Showing 54001 words to 57000 words out of 75972 words

Chapter 19 - Duk Karyar Kada Book Complete by Amnoor.txt

Advertisement

Amnoor   

19 Aug 2025

6048

ce " Wace madame din?

Docter Mariam ta nuno Raisa Wace tayi tsuru itama tana jiran jin wacece kuma zata kwashi kunyar ciki , ai ana nunata ta diro daga saman gadon ta dora hanaye biyu a saman kanta tana girgiza kai ta ce " na shiga uku na lalace wayo ni raisa daman hakane kadara , dan allah ku tsaya na fada muku walahi ba laifina bane momy allah ba laifina bane , Ma kinsan allah ban je na aikata ba wly wly laifinsa ne ta nuno Irfan Wanda yayi galala yake kalon rantse rantsen Raisa kamar Wace tayo cikin shege

Momy ta gumtse dariyarta Ma kuwa ta juya da Sauri zata bar dakin don wata irin kunya da ta darsun mata, ai kuwa da gudu Raisa ta tare kofar tana ta sheshekar kuka hanayenta still a saman kanta idanuwan nan sun kara firfitowa sunyi fulu fulu da su tsakaninta da allah tsoro take ji shi yasa taso tun kafin su tafi indiya ta fadi abinda yayi mata duk don gudun wanan ranar aman firr ya haneta daman Ma tace daga ta yarda haka ta faru da ita zata dauki ciki ne , shikenan duniya ta zageta su momy su tsaneta kowa ma ya tsaneta kuma taje lahira a ci ubanta , ta kara dora hanu a saman kanta ta juya wajen momy ,

Momy ta kasa rike dariyar su docter Mariam ma kawai dariya suke domin kowa ya gane inda zancen ya nufa,

Bara'atu kuwa daban ta fasara zancen ta ce" Momy mai yake baki dariya ne ? Yaya shin baka jin mai take cewa? Ciki ne fa da ita kuma ta rude Kenan bata san bama KO na wanene? Shegiya mai bin maza ba ga irinta ba to ai sai ki nemi ubansa domin Awatif ta fada min yaya kaloma baki ishe shi ba

Ji kake dau Irfan ya dauke bara'atu da mari , sanan ya jayo Raisa yana goge mata hawayen dake shatata a idanuwanta ya damke hanunta don ta dena karkarwar da takeyi ya nuna Bara'atu da yatsarsa ya ce " ki guji sheganta min mata , ki guji zagin min mata domin yayarki ce , wanan cikin ya shafa cikin Raisa ya ce " nawa ne , cikina ne , raisata na dauke da cikina, kuma ina matukar murna da shi, ina murnar zai kasance tsatson abin sona, idan baki manta ba kwanakin baya muna hira ni da ke nake shaida miki ki kasance cikin matan da basa yanke hukunci saman abinda idanuwansu basu gani ba , tabas ni ne nan ishara domin naji kunya marar adadi a dalilin hukuncin da na yanke kan wanan baiwar allahn, sai da allah ya nuna min wanan ta fiye min mai yawo da dogon hijabi dan munafici, ki sani bara'atu Ina matukar son matata kuma cikiin jikinta nawane idan ma baki dena yi mata kalon abinda kike yi mata ba to mu biyu ne karuwan,

Yana gama yiwa bara'atu bayani ya juyo bagan raisa ya jata a hankali ya zaunar da ita saman gadon ya ce " idan da auranki kin san mai zai faru? Momynki zatayi murna ne, Ma dinki zatayi murna ne , dady zaiyi farin ciki ne , ni banma san yanda zan kwatanta miki irin adu'ar da zan rinka miki ba , sanan duniya zata taya mu murna ne, idan kin mutu za'a sakaki aljana ne so dena kuka karki saka rashin lafiyar ki ta dawo please

Raisa tayi shiru ta dan leka tana kalon su momy Wace har yanzu murmushi takeyi aman Ma ta FITA, ta juyo ta kara kalonsa stilll ita yake kalo , ta kuma kalon momy

Momy ta matso tana fadin su dan bata waje

Irfan yayi kalar tausayi ya ce " momy ☹

Momy ta ce " aa general kuje ka yiwa docter tukuicin albishir dinta ni kuma na gana da yata

Ba dan yaso ba dan Dole ya juya yana takawa a hankali yanayin jikinsa suka fito suka bar momy da Raisa kadai


Momy ta ce """"""""""'"'''""""""""""""""""""""""""
[20/7 12:59] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_



