Showing 9001 words to 12000 words out of 88726 words
Chapter 4 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt
da martani amma sai na share ta kawai nayi wajen table ɗin
"auta zo muyi dinner" naji tace wa saurayin ok, kawai yace sannan ya ajiye wayar ya ƙaraso wajen dinning kallo ɗaya yayi min inda ya ɗauke kansa dama ni can bashi nake kallo ba
"mummy me kwashe kwashe ina kika samo ƴar somalia" ya faɗa yana ƙoƙarin zama akan kujera, dariya mummyn tayi
"asmaun ce ƴar somalia, zo kiyi serving ɗinmu kinji ƙyale wannan he likes to joke alot"
"sincerely speaking mum am not joking, kamar aljana haka take ga baƙi ga fuskan ta sam ba fara'a balle annuri"
Ga mamakina sai naji mummy na dariya har da ƙara kallo na na ɗauka ,zata kwaɓe shi amma sai naga saɓanin hakan wannan ne yasa na ƙara ɗaure fuskar tawa na fara serving mummy da soup ɗin wanda za a ci shi da bread
Na gama sai na matso zanyi serving ɗin
"in kika taɓa bowl ɗin nan bazan ci abinci ba" naji ya faɗa, ai kuwa da sauri na na ɗauki bowl ɗin na zuba soup ɗin sannan na dangwarar masa a gaban sa
Tsayawa sukai suna kallo na inda ni kuma na gyaɗa tsayuwa ta irin ta cooks waɗanda sukan abinda suke yi sannan na ɗauke kaina daga gare su
Buɗe baki yayi zai yi magana sai naji mummy ta dakatar da shi
"asmau me yasa kika zuba bayan yace idan kika taɓa bazai ci ba" kallon inda take banyi ba balle in kula ta
"mummy wallahi bazan ci abinda wannan ƙazamar yarinyar ta taɓa ba" ya faɗa yana miƙewa hana shi mummy tayi sannan ta ɗauko sabon bowl a kitchen ta sake zuba masa ta miƙa masa
"mummy bazan ci abinci ba wannan abun tana nan don sai in ƙware"
Mummy ce ta kira ni sannan ta sallame ni juyawa nayi zan fita inda naji yana cewa
"haba mummy me zakiyi da wannan fuskar ta kamar ta aljanu, gata ƴar ƙarama da ita dai dai suffar aljanun wannan in ka ganta cikin dare ai sai ka zura a guje" yana ta kushe hankalin sa akwance kamar be san cewar ina ji ba inda ita kuma mummy abin yake ta bata dariya
Takaici me kawai ya gama kamani ina fita na samu wani ɗan lungu na zauna sai kuka, mutum be sanni ba amma kalmar daya fara jifa na da ita shine kalmar kama da aljanu
Sai da suka gama ya fita daga part ɗin natan sannan ta kira ni na shiga, na tarar da ita tana waya daga ji da hjy munnira take don naji tana cewa
"lallai na yadda ƴar baiwa ce kinga yadda sabit yake ta santi wai ya ɗauka ni na girka" shiru tayi daga gani hjy munnira tana magana ne
Ban hana su hirar su ba sai da suka gama sannan ta juyo gare ni
"asmau sannu da ƙoƙari gaskiya naji daɗin abincin ki, kuma ina fatan har a gama bikin nan zaki ci gaba da kawo mana daɗaɗan abincin ki"
Ban tanka ba ta ci gaba da min bayanin irin yadda take son abincin baƙin ya kasance, breakfast, lunch, and dinner duk ni zan dinga yi amma da taimakon ma'aikatan gidan
Sai da ta gama bayanin sannan ta sa aka raka ni boys quaters inda main kitchen na gidan yake, na gani kuma naga komai sannan aka nuna min ɗakin da zan zauna wanda bashi da nisa da kitchen ɗin sannan anan ne ma'aikatan gidan suke
Sallah isha kawai nayi na kwanta dama ni hira bata dame ni balle raba dare, ina kwanciya nayi addua sai bacci 😴🤤
*******************
Kashegari da sassafe na tashi na haɗa breakfast aka kai wurin mummy, sai gata ta aiko wai in zanyi lunch inyi dayawa domin yau za a fara zuwa
Kasancewar bansan mutanen da zasu fara zuwa ba sai nayi waina da sinasir da miyar taushe me tantaƙwashi, domin kuwa ɗai ɗai ne za suce basa son waina
Sai ƙarfe 01 :00pm sannan na gama inda aka zo aka kwashe, kafin kace me wannan an dawo da coolers ɗin wai a kuma ɗaura wani abincin akwai baƙi masu zuwa da yamma
