Showing 12001 words to 15000 words out of 88726 words
Chapter 5 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt
rage burin shi su je asibitin ace bai zube ba
Cikin ikon Allah suka iso asibitin da badia ke awo suka shiga wajen ganin dr. binciken farko ya nuna ciki babu shi
Sabit kamar yayi kuka a rayuwar shi yana son yara barin ma ace yadda badia ke da kyan nan a haɗa da nashi ai Allah ne kaɗai yasan irin kyan da ƴaƴan su zasuyi
Hankalin sa ne ya tashi sosai inda duk ya bi ya tsagwami kansa don shi a tunanin sa faɗan da sukai jiya ne ya zubar mata da cikin
Badia sam hankalin ta be wani tashi ba kamar yadda sabit ya tashi nashi hankalin daga ƙarshe ma sai ita ce ta koma tana lallashin sa
" haba *SD* kar ka damu in shaa Allah we will try again, kuma cikin be fi wata biyu"
"only kin kuwa san yadda na ɗaura raina akan cikin nan wallahi nagi nake yi kamar fault ɗina ne da bamuyi faɗa ba da ƙila cikin bai zube ba" ya faɗa da alamar tausayi a tattare da shi
Lallashin sa ta dingayi, bayan an basu magani an sallame su sai ta saka rigimar ita gida zai kaita har ta warke
Ba haka ya so yaso ace ta dawo gidan sa tayi jinya amma ganin bata da lfy ya shi ƙin cewa komai kawai yai hanyar gidan su da ita
Yana ji yana gani ya kai badia gidan su ya baro ta acan don ta samu ta ɗan huta, kuma ta samu sauƙi, ko da ya dawo gida ya faɗawa mummy abinda ya sameta
Sai mummyn ta jajanta masa sannan tai masa ƙorafin zuwan badia gida, kyakkyaɓe mata fuska yayi kamar zai yi kuka, wannan ne ya sa ta jan bakin ta tayi shiru
********************
Sai da badia tayi wata guda a gida sannan ta dawo shima sai da sabit yai ta safa da marwa yana roƙon ta sannan ta dawo anna wannan karan ma da sabuwar cook ɗin su
Me suna kulu, to ita matsalar klu bata iya kowane abinci ba sai tuwo da dai dangin na gargajiya bayan kuma su sabit ƴan zamani ne ba son tuwon suke ba
Wannan dalilin ne ya sa kulu bata daɗe ba suka sallame ta, suka koma take away daga restuarant
Duk abinda ke faruwa a part ɗin sabit mummy tana sane ta ƙyale shi ne kawak don taga iya gudun ruwan sa
A ka ci gaba da yin take away har Allah ya kuma haɗa su da wata sabuwar cook ɗin, ita kuma sata duk abinda ta gani sao ta ɗauka ta ɓoye da taga lkcn ba mutane sai ta fice daga gidan
Rannan sai ta ɗauki agogon sabit ya ajiye akan dinning table yana breakfast kawai ya shiga ɗaki ya fito ya nemi agogo ya rasa
Tun yana nema shi kaɗai har badia taji suka shiga nema tare, abu kamar wasa agogo yayi ƙafa ya gudu
Sam basu kawo ita ta ɗauka ba don har da ita ake ta nema, sai badia ce kamar ance ɗaga idon ki ki kalle ta sai taga gefen zanin ta yayi wani ƙulili
Tambayar ta tayi
"ke meye a jikin ki haka" nan da na sa jikin yarinyar ya ɗaurawa, badia kuwa ta kwacume ta ta kwance mata zani sai ga agogo
Shidai sabit tunda ya ɗauki agogon sai ya fice ya barsu inda badiar ke ta dura mata zagi, daga nan ita ma ta kore ta,
Abinfa ya fara isar sabit wai duk masu girkin da aka samo musu sai sun samu matsala ne me yasa baza su samu cook ɗaya ba mtsss Allah dai ya kyauta
Kuma neman wata cook ɗin sukai inda aka kawo musu wata tivi, kana ganin ta kaga rashin tsabta, har wani tashi take don tsabar tsamin da ke fita daga jikin ta
Sabit sam hankalin sa be kwanta da ita ba don shi mutum ne me shegen ƙyanƙyami don haka ko tayi abinci baya ci sai dai yai ta raɓe raɓe yau shine cin abinci anan gobe a can
A maimakon shi da yake da mata a ganshi ya murmushe sam sai ma wani ramewa yake yi, ya ya bazai rame ba sam baya samun kulawa ko ta ɓangaren cin abinci balle kyakkyawan kula daga matar sa
