Showing 1 words to 3000 words out of 88726 words
Chapter 1 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT)
(ADMIN OF ADMINS)
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
09030159301
[10/05 09:49] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*AUREN BAUTA*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(the amazing cook)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍢🥠🍥🍤🍣🍱🍲🍡
By mmn walid and walida (mrs aliyu)
Marubuciyar
*tawa kaddarar*
*dangin sa*
*uwata*
*rabo na ce* to be continued in shaa Allah
Page 1🌹
"Sai yanzu kika dawo ƴar iska tun ɗazu da aka aike ki ɗebo ruwan sai yanzu kika ga daman dawo wa kuma kina ji na nace miki sanwar wake da shinkafa zan ɗaura da ruwan shine kika je kikai zaman ki don kina min baƙin cikin kuɗin da zan samu ko, shegiya da fuskar kamar ta aljan"
Duk wannan faɗan da inna harira bata taimakawa ƴar yarinyar da take ɗauke da ruwa akan ta, duk kuwa da ganin cewar yarinyar ta gaji sosai
sai da tayi ta gama sannan ta sauke,
"kuma kije gonar malam ki wo min in kin ga dama ki daɗe kamar kinje lahira gaida iyayen ki"
Ɗan ɗankwalin da take ɗauro karar ta ɗauka tayi waje da shi, directly gonar ta nufa wanda bashi da nisa da gidan ta ɗebo karar sannan ta kama hanyar gida tana yi tana nishi daga gani yunwa ce da kuma gajiya a tattare da yarinyar
Da sallamar ta ta shiga gidan ta ajiye karar sannan ta zundumi ruwa a randa ta ɗan sha kaɗan bata san ta cikawa cikin ta ruwa
"shiga madafi ki ɗauko ragowar ɗumame ki don yadda kike zaro min idandinan nan naki a cikin wannan baƙar fuskar taki ai wannan sai in mummunan mafarki"
Abincin ta ɗauko zata fara ci kenan inna harira ta kuma saka ta aikin hura wuta na wake da shinkafar da take saidawa
A bakin murhun ta zauna tana hura iccen tana cin sandararran tuwon dawan da idan aka jefe ka da shi sai kaji ciwo saboda tsabar taurinsa
Sai da ta gama girka wake da shinkafar tsab sannan ta kwashe a ƴar fantekar da ake kwashewa sannan ta gayaws inna harira ta gama
"lantana lantana", inna harira ta kira ƴar ta da ke yi mata talla don kuwa asmau bata da kan inna harira tace yadda fuskar ta take baƙa haka ma kwakwalwar take sam babu haske a tattare da ita
Asma'u ce ta ɗau fantekar inda lantana ta shige gaba suka tafi tallan haka suke yi kullum ita lantana itace me kan talla amma ban da asma'u
Sai bayan sallah la'asar sannan suka dawo inda suka tarar da inna harira da baƙuwa a zaune a tsakar gida akan tabarma
Ƙwalawa asmau kira tayi ta ƙarasa inda take sannan ta nuna wa matar asmau
"hjy kina ganin zatayi, don ni ƴar nan babu abinda take min anan, kullum sai dai taci tayi kashi kan talla babu shi yanzu in ta tashi aure wazai mata kayan ɗaki, ga shegen baƙi kamar kwalta"
Matar da aka kira da hjy ta dubi asmau sannan tace
"to ba wai baza tayi ba kamar yadda na faɗa miki abuja ni fa nake kai yara aikatau, wannan kuma kamar yarinya ce"
"ahap haka kike gani ai wannan in ta kama aiki kamar jaka haka take, reno shara wanki wanke wanke duk ta iya"
Hjyr ta kuma kai duba asmau wacce kan ta yake a ƙasa sannan ita sam bata fahimci inda zancen su ya dosa ba
"ni dai da waccen ce" ta faɗa tana nuna lantana ƴar inna harira, inna harira sai tayi dariya irin ta basarwan nan
"haba bazaki so kiɗau wannan ba ai alanƙosa ake ce miki indai lantana ce ba abunda zata iya, yanzu tallan wake da shinkafar da take kai min ma tace zata dena tunda ɗan me gari yace yana sonta shi yasa nake neman hanyar da kuɗi zasu dinga shigo min, ga bikin lantana ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba, kuma auren ɗan me gari kashe kuɗi gare" ta faɗa tana ajiyar zuciya
