Showing 60001 words to 63000 words out of 88726 words

Chapter 21 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

ta, murmushi na saki sannan naja hannun ta zuwa ɗakin badia

"zo muje kiga jikan naki"


Bina tayi, da sallama na shiga, suna zaune a bakin gado shi kuma babyn yana cikin gadon sa na jarirai yana ta baccin sa



A razane suke da suka ga mummy, sai suka fara kame kame


"hjy fatima yaushe kika ƙaraso, muje falo mu zauna yaron yana bacci" inji mmn badia


"ni da nazo ganin baby sai ace min yana bacci, ina ita mejegon"


Tsuru tsuru sukai, nidai tunda naga na haɗa su sai nai ficewa ta na barsu


Ɗakin nawa naji an turo ƙofar, ashe mummy ce ta shigo, sai da ta ƙaraso da sannan na bata wurin zama


"har yanzu sabit ɗin basu dawo bane ko dai wani abun ne ya samu badiar"


Ni dai ban tanka mata ba saboda sam ban san ma ina ta dosa ba,


"ni wallahi duk a gajiye nake, nace musu su shirya gobee mu koma abuja ai suna acen dama dalilin zuwa na kenan"


Ni dam ban tanka mata ba don kuwa a gaskiya na fara kewar ɗana, don haka sai nai mata shiru,


Mara ta naji ta fara murɗa min, mitsss sai yanzu na tuna sam ban ma sha magani ba, miƙewa nayi don in ɗauko magani sai naji mummy tana cewa


"asmau lfy naga kina tafiya kamar kece kika haihun, gashi kuma duk kin ɓata zanin jikin ki"


Juyawa nayi don inga inda na ɓata ban ɗago ba sai ganin mata nayi kusa da ni


"asmau ke kika haihu ko badia"

Tsare ta nayi da idona wanda a yanzu suka ciko da hawaye, ɗago min fuskar tawa tayi


"asmau ke kika haihu, ba badia ba" gyaɗa kaina nayi hawaye yana zuba a ido na


"haba biri yayi kama da mutum" inji mummy takaici ne ya kamata sai ta kama hanyar fita



Ban san me tace musu ba sai gata da babyn,

"ungo shi bashi nono ya sha ki gama in gyara ki, wallahi idan sabit ya dawo yau sai yaga ɓacin raina wanna wane irin zalinci ne"



Karɓar babyn nawa nayi na rungume shi sannan na zauna na fara bashi nono kamar dama yunwa yake ji haka ya karɓa ya fara tsotsa



Muryar badia muka ji a bakin ƙofa tana masifa


"ban gane ɗan ta bane yaushe ya zama ɗanta don kawai ta rene shi a cikin ta sai ace ɗan ta wallahi bazai sha nonon ta ba, na riga na gama booking nurse ɗin da zata dinga kular min da yaro" ta faɗa tana shigowa a fusace da zummar karɓar mummy



Mummy ce tace

"wallahi kika sake kika katse masa wallahi tallahi sai na saɓa miki"


"mummy ya za ayi jini na ya sha nonon ta"


"ya akai ya zama jininki"


Nan badia ta kwashe komai ta faɗa wa mummy, bata gama ba mummy ta fashe da kuka, adai dai lkcn sabit ya shigo



Ingiza badia yayi ya kora daga ɗakin, mummy kuwa kuka ta dingayi,ba irin lallashin da sabit be mata ba amma taƙi shiru


Shima sai ya fashe mata da kuka

"anya sabit kana tuna ranar da Allah zai kama ka kuwa akan haqqin yarinyar nan, tunda Allah ya haɗa ku kake zalintar ta, anya kana da tausayi kuwa"


"mummy don Allah kiyi haƙuri wallahi sai da ta amince muka biya ta sannan akai mata dashen"


"wannan yarinyar me ta sani, da har zaku ce wani kun biya ta yanzu ɗan na wane na wacce tai dakon cikin ne ko na ƴar lelen taka ne"


"mummy ƙwan badia ne"

"mummy ba nawa bane" na bata amsa

"amma ni alfarma ɗaya nake so a barni in kula da shi in dinga bashi nono in yaso idan na yaye shi sai badia ta karɓi abinta"


Kallona mummy tayi sannan tace

"asmau ke yarinya ce har yanzu baki san ciwon kanki ba nan gaba zaki zo kiyi dana sani"


"mummy duk yadda Allah ya tsara bawa rayuwarsa haka zai yi ta" na bata amsa
Nai ta mata daɗin baki akan maganar don bana son a jata da tsaho, ta yi mugun jinjina min sannan daga ƙarshe ta saka aka kira badiar sannan ta kuma kafa sharaɗin ni zan kula da babyn