Haka na dinga girki in sauke wannan in ɗaura wancen kamar ba gobe, kusan duk ma'aikatan yan iska ne sai dai su saka min ido ni kuwa da ince wance zo kiyi kaza gwanda nayi da kaina
Wannan ne yasaka bana samun zama kuma cikin hukuncin Allah kowane course a kan lkc nane gama shi,
Abinci ne kamar ba gobe nake dafawa don ma banayi wani dayawa amma sai dai ina yin abinci kusa kala goma a lkc ɗaya banda soups, snacks drinks duk course sai na haɗa da waɗannan
*******************
Sabit ango sai ƙamshi ake ta zuba wa burin shi ya kusa cika ya mallaki macen da yake ganin kamar babu kamar a duk faɗin duniyar nan
Duk wani preparation da za ayi na bikin anyi shi kuma an shiga bikin lfy, inda aka abokanan sa suka haɗa masa dinner a sheraton hotel, sannan akai arabian night sannan a kai mothers eve ranar kai amarya a nan gidan su sabit ɗin
Duk wanda ya ga amarya badia sai ya yaba kyan ta don kuwa gaskiya ta ɗau wanka da gyara sai dai muce Allah ya bada zaman lfy
Duk wannan abunda ake yi asmau tana kitchen tana ta faman sarrafa abinci kala kala wanda yake barin mutane da tanɗe hannu sannan ga santi
Sai da aka gama biki sannan ta nemi tafiya, mummy sam bata so amsau ta tafi ba saboda ta riga ta saba da abinci yarinyar amma ya zata yi
Ta haɗa mata kayan gara sannan ta saka driver ya kai mai da ita, inda ita kuma asmaun take jim kamar an mata bushara don kuwa gaskiya ba ƙaramin gajiya take yi ba ga rashin sabo da muatanen
Duk da dai nan ma ɗin ba wani jan mutane take yi a jikin ta ba amma ai nan ta riga ta saba da nan ɗin,
****************
Amarya badia ta tare lfy, to akwai wani al ada da suke yi a gidan inda ɗuk wacce ta shigo idan tayi sati biyu zatai girki duk a haɗu a babban falon gidan gabaɗayan su aci girkin amarya
To itama amarya badia mummy ta aika mata da wannan saƙon cewar zatai girki, hankalin badia ne ya tashi domin ita tunda take tafasar ruwan zafi ma bata sani balle wani girki
Bata ji komai ba ta kira sabit ta faɗa masa ita fa bata iya girki, sam sabit be ji komai ba, ai ba lalle ne ba ace mace dole sai ta iya girki
shi wannan karin maganar da ake cewa ```women belong to d kitchen``` sam be yadda da ita ba taya zayi ace don namiji be iya girki ba ba komai kuma wai mace idan bata iya ba sai ya zama tashin hankali
shi zai nuna wa duniya cewar matar sa bata iya girki ba kuma ba wani abu bane kawai ra'ayine kuma da ita kaɗai zai zauna har iyakacin rayuwar sa har illa maa shaa Allah
waya ya ɗauka ya kira mummyn sa ringing ɗaya ta ɗauka
"yau matar ka ce da girki da fatan ka bata kuɗin da zatai cefane"
"mummy dama abinda yasa na kira ki kenan gaskiya badia bata iya girki ba kuma ni dama ban damu ba ace wai lallai sai mace ta iya girki don haka a cire ta a cikin wannan tsarin, waɗanda suka saba girkin su ci gaba don matata bata iya ba kuma ni ma nayi supporting ɗin ta ai ba dole ne mace sai ta iya girki ba"
Mummy mamaki ne ya kamata har ta kasa cewa komai, har sabit ɗin ya kashe wayar, wai matar sabit bata iya girki ba kai wallahi da sake
Nufin ta abincin masu aiki ɗanta zai dinga ci ko me, mitar ta ta dinga yi har ta gaji tayi shiru tunda babu me lallashin ta
Takan yi takaicin rashin haihuwar ƴa mace da batai ba, don wani lkcn ƴaƴa mata ma daɗi gare su, barin ma a irin wannan lkcn da tana da mace da ba sakata ta mata maganin su ba
Kuma gashi ikon Allah dukkan nin ƴaƴan natan ukun da suke da aure da ƴaƴa babu me ƴa mace, duk jikokin natan maza ne, kullum burin ta Allah ya bawa ƴaƴan ta ƴaƴa mata lallai da anga tarbiyya
👩🏽🍳 *menu of d day*👩🏽🍳
```chicken soup served with bread, grilled fish served with jollof spaghetti and side salad, melon cocktail```
```chicken soup```
```ingredients```
-chicken breast (tsokar naman na ƙirjin kaza)
-albasa
-tafarnuwa
-maggi
-curry
-flour
_method_
1) ki sami chicken breast din ki, sai ki wanke tas sannan ki yanka shi ƙanana yankan cubes
2) ki ɗauko tukunya ki saka naman, maggi, tafarnuwa albasa, sai ki rufe don ya dahu
3) idan kazar ta hadu sai ki tsame naman sannan ki sai ki sauke ki tace, ruwan naman kawai ake so, sai ki ƙara mayar da tacecen ruwan namaki akan wuta don ya kara tafasa ki zuba naman kazar ki zuba curry
4) ki dauko flour ki kwaɓa shi da ruwa kamar zakiyi wainar flour sai ki zuba a ruwan idan ya tafasa sannan ki rage wutar sai kiyi ta juya wa kar ki ɗauke hannu don sai yayi miki gudaji, idan yayi ɗan kauri sai ki sauke a ci da bread
```grilled fish served with spaghetti and side salad```
```Ingredients```
_grilled fish_
-kifi
-albasa
-tafarnuwa
-citta
-attaruhu
-curry
-man gyaɗa
```method```
1) ki wanke kifin ki tas sannan sai ki ajiye shi a gefe
2) ki ɗauko kaskon gashin ki sai ki ɗan goga masa mai, sannan ki saka kifinki,
3) ki barbaɗa masa maggi, ki yanka albasa slice, a jajjaga tafarnuwa da citta da attaruhu duk a zuba akan kifin sannan ki barbaɗa curry sannan a gasa a oven kar ki sakar mata wuta don sai ya ƙone idan ya gasu sai ayi serving
_spaghetti_
```ingredients```
-spaghetti
-kayan miya
-mai
-maggi
-curry
-albasa
1) ki zuba mai a tukunya da ƴar albasa idan ya ɗauko soyuwa sai ki zuba kayan miyar ki ki ci gaba da soyawa
2) idan kayan miyar sun soyu sai ki zuba ruwa da maggi curry sai ki rufe
3) a wata tukunyar daban kuma ki zuba ruwa idan ya tafasa saiki zuba taliyar ki, kar ki bari ta dahu tafasa ɗaya biyu sai ki sauke ki tace sannan ki wanke ta (wannan yana sawa idan kin gama taliyar ki ruwan taliyar bazai yi kaurin nan ba)
4) idan ruwan kayan miyar ya tafasa ki ki zuba tafasasshiyar taliyar ki sannan ki rage wuta ki zuba lawashin albasa, idan ya ɗan kara tafasa sai ki sauke
_side salad_
```ingredients```
-tomato
-gwanda
```method```
1) ki yanka tomatoes ɗinki sannan ki yanka gwandar ki duk cubes zaki yanka sannan sai kiyi serving kusa da taliyar ki da kuma kifi
_melon cocktail_
```ingredients```
-kankana
-sugar syrup
_method_
1) ki yanka kankanar ki cubes ƙanana bayan kin cire ƙwallayen,
2) ki zuba sugar da ruwa a tukunya ki ɗora a wuta idan ya tafasa sai ki sauke idan ya huce sai ki juye a kan cubed kankanar ki ki saka a fridge idan yayi sanyi sai ayi serving a ci da spoon
👩🏽🍳 *bon appetit*👩🏽🍳
*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
P⃗a⃗g⃗e⃗ 6🌹
Mummy rasa yadda zatayi da sabit gashi kowa ga san ran girkin matar sabit gashi shi kuma ya kira yace baza tayi girkin ba
Ita ba wannan ne ya fi damun ta ba tunda yarinyar nan asmau mara fara'a ta tafi abincin gidan kamar cusa shi take sam bata jin daɗin sa
Juyi ta dinga yi akan gado tana ƙarawa daga ƙarshe ta tashi ta dauki land line na gidan ta kira kitchen knda ta shaida musu suyi musu dinner gabaɗaya gidan
Abin yabawa ma'aikatan mamaki saboda da safe ta kira tace karsuyi amma kuma yanzu ta kira tace suyi
Sai da yamma tayi kowa ya dawo daga aiki duk an hallara wajen cin abinci za a fara ci sai mummy
"to amaryar sabit dai bata iya girki ba kuma mijinta ya ɗaure mata gindi yace shi ba komai ai ba sai lallai mace ta iya girki sannan za a zauna da ita ba"
" haka ne mu ba kowacce mace ce akayi ta domin kitchen ba" maganar nan tayi bala'in ɓatawa mummy rai inda ta kai masa harara
"to daga yau sai ku dinga cin abinci a part ɗinku in cook zaku ɗauko bismillah amma mun daina ciyar ku"
Babu wanda ya kuma cewa komai mummy ta so daddy ya mara mata baya amma sai taji yayi shiru dama shi mutum ne me bin ra'ayin ƴaƴan sa
Sai da suka gama cin abincin ne sannan mummy ta kuma nanata musu akan su nemi me ciyar da su don ta tsame su daga waɗanda zata dinga ciyar wa, ko a jikin su daga badiar har sabit ɗin suka kama hanyar part ɗin su
Kashegari badia ta kira mmn ta ta faɗa mata abinda yake faruwa da kuma hukuncin da suka ɗauka na ɗauko cook,
Mmn badia ta sha alwashin sai ta nemo musu cook ɗin da ita kanta mummyn ma a wajen su zata dinga kwaɗayi
Cikin hunkuncin Allah aka samo musu wata agnese kafira ce, amma tsohuwar cook ce abincin ta da daɗi kasancewar ta daɗe tana yi
Kafin su tashi da safe ta haɗa musu breakfast haka ma kafin su dawo da yamma ta ajiye musu lunch haka ma dinner akan lkc wannan ne ya kwantar da hankalin ma'auratan ya kasance ba abinda suke yi daga aiki sai soyayya 😍
Ana haka ana haka badia ta samu ciki, me shegen laulayin tsiya ga miyau, ga shegen kwaɗayi, rannan da sassafe ta na tashi wa alala zata ci, don haka sai sabit ya sauko ƙasa don gayawa agnese tayi mata alala
Me zai gani agnese ce a kitchen hannun ta a hammat sai faman susa wa take yi, tana gamawa ta saka shi a hanci ta shinshina yana gani yadda ta ɓata rai daga dukkan alamu bata ji daɗin warin da hammatar ta take badawa ba sannan ba wanke hannu kawai ta koma ta ci gaba da girkin ta
Jun shi yayi kamar zai yi amai tunanin girkin ta daya dinga ci yayi, ji yayi gabaɗaya zuciyar shi na tashi, be yi ƙasa a gwiwa ba yana zuwa ya gayawa badia abunda ya gani
Aikuwa itama sai amai anan inda take, abu goma da ashirin ya haɗu ya haɗar wa sabit, shi yayi aikin aman sa don ba ba komai a aman sai ruwan da tasha
Badia da kanta ta kori agnese sannan ta kira mmn ta akan a nema musu wata sabuwar cook ɗin ko da mmn ta tambaye ta ina agnese sai ta faɗa mata abinda sabit ya faɗa mata
Ita kanta mmn ta koka da wannan abu inda tai mata alaƙawarin sake neman wata me aikin, too fa aiki ya dawo sabit sabo, ya je aiki a hanyar shi ta dawo wa doƙe ya tsaya a restuarant ya sai musu abinci kafin ya dawo
Wani lkcn in ya makara sai dai ya kira badai ta siyo musu haka suka dinga jaurar siyan abinci sune shiga wannan restuarant fita wancan don siyan abinci
Rannan sai ya kama ranar da badia zata siyo abinci ne amma sai ta manta sabit ya dawo gida gajiye ga yunwa ko da ya tanbayi abincin sai tace masa ba kak bane da siyowa
Ranshi ne ya ɓaci don abun nata kamar da rainin wayo,
"so nawa zan siyo jiya ba ni na siyo ba" ya faɗa ranshi a bace, ɗaga kafaɗar ta tayi alamar bata damu
"na manta na ɗauka kai ne yau ma" ranshi ne ya ƙara ɓaci wato ita sam bata ma san laifi tayi ba ko, nan da nan ya hau masifa inda itama ta biye masa sukai ta bala'i
Wannan shine faɗan mu me girma na farko tun aurensu amma sun yi faɗa kamar ba gobe daga ƙarshe kowa yayi zuciya ya kama hanyar ɗakin sa baza a kwana tare ba, a daren badia tai ɓari
Sabit be sani ba sai da safe da ya fito ya ganta a falo da akwati tana ta ja ita zata tafi gidan su kamar ya share ta sai kuma dai ya tambaye taa
"ina zaki da akwatin nan haka"
"gidan mu zan koma tunda wanda ya ajiye ni be damu dani ba har nayi miscarriage be sani ba"
Kalmar miscarriage ce kawai ta dawo da shi daga tunanin da yake
"what, me kika ce" ya faɗa yana kara matsawa kusa da ita cike da tashin hankali maimai ta masa tayi tayi ɓari
Jikin shi har rawa yake ya sunkuce ta sai mota yana ta adduar Allah yasa ba gaskiya bane cikin daya ƙwallafa rai da shi za a ce ya zube subhanallah
Gudu kawai yake falfalawa domin son zuwa asibiti sai da badiar tai masa magana ma akan ya rage gudun sannan ya