"to shike nan indai kince wannan ɗin zatayi ai shike nan, amma idan na tafi da ita kuma aka ƙi ɗaukar ta zan dawo miki da ita"
"na yadda amma kice su fara gwadata tukunna kafin su yanke hukunci da wannan ɗan ƙaramin jikin nata shine yake sawa mutane suna yi mata kallon yarinya ce"
Sukai sallama kan kashegari da asuba zata zo ɗaukar asmau zuwa garin abuja aikatau
***********************
Asmau sunana na kasance ni kaɗai a wajen iyaye na babana ɗan nan garin ne azore wanda yake a ƙaramar hukumar minjibir ta jihar kano,
Garin fulani ne sosai don gida tsilli tsilli zaku dinga gani in kun shigo sannan sai kuma gonar mutum a jikin gidan sa, irin dai ginin fulani, in kaga gida ɗaya sai kayi tafiyar mill kafin kaga wani
Ban san iyaye na ba kasancewar sun rasu, mahaifiyata ta rasu lkcn haihuwar ƙanina, inda aka rasa aka rasa ɗan,
Shi kuma mahaifina sai da na ɗan tasa kaɗan sannan Allah yayi masa rasuwa, sai kulawata ta koma hannun wan mahaifina
Inda yake min rikon sakainar kashi, don kuwa babu ruwan shi da duk wani daya shafe ni duk abinda matar shi zatai min baya cewa komai wannan shine taƙaitaccen tarihi na
******************
Da sassafe hjy ta zo mukai sallama sannan muka kama hanya inda naci karo da wasu ƴammata waɗanda zamu tafi da su, amma duk sun girme ni don ni sai na zama kamar wata ƴar tsana a ciki su
Sai da muka je gezawa sannan muka samu ƙaramar mota inda zata kaimu abuja, haka aka cunkusa mu a motar nan kamar dabbobi inda ita kuma hjyr ta zauna a gaba ita kaɗai
Tafiya ce kamar ta yada shege ba ƙaƙƙautawa sai da muka je kaduna sannan direban ya tsaya muka fito muka ɗan huta, sannan muka kama hanyar abuja
Lfy ƙalau muka isa abuja inda muka sauka a kubuwa, anan gidan hjy yake, ɗaki ta bamu guda, tace duk mu sauke kayan mu
Ni dai kamar an min duka haka nake ji don kuwa a gajiye nake, kwanciya nayi sai bacci, inda ƴammatan da muka zo da su kowacce take ta buri tare da fatan irin gidan da za a kaita, ni dai tunda na samu bacci ya kwashe ni sai nace saba'ul khairi
👩🏽🍳 menu of d day👩🏽🍳
*wake da shinkafa served with local salad & zobo drink*
🍲 ```wake da shinkafa```🍲
```ingredients```
```wake```
```shinkafa```
```gishiri```
```man gyaɗa```
```haɗin salad```
```method```
1) bayan kin gyara waken ki saki ki wanke ki ɗaura akan wuta, sannan ki bishi da ruwan kanwa (optional)
2)sai waken ya dahu, sannan ki ɗauko wankakkiyar shinkafar ki ki zuba ki juya ki saka ɗan gishiri sannan ki rufe
3) idan ya dahu sai ki sauke ki yi serving da soyayyan man gyaɗa, ko tankwa, da yaji sai kiyi ganishing da salad aci lfy
*LOCAL SALAD*
```ingredients```
cabbage
lettuce
carrot
cucumber
green pepper
lemun tsami
man gyaɗa
maggi
```method```
1) ki wanke lettuce, cabbage, cucumber, green pepper ɗinki, ki barsu su tsane sannan sai ki yanka su irin yankan da kike so
2)ki kankare bayan carrot sannan ki wanke shi daga nan sai ki gurza shi
3) ki ɗauko kayan haɗin da kika yayyanka ki haɗa da carrot sannan ki haɗe su waje ɗaya, ki ɗauko lemun tsami ki ɗiga kaɗan ba dagawa ba yadda dai zai miki sannan ki zuba mai ki zuba maggi ki juya sai ki juye a salad bowl sai ci
*zobo drink*
```ingredients```
Ganyen zobo
Citta
Kanunfari
Abarba
Cucumber
Sugar
Flavour
```method```