Sam badia bata damu ba, shima sabit ɗin sai ya nuna ya fi son hakan,


Mummy itace ta dinga kula dani, ko da lkcn suna yayi a can wani hotel sukai sunan su, daga ni har mummy ba wanda ya je



Amma ita da sabit da babyn sun sha hotuna kamar ba gobe, wallahi duk wannan abin da ake yi ko kaɗan a jikina be taɓa damuna ba sdon nasan akwai ranar ƙin dillance


yaro ya ci sunan bbm badia amma anace masa annur mummy tai faɗa sosai wai ai sunan daddy ya kamata a saka amma sam ba ai mara kara ba


Kaji mummy wani ɗigimi




********************

*BAYAN SHEKARA ƊAYA*





kamannin annur da sabit ya gama fitowa, sosai ga wayau kuma Sam baya yadda da badia, shegiyar ƙyuya gare shi kamar


Daga ni sai ni, ko sabit in dai ba fita yaga zai yi da shi ba sam baya yadda ya ɗauke shi


Sam badia bata damu ba, ita dai kawai burin ta taga an masa wanka an masa kwalliya tai ta ɗaukar shi a hoto ta na ɗora shi a dp, facebook da instag.


Shima haka sabit ɗin yake sai dai in ban masa wanka ya ɗau gyara ba, nan zaku ga da sabit ɗin da badiar duk suna rige rigen ɗaukar a pic


Sam wai nuna so ko jan yaron a jiki badia bata san wannan ba, ko tashi yayi da safe ya tafi ɗakin ta sai dak kawai kaji tana ƙwala min kiran in zo in dauke shi in masa wanka



Sam bata yadda ta ɗauke shi sai an masa wanka, wai ko yayi pupu ko fitsari sai dai kaji tana kirana inzo in cire masa



Wani rashin *M* ɗin ma sai in yayi pupu a ƙasa kamar ta dake shi haka take, akwai randa mukai faɗa da ita akan shi,



Ya shiga ɗakin ta ba diaper a jikin sa, sai yai mata pupu a kan gado, kawai zagin shi naji tana yi


Da gudu na tafi ɗakin ta ɗaga hannu zata dake shi, da sauri naje na tare masa,


"haba anty yaro ne"
Harara ta bini da shi sannan tace

"ni ƙazanta ta yara ce bana so, zo ki kwashe kashin nan kije kiyi masa wanka"


Tabbas ba ta san ciwon sa bane don wallahi da ta san ciwon sa da uwa tana cikin cin abincin ta ɗan ta zai yi pupu ta saki abinci ta wanke masa sannan ta zo ta ƙarasa




Ita dai bangaren kayan sawa, kayan wasa, anan fa to kusan Rabin albashinta yaron take kashe mawa,



Sai dai jawo shi ajiki ne dai batayi


Ana haka wani zazzabi ya kama shi aiko sai ya kasance ni kaɗai yake yarda in dauke shi, hatta da sabit baya yarda da shi




Anan ne wani sabon rashin mutunci ya tasowa badia inda tace ita Sam atafau ayaye yaro abata ɗanta, saboda gaskiya ita bata yadda ba tana uwar yaro amma sam be shaƙu da ita ba



A zuciyata nace me kike masa da zai sa shakuwa da ke, don kayan wasan da kike sai masa sani yayi shi yaro


Tuburewa nayi nace sam be isa yaye ba sai ya ƙara watanni, abi kamar wasa har sabit ya saka baki shima sai ya goyi bayan badia wai shima baya jin daɗin yadda annur ɗin yake masa



Ban musa ba ganin bana son sa'insa akan shi ya sa na miƙa mata shi nasan ko kukan sa na dare ya sata dole ta dawo min da shi



Ai kuwa tana karɓar sa daya tsanyare da wani kukan ko a jikinta ni kuwa wannan kukan jin sa nayi kamar ana yankan sa har cikin zuciyata naji



Ɗakina na shike ina jin sa yana cewa ```maaa``` da yake haka yake cemin don bakin sa ba wani buɗewa yayi ba



Aiko ko awa daya batayi da daukan shi ba naji ana ƙwallamin kira a ruɗe na fito inda naga yaro shame shame ahannun sabit kamar marar rai


Ruwa ne a hannun badia tana shirin sheƙa masa na karɓa a hankali na yayyafa masa yana farfaɗowa ya fara ```maaa``` ```maaa```



"na'am baby na" na amsa masa ɗagowa yayi ya kalle ni, duk da dai jikin sa ba ƙwari amma a hakan ya ɗago ya taho wajena da saurin sa ya rungume ni



