Showing 6001 words to 9000 words out of 75972 words

Chapter 3 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Amnoor   

19 Aug 2025

6016

Momy tayi hamdalah tana washe hakora ta ce muna iya shiga mu ganta docter? Dr Mariama ta ce eh aman please ayi a hankali Madame
Ta juya Momy ta bi bayan ta inda Irfane yayi cikin gida yana shiga ya tarar da Ma dinsa tayi shiru kanta a kasa da mayafi a hanun ta da alama shawara take da zuciyar ta na ta je KO kar ta je sosai yaji tausayin Ma dinsa da sasarfa ya dafa ta tayi saurin kalon sa ta kirkiro murmushin karfin hali tana yi masa ta ce yarona yaushe ka shigo sai kuma ta kali jinin dake jikin kayan sa ta langwabar da kai ta ce eyyah jikin ka duk ya baci maza muje ka bani kayan nan a wanko su ta juya tana kokarin mayar da hawayen da ke kokarin zubo mata da sauri ya rikota ya zaunar da ita ya ce Ma bata mutu ba ai har ta farfado tana dakin hutu Ma
Tayi ajiyar zuciya tayi murmushi tace alhamdulilah yarona tashi kaje ka rabu da kayan nan duk jinine ya bata su ya kali kayan ya ce love u Ma itama tace love you son

Bayan kwana biyu jikin Raisa yayi sauki suna zaune ita da Ilham da Nafisa sai labari suke suna ta sheka dariya Ilham tana basu labarin saurayin ta Samir Wanda take masifar so
Nafisa ta ce anti raisa fa waye mai buga number dayan
Raisa ta warci filo ta cila mata tana fadin ni kam bani da lokacin wanan shirmen ta mike ta shige toilette ta bar su Ilham suna ta labari suna tsaka da labarin sai jin salama suka yi su prince Imran ne da in rakiyar sa sai fadanci suke yi masa shi kuwa ya ci fuska gaban dogaran sa yake sai da ya sami lafiyayar kujera ya luntsume a ciki yayi musu nuni da su bada waje cikin kirari suka fita suka tsatsaya a kofa nan da nan aka cika masa gaban sa da kayan ciye ciye da shaye shaye cikin mutunci da girmamawa suka shiga gaisawa yana ta raraba ido yana son ganin ta inda tauraruwar tasa zata fito suna cikin haka irfane ya shigo da Afane a hanun sa domin yaji isowar su Imran ya Mika masa hanu suka gaisa ya ce soja wuta soja bindiga soja marmari daga nesa yayi dan murmushi ya ce kai kuwa likita bokan turai suka kuma tafawa Fatima ce tayi salama ta shigo da Sauri prince ya zame kasa yana gaishe da ita tana ansawa fuskar ta konce da murmushi daga bayi suka ji ana kugin Ilham kafin ta shiga sai gata ita ta fito kunya kamar kasa ta bude Fatima da Ilham da nafisa su nutse ita kuwa kanta a kasa tana fadin please ja min zip dina na kasa ja wanan daurin ya warware wando ne yanzun ma a jikinta dan dai ba matsatse bane ya dan rike daga kasa sai er ficikar riga Wace hanun dama dogo ne na hagu kuma na shimi ne babu KO bra daga ciki gata mai ZIP ce shiyasa ta kasa sakawa dalilin ciwon dake hanun ta bayan ta gama wanka da mugun takaici Ma ta ja tsaki tana yi mata hararar ke dai kin ji jiki sai a wanan lokacin irfane ya kali wajen ta bai san dalili ba sai ji yayi gaban sa ya mugun faduwa sanan ya ji mugun haushin fitowar ta a haka da sauri zuciyar sa ta ce kai kuwa me ya shafeka sai kuma ya baiwa kansa amsar dalili shine tana er Ma dina ya watsa mata harara ya kawar da kansa Fatima (Ma) ta yi mata nuni da mutanen dakin sai a sanan ta lura da su Ilham tayi saurin ja mata zip din tayi tsaye tana kalon kasa a hankali ta zauna Ma kuwa ta juya ta bar dakin
Barkan ki da warhaka yaya jikin ki fada min yaya kike a hankali ta zuba masa ido ta kuma kali jama'ar dakin inda hankalin ta ya sauka kan general da Afane Wace tun fitowar ta daga toilette take ta daga hanayen ta da maganar ta ta yara tana Mama ni mama tana nufin Raisa ta dauke ta shi kuwa sai kara riketa yake
Ta sakarwa afane murmushi tana kokarin karbar ta ta dan duka da sauri ya kuma kawar da kansa yana ta jan tsaki a ransa a dan fusace ya ce ke kar kiyi ki kayar min yarinya kinji KO taya zaki iya daukan ta a haka
Prince ya furta Raisa cikin kasala da sauri ta juya tana kalon sa sai kuma ta amsa masa ta koma ta zauna irfane ya mike yana fadin kaga Malan ina jardin idan ka gama da yayan cikinka ka iso yayi GABA abinsa bayan ya dire afane Wace ta dane cinyar Raisa

