Showing 6001 words to 9000 words out of 88726 words

Chapter 3 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

mahaifin badia yace wa sabit ya turo da iyayen sa sai a ƙarasa maganar tunda maganar ta manya ce


Sabit cike da farin ya koma gida inda ya sanar da mahaifiyar sa,

Mummy ta taɓe baki ta gyara zama, sarai ya san dalilin wannan abu mummy tana da wani aqida ne wai sai lallai mace ta iya girki, shi kuwa sabit ba shi da wannan tunani shidai kawai ya auri badia

"auta kana ganin wannan me rawar kan da kake son ɗauko wa ta iya girki kuwa, ko in nemo maka wata in yaso dai ka haɗa biyu kamar ƴan uwanka"


"mummy na ɗauka mun gama wannan maganar da ke,ni dai gaskiya bazan ƙara aure ba akan girki, kin yadda da wannan inda ni kuma na yadda bazan nemi aiki a ƙasar waje ba zan zauna kusa da ke"


Ya faɗa yana kallon ta don ya son ba abinda mahaifiyar sa ta ƙi jinin ji daya wuce yace zai fita ƙasar waje neman aiki takance duk abinda baka samu a ƙasar ka ba to bazaka same shi a waje ba



"to kuma me ya kawo wannan maganar, don kawai na tambaya ka a kan iya girkin ta"


"mummy ma'aikaciyar banki ce don haka ko aure mukai ba zama za mu dinga yi a gidan ba, ita tana wajen aiki nima haka don haka karki damu"



Taɓe baki tayi Sam ita ba haka take so ba, ta so ace sabit ya ɗauko macen da ta iya girki sosai tunda shi mutum ne me son girki different varieties amma wai ya ɗauko wani tsari wai aiki, duk cikin matan ƴan uwansa babu wacce take aiki sai matar shi kawai, lallai dole ne ta dakatar da wannan aikin taya ma za ayi ta iya kular mata da ɗanta bayan tana aiki



Sabit yadda yaga mommy ta zurfafa cikin tunani yasan tasa saƙa wani abunne don haka sai yace mata

"mummy i hope u r not thinking about any strategy don mun riga mun gama yarjejeniya da ke akan baza ki shiga maganar aure na ba"


"to me kaji nace, ni batun aikin nata ne kawai bana so"


"mum ki bar komai kawai mun riga mun gama tattaunawa da ita da aikin ta na ganta don haka bazan hanata ba, kuma aikin ta bazai hanata kula da ni ba" ya faɗa yana ficewa don yasan idan ya tsaya sai mummy ta kawo wani abun da bazai iya magance shi ba



*******************



Cikin hukuncin Allah aka kai kuɗin auren sabit inda da yake abin na manya ne aka saka wata biyu, ba abinda zamuce sai dai muce Allah ya kaimu



********************


Asmau an ƙara wayewa ta ɓangaren girki, kullum ƙara gogewa take yi ta ɓangaren sarrafa abinci kala kala, wannan ƙwarewar tata yasa ya ƙara jawo wa restuarant ɗin su customers sannan restuarant ɗin ya kuma yin suna lungu da saƙo an san shi kuma ana zuwa ko cin abinci ko yin order



Wannan iya girkin na asmau ne ya saka hjy munnira tura ta zuwa ga wani catering school don ta ƙara ƙwarewa, don duk wani abinci na zamani a restuarant ɗin sai a hankali sun fi siyar dana gargajiya



Domin a ƙara haɓaka restuarant ɗin ya kasance duk irin sunfarin abincin da kake so akwai sai hjy munnira ta tura ta catering school inda taje ta fara koyan abincin na garuruwa iri iri kama daga na turai, larabawa, chinese da dai sauran su



Shekarar asmau ɗaya tana karatu inda ta ƙware ta fi da ƙwarewa har ta kai duk restuarant ɗin itace chef de cuisine wato itace shugaban ƴan kitchen ɗin gabaɗaya duk da ƙanƙantar shekarunta



Girki take fesawa na kece raini, babu wanda zai ci abincin ta baiyi santi ba, wannan ya sa restuarant ɗin ya kuma haɓa ka har hjy munnira ta ƙara buɗe branches inda duk anan ake yin girkin sai ana gama duk sai akwasa akai can branches ɗin



Duk wannan ɗaukakar da Allah ya bawa asmau me sa ta ta fara kula da jikin ta ba, tana nan baƙar wuluk kamar da fuskar ta ake girkin, ga rashin fara'a wannan ɗabi'a ce sam a lamarin ta ba fara'a



