Showing 3001 words to 6000 words out of 88726 words

Chapter 2 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

danna wa


Tun ɗazu yake kiran ta amma bata ɗauka ba, tsaki ya ja tare da ajiye wayar

"wallahi sam banga amfanin wayar mata ba ace mutum sai yai ta kiran ki a waya amma wai bakya kusa da wayar" be gama mitar sa ba sai wayar tashi ta fara ringing


Tune ɗin daya saka mata kenan don haka wayar tana fara ringing ya gane ita ce, idon shi ya kai kan screen ɗin wayar inda aka rubutu *only u*


Ɗan tsaki ya kuma sannan ya ɗauka a yangance kamar wani mace

" *SD* don Allah kayi haƙuri wallahi ina sallah ne ka kira" duban shi ya kai kan agogon bangon ɗakin inda ya ƙarfe 03 :15pm


*only u sallah me kike yanzu kar dai kice min azahar"

" wallahi *SD* na shiga meeting ne shiyasa ban samu nayi sallah akan kari ba, ya kake "


"amma meeting sai ya hana ki sallah wai sai yaushe zaki san mahimman cin sallah haba only yanzu haka zamu yi aure ki dinga nuna wa yaran mu, yanzu lkcn sallah bazaiyi ba a bar abinda ake yi a tafi ai sallah ba"

" *SD* kasan matsalar bank fa su koman su a ka'idance yake kar ka damu in shaa Allah tarbiyya me kyau zan muyi wa ƴaƴan mu, kaji"


Ta shiga kalailaye shi da kalaman da tasan suna kwantar masa da hankali kafin kace meye wannan har sun koma kamar ba abinda ya faru,



Sai da suka gama shan soyayyar su sannan sukai sallama akan zai zo da daddare, daga nan sukai sallama kowannen su zuciyar su tana alfahari da kuma ƙaunar junan su





👩🏽‍🍳 *Menu of d day* 👩🏽‍🍳

🍲```Veg cous cous with kidney sauce``` 🍲


```ingredients```

_Cous cous_
_Butter_
_Cabbage_
_Peas_
_Carrot_
_Canned sweet corn_


```recipe```

1) ki wanke carrot ki yanka shi size ɗin da kike so, sai ki wanke peas sai ki haɗa su ki tafasa su da ɗan gishiri, tafasa ɗaya sai ki sauke ki wanke su da ruwan pampo wannan wankewar zai sa su suyi shar kuma su rike kalar su sai ki ajiye a gefe


2) a wanke cabbage a yanka sannan a ajiye shi aside, sweet corn ɗin shima a tsane ruwan shi a ajiye shi gefe


3) ki ɗaura ruwan zafi, idan ya tafasa, sai ki ɗauko cous cous ɗinki a cikin bowl, sai ki ɗan zuba masa dan ruwan zafin, ba dayawa ba ya ɗan sha, *a zuba yadda bazai yi wa cous cous yawa ba* sai ki ɗan bari ruwan ya tsotse

4) ragowar ruwan daya ke tasafa a kan wuta sai ki saka colander ```(in babu colander zaki iya yin na buhu amma a tabbatar da buhun be taɓa ruwan ba)```a kan sa, sannan ki kawo jiƙaƙƙen cous cous ɗin ki, ki zuba, ki kawo kayan peas da carrot ki zuba ki rufe ya turara


5) idan ya ɗanyi wani lkc kika buɗe kika ya dahu sai ki sauke, ki juye cous cous ɗin a wata roba, ki zuba melted butter, da sweet corn da kuma cabbage sannan a juya a zuba a food flask
~bon appétit~


```kidney sauce```