63
I'm sorry jiya nayi batan no ne maimakun 61,62 sai na rubuta 62,63 so yau zamu ci gaba da 63 thx



Ci gaban labari

Awatif dake labe tana sauraron abinda ke faruwa taji komai sanan taga lokacin da Irfan ya mike da niyar fita sai jin karar faduwarsa tayi ta fasa kara ta fito da gudu ita da kawarta ta shiga jijigashi tana fadin my please ka tashi dan allah ka tashi karka kashe min kanka a kan banza dan allah ka tashi in dan haihuwa ne kake son ka jawota jikinka sai muje a saka min a mahaifata na yarda zan haihun,
Ganin sambatun nata bai karewa yasa lili ta fito da gudu tana kiran sojan dake kofar gidan su da Sauri yazo yana tambayarta lafiya?

Ta ce " GENERAL ne , kafin ta gama fadi ya shiga cikin gidan ya tarar da Général yashe Awatif dangalgal saman kansa tana ta ihu tana jijigashi ya juya da sauri yana Kiran cikin assibitin gidan ,
Ba'a dauki wani lokaci ba sai gasu suka kakama suka dorashi saman gadon aka turashi sai cikin asibiti inda likitoci suka rufu a kansa


Cikin gida

*Ma* ta kare sauraron sharudan da elhaj Muhammad Ibrahim ya gindaya kan kar yaga Wanda yayi kokarin matsawa Raisa kan zancen Irfan sanan yana jiran takardar sakinta

Ma ta dago kanta ta zabgawa Raisa harara Momy tace am Elhaj ka manta baka saka zancen banda hantara da harara ba

Ya bude baki zaiyi magana wayar falon ta fara ringin Ma ta dauka tayi salama

Daga dayan bangaren Docter Mariam ta shaidawa Ma abinda yake faruwa , Ma ta saki wayar ta dora hanu a kanta da Sauri suka zaburo suna tambayarta lafiya?

Ma ta ce " wayo yarona yana asibiti Mariam tace bai san inda kansa yake ba

Dady ya Mike yana fadin subahanalah subahanalah muje muje

Momy tace " ni dai ba inda zanje ehe

Raisa ta juyo da Sauri a ranta tace"" To na shiga uku kar dai naje na kashe abin sona ba gaira babu dalili, ta Mike jiri ya kwasheta da Sauri Momy ta tareta ta fada saman jikinta tana fadin ke ina zakije kike kokarin tashi? Ai wly suje can su suka sani wai kamar ba shi bane yanzu yana haikar kar aje inda yake aman kuma yanzu shi ya fara zuwa , to nidai ba inda zanje kema kuwa in suna so karsu dawo daga wajen nasa,

Ita dai Raisa ta ciki na ciki da abinda take ayanawa a ranta



Asibiti
Wasa wasa General ana magani aman kamar ba mafani ake yi ba , sam baya motsi Docter Mariam ta tsorata ainun domin ta gano kamun zuciya ne shi kuwa ba ciwonsa bane duk ta hada zufa , ta fito ta shaidawa mr president Irfan na bukatar adu'a , hakan kuwa akayi elhaj Muhammad ya kirayi baban Samir ya shaida masa halin da ake ciki nan da nan aka tara almajirai aka shiga sauke kur'ani ana ta sadaka ,

Ma ta shigo cikin gidan Raisa ta dago tana kalonta Ma tace" Raisa sanadiyarki ga bawon allahn can rai a hanun allah sai ki zubar da ruwa a kasa ki sha, to ke yar gidan uban wacece da yayanki kuma mijinki bai isa ya dake ki ba ? Mutuniyar banza

Momy ta ce " please ya isa hakanan Fatima , shin kema rashin kunyar zakiyi min ne? Taya zan dora doka ki take? Ki fita a idona Fatima kinji? Duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ke duka so ki fice idan ya mutu allah ya jikansa

Fatima jikinta yayi sanyi ta zube a kasa ta fashe da kuka tace" please antyna yarona yana bukatar adu'arki walahi jikinsa yayi tsanani dan allah ki yafe masa ki zo ki duba shi dan allah

Itama ma momy Jikin nata sai yayi sanyi ta dago tana matsar hawaye ta ce " ban taba tunanin irfan zai watsamin kasa a ido ba , aman ba komai ni na yafe masa allah ya tashi kafadar sa aman fa bazan je ba gaskiya ki barni kawai a nan

Fatima tayi tayi momy taje ta duba irfan aman fir ta kiya haka ta Mike ta juya guiwa a sace ta koma asibitin

