Showing 57001 words to 60000 words out of 88726 words

Chapter 20 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

ɗauko


Ko kuma ace baƙi ne amma ba komai duk abinda Allah yaso haka zan karɓa, kuma ina fatan ya zama me jin ƙan iyaye


Ɗa na yana hannuna na fito daga labour room, da sauri suka ƙaraso tare da karɓar sa mmn badia ce ta fara karɓar sa


"namiji ne ko mace" ta tambaye ni kalmar tai bala'in ƙona min rai ba Allah ya raya ba komai amma wai ita burin ta namiji ne ko mace


sabit ne ya karɓi shi shima daga gani maganar tai masa ciwo, karɓar sa kawai yayi ya wuce ɗakin da aka bamu na hutu


Addua ya dinga masa, ina amsa wa da amin, duk wannan abun da muke ita uwar ɗan bata sani ba don sammako tayi ta tafi kwatano wai ta tafi siyo kayan da zata saka da suna



Sai da ya gama masa addua sannan mmn badia ta kuma karɓar sa ta buɗe masa diaper inda ta gano namiji ne



Nan da nan murna kamar me, har wani ƙara ruƙunƙume shi take yi, mijinta ta kira ta shaida masa badia ta haihu,


Shima yai mata murna sannan yace a bawa badiar, nan ta hau ƙarya wai badiar bacci take yi

Mummy sabit ya kira yace mata badia ta haihu ita ma mummyn tai murna sannan tace a bawa badiar tai mata barka shima duk ɗaya yace tana bacci



Haka suka dinga kiraye kirayen waya suna shaidawa badia ta haihu, ni dai kallo ne nawa


Zuwa can baby ya fara mutsu mutsun yunwa, dabino sabit ya tauna ya lasa masa a bakin sa sannan aka bishi da zam zam



Wajen azahar aka sallame daga asibitin muka kama hanyar gida, wai don renin hankali babu wanda yake ta kaina ni dana haihun sai ta baby,


Ɗakina na shige na samu na watsa ruwan zafi a jikin sannan na fito kitchen na ɗaura indomie na ci na ƙoshi sannan na wuce ɗaki na na kwanta



Wajen ƙarfe 06:00 na yamma sai ga mummy, ina kitchen ina dafa shayi
Sai ga mummy, da sauri naje na tare ta

"mummy ashe kina tafe" tsayawa tayi tana kallona


"ya naga kamar ma kece me jegon duk kin wani ɗashe"

Ta faɗa tana kai hannun ta kan fuska ta, murmushi na saki sannan naja hannun ta zuwa ɗakin badia

"zo muje kiga jikan naki"


Bina tayi, da sallama na shiga, suna zaune a bakin gado shi kuma babyn yana cikin gadon sa na jarirai yana ta baccin sa



A razane suke da suka ga mummy, sai suka fara kame kame


"hjy fatima yaushe kika ƙaraso, muje falo mu zauna yaron yana bacci" inji mmn badia


"ni da nazo ganin baby sai ace min yana bacci, ina ita mejegon"


Tsuru tsuru sukai, nidai tunda naga na haɗa su sai nai ficewa ta na barsu


Ɗakin nawa naji an turo ƙofar, ashe mummy ce ta shigo, sai da ta ƙaraso da sannan na bata wurin zama


"har yanzu sabit ɗin basu dawo bane ko dai wani abun ne ya samu badiar"


Ni dai ban tanka mata ba saboda sam ban san ma ina ta dosa ba,


"ni wallahi duk a gajiye nake, nace musu su shirya gobee mu koma abuja ai suna acen dama dalilin zuwa na kenan"


Ni dam ban tanka mata ba don kuwa a gaskiya na fara kewar ɗana, don haka sai nai mata shiru,


Mara ta naji ta fara murɗa min, mitsss sai yanzu na tuna sam ban ma sha magani ba, miƙewa nayi don in ɗauko magani sai naji mummy tana cewa


"asmau lfy naga kina tafiya kamar kece kika haihun, gashi kuma duk kin ɓata zanin jikin ki"


Juyawa nayi don inga inda na ɓata ban ɗago ba sai ganin mata nayi kusa da ni


"asmau ke kika haihu ko badia"

Tsare ta nayi da idona wanda a yanzu suka ciko da hawaye, ɗago min fuskar tawa tayi


"asmau ke kika haihu, ba badia ba" gyaɗa kaina nayi hawaye yana zuba a ido na


"haba biri yayi kama da mutum" inji mummy takaici ne ya kamata sai ta kama hanyar fita



