Showing 48001 words to 51000 words out of 75972 words

Chapter 17 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Advertisement

Amnoor   

19 Aug 2025

6142

fita zakayi ba?

Yayi jim ya juya yana kalon baba tsohuwa ya ce"" baba aure zan kara a nan kasar

Baba ta zaro ido ta ce " kai kuwa wanan yaro mai akayi maka zaka kara aure?

Ya ce " baba ina bukatar mai sona a kusa da ni

Baba ta shiga tafa hanu tana kalon Raisa wace tayi kamar bata gane mai yake nufi ba tana yiwa bebynta kis a kumatu

Baba ta ce " ke yar nan ke kuwa kina kalon ina har zai kara aure ?

Raisa tayi kamar bata jin mai suke cewa

Baba ta juyo harda hada hanayenta biyu tace:: gememal dan allah karka kara aure yo so kake idan mun koma uwar gida taga laifina?

Irfan ya ce " dan an kara aurene akayi laifi?

Baba ta dan karkata bakinta Wanda duk yayi jan goro ta ce" allah abin godiya to allah dai yayi zabin da yafi zama alkhairi

Irfan ya ce " amin amin baba sai mun dawo , ya mike ya kama hanya Raisa ta bi bayansa ji take kamar zata kife kasa basu zame KO ina ba sai wata Babar kasuwa irfan ya kwashi kayan maza kalar na indiyawa tun a nan ya shiga wani daki ya saka wando da rigar ya dan yafo kalar na wuyan nan da suke yafawa ya fito
Raisa ta zura masa ido a ranta ta ce" toh kaji

Ma'aikatan shagon suka kai musu kayan har cikin mota

Irfan ya kali dreban sojin dake tuka shi ya ce : ka kaimu wajen da za'a samu yan mata masu kyau wa'inda zasu birgeni

Ya dan juyo ya kali Irfan da Raisa ya ce " ohk sir , a ransa kuwa yana murnar ashe dai wanan ba matar general bace ? Kai shikenan ni kam naga mata ( zako kaga mutuwar ka bawon allah)


Wata unguwa suka nufa suna yin parking wajen da yara da mata da kuma yan mata grup grup kowa yana sha'anin gaban sa

Mustapha ya ce " oga ga nan unguwar su kawata ne

Irfan ya ce ohk muje to , Mustapha ya zagayo ya Bude masa kofa ya fito , yana fitowa abinka da taron mata suka fara zungurin juna suna nuno shi , shi kuwa ya harde yana binsu da kalo can ya hango wata tsaleliya gashin nan an tufke shi ta sha sahari dinta cibiyarta a fili kayan ruwan madara ne sai suka yi mata mugun kyau ya daga janunsa ya yafito ta

Ta zaro ido ta nuna kanta da alamar tambayar ita?

Ya daga mata kai kawayenta suka turota

Tana zuwa ta hada hanayenta waje guda ta ce " namaste

Muryar tata kuwa gwanin dadi , Mustapha ya matsa ya amsa mata da namaste Sanan yayi mata bayanin mai gidan sa ne yana son yin magana da ita aman da turanci domin baya jin yaren talgu

Ta ce " ohk ai na iya turancin

Mustapha ya bude musu bayan motar suka shiga shi kuwa shi da Raisa suka tsaya daga waje suna tsaron su , sun dade suna tataunawa kafin ta fito ta je wajen wasu mata suna zaune suyi kuskus dinsu , ta kuma je wajen wasu tsahi suma suyi kuskus dinsu sai gata ta dawo da wani uba ya gaisar da su General sanan ya kamo hanunsa ya hada da nata ya ce " na baka amanar yata merry ka kular min da ita karka walakantata sanan karka canza mata adininta


Irfan ya ce " na gode sosai Ita kuwa ta rungume shi suka shiga bayan motar sai kalamun soyaya suke su kuwa su Mustapha ba mai cewa dan uwansa wani abu shi yana tukinsa ita kuwa tana kalon kasa daga nan ma suka nufi wajen sha ice cream suna isa Raisa ta budewa Irfan mota ya fito ya ce " budewa madame

Wani haushi ya kamata aman bata ce komai ba ta juya ta budewa merry ta fito daga cikin motar sai wata takama take suka shige Raisa na biye a bayansu suna isa suka kama table guda Irfan yayi gaba wajen masu sayarwar ya sayi guda biyu ya kali Raisa

Ya ce " anshi na Merry ki rike mata

Abin ya ishi raisa ta ce"" i'm sorry General ni fa bodyguard dinka ce ba ta wata katuwar banza ba dan haka kai da ka daukowa kanka kai zakayu mata wahala

Irfan ya ce " madame KO dai kina kishi ne?