Tana zuwa ta tarar da elhaj Muhammad a inda ta barshi saman wata Babar kujera a offishin docter Mariam gabansa wata computer yana kalon aikin da ake yiwa irfan GABA daya dana sani yake yi ta yanda akayi zuciya ta debe shi da ya sani da bai ce zai raba shi da matar sa ba , wata zuciyar tace " elhaj itama fa da nata ra'ayin kawai dai ayi fatan allah ya tashi kafadar sa daga baya a san abin yi ,


Hajiya khadija, Fatima da Mr president sunyi kuri suna kalon sa ta computer nan kowa da carbi yana ja yana kalon sa lokaci lokaci domin Docter tace masha allah yana iya farkawa a kowani lokaci









92245338
[20/7 12:59] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_




64

Tun dare har garin allah ya waye irfan bai motsa ba suma basu motsa daga zaman jiran farkawar sa ba sosai hankalin su a tashe yake
Mr president ya dana Kiran docter Mariam

Tana zuwa tace " yes sir

Dady ya ce " docter ko a fita da shi ne?

Docter Mariam tace" Ur excellence KO an fita da shi bakin aikin nan da muka yi masa ne because mun daidaita matsalar , sai dai alurar da muka yi masa mai karfi ne dan ya samu ya huta sosai

Dady ya ce " ohk Kenan jikin da sauki?


Docter Mariam ta ce" eh a yanzun dai muna iya cewa da sauki tunda numfashin sa yana tafiya daidai , sai dai bamu san irin farkawar da zaiyi ba shiya nace ku shiga idan ya farka kuna kusa

Dady ya ce " ohk ohk , suka Mike su duka suka nufi dakin da aka kwontar da shi


Karfe 11 kofar dakin duk family din ne harda su anty leyla da su bara'atu da da su Awatif harda momyn Awatif , Kowa yana adu'ar allah ya tashi kafadar General



Cikin gida

Raisa KO sau daya bata samu barci KO barawo ya saceta ba momy na lure da duk motsin da zata yi tana kalon kofa tana kalon waya da dai sauran su s kuma taga ta kama cikinta ta lumshe ido ita dai bata ce mata komai ba

Karfe 13 da rabi Ma ta shigo ita da su anti leilatu suna fara'a

Anti leilatu ta ce"" sai Hajiya momy da yarta kuna gida abinku ba KO irin yar wayar nan aji ya oga?

Momy ta ce " leila ki kiyayeni

Leila ta ce " mu dai hakuri muke bayarwa allah ya huci zuciyar momy da yarta


Ma ta zauna ta ce " Leila kirawo kukun nan ya fadawa iya a kara gyarawa su mamar Awatif dakuna

Leila ta ce " ai har na fada

Raisa dai binsu take da kalo , a ranta tana jin idan fa bata je taga irfan ba tana iya mutuwa ,

Suna zaune suna labari sai ga su Bara'atu sun shigo da mamar Awatif aka shiga gagaisawa suf Raisa ta Mike ta faki ido tayi gaba abinta sai cikin asibiti


Tana isa ta samu da kyar ta karasa dakin da yake domin tasan nan ake kontar da yan gidansu , ta tura gabanta na mugun faduwa a hankali ta shiga ta tarar da su shi yana dan jingine jikin gadon ita kuma Awatif tana tsaye tana ziga shahi

Raisa ta dan dakata dalilin ganin suna dan taba hirarsu ta juya da nufin komawa don taga da sauki sai ji tayi yace *My raisa zo mana* ya Mika mata hanu yana dan murmushi

Raisa ta juyo kamar Wace Kwaï ya fashewa a ciki a hankali ta tako har gaban gadon nasa ta dago kanta idanuwanta suka sauka a cikin nasa kawai sai taji zuciyarta ta karaya bazata iya jure fushin da take yi da shi ba kawai sai ta fada kirjinsa ta rukunkume shi ta saki kuka

Shima tsam ya riketa yana ajiyar zuciya yana dan bubuga bayanta a hankali ya lalubo bakinta ya shiga aika mata kiss,

Karar faduwar cop din hanun awatif ya dawo da su daga duniyar da suke kokarin fadawa su kwakwata sun manta ma cewar wai da mutun a wajen,

Awatif ta zaro ido ta nuna su kawai sai ta fashe da kuka

Raisa ta Mike tana kalonta ta juyo ta kali irfan shima ita yake kalo sai ta juya zata fice ya ruko hanunta ya kara jawota jikinta ta shakiii kanshin turaran dake jikin rigarsa kawai sai ji tayi tana kelaya amai da Sauri irfan ya riketa da kyau yana yi mata sanu gaba daya ta jike masa jikinsa da amai kuma aman yaki tsayawa sai kakari take tun karfinta shi kuwa yana ta aikin sanu , Awatif ta rufe hancinta ta juya da Sauri ta bar dakin domin ba karamin kyankyamin amai take ba

