Showing 87001 words to 88726 words out of 88726 words
Chapter 30 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt
 after every six months kafin ƙafar ta dawo dai dai a cire masa 
 Sam banji daɗin wannan labarin ba duk da dai na godewa Allah amma nafi son jin sakamakon operation ɗin ƙwaƙwalwar 
 Ƙara kwantae nama da hankali yayi akan kar mu damu, wanda zai masa na ƙwaƙwalwar ƙwararre ne,
  
  Riƙe hannun likitan nayi 
"pls can i watch da operation" na tambaye shi 
Gyaɗa kansa yayi sannan yasa wata nurse ta rakani, sai da na canza kaya zuwa kaya irin nasu na likitoci sannan na shiga nima amma daga gefe nake inda zan dinga kallon komai da komai
   Wani irin ɗan iskan operation akai masa wanda ba 'ai masa allurar bacci ba idon sa biyu 
  Sai da aka fara masa aski sannan aka yanke fatar kansa sannan aka buɗe ƙoƙon kan nasa da wani abu kamar ana drilling grrrrrrrrrr haka kawai kake ji yana yi 
  Sun daɗe suna abun su nidai ina gefe ina kallo a wata na'ura yadda suke abin nasu, ashe haka ƙwaƙwalwar mutum take 
 Tsab suka dinga abin a hankali a hankali, shi kan shi dr. ba directly yake abin ba, ta microscope kake ganin komai na cikin ƙwanyar kan nasan, yana yi ana goge masa gumi sannan ana miƙo masa duk wani abu da yake buƙata 
  Sai da ake je wajen da jijiyar ta toshe sannan  sannan naga ya buɗe ya saka wani abu kamar ɗan zare ya soka cikin wata jijiya haka 
   Tsab abin ya shige  ya kuma ɓata ɓat a cikin jijiyar, wani ɗan abu kamar allura suka saka a gurin da wannan abun ya shige sannan suka kunna 
   Ba wani ƙara da abin yake yi sai dai jijiyar ce take ta girgiza kamar ana jijjigata 
 Sun yi hakan kusan na minti ɗaya sannan suka dakata, wani likita ne yaje gaban sabit yai masa magana 
 Abin mamaki sai ya amsa, kaiii
 Ya tambaye shi sunan sa, tsab ya bada amsa, ɗagowa sukai suka kalle ni alamar gaskiya ya faɗa na ce yes 
 Suka dinga masa tambayoyi akan rayuwar sa yana basu amsa dai dai kuma duk amsar da ya basi sai sun tambaye ni na gyaɗa kai 
 A haka suka ci gaba da masa aikin ƙwakwalwar ana yi masa suna masa tambayoyin har aka gama 
   Sai da aka gama tsab sannan akai masa allura waccw ta saka shi bacci dole sannan suka rufe masa kan nasan shike nan aka gangaro da shi
 Kuka na dinga yi na murna kamar me, har sujjadar shukuriyya sai da nayi na godewa Allah daya bashi lfy 
 Kwana huɗu aka bashi akan zai yi bacci kafin na sai su tashe shi, in dai be tashi ba in kuwa ya tashi shike nan 
********************
Ranar da sabit zai farfaɗo ranar daddy da badia suka ƙaraso bata tanka min ba nima bance mata komai ba amma sosai ta nuna mamakin ganina da tayi da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe
 Ina kallon ta har ƙasa ta durkusa ta gaida mummy, nace ai yanzu mummy tana da mutunci tunda dai kunji labarin haukacin ɗan ta ya warke 
  Tashi nayi na basu wuri don naji tana son ayi hira da ita, ɗakin da sabit yake kwance na shiga na zauna kusa da shi 
 Ɗan kwantar da kaina nayi kusa da shi, ban san lkcn da bacci ya kwashe ni ba, ina cikin baccin naji kamar ana taɓa min kai na 
 Buɗe ido na nayi sabit ne amma idon sa a rufe yake sai bakin sa daya furta wata kalma wadda sai da na ƙarasa kusa da shi sannan naji inda naji yana cewa 
"only" kut mar lallai ma sabit ɗin nan kana farfaɗowa badia ka tuna ba ni ba ko 
 Haushi ya kamani kamar in make shi ficewa nayi daga ɗakin zuciyata a kufule
  Mummy suna zaune da badia na same su kallon ta nayi a wulaƙance sannan nace 
"ya farfaɗo yana neman ki" dukkan su juyowa sukai suka kalle ni 
"niiii" inji mummy, girgiza kansa nayi sannan nace 
"only naji yana kira" da saurin ta badia ta miƙe 
"Allah sarki *SD* na ko da ka farfaɗo ni ka fara nema aka ce true love never fades" tashi tayi cike da yanga ta shige ciki ta bar mummy da mamaki ni kuma da takaici 
"wallahi mummy bazan kuma ɗaukar wulaƙancin sabit ba"
 Kasa magana mummy tayi 
"hmmm banni dai ya kasa nema na ya kasa neman kowa sai wannan ƴar iskar wallahi bari ya dawo hayyacin sa sai dai ya zaɓa ko ni ko ita" 
  Haɗa kai mukai ni da mummy muna ta jajan tawa juna,
 Buɗewar ƙofar ɗakince ta samu juyawa mukai duban mu ga ƙofar, badia ta fito ranta a ɓacd ko kallon inda muke bata yi ta fice fuuuuuu kamar wacce aka zaga 
 Binta mukai da kallo sannan muka miƙe muka shiga ɗakin, inda muka tarar da sabit a zaune 