Raisa tayi murmushi ta ce *kishi* allah ya sawaka ka kara goma bayanta allah ya bamu na gari

Ya hadiyi wani Abu a wuyansa yayi murmushin karfin hali ya hade fuska ya ce mata " toh malama amshi maza muje ki kai mata

Ba yanda ta iya haka ta amso na Merry Wace suna zuwa ta cewa Raisa ta bude mata ,
Raisa tayi kikam taki motsi Irfan ya watsa mata harara yayi mata nuni da ta bude mana

Ranta ya kai kololuwar baci hakan ya sa ta dan kara matsowa kusa da Merry da gangan hanunta ya kwashi karkarwa kawai tana budewa ta juye shi a kan Merry , merry ta zabura tana Duban jikinta ta ce " oh no kayana jikina ya bace har gashina

Irfan ya boye dariyarsa ya taso ya shiga goge mata yana fadin bata gani bane kinsan daman bata taba abu mai sanyi dan dai kar na fada miki ne ki ga kamar na Goya mata baya , muje gidan namu sai kiyi wanka ki canza sababin kaya i'm sorry my merry

Raisa ta maimaita a cikin ranta " gidan mu? My merry? Tap lale Irfan akoy macuci azalumi ranta ya kara baci ta juyo ta ce:::::::::::::::::::::::::::::::::


































Thx
[20/7 12:58] Sajida: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_



57

I'm back , ๐Ÿ˜„, na gode sosai da adu'ar ku allah ya bar zumunci Thank u ๐ŸŠ
Bazan taba dena Mika gaisuwata ga marubuta baki daya ba allah ya kara zakin hanu
My world *EXCLUSIVE* allah ya barmin ku allah ya kara kare mu gaba daya โค




Ci gaban labari

Raisa taji wani irin abu ya tsaya mata a wuyanta har tayi niyar zabgawa Merry mari kawai sai ta juya ta nufi mota tana zuwa ta bude ta shiga tana ajiyar zuciya Mustapha yayi tsai yana kalonta ya bude ya zauna kusa da ita ya ce " Madame yaya dai ? Oga ba ya bata miki rai naga kina fushi?

Raisa ta kare masa kalo ji take kamar ta shake shi a ranta take cewa mai kama da goril sai gani yayi tana mutsu mutsu da baki hakan yasa ya fito daga motar ya BArta domin yaga alamar an bata mata ran sosai


Sai da suka kwashe awa daya da minti ashirin sai gasu sun fito daga wajen shan ace cream din Raisa ta juyo ta zuba musu ido ta canja kayan jikin nata Ran raisa ya kuma baci a ranta tace " shegiya mai kyau (๐Ÿ˜ณ๐Ÿ™Š)


Suna isowa masaukinsu Raisa ta fito KO tsayawa batayi ta budewa General kofa ba ta tura dakin ta shiga suna biye a bayanta tana shiga yarta tazo da gudu da niyar ta dauketa yanda ta saba kawai sai ta kauce ta nufi dakin da ta sauka Afane ta juya tana binta tana fadin mamamamana Shi kuwa Irfan ya lumshe ido a ransa yace *Raisa kishi kike yi KO fushin na sakaki aikin da ba naki bรข? Ya allah ka fahimtar da ni* ya bi bayan Afane ya dauketa domin har ta fara kuka tana Kiran mamamarta da kyar ya samu tayi baci aman sam taki yarda Merry ta dauketa domin bata Santa ba kuma mamarta bata saba mata taje wajen kowa ba

Baba tsohuwa tayi kuri tana kalon Irfan sarai yasan da magana a bakinta hakan yasa ya jata suka fita yayi mata wani zance sai gani nayi tana washe baki tace " aoh ai sai ka fadan ga inda ka nufa dan nan to allah ya taimaka ๐Ÿ˜๐Ÿ˜ ta shiga washe hakora kamar gonar auduga




Raisa na shiga daki direct bayi ta fice ta sakarwa kanta ruwa ta zauna da kayanta a jikinta KO cirewa bata yi ba tayi shiru ruwa na sauka a jikinta harda wayoyinta a jikinta bata aje su ba tayi kuri zuciyarta na wata irin tafarfasa tana son sanin wai duk dan Merry ta Sakata aiki ne ranta yake baci haka? No ai wanan ba komai bane
Ta lumshe idanuwanta kawai sai hoton inda suka fito suna murmushi ya fado mata ba shiri ta mike tsaye kanta ya bugu da panpan dake zuba nan da nan sai ga jini ya fara daso aman KO ta kansa bata bi ba domin abinda take son gaskatawa ranta tana son sanin shin amsar da zuciyarta ta bata hakane KO ba haka bane? Tana son sanin mai ke neman hargitsa mata tsarin rayuwarta? Tana son ta gane wai shin a duniyar take KO ta mutu ? Domin tunda uwarta ta haifeta bata taba jin makanmacin wanan tashin hankalin ba