Ban san me tace musu ba sai gata da babyn,

"ungo shi bashi nono ya sha ki gama in gyara ki, wallahi idan sabit ya dawo yau sai yaga ɓacin raina wanna wane irin zalinci ne"



Karɓar babyn nawa nayi na rungume shi sannan na zauna na fara bashi nono kamar dama yunwa yake ji haka ya karɓa ya fara tsotsa



Muryar badia muka ji a bakin ƙofa tana masifa


"ban gane ɗan ta bane yaushe ya zama ɗanta don kawai ta rene shi a cikin ta sai ace ɗan ta wallahi bazai sha nonon ta ba, na riga na gama booking nurse ɗin da zata dinga kular min da yaro" ta faɗa tana shigowa a fusace da zummar karɓar mummy



Mummy ce tace

"wallahi kika sake kika katse masa wallahi tallahi sai na saɓa miki"


"mummy ya za ayi jini na ya sha nonon ta"


"ya akai ya zama jininki"


Nan badia ta kwashe komai ta faɗa wa mummy, bata gama ba mummy ta fashe da kuka, adai dai lkcn sabit ya shigo



Ingiza badia yayi ya kora daga ɗakin, mummy kuwa kuka ta dingayi,ba irin lallashin da sabit be mata ba amma taƙi shiru


Shima sai ya fashe mata da kuka

"anya sabit kana tuna ranar da Allah zai kama ka kuwa akan haqqin yarinyar nan, tunda Allah ya haɗa ku kake zalintar ta, anya kana da tausayi kuwa"


"mummy don Allah kiyi haƙuri wallahi sai da ta amince muka biya ta sannan akai mata dashen"


"wannan yarinyar me ta sani, da har zaku ce wani kun biya ta yanzu ɗan na wane na wacce tai dakon cikin ne ko na ƴar lelen taka ne"


"mummy ƙwan badia ne"

"mummy ba nawa bane" na bata amsa

"amma ni alfarma ɗaya nake so a barni in kula da shi in dinga bashi nono in yaso idan na yaye shi sai badia ta karɓi abinta"


Kallona mummy tayi sannan tace

"asmau ke yarinya ce har yanzu baki san ciwon kanki ba nan gaba zaki zo kiyi dana sani"


"mummy duk yadda Allah ya tsara bawa rayuwarsa haka zai yi ta" na bata amsa
Nai ta mata daɗin baki akan maganar don bana son a jata da tsaho, ta yi mugun jinjina min sannan daga ƙarshe ta saka aka kira badiar sannan ta kuma kafa sharaɗin ni zan kula da babyn



Sam badia bata damu ba, shima sabit ɗin sai ya nuna ya fi son hakan,


Mummy itace ta dinga kula dani, ko da lkcn suna yayi a can wani hotel sukai sunan su, daga ni har mummy ba wanda ya je



Amma ita da sabit da babyn sun sha hotuna kamar ba gobe, wallahi duk wannan abin da ake yi ko kaɗan a jikina be taɓa damuna ba sdon nasan akwai ranar ƙin dillance


yaro ya ci sunan bbm badia amma anace masa annur mummy tai faɗa sosai wai ai sunan daddy ya kamata a saka amma sam ba ai mara kara ba


Kaji mummy wani ɗigimi




********************

*BAYAN SHEKARA ƊAYA*





kamannin annur da sabit ya gama fitowa, sosai ga wayau kuma Sam baya yadda da badia, shegiyar ƙyuya gare shi kamar


Daga ni sai ni, ko sabit in dai ba fita yaga zai yi da shi ba sam baya yadda ya ɗauke shi


Sam badia bata damu ba, ita dai kawai burin ta taga an masa wanka an masa kwalliya tai ta ɗaukar shi a hoto ta na ɗora shi a dp, facebook da instag.


Shima haka sabit ɗin yake sai dai in ban masa wanka ya ɗau gyara ba, nan zaku ga da sabit ɗin da badiar duk suna rige rigen ɗaukar a pic


Sam wai nuna so ko jan yaron a jiki badia bata san wannan ba, ko tashi yayi da safe ya tafi ɗakin ta sai dak kawai kaji tana ƙwala min kiran in zo in dauke shi in masa wanka



Sam bata yadda ta ɗauke shi sai an masa wanka, wai ko yayi pupu ko fitsari sai dai kaji tana kirana inzo in cire masa



Wani rashin *M* ɗin ma sai in yayi pupu a ƙasa kamar ta dake shi haka take, akwai randa mukai faɗa da ita akan shi,