```ingredients```

_Kidney_
_Attaruhu_
_Albasa_
_Maggi_
_Man gyaɗa_
_Tomato paste_
_Curry_
_thyme_


```recipe```

1) a wanke kidney a cire tsakiyar nan don kuwa wataran har tsakuwa ake gani


2)sannan sai ki tafasa ta da albasa da maggi da thyme, idan ya tafasa sai ki tsame ta a gefe


3) a grating attaruhu da albasa, ki saka man gyada kaɗan a tukunyar ki sai ki dan bishi da albasa da tafarnuwa, idan man ya ɗau zafi sai ki zuba attaruhun ki da albasa a barshi ya soyu


4) idan ya ɗauko soyuwa sai ki ɗauko kidney ɗin nan ki saka ki ƙara maggi, tomato paste sannan ki sa curry sai ki rage wuta ki bar shi ya ƙarasa

👩🏽‍🍳 ```bon appétit```👩🏽‍🍳

*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 3🌹






Badia ƴa ce a wajen alh hamza da matar sa hjy bilki, dukkan su ma'aikatan banki ne, inda alh hamza yake aiki a *CBN* ita kuma hjy bilki take aiki a zenith bank


Ƴaƴan su uku mata biyu sai namiji 1 hauwa ita ce babbar ƴar su dr. ce a asibitin general hospital dake abuja tana da aure da ƴaƴa biyu


Sai badia wacce a yanzu take aiki a zenith bank amma ba branch ɗin su ɗaya da mmn ta ba, sai ɗan autan su nura wanda yake karatu har yanzu a china



Rayuwar gidan su badia irin rayuwa ce ta western style babu ruwan iyaye da matsawa ƴaƴan su duk abinda kayi dai dai don haka rayuwa ake yi ba kwaɓa balle harara



Yo ina ma suka ga iyayen nasun balle su kwaɓe su in suna ba daidai ba, kuma cikin hukuncin Allah sai ya shirya musu ƴaƴan babu me abin ashsha masu zuciyar samun na kansu ne amma batu addini sai a slow



Badia sun haɗu da sabit ne lkcn da ya zo bank ɗin su bayan ya samu matsala da master card ɗinsa sai ya kasance badia ce ta gyara masa matsalar



Badia irin dogwayen matan ne masu ƙirar coca cola, fara ce amma duk da farin ta hakan bai hanata shafa man da zai ƙara mata haske ba, Allah yayi da son gayu, don haka take da manema dayawa, gayun ta da kyan ta da kuma iya ɗaukar wankan ta yasa take taƙama da kanta



Tunda ta ɗaura idon ta akan sabit taga gaskiya wannan yayi mata don haka sai tai tayi masa salo salo daban daban ko zai taya, amma ga mamakin ta sai taga kamar ma tana yi da dutse ne



Don haka sai ta kau da ƴar kunyar nan tamu ta mata tace masa suyi exchanging contact incase ko wani matsalar zai kuma tasowa ba sai ya sha wahalar zuwa bank ba



Sabit be kawo komai ba don haka sai ya yadda da abinda tace, ko bayan da to koma gida ta ɗauka zai kira ta amma sai taji shiru, kwana da kwanaki kullum jiran call ɗin sa take amma shiru



Rannan sai ta kira shi inda ga mamakin ta wai yama manta da ita, sam bata ji daɗin yadda yai mata ba amma kuma sai ta ɗau ƙudurin in shaa Allah daga lkcn ba zai kuma cewa ya manta da ita ba



daga lkcn ta zama me kiran shi, tun yana basarwa har yazo yana ɗan dauka har kuma cikin hukuncin Allah suka fara soyayya har gashi suna shirin gabatar da junan su ga gabatan su don a tabbatar da soyayya su,



******************



Sabit ɗa ne na huɗu kuma ɗan auta a wajen hjy fatima da kuma alh bashir, mahaifiyar shi shuwa ce mace me kyau da kwarjini ga ƙaunar ƴaƴan ta, ita bata damu ba ko zata ɓatawa kowa indai hakan zai farantawa ƴaƴan ta wannan soyayyar da ƙaunar da take wa ƴaƴan natan ne ma har yasa ta sa mijinta ya gina wa kowanne daga cikin ƴaƴan natan ɓangaren shi a cikin tafkeken gidan da suke,



Sannan ƙwararriya ce wajen haɗa sanwa, idan ta shiga kitchen ta haɗa dinner sai mutum ya manta sunan sa saboda tsabar daɗi da kuma tsari, wannan ne ya sa ta sha alwashin duk ɗan ta daya yi aure matar bata iya girki ba sai ya ƙara kuma a hakan ake har yanzu



Alh bashir mutumin adamawa ne fulani ne fari kyakkyawa da shi, wannan kyan na bayin Allahn nan yasa idan kaga ƴaƴan su sai ka saki baki barin ma ace sabit wanda kamar su da hjy fatee har ya ɓaci, don haka duk cikin ƴaƴan su ya fi su fari da kyau