Sun tashi da safe sun fice gabaɗaya idan sun dawo da yamma kowanne su a gajiye yake don haka kowa ta kai ta kai yake balle badia ita bata san wani wahala da wani ba balle tace wannan mijinta ne ai ba yaro bane zai iya kula da kanshi haka take cewa
Tun mummy na ɗauke kai har abin ya zo ya fara damunta ta kasa shiru kun san tsakanin ɗa da mahaifi balle kuma mummy me shegen son ƴaƴa
Don haka rannan da ya shigo da safe gaishe ta sai ta gabatar masa da abinci be ji komai ba ya zauna ya takr cikinsa kamar wanda ake wa horon yunwa
"yanzu sabit rayuwar da ka ɗaukar wa kanka kenan ta horƙn yunwa, baza ka zauna ka faɗawa matar ka gaskiya ba ta tashi ta zama mace ta iya girki don ka dinga ci amma sai ka dinga ɗaurewa karya .....🙊 kullum kai kenan zama da yunwa wai akai a matsayin na me mata to meye amfanin auren kenan"
Ta ɗauka zai tanka ko ya kare matar tasa sai taji yayi shiru yana gama ci sai ya miƙe
"mummy don Allah ki neman mana cook me tsafta wacce zata dinga mana girki" yana gama faɗar haka yai ficewar sa maganar tayi mutuƙar ƙona wa mummy rai wato har yanzu shi ba daddara ba
👩🏽🍳 *menu of d day*👩🏽🍳
```danbun shinkafa served with offal pepper soup and kunun zaƙi```
```danbun shinkafa```
_ingredients_
-shinkafa
-zogale
-gyada
-mai
-maggi
-cabbage
-carrot
-green pepper
-albasa
-attaruhu
1)ki ɗauki tukunyar ki ki zuba mata ruwa ba dayawa ba idan kina da colander ki ɗora idan ba colander kuma sai ki saka murfin tukunya wanda zai shige cikin tukunyar a tabbatar ruwan yana ƙasan murfin yadda idan an saka buhu ruwan bazai taɓa shi ba, ki ɓarza shinkafar ki sai ki tankaɗe ta ko za a samu gari a yi amfani da barjajjen kawai, ki wanke sai ki zuwa a buhu ko colander, sai ki saka a tukunyar sai ki rufe
2) ki samu zogalen ki (idan ɗanye ne ki zuge ki wanke, idan bushash she ne sai ki jiƙa shi da ruwan zafi ki ajiye shi)
3) ki ɗauko gyaɗar ki ki ɗan daka ta sama sama kar ta dake
4) idan shinkafar ta fara tirira sak ki sauke ki juye aroba ki zuba zogale gyaɗa ki juya ki ɗan yayyafa mata ruwa si ki ƙara mayar wa
5) ki wanke cabbage, green pepper, carrot (bayan kin kankare shi) sai ki yanka yadda kike so ki ajiye,
6) ki yanka albasa manya manya, jajjaga attaruhu duk ki ajiye, idan shinkafar ta tirara sosai sai ki sauke ki juye a roba ki zuba ƙayan cabbage ɗin nan albasa attaruhu maggi mai, gishiri ki juya a ɗanɗana idan komai yaji sai a ƙara yayyafa mata ruwa a kuma mayar wa a buhu a mayar tukunya sai a barshi ya tirara sosai har sai komai ya dahu sai a sauke ayi serving
*p s* a dinga yi ana duba ruwan ƙasan tukunyar idan ya ƙone sai a ƙara, ga masu amfani da buhu kenan
_offal pepper soup_
```ingredients```
-kayan ciki
-dankali
-attaruhu
-albasa
-maggi
-curry
-thyme
```method```
1) a wanke kayan ciki tas da kyau yadda za a cire duk wani ƙazanta da ke tattare da su sai a ɗora a tukunya a sakar masa ruwa sosai ya sha kansa, a zuba thyme albasa tafarnuwa, maggi sai a rufe a barshi yai ta tafasa
2) ki fere dankalin turawanki ki yanka shi irin yankan da kikai wa kayan cikin sai ki ajiye a jajjaga attaruhu, a ƙara yanka albasa sai a ajiye su
3) idan kayan cikin ya dahu sai ki zuba dankalin ki da albasa da attaruhu da curry da maggi in baiji ba ki ƙara ruwa sai ki rufe ki rage masa wuta ya ƙarasa dahuwa a hankali idan ya ƙarasa saiki sauke sai aci shi da ruwa ruwan sa da danbun shinkafa
*KUNUN ZAKI*
*ingredients*
_Gero_
_Citta_
_Sugar_
_Lemun tsami_
_Flavor_
_kanunfari_
_kimba_
*method*
1) Ki jiqa geronki a ruwa tare da in da hali da daddare kafin safiya ya jiƙu