1) ki ɗauko zobo sai ki wanke shi ki zuba masa ruwa ya sha kansa sannan ki ɗaura a wuta, tare da citta, ɓawon abarba, sai dakakken kanunfari ( ```sirrin daka kanunfari shine ƙamshin shi ya fi fitowa idan an daka shi akan a watsa shi haka```)
2) idan zobo ya tafasa ya dahu sai ki sauke shi ki juye a babban mazubi yadda zai sha iska, kafin ya huce kuma bari mu haɗa ragowar
3) ki fere yanka abarbar da cucumber ki ƙanana yadda dai zasu miki daɗi wajen blending sai ki markaɗa su kina yi kina tacewa kina ƙara markaɗawa har dai a samu yadda ake so
4) sai ki ɗauko wannan zobon naki ki tace ki ɗauraye ganyen ki kuma tace wa har sai maa shaa Allah, sannan ki haɗa da ruwan cucumber & abarbar nan
5) ki zuba sugar, flavour ki zuba a jug a saka shi a fridge yayi sanyi sai shaa
👩🏽🍳 *Bon appetit*👩🏽🍳
*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:49] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
page 2 🌹
Kashegari da sassafe aka tashe mu, koko da ƙosai aka bamu, muka karya sannan hjy ta tasa mu a gaba domin neman wa kowa gidan aiki
Muka dinga zagaya gari zuwa gidajen masu hannu da shuni da kuma masu matsakaita ƙarfi ana ajiye mu da ɗai ɗai,
Sai da ya rage mu biyu sannan muka hau mota muka nufi wuse zone 4 kamar yadda naji hjyr tace wa driver taxi ɗin da muka shiga
A ƙofar wani restuarant muna sauka inda muka shiga ciki,
Hjy ce ta nuna mana wani ɗan loko wai mu zauna a can kafin ta dawo, kusan minti biyu ta ɗauka sai gata inda ta kira mu muka bi ta cikin gidan
Wata mata ce muka samu tana zaune a saman wata three sitter daga gani itace me wurin
"gasu nan kamar yadda na faɗa miki su biyu ne" matar da ke zaune a ɗakin ta gyara ɗan glass ɗin da ke fuskar ta sannan ta kalle mu kamar ta ga wasu kashi ko abun ƙyanƙyami
"me zanyi da waɗannan jariran" ta faɗa a wulaƙance
"na faɗa miki indai zaki kawo min ƴar aiki babba nake so amma me zan yi da waɗan nan, gwara ma waccen amma wannan kamar ba a daɗe da yaye ta ba"
Ta ƙarashe zancen ta idon ta akaina
"wallahi hjy munnira ƙaramin jiki gareta amma da shekarun ta"
Mahawara suka fara yi inda hjyr da ta kawo mu ta fi hjy munnira baki don haka dole hjy munnira ta yadda ta ɗauke mu bayan an sani shara nayi
Sai da suka gama cinikin abinda za a dinga biyan mu a shekara sannan hjy tai sallama da mu, ita kuma hjy munnira ta kira wata laure wai ta tafi da mu ta nuna mana aikin daya dace mu
Can bayan gidan muka je inda anan ake duk wani hada hada na girki, ƙaton kitchen ne, sai kuma wajen wanke wanke sai kuma wasu ɗakuna guda biyu da ke can gefen daga ƙarshen katangar inda anan akace mu ajiye kayan mu
Kowaccen mu aka haɗa ta da aikin daya dace da ita, ni dai kitchen aka kai ni inda wacce muka zo da ita aka kai ta wajen wanke wanke
Ina shiga kitchen, naga girman kitchen ɗin, ban taɓa ganin irin wannan kitchen ɗin ba sai yanzu
Girki ake yi kamar ba gobe, tsayawa kawai nayi ina kallon ikon Allah tare da ƙarewa kitchen ɗin kallo,
"ke ya sunan ki" naji wata ta faɗa
"asmau" na faɗa a hankali, kallon banza naga ta bini da shi
"ke amina waye yace a kawo mana ƴar jaririyar nan kitchen mu da muke aikin wuta" ta faɗa kamar taga kashi
"hjy ce tace a kawo ta nan" inji wacce aka ƙira da aminar
"to sai sa ta tsabtace jikin ta don nan bama gayyata ƙazanta" sim sim sim na fice inda na nemi hanyar da ɗakunan kwana suke
Ƴar jaka ta na ɗauko, sam babu wasu kayan arziƙi don duk kayan da nawan yawancin su ba wanki, wasu kuma a yayyage
Zama nayi ina kallon ikon Allah, ban jima da zama ba sai ga wata ta shigo
"me kike yi a ɗakin nan bayan kowa yana waje yana aiki, kar dai bincike kike mana a kayan mu"