Sosai na matse ɗana a jikina sai ajiyar zuciya yake saki, wanda hakan ya sa zuciyata ta karye naji hawaye ya cika min ido na



Bani ba hatta sabit sai da jikinshi yayi sanyi ni ko hawaye suke sulalo min ganin yadda yaron cikin ɗan lokaci kadan ya fita hayyacin shi amma da ganina yawani lafe ajikina harda ƙara rungumeni


Bacci ne ya kwashe shi a kafaɗa ta ina ɗan jijjigashi ko da yai baccin sai na sauke musu shi


"zo ki ɗauke shi" inji sabit


"ya ci gaba da zama a wajen ki har sai ya saba da badiar sai ya koma, ke kuma dia ya kamata ki dinga samun time kina spending da shi mana don ya saba da ke kooo" ya faɗa da sigar lallashi


"ok shike nan zan duba"


Wuce wa nai da shi ɗakina muka kwanta, kallon shi nayi sannan nace

"annur ɗana ina alfahari da kai, kuma wallahi da kai sai na nuna wa duniya cewa ni asmau ƴar halak ce"



********************


Tun daga lkcn badia take shigowa ɗakina wai don annur ya fara sabawa da ita, amma ko ta shigo tana manne da wayar ta tana chatting shi kuma daya ganta to ahike nan ya liƙe min kenan har sai ta fita



Sam wannan method ɗin be yi ba haka naji tana faɗawa sabit, sai suka tsiri fita da shi yawo, kunsan yaro da son yawo, wannan ne ma sa ya ke ɗan yadda ta ɗauke shi in dai har ya ganta da mayafi ko hijab amma da ta zauna shikenan sai ya fara ```maaam``` yana kuka



*******************
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 23🌹








Da azimi ne muka shirya muka kama hanyar abuja don muyi sallah acan a lkcn annur yana da wata 18 yayi wayo sosai


Kuma kullum kamar sa da sabit ƙara tatsowa take yi, ita kanta badiar tana koka wa duk da dai wani lkcn takance ya ɗauko farin ta


Nakan yi dariya kawai in basar, tun da muka dawo naji canjin ruwa sai na gara laulayi, ada ban ɗauka da gasken ciki gare ni ba sai da muka dawo abuja


Jakar ubacan zamu ga yadda za ayi da sabit da wannan cikin wallahi bazan taɓa yadda ya kuma zubar min ba


Tsab muka koma muka ɗinke da anty fannah har tana min maganar wai na liƙe wa annur bayan uwar sa ƙiri ƙiri take nuna wa bata son mu'amalar mu da ɗanta


Nakan yi murmushi nace ai ba dan ita nake yi saboda yaron make yi, satin mu ɗaya da dawo ta ƙwace annur daga hannuna wai ya isa yaye


A lkcn gaskiya nima na so yaye shi saboda ga ciki abun yana min yawa, gidan su takai shi, batare da sanin sabit ba


Ko da ya dawo daga yawon sa ya tarar an kai masa ɗa gidan su ranar sai da sukai ɗan ƙaramin yaƙi da shi


Ina jin su

"wallahi baza ka hanani kai ɗana gidan mu ba, don ba kai kadai kake da iko da shi ma nima uwar sa ina da shi"


" ta ina kike uwar sa abinda sam baki san komai nashi ba, ki bar wacce take ɗawainiya da shi tai magana mana" inji sabit


Ai kuwa badia sai kuka wai sabit yai mata gorin ba daga jikin ta annur ya fito ba, kuka ta dinga yi wiwi wai Allah ya haɗa ta da mijin da bai san ƙaddara ba


Ƙofata na ja na ƙara rufe wa can ta matse muku ina jin shi yana lallashin ta a zuciya nace an dai faɗi ba nauyi



Ranar da daddare ya shigo ɗakina da ƴaɗ fara'ar sa, ina zaune ina ta shan mangwaro na ko ƙarasa nuna ma be yi har wani ɗan tsami tsami yake yi amma ni a hakan nake son sa


"na lallaɓa wannan rigimammiyar ta kwanta sauran ke"


Ya faɗa yana ƙarasowa kusa da ni


"shan mangwaro cikin dare" ya tambaya, murmushi nayi sannan nace

"ai annur ya kusa ƙani ko ƙanwa" wato ko gabaɗaya tuni wani fara'a da annushuwar da ke tattare da shi kau


"ban gane ba me kike nufi" ya faɗa, ban ɗauka zai ɗau abinda zafi ba sai nace masa


"ciki gare ni kusan 2mnths"

