne da tsoron kar itama ta aikata masa hakan yasa yake shareta , lale Irfan bahagume ne a hankali ta dora kanta saman fafadan kirjinsa ya rungumeta su duka suka saki ajiyar zuciya a tare kuma sai suka yi dariya ya shakuni hancinta ya tsurawa bakinta ido nan da nan ya fara tinanin cafke shi , ganin irin kalon da yake yi mata yasa ta tura shi kadan tana cewa , my being kaga dakata akoy wata matsalar fa dakata na gama test din nan

Irfan ya juya ya kali jeran yan kananuwan robobin ya dauko gidan test din ya duba ya zaro ido ya ce " life are u pregnant?

Ta ce " Allah ya kiyaye gwadawa zamu yi idan har cikine da ni wly bazai yiwu ba cireshi za'ayi

Irfan ya kaleta da sauri ya ce " cikin?

Ta ce " eh , please ka dan dakata daga waja nayi fitsarin na gani

Irfan ya girgiza kai a ransa ya ce lale akoyta yarinya , a fili ya ce ba komai ke dai kiyi kawai , domin yana tsoron tayin kafin ya shigo ta zubar ( to kaji tamkar ruwa dai ?)


Ba yanda bata yi ba ya kiya hakan yasa tayi a gaban nasa gaba daya result daya ne positif Raisa ta kwala ihu tana faman FITA ya jayota ya rukunkumeta tana kukan wly bata so , sai da ya barta tayi mai isarta sanan a hankali ya ce " kyautar Allahnce bakya so? KO ni din ne son nawa bai kai a kara haihuwa da ni ba?

Cikin kuka ta ce " General watan 2winc uku fa taya za'a ce ina dauke da wani cikin tamkar kaza?

Irfan ya dane dariyarsa wai tamkar kaza ya ce " kin manta abinda fiyayan halita ya ce damu ? Cewar mu hayayafa domin gobe kiyama yayi alfahari da mu? Haba my beby yanzu fa kafin ki haihu sunyi shekara fa kinga daman basu wani damu da nono ba sai kawai mu yaye su KO?

Raisa ta ce " daman momy ta fada min sai da tagargadeni naki sauraronta , salon nayi ta zuba yaya na tsufa ka kyalaro wata sabuwa KO?

Irfan ya ce " astaghfrulah wane ni ? Haba beby ba wata kuma anyi daya ba za'a kuma yin na biyu ba , kuma wa ya fada miki jikinki na tsufa ne? No ke KO yaya dari zaki haifa kina nan a yan matana ya karasa fadi yana sakar mata murmushi ,

Raisa ta sakar masa murmushin itama ta rungume shi a hankali yayi mata rada a kune , ta bushe da dariya ta ce ina sam ta kiya salon ya kara mata hani?

Irfan yayi kalar tausayi ya ce " please ki bani mana bazan kara wani ba , dan dai su kara kwari ne

Tana dariya tayi gaba da gudu ya biyota yana fadin karta lahanta masa yaya ( to kaji mai yaya ) ,

Bayan sun gama sunyi wanka ta canja kayanta suka fito banban falon inda suka tarar da su momy , su duka da kalo suka bisu

Momy a ranta ta ce " au har an shirya , a fili kuwa ta ce " bebyn momy zo ki shayar da yaran nan please kinga yau fa kwatakwata basu sha ba ni ban taba ganin iyaye irinku ba sai iya selfi da yara ba'a iya tatalin su ba sai yaushe zaku zauna da yayanku?

Irfan ya kali Raisa itama ta kaleshi a tare suka ce " an yaye su

Momy ta dago ta sauke idanuwanta saman kansu tana yi musu kalon KO sun haukace?

Irfan ya dan kakaro murmushi ya ce " am momy daman yau akace an yaye su

Momy ta ce " wani mahaukaci ya ce din?

Irfan ya kama baki ya ce " tofa momy momyn beby gwara a yaye miki jikokin ki kinga mission zamu tafi

Momy ta ce " ai KO uban mission zaku tafi sai ta shayar da yaran nan kaji min yaya marasa tausayi ku fita a idona na rufe wly

Irfan ya ce " momy rayuwar soja ce haka mu duka sojoji ne dole mu baiwa kasar mu kulawa

Momy ta ce " kasan Allah irfan ka FITA a idona ba sojoji ba mutuwowi kaji yaro da zancen banza ke Fatima ba zaki kama min ba?

Ma da take bin su da kalo nan ta karewa Raisa kalo tabas Raisa cikine da ita domin tayi wani fari ba farin jego bane , ita inama tayi wani jego? Sanan gashin kanta ya kara zama baki wuluk ta juyo ta kali momy ta dage sai fada take kan a shayar da yara a ranta ta ce " ku kuwa haka zakuyi ?

Ma ta ce " momyn yara dan dakata mu gani

Momy ta ce mai zamu gani kuma?

Irfan ya kara gyara zama ya fara jawo musu aya yana fasarcewa yana yi musu nuni da haka Allah yayi

Momy ta hasala ta ce " irfan shin ka manta mu muka haifeka ? Gidan ku kaji KO? Bazaka fada min dalilin yaye yara da kayi?

Irfan ya Mike tsaye itama da Sauri ta Mike ita dai Ilham banda toshe baki ba abinda take tana faman yin dariya tana gudun jawowa kanta Irfan ya damki hanun matarsa cikin yan sakoni ya ce " daman She is pregnant sanan mun kaura gidan mu na vilas , da Sauri suka bar dakin , momy ta dora hanu a kai Ilham ta bushe da dariya , Ma ma dariyar take yi , momy kuwa banda fada ba abinda take yi tamkar ta ari baki

Ma ta ce " to aunty Sai reno 2winc din gashi yau Allah ya baki cikin sauki

Momy ma dariyar ta kufce mata tace" wani abin sai sojoji ( tabas wani abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login