Ƴaƴan su huɗu isma'il shine babba, likita ne matan sa biyu, ta farkon auren soyayya ne, amma matar bata iya girki ba don haka sai ta saka shi ƙara aure inda ita ma ta biyu ya kasance da babu ce hausawa suka ce gwanda ba daɗi



Wannan yasa har yanzu isma'il a ɓangaren iyayen shi yake cin abinci, na biyun su shine sulaiman shi ma matan sa biyu duk babu gwanda wajen girki sai na uku mansur wanda shima matan nasa biyun amma su da ɗan sauki sauƙi



Sai auta sabit wanda ake ta shirye shiyen auren sa tooo shin badia ta girki kuwa bari dai mu bisu mu ji ita kuma ya nata yake



********************




Sai ƙarfe 06 :30pm na yanna sanna ya shigo gida duk saurin sa na dawo wa gida da wuri don ya samu ya shirya ya tafi wajen badia amma hakan bai samu ba


Wanka kawai ya shiga yana cikin wankan ne ma yaji wayar shi na ringing ko be gani ba yasan badia ce don ringing ɗin daya saka mata ne



Hankalin sa akwance ya ƙarasa wankan sa ya fito, yana fitowa wayar tana kuma shigo wa, towel ɗin da ke hannun sa ya ajiye sannan ya ɗau wayar

" *SD* sai yaushe zaka zo tun 05:00pm nake jiran ka amma shiru kamar bazaka zo ba"


"only yi haƙuri wallahi aiki ya tsare ni a office, more over ina son mu haɗu da alh ku don ina son jin yadda za a tsara wannan lamarin don na ƙagu in ganki a gidana"


Ɗan dariya tayi irin na nuna jin daɗi sannan tace masa

"kamar kasan kuwa ya dawo shima, bari in gaya masa kana son ganin sa don kar ya fice"

"dats my only shiyasa nake son ki, kuma nake ce miki only don daga ke ba ƙari" ya faɗa hankalin shi a kwance don shi mutum ne da baya son tarkacen mata


Tayi bala'in jin daɗin wannan maganar tasan wanda har ta kasa ɓoye murnar ta ta fara zuba masa shagwaɓa


inda shi kuma wannan abun nata na bala'in birge shi yana bala'in son yaga mace ta iya shagwaɓa, haba me zakayi da macen da babu wani sanyi a tattare da ita, shi ya fi son mace faran faran wacce kullum zaka ganta very lively sannan wacce ta iya shagwaɓa


Ta kasance fara doguwa kyakkyawa duk wannan abun daya ke nema a mace ya same shi a badia shi yasa yake tunanin daga ita babu ƙari, haba gashi fari kyakkyawa ai sai fara me kyau inji sabit



Sauri yai ya ƙarasa shiryawa inda ya shiga masallacin gidan su yayi sallah magariba daga nan ya wuce gidan sahibar tasan


A ƙofar gidan su ya faka motar sa sannan ya kira ta, tana zaune a gaban dressing mirrow ta gama tsara kwalliyar ta irin yadda sabit yake so taji call ɗinsa


Ɗauka tayi a yangance sannan cikin shagwaɓa tayi masa magana

" *SD* sai yanzu ka zo duk na bushe kwalliyar da nai maka duk ta goge" ta faɗa kamar gaske, wannan maganar tata har cikin ranshi ya ji ta yadda ta kashe muryar ta sannan cike da shagwaɓa

"awa nawa kike ki sake min wata zan iya jira a waje"

"wasa nake maka bari insa a shigo da kai"

"ok " ya amsa tare da maida wayar aljihun sa sannan ya tsaya gana jiran ai masa iso zuwa cikin gidan, bai daɗe ba sai ga me aikin su ta fito inda ya bita har farfajiyar gidan inda suka saba taɗi ya samu wuri akan ɗaya daga cikin fararen kujerun da suke wajen ya zauna



Ko da ta gama kwalliyar tata da fesa duk wasu turakan da ta san masu ƙamshi ne sai ta ɗauko hijab ta saka, tana ta mita a ranta


Ita ta rasa irin sabit, duk irin kwalliyar da tayi sai dai yace tabi kwalliyar da hijab, sannan kuma ya hana su taɗi a ckkin sitting room sai dai a waje yacce duk wanda zai shigo ko zai fita sai ya gansu, wallahi daba dan san da take masa ba da tuni sun rabu don wani lkcn abin nashi kamar ɗan ƙauye haka yake yi ba wayewa ta faɗa tana fita wajen sa




👩🏽‍🍳 *menu of d day*👩🏽‍🍳