Ya shiga ɗakin ta ba diaper a jikin sa, sai yai mata pupu a kan gado, kawai zagin shi naji tana yi


Da gudu na tafi ɗakin ta ɗaga hannu zata dake shi, da sauri naje na tare masa,


"haba anty yaro ne"
Harara ta bini da shi sannan tace

"ni ƙazanta ta yara ce bana so, zo ki kwashe kashin nan kije kiyi masa wanka"


Tabbas ba ta san ciwon sa bane don wallahi da ta san ciwon sa da uwa tana cikin cin abincin ta ɗan ta zai yi pupu ta saki abinci ta wanke masa sannan ta zo ta ƙarasa




Ita dai bangaren kayan sawa, kayan wasa, anan fa to kusan Rabin albashinta yaron take kashe mawa,



Sai dai jawo shi ajiki ne dai batayi


Ana haka wani zazzabi ya kama shi aiko sai ya kasance ni kaɗai yake yarda in dauke shi, hatta da sabit baya yarda da shi




Anan ne wani sabon rashin mutunci ya tasowa badia inda tace ita Sam atafau ayaye yaro abata ɗanta, saboda gaskiya ita bata yadda ba tana uwar yaro amma sam be shaƙu da ita ba



A zuciyata nace me kike masa da zai sa shakuwa da ke, don kayan wasan da kike sai masa sani yayi shi yaro


Tuburewa nayi nace sam be isa yaye ba sai ya ƙara watanni, abi kamar wasa har sabit ya saka baki shima sai ya goyi bayan badia wai shima baya jin daɗin yadda annur ɗin yake masa



Ban musa ba ganin bana son sa'insa akan shi ya sa na miƙa mata shi nasan ko kukan sa na dare ya sata dole ta dawo min da shi



Ai kuwa tana karɓar sa daya tsanyare da wani kukan ko a jikinta ni kuwa wannan kukan jin sa nayi kamar ana yankan sa har cikin zuciyata naji



Ɗakina na shike ina jin sa yana cewa ```maaa``` da yake haka yake cemin don bakin sa ba wani buɗewa yayi ba



Aiko ko awa daya batayi da daukan shi ba naji ana ƙwallamin kira a ruɗe na fito inda naga yaro shame shame ahannun sabit kamar marar rai


Ruwa ne a hannun badia tana shirin sheƙa masa na karɓa a hankali na yayyafa masa yana farfaɗowa ya fara ```maaa``` ```maaa```



"na'am baby na" na amsa masa ɗagowa yayi ya kalle ni, duk da dai jikin sa ba ƙwari amma a hakan ya ɗago ya taho wajena da saurin sa ya rungume ni



Sosai na matse ɗana a jikina sai ajiyar zuciya yake saki, wanda hakan ya sa zuciyata ta karye naji hawaye ya cika min ido na



Bani ba hatta sabit sai da jikinshi yayi sanyi ni ko hawaye suke sulalo min ganin yadda yaron cikin ɗan lokaci kadan ya fita hayyacin shi amma da ganina yawani lafe ajikina harda ƙara rungumeni


Bacci ne ya kwashe shi a kafaɗa ta ina ɗan jijjigashi ko da yai baccin sai na sauke musu shi


"zo ki ɗauke shi" inji sabit


"ya ci gaba da zama a wajen ki har sai ya saba da badiar sai ya koma, ke kuma dia ya kamata ki dinga samun time kina spending da shi mana don ya saba da ke kooo" ya faɗa da sigar lallashi


"ok shike nan zan duba"


Wuce wa nai da shi ɗakina muka kwanta, kallon shi nayi sannan nace

"annur ɗana ina alfahari da kai, kuma wallahi da kai sai na nuna wa duniya cewa ni asmau ƴar halak ce"



********************


Tun daga lkcn badia take shigowa ɗakina wai don annur ya fara sabawa da ita, amma ko ta shigo tana manne da wayar ta tana chatting shi kuma daya ganta to ahike nan ya liƙe min kenan har sai ta fita



Sam wannan method ɗin be yi ba haka naji tana faɗawa sabit, sai suka tsiri fita da shi yawo, kunsan yaro da son yawo, wannan ne ma sa ya ke ɗan yadda ta ɗauke shi in dai har ya ganta da mayafi ko hijab amma da ta zauna shikenan sai ya fara ```maaam``` yana kuka



*******************
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 23




Bayan kwana biyu sai ga mummy nai murnar ganin ta sosai har da saƙo na daga anty fannah Allah sarki anty fannah nayi kewar ki sosai