Ga miskilanci sai ta wuni bata cewa kowa uffan ba, don haka da wuya kaji anyi faɗa da ita ko cecekuce, ita dai kawai tayi aikin ta ta koyi sabon girki sannan tayi kuma a yaba



Rashin fara'ar da sakin fuskar ta yasa duk mazan da ke cikin kitchen ɗin suke ganin girman ta duk da dai a kitchen ɗin har yanzu ita ce ƙarama, don har yanzu batai 16yrs ba, ga ƙaramin jiki sai ka ɗauka ma she is only 13yrs amma sai shegen basirar sarafa abinci kamar da wannan hikimar aka haife ta




******************


Ko da lkcn auren sabit da badia ya matso sai mummy ta zo restuarant ɗin hjy munnira akan tana son cooks waɗanda zasu dinga yi mata girki da bikin ko dan baƙin da zasu zo na kwana



Ganin yadda mummy tace wa hjy munniran zata biya su labour ɗin su ne yasa hjy munnira amincewa har da saka asmau a ciki tunda girkin kwana uku kawai zasu yi anyi bikin an watse, don haka sai ta yanke hukunci tura asmau ita kaɗai tunda mummy tace akwai ma'aikatan da zasu taya su aiki, ita kuma hjy munnira bazata iya barin iyayen kuɗin nan da mummy take da niyyar biya ba




Asmau bata san hawa bata san sauka ba kawai sai taji hjy munnira tai mata maganar tafiya gidan wata wai zata dinga abincin biki da taimakon wasu



Fuskar nan tata da kullum take cunkushe ba fara'a ta ƙara tsuke ta sannan tace

"hjy ban gane ba, ai ni aiki na anan yake"


"can ma aiki zaki yi na kwana uku ki dawo, biyan ki nake yi don haka ina da ikon tura ki duk inda na ga dama, sauran inkin je ki ci gaba da wannan turɓune fuskar taki" ta ƙarashe zancen ta tana ficewa tare da barin asmau ita kaɗai a ɗakin



Ran asmau yai mugun ɓaci wai taje wani gida aikatau duk da dai aikatau aka kawo ta amma yanzu ai ta wuce wannan matsayin amma shine matar nan take son kai wani gida wai ta zame musu cook ta biki, ƙara cunkushe wannan fuskar tata tayi sannan ta fito ta fara haɗa kayan ta




A cikin restuarant ɗin taci karo da driver na gidan da zata yana jiran ta, inda bayan ta fito hjyr take ce masa

"gata nan ita kaɗai ce zata" bin asmaun yai da kallon raini inda ita kuma ta daka harara tare da ƙare haɗe ranta


"hjy madam fa mutane uku tace ya zaki haɗani da wannan ƴar yarinyar" dariya hjy munnira tayi sannan tace


"kace wa madam wannan itace best chef ɗin gidan nan shigasa na bata aron ta" ƙara kallon baƙar yarinyar yayi sama da ƙasa yadda ta wani haɗe ranta kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa ga ƙanƙanta amma wai ace ta fi kowa iya girki lallai ashe ma girkin ba wuya, ya faɗa a ransa


"muje to da rabon madam ta dawo da mu"

"in bata yadda ba kace ta gwada giɗkin yarinyar kafin a dawo da ita" gyaɗa mata kai kawai yayi suka fice inda asmaun ta fice ba tare da tayiwa hjy munniran sallam ba don har yanzu haushin ta take ji




Sunyi tafiyar kusan minti ashirin sannan suka ƙaraso wani tafkeken gida, tunda muka fito drivern nan yake min surutu iskar da ta kwaso shi ma ban shaƙa ba balle zancen sa ko da ya ga alamar banni da niyyar tanka masa sai ya ja bakin sa ya tsuke har uka isa gidan layi guda ya cinye, a ƙofar wani makeken get driver ya tsaya inda suka fito tare



Tsayawa tayi tana ƙarewa gidan kallo dabadan hjy munnira ce ta ce mata ta biyo shi ba da ba abinda zai sata biyo shiva wannan gidan kamar na yankan kai



Sai da suka ƙwanƙwasaƙofar sannan wani turƙeƙen arne ya leƙo

"who's knocking" ya tambaya da wata muryar sa wacce zata iya sawa mutum ya zura a guje, ganin driver ɗin ne yasa shi wangale baki wai yana murmushi



Shi kanshi murmushin ƙara masa muni yake balle kuma, buɗe mana get ɗin yayi muka shiga, inda muka tasamma tafiya kamar zamu wata unguwa ba acikin gida muke ba



Sai da mukai tafiya me nisa sannan muka isa wata ƙofa inda drivern ya danna door bell sai ga wat ƴar dattijuwa nan ta zo ta buɗe