2) ki wanke a ki haɗa da citta kanunfari da kimba a markado ki tace. Sai ki dibi kadan ki dama koko dashi ki ajiye shi ya huce
3) idan ya huce ki zuba ruwa ciki, Kisa sugar da flavour da ruwan lemun tsami kisa a fridgeyayi sanyi, idan an tashi sha sai an ɗan juya shi kafin shaa🍸
👩🏽🍳 *bon appetit*👩🏽🍳
*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
P⃗a⃗g⃗e⃗ 7🌹
Duk a tunanin sabit mummy zata nemo musu cook amma sai yaji shiru kamar an shuka dusa don haka sai ya yanke hukunci tunkarar ta ya tambaye ta
Ai kuwa yana kawo mata zancen cook ɗin ta rufe idon ta tai masa tas tai masa wankin babban bargo sannan ta kore shi jikin shi a saɓule haka ya fita daga part ɗin nata
Shi sam ya kasa gane mummy to menene don macr bata iya girki ai shi be ga wani abu ba ace mace bata iya girki
Shi wai ace ai wacce ta iya girki shi sam abin baya birge shi, ko yaga abokan sa suna kurin matan su sun iya girki shi tausayin matan ma yake ji gani yake yi kamar an tauye wa matar haƙƙin ta
Don haka in shaa Allah zai ci gaba da neman cook har su dace amma badiar sa fara tas da ita ga gayu ai kitchen be dace da ita ba
*******************
Bayan kwana biyu sai mummy ta tashi da zazzaɓi me zafi inda aka kai ta asibiti bayan test ɗin da akai mata sai aka gano damuwa da kuma rashin bacci yake damun ta
Haka ƴaƴan suka tasa ta a gaba sukai tai mata faɗan wai me ta rasa, aka bata magani aka sallame ta, ko da ta dawo gida sai ta kasa cin komai duk abinda aka bata sai tace baza ta iya ci ba haka suka yi da ita har ta kwana bata ci komai ba ciwo kuma sai ƙara gaba yake
Kashegari tana tashi sai taji sha'awar wani pepper soup da asmau ta taɓa yi lkcn zamata da bikin sabit don haka sai ta faɗawa sabit akan ya je yasa a yi mata
Be wani ɓata lkc ba ya karɓi address ɗin restuarant ɗin hjy munnira, yana zuwa ya ci karo da hjy munnirar ashe ma mummyn ta kira ta faɗa mata har tasa asmaun ɗaurawa
Don haka bai daɗe ba ya karbo ya taho, ko da ya kawo yadda ya ga mummy tana shan pepper soup ɗin nan ya saka shi ma ɗan zubawa don sha
Ai kuwa daga ƙarshe tas ya shanye har mummy na cewa ya bar mata na anjima, sai a lkcn ya faɗa mata ai ya shanye
"ai yarinyar ce ta iya girki ga ƙanƙanta amma girkin ta ko babba sai haka" shi dai sabit don santi ko tankawa be yi ba
Tun daga lkcn ya zama daily customer na restuarant ɗin kuma yana zuwa zaice a sa yarinyar da mummy take son girkin ta tayi masa
Tun daga lkcn ya kasance kullum shi yake zuwa yana yi musu order shi da badia
Baya iya cin abincin ko ina sai na restuarant ɗin safe rana yamma kullum yana hanya
Rannan sai yaje da safe wurin mummy tana zaune ta gama breakfast, tayi masa tayi sai ya ƙi ci, gyara zama yayi sannan ya fara koro mata bayani
"mummy tunda mun neman cook me zai hana kije restuarant ɗin nan kice su bamu cook ɗaya ta dinga mana girki, wallahi kullum na fita daga gidan sai na cen cin abinci
Kuma idan aka taso haka har na fara gajiya"
Taɓe baki mummy tayi sannan tace
"yo me kake son inyi maka tunda kai ka riga ka yadda matar ka ba matar kitchen bace ai sai kaje kai ta muku order ɗin tana zaune ba abinda take yi" ta faɗa tana mikewa don barin wajen
Binta yayi yana mata magiya tare da faɗa mata irin wahalar da yake sha wajen yin order ɗin kullum
Buris tayi da shi kamar bata ji ba duk da dai abinda ya faɗa mata ya taɓa mata zuciya sosai, amma saboda tana son ya gane kuskuren sa sai ta yi kamar bata san yana yi ba
Magiyar yaci gaba da yi mata kamar zai yi kuka kun san tsakanin ɗa da mahaifi ai kuwa nan da nan zuciyar ta ta tsinke inda tai masa alƙawarin zuwa da yamma