To fa wai me ke damun bodyguard ne? Ni ma ina son sani muje zuwa duniya labari taku har kulun SAJIDa๐ŸŠ๐ŸŠ
[20/7 12:58] Sajida: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_




58


Raisa tayi tsaye gaban madubin bayin ta kurawa fuskarta ido tana kalon kanta a madubi ita kadai kamar zautata ta dora hanunta daidai zuciyarta ta ce " *da kema kina raye?* ta ci gaba da fadin ashe kema zaki kamu da soyaya? Ashe kinsan idan aka rabi abin sonki kiyi hawaye? Aman kinsan bakiyi mini adalciba, kinsan sam baki kai kanki wajen da ya dace da ke ba , haba kema haba, shin mai yasa kika ki kaunar Wanda har hawaye ya zubar dalilinki duk munin ki duk irin yanda mahaifiyarsa ta nuna bakiyi mata bรข? Shin mai yasa zaki kaunaci Wanda ya kyamaceki? Ya muzguna miki harma yayi raping dinki yana takamar shi ya fi karfinki sanan yana tutiya da girman da aka nada masa saman ki kuma wanda a kulum a gabanki baya ce masa komai ya rungumi mace? Ta buga hanunta jikin miroir din sanan ta kuma silalewa kasa cikin bayin ta kwonta ta shiga rusa kuka tana fadin " Mai yasa komai nawa ba irin na sauran mutane bane? Shin yaushe zanyi farin ciki ni Raisa ? Yaushe zan kuma ganin soyayata dan yanda nake ba dan halayana ba ba dan matdayina ba a idanuwan wani bayan my Imran? Ta rintse ido tana tuna lokacin da Irfan ya tsuguna yana kokarin fada mata zancen banza bugun zuciyarta ya tsananta Jikinta ya kwashi zapi muryarta ta disashe har wata karkarwa take tana furta ta mutu ta lalace can cikin makoshinta ta furta *I LOVE IRFAN I LOVE MY GENERAL I LOVE MY ENEMY*


General zaune yana ta kalon agogon hanunsa yana son shiga yaga Wai mai takeyi ne a dakin kuma yana gudun wani Karin rainin karta gane cewar ya damu da ita ,

Yar wayar dake kusa da shi ta fara nuna jar wuta ya Mika hanu ya dana sai jin muryar mai yi musu abinci yana cewa" an gama abinci, Irfan ya ja tsaki sai kuma ya Tuna ai zata fito cin abinci hakan yasa ya mike ya watsa ruwa domin ya FITA ya ci abinci

Sai da taga zazabi na neman kayar da ita ga wani irin baci da take ji da yinwa kamar mai hakan yasa ta mike da kyar jikinta duk abun jini ne ta cire kayan ta watsa ruwa ta fito ta zurma wata riga ja ta haye gadonta ta lumshe ido sai baci

Cikin bacinta tayi mafarki afane na tsala kuka tana Kiran mamamata firgigit ta farka tana lalube sai yanzu kukan Afane ya dawo mata a fili ta furta oh shuiiiiiit my afane ta diro duk da jikinta ba kwari ta dauko bandeji ta daure ciwon dake kanta ta kali saman bed din jini ya dan zuzubu kawai ta bude kofar tana fitowa taga baba tsohuwa tana kalon talabijin ana labari da turanci kamar Wanda tasan abinda ake cewa gaba daya hankalinta yana wajen Raisa tayi murmushi da sanda ta ISO daidai kusan kafar baba ta dan shafa kafar

Baba ta zabura da karfi tace""""" anabi Muhammadu ka ceceni

Haba raisa mai zatayi banda dariya tana dan rike ciki

Baba tace kaji mini ja'irar yarinya yo ke bakya salama ne ?


Raisa ta ce" ina fa zaki ji salama ke da kike kalon labaru da harshen turanci , wai ni baba kinsan me suke cewa?

Baba tace ohon musu ni dai ba ina kalon su bane kawai ki duba kiga halitarsu kamar yar tsanar Awanne

Raisa ta ce " kai baba ki dena Kiran sunan yata da wani Awane kawai ki rinka ce mata princesses idan bazaki iya kiranta da Afane ba

Baba ta kama baki tace" kaga da yawa inji matar kadan to ai gwara wacen din da wanan ke dai a samu na fatiyar ma ya isa ke da kika kyale yartaki ma tana wajen abanta tana kuka


Raisa ta zaro ido ta mike da sauri ta kama hanyar dakin Irfan saman table ta gansu zaune shi da Merry suna cin abinci gabanta ya yanke ya fadi har zata juya kawai sai ta dake ta nufi dakinsa kanta a sama KO salama bata yi musu ba , tana shiga ta shiga dudubawa can saman bed ta hango Afane tana barcinta

Ta matsa a hankali ta duka zata yaye bargon ta dauketa sai taji muryar Irfan yana cewa " bakya tsoron ta farka tayi miki kukan dare? Kinga kuma harda sabuwar amaryata karta dameta da kuka

Ran Raisa ya baci ta juyo ta kare masa kalo kawai sai ta juya domin tana tsoron kalmar da zata fito daga bakin zuwa ga Irfane

Shi kuwa sai da ta dago ya lura da yanda ta daure kanta da bandeji sanan hanunta ma da alamar ciwo bai san sanda ya karasa ya juyota da karfi ya shiga tataba kanta
Ya ce " ke mai yaji miki ciwo haka a kanki?