```Alala```




Ingredients


_Wake
Kwai
Hanta
Dankali
Alayyahu
Oil
Maggi
curry
Attarugu,
albasa
Leda


```method```



1) surfa waken ki saiki wanke shi sosai kisa attarugu , albasa da ki kaishi inji a Markado miki


2) ki wanke hantar ki ki dafa ta da albasa,maggi thyme idan ta dahu saiki sauke ki aje gefe


3)ki fere dankalin turawanki ki yanka shi cubes ƙanana, sai ki yanka dafaffan ƙwan ki shima ƙanana, alayyahu a fara wanke shi sannan shima a yanka shi sannan a ajiye

4) sannan sai ki ɗauko markaden ki saiki dauko mai ki zuba aciki kisa maggi da curry ki kara ruwa in ƙullun yayi kauri amma ruwan da kika tafasa hantarki kikara yanka albasa ki buga kullon ki ɗauko hantar ki da ƙwan ki, da dan kalin da alayyahu kixuba ki ƙara bugawa, sai ki ɗan ɗana, idan komai yayi sai ki saka cray fish (niƙaƙƙe amma optional ne)



5) sannan kije ki ɗora tukunyar akan wuta kisa ruwa bayan ki ɗora saiki zo kina ɗiban ƙullun kina sawa aleda kina ƙullawa kina sawa cikin ruwan zafin nan har ki gama ki rufe har ta dahu saiki sauke .


*Minced meat sauce*


Niƙaƙƙen nama
Attarugu
Oil
Green papper
Maggi
Albasa
Tafarnuwa



```method```
1) ki ɗauko frying pan sai ki zuba ɗan man ki ki saka masa albasa kaɗan idan ya ɗan yi zafi sai ki zuba niƙaƙƙen naman ki sannan ki ƙara zuba albasa, tafarnuwa maggi sai ki ta juyawa har sai ya koma brown, ba a ɗauke masa hannu don sai ya ƙone



2) idan naman ya koma brown sai a ɗan zuba ruwa a rufe ya dahu, ruwan kadan ba dayawa


3) idan naman ya tsotse ruwan sai a zuba niƙaƙƙen attaruhu, da albasa curry sannan sai a rage masa wuta har ya soyu, shima a dinga juyawa don kar ya kone

Sai aci da alalan




*Pineapple drink*

madara
sugar
abarba
flavour

1)ki fere abarbar ki ki markaɗa a blender sai ki tace saboda ba duka bane suke markaɗuwa ba


Sannan sai ki ƙara mayar da wadanda basu markaɗu ba ki ƙara markaɗawa suma ki tace ki ci gaba da markaɗawa har dai ki samu yadda kike so

2) ki juye a cikin roba mai kyau sai ki ɗauko wannan madarah ki juye a cikin wannan ruwan abarbar ki zuba sugar (amma nafi gane in dan tasafa sugar da ɗan ruwa idan ya narke sai ki sauke ki barshi ya huce) kisa flavour

3) a juye a jug a saka a fridge don ya yi sanyi sai sha 🍸


👩🏽‍🍳 *bon appétit* 👩🏽‍🍳


*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 4🌹



Da sallamar ta ta ƙaraso inda yake cike da tafiya cikin yanga da karairaya sai kace zata karye, iskar farfajiyar sai ɗauka hijabin da ke jinkinta yake inda ƙamshin turaren ta yai masa sallama


A rayuwar sabit in akwai abinda yake so da badia be wuce ƙamshin ta da gayun ta ba ga uwa uba fara ce tas kamar jinin larabawa, ƙarasowa tayi cike da yanga da kuma shagwaɓa ya zauna kujerar da ke kallon tasa sannan tai narai narai da ido kamar me shirin yin kuka sannan tace

" gaskiya *SD* ka shanya ni, tun biyar nake ta jiran ka sai yanzu, kuma kasan dokar ka ta gama hira ƙarfe 08:00pm gashi yanzu takwas ɗin ta kusa" ta ƙarashe zancen ta tana kyakkyaɓe fuska kamar me shirin kuka



Wannan abun da badia take yi shine abinda yake ƙara hargitsa wa sabit tunani har yake ganin kamar bazai iya rayuwa ba tare da ita ba


Haƙuri ya shiga bata inda ya kuma kawo mata uzurin office ne ya hana shi zuwa da wuri, sai ya kawo mata zancen da yasan zatai farin ciki da shi na batun auren su



Nan ta nuna murnar ta kamar ba gobe bata da wani ragowar buri a rayuwar ta daya wuce ace ta mallaki sabit a matsayin miji, miji na nuna wa sa'a, mijin daya ke kallon ta ya daki ƙirjin sa cewar daga ita ba ƙari, mijin da a kullum zai dinga saka ta cikin farin ciki



Tattaunawar su suka ci gaba akan yadda za a gidanar da bikin da kuma shirye shiryen da zasuyi na bikin, har mahaifinta ya dawo sannan sukai sallama inda ya je domin su tattauna da shi akan magabatan sa da yake son turowa




Cikin hukuncin Allah sukai tsaida magana inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login