"wallahi ba haka bane, wanka akace inzo inyi in canza kaya kuma naga kayan nawan duk babu wanki" na faɗa d ido na duk ya kawo ruwa saboda banji daɗi zargin da tai min ba
Jakar tawa ta zazzage a ƙasa ta fara duba kayan cikin ta, bakin ta a taɓe
"kije wajen wanke wanke ki samu ƙananan sabulai ki haɗa ki zo kiyi wanki"
Miƙewa nayi na fita, nai mamakin dana ƙarasa wajen wanke wanke na samu sabulai, kamar ba da kuɗi a ka siye su ba, tsinta na fara yi har na haɗa iya wanda nasan zai ishe ni sannan na tafi ɗakin
Kaya na na ɗiba sannan na je bayan ɗakin inda banɗakin mu yake na wanke kayana tas sannan na shanya
Wanka na shiga da ragowar sabulun na saɓi jikina kamar ba gobe, don a
Don kuwa a azore ban isa in samu wannan damar ba, sai dana gama wanka na sannan na fito
Sai yamma sannan kayana suka bushe na kwashe, a ranar dai ban koma kitchen ba sai kashe gari
Cikin hukuncin Allah na fara aiki a kitchen amma ba abinda nake yi sai aike, dauko wannan ɗauko wancen haka dai
Kafin ka ce me wannan har na zama ƴar gidan, na son komai na kitchen, sannan na san inda ake ajiye komai
Gidan cin abincin hjy munnira gidane da a kullum a ke dafa kusan buhu biyu na shinkafa da ta tuwo
Babu irin variety na abincin da ba a yi, waina sinasir, alkubus fankaso, ta ɓangaren shinkafa ma
Jollof rice fried rice, duk dai wasu sunfari na dafa abinci ana yi, ba wai duka a ke ci anan ba, akwai waɗanda ake fita da su,
Don kuwa akwai certain hotels ɗin da suke zuwa suna yin order abinci anan gidan, ga kuma costomers da suke zuwa suna siya su tafi da shi
Ga waɗanda suke siya su ci anan, akwai wasu mutane ma da ake musu abincin gidajrn su anan, kullum akwai abincin da za a dafa na certain gida akai masa
Nakan yi mamaki amma dana ji cewar yawanci gidanjen ministers ne da house of reps da senators ake kai musu waɗanan abincin saboda mutanen da suke tarawa sai na daina mamaki duk da dai ban san ko su waye ba
don haka aiki a gidan nan in aka tashi tun safe sai mukai ƙarfe 10 :00pm bamu gama ba
Amma kuma mu girki ne kawai akwai ƴan wanke wanke, akwai kuma ƴan service, akwai masu kaiwa gidaje, group group ne kowa da group ɗin sa kuma kowa ya san aikin sa
******************
*b̫a̫y̫a̫n̫ s̫h̫e̫k̫a̫r̫a̫ b̫i̫y̫u̫*
Na zama ƴar gida yanzu don kuwa ba abinda bana shiga ayi da ni ta ɓangaren girki,
A lokcn ne hjy munnira ta ƙara buɗa restuarant ɗinta inda yanzu babu abinda ba a yi, snacks ne ɗrinks ne, duk daia abinda kake so idan ka zo restuarant ɗin mu,
Kuma kullum cikin hukuncin Allah ƙara samun costomers muke yi, yanzu ba a shakkar bani girki ko ya yake don kuwa a gaskiya na iya
Kasancewar ni ce ƙarama a kitchen yasa kowa sai kaji yace asmau don Allah juya min kaza, kwashe kaza, wannan ne ya sa ni ko wane ɓangare na kitchen ina shiga
Ba kamar cooks ɗin kitchen ɗin ba, yadda in a ɓangaren sarrafa shinkafa kake to ana zaka zauna, in a ɓangaren snacks kake to anan zaka zauna, haka ma in a ɓangare drinks kake ko miya ko salad ko wani abu na kitchen
Ma'aikatan a rarrabe suke kowa yasan aikinsa, amma banda ni, ni ina kowane ɓangare kuma duk inda naje sai na tabbatar da cewar na koyi abunda suke
Wannan ne yasa a kitchen ɗin nai fice tunda komai aka bani zan iya kuma zan yi shi kamar ba ƴar ƙaramar yarinya ce tayi ba
*****************
Sabit yana zaune a office ɗinsa cikin fararen yadinsa waɗanda kana kallon su kasan ba ƙananan kuɗi aka sa wajen siyan su ba, wayace a hannunsa yana ta