Murna yayi mata sosai hadda bata kuɗi wai ko da za abuƙaci payment a take kuma cash, tausayin sa ne ya kamata, ohhh Allah Allah be haɗa shi da mace da ta san darajar aure ba ga shegen ra'ayin shi na ƴan boko ta faɗa tana mita
Sai bayan la'asar sannan mummy ta saka driver ya kaita wajen hjy munnira, don ta gabatar mata da buƙatar ta na son karɓar asmau a matsayin cook
Kasancewar mumy ta nuna wa hjy munnira ƴaƴan banki ya sa maganganun nasu basuyi wani tsaho ba hjy munnira ta yadda da zata ba mummyn asmaun inda za adinga ba hjy munnira kuɗin aikin natan
Asmau bata san hawa ba bata sauka ba kawai sai ce mata akayi ta haɗo kayan ta, ta ɗauka azore za ta koma har ta fara jin ba daɗi,
Ko da suka fito ta ci karo da mummy sai ta ƙara haɗe wannan fuskar tata da sam ba fara'a, mummy tana hango ta ta saki murmushi duk da dai asmaun ranta a haɗe yake
"wai ni hjy munnira yarinyar nan bata fara'a ne", mummy ta tanmbayi hjy munnira dariya kawai hjyr tayi bata tanka ba don itama bata taɓa ganin murmushin ta ba balle dariya, babu bayanin da hjyr tayi wa asmaun kawai dai tace mata zaki koma gidan hjy ki dinga musu girki
Ƙara haɗe girar ta tayi wai me yasa mutanen nen suka son mai da ni wata mara gahilu ne daga ni ce nan sai nice nan
Gani bata tanka musu ba yasa mummy ta miƙe
"to hjy mudai mun tafi fatan mu Allah ya bamu damar riƙe wannan amanar"
"to hjy na gode ai asmau bata da matsala sam baza ki ji ta tana cecekuce da wani ba magana ma bata dame ta balle kuma faɗa"
"ai ba sai kin faɗa ba daga ganin yanayin ta" sukai sallama sannan suka kama hanyar gida
Ko da suka iso gida sai mummy ta sa aka bata tsohon ɗakin da ta zauna lkcn biki sannan mummyn tai mata bayanin yadda take son abincin ya dinga kasancewa
Tun daga lkcn asmau ta fara girki a gidan breakfast lunch dinner kullum ba fashi, da farko daga mummy sai ɓangaren sabit kawai take wa abinci amma da ragowar ƴaƴan suka gano daɗin abincin sabuwar cook ɗin duk sai hutash she da matan su
Tun daga lkcn duk abincin gidan asmau ce take yi, kowa ya saba da cin daddaɗan girkin ta me sanya mutum santi, kafin kacr meye wannan sabit ya murmure yayi ƴar kiba yai fresh da shi abin shi kamar ba shi ba wannan abun yasa kullum mummy take godewa Allah daya haɗa ta da asma'u a matsayin cook ɗin su
Ba sabit ba gabaɗayan yaran ta duk sun saba da wannan girkin da baiwar Allahn nan take yi sam babu wanda ya taɓa sawa a ransa cewar wataran zata bar gidan kunji ɗan adam
*BAYAN SHEKARA BIYU*
Ba abinda ya canza a rayuwar gidan su sabit sai lalacewar matan gidan, yo lalacewa mana don yanzu kowacce ta sakankance da asmau
Duk wani abu da suke so daga sun ɗaga waya sun kira kitchen sun faɗa nan da nan za a kawo musu
Ta ɓangaren sabit kuwa sau biyu badia na kuma samun ciki yana zube wa inda daga ƙarshe aka gano cewar indai har suna son ciki ya zauna a marar badia sai da ta ta samu cikin ai mata ɗaurin mahaifa
Ga sabit da shegen son ƴaƴa duk inda yaga ɗa sai ya ɗauke shi barin ma ace ɗan fari ne, shi dai yana son mutum fari duk munin farin mutum baya gani
Haka zalika duk kyan baƙin mutum sabit baya gani sai yace ak shi wai baƙin ne yake kare masa ganin kyan, sai yayi taji ana cewa black beauty black beauty amma shi sam be taɓa sanin me kyau a baƙi ba
Har musu suke yi da abokan sa musammam masu baƙaƙen mata akan ɓaƙi ma yana da nashi kyan amma sabit sam be gane wannan karatun ba shi dai in kai baƙi ne to kawai kallon muni yake maka
Duk da dai yana da son yara amma baya son baƙin ɗa gashi mataɗ shi Allah ya haɗa ta da matsalar haihuwa inda suke