"only " naji ya kuma cewa yana kallona, harara na doka masa, wacce ta sashi murmushi 
"mummy kinga only baby ta tana harara ta ko bayan bani da lfy" 
 Kallon sa tayi taid murmushin jin daɗi sannan tace 
"wannan tsakanin ku kunfi kusa, ni dai duba lfyr ka nazo yi tunda na ga ka watsatsake barin in kama hanyar in tafi apartment ɗin mu in huta, Allah ya ƙara sauƙi" 
 Gaba ɗayan mu muka haɗa baki muka ce amin, tana gamawa ta fice ta bar mana ɗakin,
"zo nan mu only" kallon sa kawai nayi na ɗauke kaina, lallai ma sabit ɗin nan gwanjon sunan da yake kiran matar sa zai laƙa min saboda ya mai da ni second hand 
  Matsamin yayi sosai wai in ban matso ba zai taho da kansa, ganin ƙaton bandage ɗin dake ƙafar sa ya sani matsawa kusa da shi 
 Hannuna ya riƙe, ya kalle ni cikin idona sannan yace 
"asmau ban taɓa son kowacce mace ba kamar yadda nake sonki don Allah will u be my only wife 4 ever" 
  Girgiza kaina nayi
"ni dai wallahi bana son only ɗin nan gwanjon sunan badia ne" na faɗa fuskata kamar zanyi kuka 
"kin riga kin gama da ni a duniyar nan kin min abinda bazan taɓa iya mantawa da ke ba da kuma soyayyar ki gare ni don haka duk abinda kike son a dinga kiran ki da shi hakan za a yi, yanzu gaya min wane suna kike sooo" 
 *ASMA'UN SABIT* 
shine kawai abinda na iya faɗa, 
In shaa Allah in Allah ya yarda ni da asmaun sabit har abada 
    Sosai mutumin nan yana kwance yake nuna min soyayya sunfari sunfari kamara ba patient ba, wani abun ma in yayi sai ya bani kunya ko kuma mamaki wallahi sabit ya ɓaci sam baya jin kunyar kansa 
 Yana kwance a gadon asibitin nan amma maganar da ke bakin sa tafi ƙarfin sa, sam mummy bata wani daɗe wa inta shigo ɗakin da ta shigo ta ganmu sai ta fice ta bar mu mu sakata mu walawar mu 
   Tun randa ta shigo ta ganni a kanannade a jikin ɗanta lips ɗina a nashi, a hankali ta mai da ƙofar ɗakin ta rufe wallahi na ganta sabit ne de sam be san ta shigo kasancewar ya juyawa ƙofar baya 
 Tun daga lkcn bata kuma zuwa asibitin ba, ni kuwa kunyar ta sosak nake ji amma da yake ita uwar zamani ce sai bata nuna min komai ba 
  Satin sabit biyu da operation na haihu inda na sauka lfy na samu ƴa ta kyakkyawa itama baƙa kamar twins, 
 Murna awajen sabit kamar me sam be nuna wani abun akan kalar ta ba sai ma huɗuba da yayi mata da sunana 
"Allah ya raya min ke asmaul husna ta" shine abinda yake cewa
  Watan mu biyu sabit ya warke ras kamar bashi ba ga ƴata itama tayi wayo sosai, sai alkcn muka dawo nigeria cike da murna da farin ciki
 Nai mamakin dana ga a gidan mummy zamu zauna ashe isma'il ne ya koma can gidan namu shi da iyalan sa mu kuma zamu ci gab da zama anan kafin sabit ya gama nashi
   Rayuwa muka shinfiɗa ni da sabit ɗina da kuma ƴaƴan mu waɗanda babu yadda mummy batai ba sabit ya bata ɗaya amma ƙiri ƙiri yaƙi sai dak suje can suyi wasa ko da rana amma in dare yayi ko sunyi bacci sai ya ɗauko su sun dawo part ɗin mu 
 Babu wanda yasan sabit ya saki badia sai da daddy yace yaje ya dawo da ita inda anan ne ya ke shaidawa cewar shi ya sake ta ko kaɗan daddy be so hakan ba mummy kuwa har addua sai da tayi masa saboda nuna murnar ta 
  *BAYAN SHEKARA GOMA*
  Rayuwa babu yadda bata juyawa ,muna zaune lfy da mijina inda a yanzu ina da ƴaƴa takwas shida daga cikin su mata ne kuma baƙaƙe sai ɗan autana me sunan daddy wanda yake kamar annur fari tas kamar sabit 
 Na ɗauka irin sabit zai rawar ƙafa dan haife shi amma sai naga saɓanin hakan 
"kai yanzu yayin baƙaƙe akeyi" ya faɗa lkcn da ya ɗau baby irfan, harara na doka masa 
"ina ka koma kenan" na tambaye shi 
 Murmushi yayi ya ajiye irfan ya matso kusa da ni tare da rungume ni sosai sannan yace 
"kalar asmaun sabit ce dole ne in sota
I really love u my asmaun sabit" ya faɗa yana haɗe lips ɗinsa da nawa 
 *TAMMAT BI HAMDULILLAH*
*Godiya sosai ga dukkan masoyan wannan littafin anan na kawo ƙarshen sa Allah ya sada mu da alkharinsa*
*ayi ramadan lfy Allah ya bamu alkhairin da ke cikin ta sannan ya raba mu da sharrin da cikin ta* 
 *pls kusa my cutie walid a  adduar ku mura 🤧🤧 ta danƙe min shi*
  Sai mun haɗu a next Littafina 
*RABONA CE* wanda in shaa Allah bayan sallah amma kafin lkcn 
*I LOVE Y'ALL*😘😘😘
  Bis salam nice a kullum 
```mmn walid and walida ce```
 Mrs Aliyu 🤝🏻
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT) 
(ADMIN OF ADMINS)
        (admin 
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣









