Showing 33001 words to 36000 words out of 88726 words
Chapter 12 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt
sauce*
```ingrdients```
-egg
-attaruhu
-albasa
-maggi
-sardine
*method*
1) ki jajjaga attaruhu da albasa sannan ki a jiye su
2) ki samu sauce pan ki zuba mai da albasa kaɗan idan man yai zafi sai ki zuba jajjagenki sai ki bari ya tafasa
3) kasancewar ba ruwa don haka bazai ɗau lkcn ba, ki zuba maggi, da sardine (bayan ki dagargaza shi) sai ki juya
3) ki fasa ƙwai a bowl daban sai ki kaɗa, idan miyar ta ɗan ƙara soyuwa sai ki zuba kwan sai a barshi kar a juya amma a rage masa wuta
4) idan ƙwan ya dahu sai a ɗan juya kaɗan don kar ƙwan ya dagargaje sai a saike
*banana cocktail*
```ingredients```
-banana
-sugar syrup
-milk
-flavour
*method*
1) ki tasafa ruwa kaɗan da sugar idan sugar ta narke sai ki sauke ki juye don ya huce
2) ki zuba madara a cocktail bowl sai ki zuba syrup da flavour ɗin ki sai ki saka a fridge don yayi sanyi, idan an tashi za ci sai a yanyanka ayaba ƙanana a zuba sai aci a take
👩🏽🍳 *BON APPETIT*👩🏽🍳
*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:51] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
P⃗a⃗g⃗e⃗ 14🌹
Gyara jikina ya kankama ko dana koma gida ban dena ba sai ma abinda ya ƙaru yanzu na zama ƴar gayu don anty fannah har tsokana ta take yi wai na kile na haɗu saura haɗuwar mu da sabit
Na kan ɓata rai a ni yanzu na fi ƙarfin sabit sai wanda zai so ni mu gwada soyayya tare wacce zata kasance a tsaftace ba mix ba irin ta sabita ba
Duk wannan abun da nake bamu taɓa haduwa da shi ba tunda ba ɓangaren sa nake zuwa ba tunda badia tayi ɓari Allah ya yaye min wannan bautar
Sai dai ita badiar wacce ganina da ita na farko bayan na waye sai da ta tsorata da ganina inda ta dake sannan ta fara kushe ni har da cemin
"inde ma don sabit kike yi to ki sa ranki a inuwa don bazaki taɓa birgeshi ba sabit sai ni kaɗai" sam ban raga mata ba nima clna ce mata
"ai ni mijin da zan aura sabo zai kasance dal a leda ba saura ba" maganar ya ƙona mata rai kuma ƙiri ƙiri ta nuna hakan
Tana shirin mai da martani ne sai anty fannah don haka sai ta haɗe rai tare da barin wurin tunda basa shiri dama ko da anty fannah ta tambaye ni me ya haɗa mu sai nace mata ba komai
Don bana son ta ga ko na zaƙu in haɗu da ƙanin ta na fi son ta fara yi min maganar sa da kanta bana son nuna gazawa ta bayan na zama me class 😎
Rannan da safe na tashi mai na ya ƙare don haka sai naje part ɗin anty fannah na faɗa mata in zata fita zan bata kudi ta siyo min, sai ma tace min inzo bayan azahar sai muje siyayyar tare don itama zatayi
Da murnata na koma na je na ɗauka girki kafin wannan na gama na bayar aka kai kowanne part nashi sannan na ɗauki na mummy don in kai mata
Da sallama na shiga falon na ajiye mata, tunda na ɗau gyara na zama kamar wata sabuwar aba a wajen mummy kullum na shiga sai tayi ta bina da kallo kamar bata taɓa gani na ba
Yau ma haka na kai mata har nayi hanyar waje zan fita sai ta kira ni, dawowa nayi na tsaya sai kuma ta rasa abinda zata faɗa min can dai sai tace
"kije kice wa badia ina son ganin ta" rai nane ya ɓaci ba abinda na tsana daya wuce wai inje part ɗin sabit
Jikina a saɓule haka na fice na kama hanyar, na zo dai dai hanyar da zan shiga part ɗin sabit ne naga anty fannah
"muje ko don na gama shirya wa" ta faɗa min
"gani nan zuwa mummy ce ta aike ni wurin anty badia" na faɗa murmushi naga ta saki sannam tace min
"maza kije ki dawo kuma ki dinga tafiya da nutsuwa kamar yadda na koya miki" ban kula taba hmmm kaji ta tafiyar da tace min sai a gaban mijina zanyi shi shine take son inyi shi zan shiga part ɗin wannan mara *M* ɗin