Mummy tai ta faɗa wai badia mahaifar ta bata da ƙwari kuma gashi ta kuma samun ciki amma ta ƙi zama ta kula da kanta



ba wanda ya tanka sai dai lallashi da suke ta bata wai zasu kula da cikin, ni dai ina gefe ina kallon ikon Allah wannan rayuwa wato akwai abin mamaki sosai



Kwanan mummy biyar sannan ta kama hanyar gida, kamar nayi kuka ranar da ta tafi, don kuwa yanzu zan koma rayuwa ni kaɗai


A hankali cikin ya ci gaba da girma har lkcn da zai zo duniya yayi


Rannan da yamma sai ga mmn badia tazo gidan ita da wata mata, ɗakin badia suka sauka sam ban sam me ya kawo su ba amma kuma bini bini a bini da ido



ranar wata talata da safe na tashi da nakuda, tun ina yi ni kaɗai har dai dana ga abin bana ƙare bane na fita, ina fita naci karo da wannan matar zata shigo ɗakina


"kar dai naƙuda kike yi ƴannan" gyaɗa mata kai nayi don bazan iya magana ba sabida ciwon da ke damuna



Sabit ta kira shima ya fito jiki si ɓari yake yi yaji ina labour, asibiti muka je, inda aka shigar da ni labour room Awa uku cur na ɗauka sannan Allah ya sauke ni lfy, ajiyar zuciya na saki dana ji Allah ya raba ni da wannan cikin lfy



Ɗagowa nayi na kalli yaron......... Fari tas da shi kana ganin shi kaga sabit


Miƙo min shi nurse ɗin tayi na karɓi kayana na tsaya ina kallon sa, godiya nai wa Allah daya sani ina da rabon ganin jini na



Sai da nurse ɗin gama gyara ni sannan ta karɓi babyn don gyara shi, shima, ko da aka gama shirya shi zata fita da shi na kira ta na karɓi abuna



Ƙare masa kallo nayi kamar sabit yayi kaki ya yar addua nayi masa sosai, na so ace yaron kamata ya ɗauko


Ko kuma ace baƙi ne amma ba komai duk abinda Allah yaso haka zan karɓa, kuma ina fatan ya zama me jin ƙan iyaye


Ɗa na yana hannuna na fito daga labour room, da sauri suka ƙaraso tare da karɓar sa mmn badia ce ta fara karɓar sa


"namiji ne ko mace" ta tambaye ni kalmar tai bala'in ƙona min rai ba Allah ya raya ba komai amma wai ita burin ta namiji ne ko mace


sabit ne ya karɓi shi shima daga gani maganar tai masa ciwo, karɓar sa kawai yayi ya wuce ɗakin da aka bamu na hutu


Addua ya dinga masa, ina amsa wa da amin, duk wannan abun da muke ita uwar ɗan bata sani ba don sammako tayi ta tafi kwatano wai ta tafi siyo kayan da zata saka da suna



Sai da ya gama masa addua sannan mmn badia ta kuma karɓar sa ta buɗe masa diaper inda ta gano namiji ne



Nan da nan murna kamar me, har wani ƙara ruƙunƙume shi take yi, mijinta ta kira ta shaida masa badia ta haihu,


Shima yai mata murna sannan yace a bawa badiar, nan ta hau ƙarya wai badiar bacci take yi

Mummy sabit ya kira yace mata badia ta haihu ita ma mummyn tai murna sannan tace a bawa badiar tai mata barka shima duk ɗaya yace tana bacci



Haka suka dinga kiraye kirayen waya suna shaidawa badia ta haihu, ni dai kallo ne nawa


Zuwa can baby ya fara mutsu mutsun yunwa, dabino sabit ya tauna ya lasa masa a bakin sa sannan aka bishi da zam zam



Wajen azahar aka sallame daga asibitin muka kama hanyar gida, wai don renin hankali babu wanda yake ta kaina ni dana haihun sai ta baby,


Ɗakina na shige na samu na watsa ruwan zafi a jikin sannan na fito kitchen na ɗaura indomie na ci na ƙoshi sannan na wuce ɗaki na na kwanta



Wajen ƙarfe 06:00 na yamma sai ga mummy, ina kitchen ina dafa shayi
Sai ga mummy, da sauri naje na tare ta

"mummy ashe kina tafe" tsayawa tayi tana kallona


"ya naga kamar ma kece me jegon duk kin wani ɗashe"

Ta faɗa tana kai hannun ta kan fuska

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login