" *WAT* * ya faɗa da manyan harufa,

"ina turaren da na baki kina sakawa kuwa"


"wane turare"

"turaren mana dana baki"


Sai yanzu na tuno ya kuma bani turare bayan na haihu, da farko turare ya ɓata lkcn da nake da cikin annur amma ina haihuwa sai ga turare ya dawo


Ko kaɗan ban kawo komai ba, zaman mummy a gidan ta nai min biƙi ya sani bata da ta tashi tafiya, sabida gaskiya turaren ba dai ƙamshi ba


Da ƙyar ma ta karɓa sai dana matsa mata,


"me turaren yayi"

"tambayar ki nake yi kina amfani da shi ko bakyayi" to kuma zancen sa ya fara bani tsoro


Muye kuma na zancen turare daga samun ciki,

"na bawa mummy" a zabure ya miƙe


"wace mummyn" kallon shi kawai nayi yanzu kuma wallahi na fara tsorata, a fusace ya fice


Ko ma dai menene a cikin turaren wannan shina abinda ake cewa ramin mungunta



Mummy tana bacci sabit ya dinga buga musu ƙofa, da ƙyar ta tashi ta buɗe masa


"lfy auta" ta tambaye shi

"mummy ina turaren da asmau ta baki a lagos"

"amma auta maganar turare shine baza a yi shi ba sai yanzu cikin dare"

"mummy don Allah kice bakiyi anfani da shi ba" tsayawa tayi tana kallon sa


"wani abun ka saka a turaren ka bata ni kuma bata sani ba ta bani" rasa bakin magana yayi kawai sai ya shige cikin ɗakin ta


Turaren yananan kan mirrow ɗin ta ɗauke wa kawai yayi yai ficewar sa, bin sa tayi da kallo sabit zan ga ranar da zaka dawo hanya madaidaiciya


Ɗakina ya dawo a lkcn na gama shan mangwaro na har nayi shirin kwanciya don sam ban ɗauka zai dawo ba


"ke kuma na dawo gare ki, wannan cikin ban san da shi ba kuma bana son shi yanzu, nawa annur ɗin yake don haɗama har kin kuma samun wani cikin to ban yadda ba, nine me gidan kuma idan lkcn da ya kamata ki kuma haihuwa yayi zan faɗa miki, a kuma ɗaukar ƙwan badia a kuma dasa miki"



Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tunkaro ni, lallai ma sabit ɗin nan wato ya mayar da ni baby making machine ɗin sa ko


To wallahi baza ta saɓu ba, ya ɗauka zan masa lakwa lakwa kamar yadda nake masa ada sai ya ga ma buɗe masa wuta nima



Ai ma koya a wajen badia naga alamar sabit zuma ne sai anci da wuta ake zaman lfy da shi,


Faɗa daya ga inayi masa nr ya sashi saukowa

"asmau ba wai bana son ki haihu bane, amma kinga kamar yadda annur yake haka nakr son ƴaƴana su kasance bana son ƴaƴana kiga wasu farare wasi baƙaƙe"


"wannan kuma kai ta shafa wallahi bazan kuma zubar da ciki na ba ka zubar min dana farko wallahi baka isa ka kuma zubar min ba"



Hayayyaƙo min ya kuma yi, daga ganin sa shi ba mutum ne daya iya lallashin mace ba, ko nice dai baya son lallashi oho, yana hawa nima na hau, ko da ya ga yayi lallami yayi faɗan amma duk da haka na ƙi yadda



Sai ya ɗauko wannan shegen turaren

"gashi nam kya ci gaba da shafawa" ya ajiye ya fice

"kuma wallahi kije kiyi nazari na faɗa miki annur be isa ai masa ƙani ba, inma ya isa da ƙwan badia nake son cikin nan"



Inda ya ajiye turare nan na barshi ban ɗauka ba ƙiri ƙiri sabit yake nuna min baya son haihuwa da ni kuma wallahi bazan bari ya samu abinda yake so ba



Kashegari da sassafe na kama hanyar part ɗin mummy don in kai mata ƙarar sa don wallahi abun nashi ya fara isata


Tana zaune tana lazimi na shiga, sai dana jira ta idar muka gaisa sannan na faɗa mata,

"je ki kwaso kayanki daga ɓangaren naku ki dawo nan inga in zai zuwa nan ya ce zai taɓa miki cikin"


Ba haka na so ba naso ace ta kira shi tai mishi nasiha ko faɗa amma dai ko ba komai an samu ci gaba a sha'anin natan



Daga nan ɓangaren anty fannah na wuce itama na fɗa yadda mukai da shi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login