"mlm garba tun ɗazu hjy take ta jiran ka har ta gaji ta hau sama sai ku ɗan jira kaɗan sai ta sakko naga ma kamar ba a samu masu girkin ba ko, ai dama na faɗa wa hjy ko miliyan zata basu baza su bata wacce zatai mata daddaɗan girkin da take siyar wa ba ita dai tafi son kawai ai ta siya a wajen ta" duk wannan bayani tunda ta ɗauko shi bata numfasa ba sai da ta kai aya



Wanda aka kira da mlm garban wato drivern bai ce komai ba sai kawai ya nemi waje ya zauna, ni bece min ga guri ba don haka sai na ci gaba da tsayiwa ta



Ina da wani abu in ba bani abu kayi ba ko kuma ba nunain kayi ba bazan taɓa motsawa ba balle insan Allah ya yi ruwan abun anan



Sai daya ga na daɗe da tsayuwar sannan yace min

"baza ki zauna ba, ke gaki ƴar ƙaramar ki da ke amma zuciyar ki kamar ta kafirai tunda muke tafe nake ta miki hira amma kamar gunki yanzu kuma ki nemi waje kin tsaya an gayamiki hjy yanzu zata sauko ne"



Iskar da ta kwaso shi ban kalla ba balle shi, ya buɗe baki kenan zai ƙara magana aka buɗe ƙofar falon wannan dattijuwar ce dak ta kuma fitowa


"hjyr ta sakko" tace da mu, tashi yayi yai gaba ni kuma ina biye da shi a baya muka shiga fatana Allah yasa hjyr tace baza ta karɓe ni ba




👩🏽‍🍳 *menu of d day*👩🏽‍🍳


*chinese fried rice served with russian salad & mixed fruit juice*



*chinese fried rice*

```ingredients```

-rice (a tafasa sannan aka wanke)
-eggs
-carrot( a kankare shi a wanke sannan a yanka shi cubes)
-peas
-green beans(a wanke a yanka shi kamar girman carrot)
-man gyaɗa
-tafarnuwa
-albasa
-curry
-nama tafasashshe shima a yanka shi ƙanana


1) ki haɗa carrot, peas, greenbeans ki dafa su da gishiri, idan sun dahu ki sauke ki wanke su da ruwa, (wannan yana sawa suyi retaining colour ɗin su)


2) ki ɗauko frying pan, ki zuba mai da ɗan albasa sai tafarnuwa, idan man ya ɗan fara soyuwa sai ki zuba naman, da kayan veges ɗin da kika dafa kiyi ta juyawa


3) idan sun ɗauko soyuwa sai ki matsar da gefe, sannan ki ɗauko kwai wanda kika fasa kika kaɗa shi sai ki zuba a gefen da ba komai ki bar shi ya ɗana fara soyuwa


4) da kinga kwan nan ya dauko soyuwa sai ki saka cokali ki fara dagargaza shi, kina yi kina juyawa haɗ ya soyu sannan ya zama dagargajajjen ƙwai, sai ki haɗe da ragowar veges ɗin da kika matsar gefe ki ci gaba da suya



5) idan sun soyu ko ince sun ɗanyi laushi, sai ki ɗauko shinkafar ki wacce kika tafasa ta kika wanke ta tsane sai ki zuba, ki zuba maggi curry da duk wani seasoning ko garnish da kike so sai ki cigaba da juyawa har sai ta soyu ita ma sai ki sauke a juye




*russian salad*

```ingredients```
-Dankalin
-peas
-cucumber
-carrot
-green pepper
-egg
- bama mayonnaise


```method```

1) Ki free dankalin turawan yanka shi ƙanana sannan a tafasa shi a sauke a barshi ya huce)

2) a kanakare carrot sannan ayi yanka shi kamar yankan da akai wa dankalin a haɗa shi da peas a dafa su (irin dahuwar da nake faɗa)


3) a yanka cucumber irin yankan carrot, dafaffan ƙwai shima green pepper ɗin


4)ki haɗa komai a roba, dankalin, carrot, peas, egg, cucumber, green pepper sannan a dan barbaɗa maggi saboda ɗanɗano sai a saka mayonnaise a juya sai a juye a mazubi



*mixed fruit juice*