Ƙara sauri nayi ko dana ga na kusa zuwa ƙofar falon sai na saka gudu don inje in dawo da wuri,
Kiciɓis muka ci da wani dai dai corridor ɗin da zai sada ni da ƙofar falon, ruƙo ni yayi wanda da badan ruƙon ba da tuni nayi ƙasa
Ko da nayi gaining balance ɗina maimakon ya sake ki sai ya ƙara riƙe ni tare da shaƙar ƙamshin da nake yi
Can sai ya sassauta min riƙon inda ya kwantar da ni akan hannun sa muka haɗa ido *WAT* sabit ne
"kina gudu ina zaki je, dubi jikin ki lenge lenge kamar bakya cin abinci da badan na riƙe ki ba da tuni kinyi ƙasa kuma irin masu jikinku basa wahalar karye wa"
Ya faɗa fuskar sa taf da fara'a har wani kashe min ido yake na salon yaudara, hankaɗe shi nayi wanda yai taga taga zai faɗi sai kuma ya tsaya ƙyam duk da haka ina jikin nasan
"kar ki kayar da muna preety" ya faɗa
Haushi ya kuma kama ni, na kuma haɗe raina sai ya sake ni
"ki dinga tafiya a hankali don kar kiyi wa kanki illa" ya faɗa wanda ni ko ta kanshi ban bi ba na shige ciki
*******************
Sabit tsayawa yayi yana tunanin wacece wannan gaskiya tayi matsalar ta ɗaya baƙa ce kai da fara ce wannan da anyi haɗuwa
Kasa daurewa yayi sai daya bi bayan ta don yaga ko meye dangantakar su da badiar
Ima shiga falon ma dinga ƙwala mata kira, sai mula sannan sai gata ta sauko
"bashi na ci miki da kike min wannan kiran"
"mummy ce tace kije" na bata ansa
"me zata min" ta tambaya
"wannan kuma imkinje kyaji" na amsa mata tare da juya domin in fice cin karo muka ƙarayi da shi amma wannan karon sam jikin mu be haɗe ba
"asmau" naji badia ta ƙwala min kira, juyo wa nayi ba tare da na tanka mata ba
"me zaki dafa da daddare"
"tuwon semo miyar egusi" na bata ansa
"bana son tuwo jollof nake so kuma ki kawo da wuri, *SD* me kake son yin dinner da shi" ta tambaye shi
Be amsa ta ba saboda gabaɗayan hankalin sa baya tattare da shi sai da ta ƙara mai maitawa har da ƙwala masa kira sannan ya amsa inda kunya ta saka shi shigewa kitchen wanda ni kuma na fice na bar musu falon ina jiyo badia tana tambayar sa wai tunanin me yake a zuciyata nace can ta matse muku
Ina fitowa na ɗanyi nisa daga part ɗin nasu najiyo ana kirana ban tanka ba don nasan sabit ne ƙarasowa yayi ya sha gabana
"kina ji ina ta kiranki" shan kunu nayi nai masa banza
"naji kince tuwo zaki da daddare ni bazanci tuwo ba kiyi min parpesun naman kai da meat pie" kallon sama da ƙasa nai masa sannan nace
"ai na riga na gama rufe girkin da zanyi yau, in zaka ci abincin da matar ka zata ci wato jollof too in kuwa baza ka ci ba sai ka sata ta girka maka ai ta koyi girki a wajena"
"ban gane kin rufe karɓar girki ba, ni mijinki nace miki ga abinda zan ci shine zaki wani ce kin rufe karɓar girkin to ni zaki yi wa biyayya ko wa"
"ni ban san da wani batun aure ba aiki nake yi ake biyana, kamar yadda ka ɗauki auren ka yada shi a kwandon shara haka ni ma na ɗauke shi na saka shi a masai kaga yanzu ba wannan batun ake ba don haka ka ajiye wani batun mijin aiki ne na yau na rufe karbar order in kana son parpesu gobe da safe ka kira kitchen ka faɗa" ina gama faɗa masa na raɓa ta gefen shi na wuce
Lallai le ma yarinyar nan ni zata ce wa haka, ni da nake a matsayin mijin ta nace ga abinda zan ci shine bazata girka ba sai wasu Ƙarti zata girkawa abinci wallahi da sake ya za ayi wai matata ni baza ta min abinda nake so, wallahi hakurina ya zo ƙarshe dole ne a matsayin ta na matata ta kasance tana ƙarƙashina sannan tana bauta min ne ni kaɗai