Ilham da nafisa suka silale domin sun lura Imran na son yin magana da Raisa
Cikin nutsuya ya shiga fayace mata abin da ke ransa ita kuwa kawai sai ta bushe da dariya tofa😳😳 abi yazo ga gwanai kukan aure da salalami
Tace prince shin da wa kuka saka wanan gasar KO wani abu ka sha dai KO kuwa mafarki kayi? Idan kuwa ba daya lale kana bukatar shiga asibiti shin me zakayi da kato dan uwanka???? Kaga ni fa katone duk abin da kato zaya yi nima zan iya kaga ni ban iya ado ba ni ban iya kwarkwasa ba ni ban iya daura Zani ba ni ban iya girki ba a tsaitsayen nan haka nake so please ka dena yaudarar kanka ka dauko yarinya mai suna mace aman ba ni ba
A nitse ya taka har gaban ta ya dan gurfana gaban ta ya ce ki yarje mini ni kuwa nayi miki alkawarin zan nuna miki akoy abinda namiji zai yi Wanda mace bata isa ta aikata shi ba kuma zan nuna muki yes kema macece domin ke Zara ce zan nuna miki duk girman mace da karfin ta da takamar ta a kasan namiji take domin NAMIJI BAYA kadan na (Aisha)
Tayi murmushi tana fadin sanun ka da kokari prince aman da kake wanan zane kai fa dan gata ne baka san meye wahala ba ni kuwa soji ce ban san meye hutu ba
Ya kuma yin murmushi mai birgewa ya ce eyyah i love you Raisa
Sai da gaban ta ya fadi domin bata taba kawowa ranta cewar watarana itama zata ji wanan kalma daga bakin namiji tayarda tabas allah gafurun Rahim ne gagara misali
Ta kalesa tayi kalar tausayi tana fadin kayi kokarin koya min sonka
Yayi Saurin fadin thank you my love da wanan damar da kika bani insha allah zaki amsa Kiran Madame Imran Raisa suna cikin tataunawa yana gyara mata bandejin da ya warware yana gamawa daya daga cikin dogaran ya kwala salama sai da ya gama ya luluba mata mayafi ya bada umarnin a shigo ya shigo yana mikawa prince waya ana kiransa ya daga ya kara yana salama daga dayan sharen aka amsa sa...........
Love u β€β€β€β€πŸ˜‰
+227
92
24
53
38
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kado🐊🐊 ta ruwa ce🌧🌧🌧na SajidaπŸ€”
🐊🐊🐊🐊🐊🐊🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊
11

Aba yace son mun gama komai da iyayenka kasan rigimar su ai kawai tare zasu tafi saudiya idan sun yi sala bayan azumi suyi sayayar lefe su biyo ta dubai su kuma yin oder komai sai su dawo aman ni sai kusan salah zan tararda su so kaga bayan salar azumi da wata daya sai a daura aure
Irfane ya ce OK Aba duk yanda kuka yi daidaine
Aba ya ce allah yayi maka albarka allah ya jibanci lamuran ka
Ya ci gaba da ansawa a nitse

Beby ki saurareni shin bana baki tausayi ne? Don allah ki tausaya min wly idan baki bada amanar ayi auren mu just bayan salah ina iya shiga wani hali wai ke an fada miki kowa ma irin ki ne? Raisa ce zaune cikin family dinta Imran yayi kiranta yana yi mata korafin shi fa ya gaji da wanan lamari yana son malakar ta a matsayin mata
Ta bushe da dariya ta dan kauce wayar ba tare da ta fadamasa ba da ya kwabeta baranbaramar da zata barko masa cikin dariya ta kali Hajiya Sajida tana fadin Momy kinji Imran wai ya gaji shi fa aure yake so idan ba haka ba yana iya shiga wani hali wai na tausaya masa to goyon shi zanyi ne ta kuma bushe da dariya inda Hajia khadija da Fatima suka rinka sine kai domin sun san inda zancen ya dosa

Ilham ta tayata dariya tana wani abu sai oga Raisa
Raisa ta cuno baki ta ce Momy me nayi kuma naga su Ma sai sine kawunan su suke uwa suna gaban siriki ta kuma bushewa da wata dariyar
Momy ta ce oh beby shin jiya ma ba na fada miki ba'a fadin wasu zancen da zakiyi da saurayin ki ba?
Tace Au harda wanan?