Raisa tace " awchhhhhhh karka taba min da zafi faduwa nayi

Sai da yayi tsam domin yanda tayi maganar verry slowly ya dan tsura mata ido jikinta zafi zau sanan jijiyar kanta tana dan harbawa irin idan mutun yana ciwon kan nan mai tsanani a hankali ya dora yatsarsa guda saman ciwon ya dan warware sai yaga kamar cakuwar wani abu ne ya dago habarta yana kalon kwayar idanuwanta , ya kasa gane shin kalon tsana ne KO kalon meye wanan Raisa take yi masa?

Yayi ajiyar zuciya ya saki habar tata sanan a hankali ya ce" mai ke damunki ne Raisa ?

Ta ce " faduwa nayi ta juya a hankali zata dauki Afanne yayi gagawar rike hanayenta Sanan ya ce"" kuyi koncinku a nan ni sai na kwana a falo


Raisa ta ce " Amaryarka fa?

Irfan yaso ya gane KO dai Raisa ta fara jin abinda yake ji ne? Aman sai wata zuciyar tace masa kai ta fada maka fa bata sonka dan haka dena wanan tinanin

Ya ce" aa zamu konta a dakinki ni da ita

Raisa ta dan girgiza kanta tace" no barshi, ya dace ita matar so a kula da ita a wajen da ya dace da ita ba ko'ina ba

Irfan sarai ya gane habaici ta yaba masa ya bita da kalo harta fice da Afane a hanunta ya kuma sauke nanauyar ajiyar zuciya ya juya domin ya saka kuku ya kai mata abincinta








To irfan ND Raisa soyaya๐Ÿค”
๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„
[20/7 12:59] Sajida: *DUK KARYAR KADA๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ๐ŸŠ*
*TA RUWA CE๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง๐ŸŒง*

*NA*
_*SAJIDA*_

_โ™ปEXCLUSIVE WRITER'S FORUM_




61

Ya jayota kiiiii ya nufi cikin gidansa da ita , ita kuwa baba tsohuwa ta diro da afanne a hanunta itama ta nufi wajen iyayen domin da gani wanan ransa ba karamin baci yayi ba duk da bata san me ya faru ba aman gwara iyayen su je kar ya aikata mugun aiki



Yana isa falo da ita suka tarar da Awatif da kawarta suna zaune sun kuna kida suna ta kyalkyaltar dariya

Awatif ta zabura ta ce " my heart kaine KO gizo ne idona yake yi min?

Irfan da har yanzu maganar sa bata zama normal ba ya dubeta yace cikin inda inda""" get O..............out Aaaaaawatif


Awatif ta zaro ido da Sauri ta damki hanun kawarta suka yi dakinta domin taga alamar ransa a bace tun kafin shafi ta shafeta gwara tayi tafiyar ta


Ya juyo wajen Raisa Wace saida taji alamar fitsari zai sako mata ta matsa jikin babar kujera ta takure ta saka kanta tsakiyar cinyoyinta gabanta sai faduwa yake

Ya karaso a hankali ya tsuguna ya ce " *Raisa*

Tayi shiru taki dagowa ya saka hanunsa da ya dauki zafi gaba daya jikinsa wani mugun dumi ya kwasa , ya dago fuskar tata idanuwanta a rufe ruf

Ya ce *Bubbbbude iidonki please*

A hankali ta bude idanuwanta ta sauke su saman fuskarsa

Ya nisa da kyar ya hado kalmomin bakinsa ya ce " Raisa har yanzu kina son Saurayinki ne? Har yanzu baki fara sona ba? Please tell me please

Raisa ta cije tayi niyar rama abinda yayi mata, sanan abinda yake kan yi mata ta ce " *yes irfan har yanzu ina masifar son mijina*


Irfan ya rintse idanuwansa yace no no no kawai sai ji tayi ya makureta ta shiga kakarin amai tana famar ta ceci kanta sai ji yayi an daukeshi da mari an kara masa wani dajin marin yasan wanan ba Hanun momy bane


*DADY* ya samu da kyar suka kwaci raisa Wace har ta kusan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login