Yana masifa ya kama hanyar part ɗin mummy dole ne duk abinda za a yi ayi a yau amma ban yadda ba ace matata ban da iko da ita
Har ya shiga ɓangaren mummy yana masifa, tana zaune ta ga shigowar shi ko sallama babu duk a tunanin ta ma ko faɗa sukai da badia ta ɓata masa ransa
"lfy auta na ganka haka wa ya taɓa min kai," ran shi a ɓace ya zauna kusa da ita sannan yace
"gaskiya mummy na gaji da wannan abun da ake min wai ace matata ta zama baiwa a gidan nan, kowa zai iya juya ta yadda yake so amma banda ni mijinta gaskiya bazata saɓu ba na gaji lkc yayi da matata zat dawo ƙarƙashin iko na" sam mummy bata fahimci sai tace masa
"auta wake juya maka badiar taka" mummy ta tambaya, ɓata rai yayi sam baya son ambatan sunan asmau don gani yake yi kamar ajinsa zai zuba amma ganin mummy sam bata ɗauko maganar tashin ba ya sa shi ambatan ta
"ba badia nake nufi" ya faɗa ƙasa ƙasa, dariya ne ya so ƙwace wa mummy amma sai ta dake lallai tarkon data ɗana ya kama ɗan natan ke nan
Amma sai ta nuna sam bata gane me yake nufi ba
"auta a gidan nan kana da wata mata ne bayan badia, only ɗin taka" ɓata rai taga yayi sannan ya ƙara sunkuyar da kansa tare da yin ƙasa ƙasa da muryar sa kamar wanda yake jin kunyar furta kalmar sannan yace
"ɗayar matar tawa mana, mummy kar ki ce kin manta ta mana" shiru mummyn ta sake yi kamar me tunani dariya ce take son suɓuce mata amma kuma tafi son sai ya faɗi sunan ta da kanshi
"in banda abin auta ai da ka faɗa min in ka kuma ganin wata kana son ƙarawa, ai dama na san nan gaba dole ka nemi ƙari tunda baka samu mace ba har yanzu"
"mummy wai asmaun ce kika manta" ya faɗa a fusace dariya ce ta suɓuce wa mummy
"dama ina son jin sunan ta daga bakin ka yanzu me ya haɗa ku da asmaun kazo kuma kana complain"
"mummy yarinyar nan ko kaɗan bata san matsayin miji ba" nan ya labarta mata abinda ya haɗa su da asmaun sannan ya ɗaura da cewar
"gaskiya hakuri kawai nake yi ni matata bata da lkcn da zata kula ni kullum sai dai ta dinga girkawa wasu abinci amma ni sam bata da lkc na gaskiya baza ta saɓu ba nagaji" yai ta mita
Mummyn sakin baki tayi tana kallon ikon Allah sannan a ranta tana godewa Allah daya dawo da hankalin sabit kan asmau, don kuwa ko ba komai asmau sai tafi badia iya kula da sabit sosai
Bata da wani buri daya wuce ace ta samu me kular mata da ɗan autan ta sabit, badia ba me son aiki bace don haka gaba kaɗan sabit zai rasa macen da zata kula da shi
Amma asmau daga ganin ta zata juri wahala kuma zata iya ɗawainiya da wahalar sabit kuma ta asmau sabit zai samu zuria sosai tunda tasan shi da son ƴaƴa
Amma badia ba lallai bane ta haifawa sabit ƴaƴa dayawa, juyowa tayi ta kalle shi sannan tace
"auta yanzu me kake so"
"ni dai kawai so nake yi dum lkcn da na kira ta tai min wani aiki bana son ta kuma cewa wai zatai aiki wani ko kuma tana wani ya sata aiki nafi son ina bata umarni kawai ta ɗauka"
Gyaɗa kai mummy tayi sannan ta jinjina maganar sa
"in shaa Allah zan mata faɗa akan ta dinga bin umarnin ka a matsayin ka na mijin ta" daga nan ta shiga lallaɓa shi tare da kwantar masa da hankalin sa akan babu wanda ya isa ya raba shi da *ASMA'UN SABIT* ɗin sa
Kanshi me ya fasu kamar an masa kyauta sai da ta kwantar masa da hankalin sa sannan yai mata sallama ya kama hanyar sa mummy bin bayan sa tayi da kallo, lallai sabit daga gani ka fara dawowa hanya madaidaiciya ka fara gane cewa ```ba kowacce ƙwarya me kyau ce take da daɗin shan fura ba```
********************
Ko da muka dawo kasuwa sai mummy ta kira ni akan tana son ganina sam ban kawo komai ba don haka na shirya na tafi pary ɗin nata