```ingredients```
-Kowane kayan marmari da suke tashe

-sugar
-flavour


```method```


1) ki haɗa kayan marmarin nan tas ki markada kina makaɗawa kina tacewa kin sakewa har a samu yadda ake so


2) a zuba suga da flavour sannan a saka a jug a saka fridge don yayi sanyi sai sha


👩🏽‍🍳 *bon appetit*👩🏽‍🍳



*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:50] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e 5 🌹




Muka shiga falon ba abinda yake tashi a haɗaɗɗen falon sai ƙamshin turaren ƴan maiduguri da kuma sanyin ac



Falon ya sha gyara sosai na kayan ƙawata falon, duk da dai ban taɓa shiga haɗaɗɗen falo irin wannan ba amma hakan be sani na fara ƙauyanci ba


Kallo ɗaya nayi wa falon na ɗauke kaina inda kaina ya sauka kan wata farar mace kamar balarabiya tana zaune a kan couch ɗin da ke falon



Fara ce tas da ita ta sha jan lalle wanda yake ƙara mata kyau da kwarjini, kana ganin ta kasan ta manyan ta amma gayun ta da ɗaukar wankan ta sai ya ɓoye mata tsufan nata



kusa da ita mlm garba ya zube yana ɗiban gaisa inda nima na ɗan tsugunna

"mlm garba ina masu girkin naga da wannan yarinyar" ta tambaya

"ai hjy babu yadda banyi ba akan ta bani masu aiki amma sai tace min sai dai mu tafi da wannan yarinyar wai babu wanda ya fi ta iya girki"


Ina jin shin shi yana ta bayanin yadda sukai da hjy munnira ni dai ban tanka ba kaina a ƙasa, ɗago wa tayi ta kalle ni sannan tace

"don ta raina min hankali wannan ƴar mitsitsiyar yarinyar me zata yi, duk irin kuɗin dabna bata na saka a jakar ta amma baza su sa ta bani su aro na kwana uku ba, shike nan ka mayar da ita kace nace wai ta baka kuɗin ka dawo mun da su na samu wasu cooks ɗin"


Tana gama faɗar haka na miƙe don dama ni haka nake so

"a a tsaya mana, hjy ita hjy munnirar tace ki fara cin girkin ta kafin ki yanke hukunci"



Musu suka shiga yi da hjyr da mlm garba kasancewar yana shegen surutu yasa shi yin galaba akan ta don haka sai tace min in shiga kitchen ɗin ta mata abinci dare


Miƙewa nayi sannan da dakakkiyar fuskata nace mata

"ina kitchen ɗin yake"kallo ta bini da shi

"bakya fara'a ne, ko gidan ne bakya son zuwa" ƙara cunkushe fuskata nayi, don naga alamar waɗannan masu kuɗin da ka sakar musu fuska sai raini ko su mayar da kai wani ɗan iska, don haka sai nai shiru nayi kamar banji ta ba


"hjy ina jin haka take don tunda muka fito banji tace ƙala ba, itama hjy munnirar da take mata magana bata kula taba" mlm garba ya faɗa



Bata kuma cewa komai ba sai sallamar mlm garba da tayi sannan ta kira wannan dattijuwar akan ta nuna min kitchen



INa shiga kitchen ɗin fridge kawai na nufa na buɗe, tsayawa nayi ina kallon abinda ke ciki, babu ba abinda babu ta ɓangaren nama da veges



Kallon fridge ɗin kawai nayi na gane me ya kamata in dafa

``` chicken soup served with bread``` shine starter na

Sannan nayi ```grilled catfish served with jollof spaghetti with side salad``` a matsayin main dish


Sannan sai ```water melon cocktail``` a matsayin dessert
*zaku samu recipe ɗin a ƙasa page ɗin in shaa Allah*


Na riga na saba da three course meal, duk ina in dai lunch ne kƙ dinner, ina gamawa nayk serving ɗin shi a kan dinning table sannan nazo nace mata na gama


Ok kawai tace min bari inyi sallah magariba sai kizo kiyi serving ɗina,


Ban tanka mata ba sai ta kira wannan dattijuwa akan ta nuna min inda zan yi sallah, bin ta nayi naje na gabatar da sallah magariba ta nai nafilar dana saba yi ta bayan magariba sannan nai addua ta dana saba akan Allah ya zaɓa min komai na al khairi sannan ya haɗa ni da miji na gari in dai ina da rabon aure



Tunda gaskiya ni bana sha'awar komawa azore har abada, anan kuwa wa zai auri ƴar baƙa kamar ni




Sai da na idar sannan naji matar nan tace min hjy na kiran ki, ƙarasa wa nayi falon nata na shiga da sallamata, tana zaune ita da wani ɗan matashi,


Bazan iya kallon fuskar sa ba saboda ya juya wa ƙofar baya itace ta amsa min inda shi kuma hankalin sa yana kan wayar sa yana ta daddanawa


"kin ƙarasa ko zo kiyi serving ɗin mu don har na fara jin yunwa tun ɗazu ƙamshin abincin nan ya dame ni" ta faɗa da fara'ar ta wanda nima yakamata in mai da mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login