Irfan ya Mika hanunsa ya dana Kiran nurse still yana rike da ita

Nurse aishe ta shigo ita da docter

Docter Mariam tace " subahanalah mai yake damunta

Irfan yace " walahi nima ban sani ba docter please kamata please tun kafin aman ya jigata ta

Docter Mariam ta kama sukayi bayi da ita , nurse aishe ta dauke zanin gadon ta kawo kayan goge goge ta goge ko'ina tas daidai nan aka fito da Raisa duk ta galabaita bata dena yunkurin aman ba duk da ba komai a cikinta aka turo wani gadon akayi shinfida lafiyaya , docter Mariam tayi mata alurar amai sanan ta fice da fitsarinta da ta dauka a wani dan silba karami

Irfan ya tashi ya kara gyarawa Raisa konciyarta ya haye saman gadon ya rungumeta tsam tamkar za'a kwace masa ita yana fadin sanu my Angel , ita dai sai hajijiya take tana rawar sanyi

Su momy ne tafe bayan dady ya nuna bacin ransa na taje taga irfan su Ma suka rufun mata dole ta taso suka zo gaba dayansu don su ganshi , ita duk a tinaninta Raisa na baci saboda Bara'atu na gidan su kuwa basa jituwa da juna hakan yasa ta bi su Ma don su koma sugan shi sai ta dawo


Suna tura kofar suka shiga suka tarar da Su konce Raisa sai makyarkyatar sanyi shi kuwa sai aikin sanu yake
Momy tayi kira ta salamce tana tafa hanu daidai nan Docter Mariam ta shigo da takarda a hanunta tana ta washe baki

Momy ta kaleta ta ce " Docter lafiya kike ta murmushi?



Docter Mariam ta ce " Aa momy ai sai ma na taka rawa General tashi ka anshi albishir

General da raisa suka mike a tatare suna kalon Docter Mariam inda gaba daya dakin suka tsura mata ido , nima garin galonta har wayata ta kufce ,,,,,,,,,.......'''''',,,,,,,,,,,,







To fa shin meye albishir din nan da Docter Mariam zata bayar ga family din Elhaj Muhammad Ibrahim ????



92245338








🙆
[20/7 23:48] ~Amnoor👯🤸🏻‍♀: [20/7 12:52] Sajida: *DUK KARYAR KADA🐊🐊🐊🐊*
*TA RUWA CE🌧🌧🌧🌧*

*NA*
_*SAJIDA*_

_♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM_



65


Allah ya barmin ke my lovely *AMAL* this page's for you ❤❤


Labari
Gaba daya dakin suka tsurawa docter Mariam ido suna jiran albishir dinta

Ta mikawa General takardar tana fadin " congratulation Madame na da shigar cikin wata daya da kwana biyu ,

Momy ta ce " Wace madame din?

Docter Mariam ta nuno Raisa Wace tayi tsuru itama tana jiran jin wacece kuma zata kwashi kunyar ciki , ai ana nunata ta diro daga saman gadon ta dora hanaye biyu a saman kanta tana girgiza kai ta ce " na shiga uku na lalace wayo ni raisa daman hakane kadara , dan allah ku tsaya na fada muku walahi ba laifina bane momy allah ba laifina bane , Ma kinsan allah ban je na aikata ba wly wly laifinsa ne ta nuno Irfan Wanda yayi galala yake kalon rantse rantsen Raisa kamar Wace tayo cikin shege

Momy ta gumtse dariyarta Ma kuwa ta juya da Sauri zata bar dakin don wata irin kunya da ta darsun mata, ai kuwa da gudu Raisa ta tare kofar tana ta sheshekar kuka hanayenta still a saman kanta idanuwan nan sun kara firfitowa sunyi fulu fulu da su tsakaninta da allah tsoro take ji shi yasa taso tun kafin su tafi indiya ta fadi abinda yayi mata duk don gudun wanan ranar aman firr ya haneta daman Ma tace daga ta yarda haka ta faru da ita zata dauki ciki ne , shikenan duniya ta zageta su momy su tsaneta kowa ma ya tsaneta kuma taje lahira a ci ubanta , ta kara dora hanu a saman kanta ta juya wajen momy ,

Momy ta kasa rike dariyar su docter Mariam ma kawai dariya suke domin kowa ya gane inda zancen ya nufa,

Bara'atu kuwa daban ta fasara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login