Ina shiga na zauna sannan ta fara min faɗa akan halin ko in kula da nake nunawa mijina ```wai sabit```😏
Faɗa ta dinga min wai in dinga kula da buƙatin sa, menene da menene ni jin maganar tata ma nake yi kamar soki burutsu tunda dai ba ɗauka zanyi ba ai ni da sabit sai dai daga nesa amma nai masa nisa sai dai wata ba ni ma'un ba
Ta gama saki burutsun ta tsap ban tanka mata ba, sai da ta gama sannan ta sallame ni yadda na tashi na kakkaɗe rigata haka zancen nata ya zube daga kunnuwa na sukai ƙasa banji ba balle ince zan aiki da su
Komawa nayi hidimar gabana na tattara lamarin sa na watsa a kwandon shara, tsakanina da shi ya kira kitchen ya faɗi abinda yake so in faɗa masa
Wani sabon salo daya ɗauko shine kullum in an gaya masa menu na gidan sai ya canza kuma abu me wahala yake ɗauko wa sam bana jin komai haka zan dafa masa
Sai kuma ya canza salo wai innai girki in dinga kai masa nan ma nace bansan zance ba sai da mummy tai min magana sannan na fara kaiwa part ɗin nasaa
Amma bana tashi kawai sai inna ga matar sa na nan ta yadda ba yadda za ai yai min magana ko ya kawo min wani renin sense
Amma duk da haka ban tsira ba, idan na kai masa yai ta sani aiki kenan yi kaza gyara kaza, zuba min abinci kwashe kaza
Haka dai amma ban taɓa tunanin sakar masa fuska ba don dana shiga ɓangaren nasa idan na cukune fuskar nan tawa har na fito be isa ya ga sakin fuskar tawa ba balle yace ze kawo min wani wargi
Har yanzu be isa in kula shi be kai matsayin da zan tanka masa ba, duk da dai idan na shiga ɓangaren nasun yai ta surutu kenan ko kuma yai ta tambayar
Da me dame nayi abincin wai saboda badia ta koya, in na daddage na tsuke wannan fuskar tawa sai dai yayi tambayar sa ya gama amma ƙala bazan ce masa ba
Sai dai in ya gaji ko badia tai masa magana sannan zai dena amma gobe bazai daddara sai ya sake, sam wannan abun da yake yi be sani tanka masa balle inji ina sha'awar mu'amala da shi ni asmau sai namiji wanda ya san darajar mace ba muna maza ba
[4/26, 11:44 PM] Oum Haidar: *******************
Na ci gaba da kula da tattalin kaina ina yi wa ƙanin anty fannah tanadi,
Watan azimi ne ya kama don haka anty fannah in ta zo kitchen tun safe bata barin shi sai mun gama abincin iftar, in itace da girki muna gama wa sai ta tafi in kuwa ba ita baca sai mu sha ruwan mu tare
A lkcn na gano ashe macece me ibada sosai karatun qur'anin nan da azkar baya wuce ta safe da yamma, ganin haka ya sa nima na fara mata maganar akan ta koya min in ƙara sani sosai akan addini na tunda de Allah be sa na je islamiyya ba sosai ba
Karatu sosai muka fara da anty fannah ba ɓangaren da bama taɓowa, wasu karatun inji kunya wasu kuma ba komai, kamar karatun ɓangardn tsarki 🙈
Ba a karatun ilimin addini ba har da na ilimin aure, wallahi wani lkcn idan tana wani maganar sai inji kamar in nutse a ƙasa saboda tsabar kunya amma ita ko a jikin ta kamar ba itace take faɗa ba, lallai sai a lkcn nasan cewar ni babbar jahila ce wacce ba abinda ta iya sai girki
Lallai girki ba shine kaɗai abinda zai jawo hankalin miji zuwa ga matar sa ba har yaji bazai iya rayuwa sai da ita akwai dabaru dayawa ko in kissa
Kamar su kissar iya magana ```wata bata da wani salo na iya yi miji magana yadda take yi wa ƙawarta haka take yi wa aikinta shi ma miji haka, ba wani ɗan laƙwasa harshe ko yango ko kararraiya```
Sai kissar iya zance
```wasu matan sam basu iya tauna magana kafin su faɗe ta ba haka suke suyi ta zuba kamar ƴaƴan kanya marasa daɗi``` inji mmn farency 😜
Sai kissar iya kwalliya,kissar tafiya, yanga, rangwaɗa,