Momy ta ce harda shi
Tayi murmushi ta kali mahaifiyar ta wace garin harare har kamar idanuwanta su fado ta kuma yi dariyar

Hajia khadija ta ce Ilham idan Samir ya shirya ba sai mu hade mu sha bikin mu ba
Da gudu ta tashi ta shige dakin su tana rufe fuska Momy ta ce gulma

Raisa ta ce Momy na fada ?
Tana murmushi ta ce eh fada min ya ta
Ta ce ai shi Samir din ya dade da fadin irin abinda Imran ya fada yanzu Kenan ita bata fada ba to ai ita Ilham din ta ce cikin Sauri ta hadiyi maganar ta tana fadin Aussshhhhhh sanadiyar jifanta da Fatima tayi
Ta dafe wajen tana raurau da ido da gudu ta Mike ta tararda el uwarta domin taga Fatimar na kokarin tardota
Su kuwa mai zasuyi in ba dariya ba sai bayan komai ya lafa hajiya khadija ta ce to hajia alhamdulilah zan kaiwa Elhaj wanan labari mai dadi
Momy ta ce duk yanda kika yi Mamar yara su duka suka yi murmushi

Hajia khadija ta sha ado tana zaune tana yi wa Mr president labari mai dadi bayan sun gama cin abinci wanan na daya daga cikin al'adun gidan nan domin Karin shakuwar iyalan,
Ta ce Elhaj ina da albishir fa
Ya tatara hankalin sa kanta ya ce fada min amaryata tayi dariya tana fada masa yanda suka yi da su Raisa abin ya bashi dariya ya ce kai yata masha allah kice cikin ikon allah za'a hade da na yarona
Ta ce eh nima hakan nace aman har aji ta bakin su
A haka na fito na baro master president da hajiya khadija su karasa tataunawar tsakanin su





Washe gari da safe
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kado🐊🐊 ta ruwa ce🌧🌧🌧 na SajidaπŸ€”
🐊🐊🐊🐊🐊🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊
Cikin girmamawa ya ansawa mahaifiyar sa wato gimbiya Balkisa mai gadon zinari Mata ga sarki Abdul Rahamane har ya gama wayar Raisa na kalon sa tana karantar yanayin sa yana gamawa ya kaleta dauke da murmushi a fuskar sa ya ce : sarakuwar ki na gaishe ki
Tayi gaugawar rufe fuska irin taji kunyar nan na ce lale wai su Raisa da kunya sai kuma ta bude fuskar suka ci gaba da tadi har dai lokacin salar la'asar ya gabato ya tashi ya fita domin samun jam'i ita ma ta shinfide Afane wace ta dade da yin baci ta tashi ta shige bayi domin salatar salar.


Haba prince taya zaka zubar min da kima ta a wajen wanan mata mazan ? Wai mai yake rudar ka a tatare da ita? KO dai tausayin ta kake ji ne? Irfane ne ke ta surfa fada har da zufa ga amin nasa wato Imran don yayi masa albishir din samun soyayar Mata maza kamar yanda yake kiranta,
Imran ya ce abokina ka tayani son wace zuciyata ta zaba idan ba hali ka kauda kanka plz domin ina jin maganar ka kuma a ganina Raisar nan fa musulma ce shin idan baka Goya min baya ba taya zamu shawo kan hajia(Balkisa) kasan fa har yanzu bata bar zancen zubaidar nan ba,

Irfane ya dan ja nunfashi sanan ya ce kar ka ce ban fada maka ba ka zubar da girman ka

Imran ya ce a gaba ma yana kyalkyaltar dariya irfane ya tashi ya bar masa wajen mai gaba daya ma cikin bacin rai

Bayan sati biyu
Abubuwa da yawa sun faru ciki har da kankamar soyayar Imran da Raisa Wace a kulun ta allah sai ta barko wani abin na takaici KO kayan dariya KO kayan haushi sam bata san ana dan risinawa idan ana zance da saurayi (sai ka ce Oo) shi kuwa gogan abin na birge shi
Soyayar Ilham da Samir na matukar birge jama'a domin ana gudanar da ita cikin tsafta da soyayar juna
A haka har raisa ta gama hutun rashin lafiar da tayi inda ta koma bakin aikin ta cike da kuzari
General ne gurfane gaban mahaifin sa yana saurarar sa
Aba ya ce................

+22792245338 ❀sajida❀
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kado🐊🐊ta ruwa ce🌧🌧🌧na Sajida😜😜
🐊🐊🐊🐊🐊🐊🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🌧🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊🐊
12

Yau ta kama ranar asabar kenan yau azumi sauran kwana 13 daidai
A yau ne Awatif zata koma gida tun karfe takwas da rabi take zaune tana jiran Irfane domin suyi salama a motocin gida za'a kaita domin ta ce sai ta biya gidan su kawar ta titi bazata bi jirgi ba shi kuwa gogan har yanzu bai shigo ba

Ki maida hankali ki dauko min rayuwata muje na yiwa matata bankwana ; Raisa ta gama karanta abin da irfane ya rubuta ta juyo ta kalesa ta ce na dauko Afane tayi baci shine na shigo na sanar maka

Bai ce komai ba ya mike ya kama hanyar fita ta tataro wayoyinsa tana biye a bayansa da sauri har suka isa wajen motar tasa ta Bude masa ya shiga tayi mazaunin direba cikin kwarewa take murza motar har suka iso da yake da sunan sa jikin motar ba'a tsayar da su ba aka bude musu suka shige
Suna shiga ta bude ta dauki Afane wace tayi lamo tana ta sharar bacin gajiya tayi ciki da ita a hankali take takawa har ta iso wajen shiga ta dan tura kofar da kafarta ta shige tana shiga ta buge mutun kanta a kasa ta ce sowie domin bata son yin hayaniya ta tayar da afane, ita kuwa abin sai ya mugun bata mata rai dama gashi tana ta maman jiran sa bai zo ba ga kuma wanan bakar ta zo ta buge mata er yatsar ta wani haushi ya cika ta sai huci take
A nitse ta shinfide Afane ta juyo domin zuwa dauko wayoyin Irfane da sauran kayan wasan Afane da dan gudu gudun ta ta fito saΓ― taji ance banza jaka marar hankali kawai ta dan rage Saurin da take aman bata tsaya ba ta ci gaba da tafiya Awatif ta kuma cewa marar tarbiya wace iyayenta basuyi bismillah wajen haihuwarta ba jaka marar usili ai bata san lokacin da tayi kukan kura ta kifawa Awatif mari kamin ta farga ta kara mata wani sanan ido a rufe ta nuna ta da yatsa tana fadin ke ki shiga hankalin ki ba Wanda ya isa ya zagar min iyaye na kauda kai sanin darajar iyayena ya sa bana zagin na wasu so ki rufawa kanki asiri domin kan Ma and Pa ina iya aikata komai, daidai wanan lokacin ya kutsa kansa cikin falon sarai yaji komai abin da ya faru dama ya san a rina tamayi kokari
Awatif ji tayi kamar kunan ta ya dade ne bata ji domin a iya tinanin ta tun da allah ya haliceta hanun wani dan Adam bai taba shafar jikin ta da niyar yi mata rauni ba sai gashi yau harda mari marin ma karamar yarinya marar usuli

Gyaran muryar da irfane yayi ne ya maido da hankalin su gareshi Awatif na ganin shi taje da gudu ta rungumeshi tana rusa kuka shi kuwa sai ya kasa gwalarta duk da yana son yin hakan aman gudun kar yarinyar nan ta raina matar da zaya aura saΓ― yayi shiru kawai ya kauda kansa
Ita kuwa ta kare musu kalo sai taji sam bata ji dadin rungumar da awatif tayi wa irfane (to fa Raisa yaya dAΓ―??) cikin kasala ta juya ta nufi dakinta ta fasa dauko kayan tana shiga ta konta tare da rintse idanuwanta tana karanto duk adu'ar da tazo bakinta har ta samu baci yayi awan gaba da ita,

Raisa na barin wajen yayi gaugawar cireta daga jikin sa ya fara magana cikin kakausar murya yana fadin Ma(Fatima) ta kasance kanwa a gurin Momy sanan uwa a wajena Momy haihuwata kawai tayi aman Ma ita ta san dawainiya da ni har yanzu kuma na kan konta saman cinyar Ma nayi mata kuka duk irin girmana don haka ina mai gargadinki bacin rai kar ya kaiki ga aikin da na sani

Da Sauri ta ce sorry husband sorry bazan karaba

Yayi dan murmushi yace ya huce
A haka ta shishiga duk tayi musu bankwana sanan ta kama hanya da dumbin alkhairi da kuma in rakiya

Mafarkin da tayi shi ya saka ta farka cikin gigicewa tana kankame jikin ta mafarkin ya tsoratar da ita shin mai ya kaita cikin lambu da irfane ba a matsayin bodyguard ba aa a matsayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login