Showing 81001 words to 84000 words out of 88726 words

Chapter 28 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

badia, wallahi dana ganta sai da gabana ya faɗi


Rabo na da ita tun a court da aka raba mu, da sallamar ta ta shigo kamar gaske, me aiki na aika ta kawo mata abin sakawa a bakin ta


"a a barshi ba zama zanyi ba, dama nazo ne in miki sallama don kuwa gobe zan tafi lagos daga nan zan yi wa sabit rakiya zuwa istanbul don akwai course ɗin da zaiyi na wata biyar acan"


Ji nayi kamar an ɗauki guduma an doka min a kaina, sam sai na kasa gane inda zancen ta ya dosa na kasa gane maganar ma da zan mata ko baƙa zan mata ko me daɗi zan mata


Lallai sabit ɗin nan na gaishe shi wato bazai taɓa dena abinda yake min ba ko


"kin san daa nace ya tafi da ke da farko har ya yadda amma daga baya sai yace shi baya son gayyar ƴaƴa haka kurum kije da ƴaƴa ki hana shi sakewa shi yasa nace to shike nan bari kawai in bi shin"



Kalaman ta ƙara ƙona min rai suke suna kuma tabbatar min da sabit ba zai taɓa canza wa ba,


Zata buɗe baki ta ƙara wani maganar anty fannah ta katse ta

"wannan tsakanin ki ne ke da mijin naki sai kuje can ku ƙarata amma mu ba abinda ya dame mu ko kinga wani abu daya shafi sabit a nan in ba ƴaƴan sa ba, don Allah ki tashi ki tafi in ba fitina kike nema ba"


"toooo daga zuwa abin arziƙi sai ya zama na tsiya, to shi ke nan bari in tafi amma a sani duk abinda mace zata yi wallahi baza ta kamo ƙafa ta don kuwa ance farar mace alkyabbar mata, duk wani jiji da kai da mace zata yi ta tuna cewar sai naga dama zan bar ta ta sake da miji





Anty fannah ce ta miƙe suka fara cacar baki da badiar inda daga ƙarshe sai baaba ce ta raba su domin ni ina zaune kamar gunki ba motsi


Wallahi sabit ya gama bani mamaki wallahi na gama dawowa daga rakiyar sabit har abada, da ƙyar na iya riƙe kukana har badiar ta fice sannan na saki abina


Janye ni anty fannah tayi zuwa cikin ɗaki inda sai da ta lallashe ni sannan ta tambayeni menene na kukan


Tsap na kwashe yadda mukai da sabit na faɗa mata itama sam bata ji daɗi ba kuma ta jinjina da lamarin amma sai ta ce min ki kira shi kiji ya mw ya faru


"wallahi anty bazan kira shi ba bazan kuma yadda da maganr sabit ba, ya cutar da ni na yafe masa ya kuma wallahi wannan karon bani bashi ai ba zuciyar dutse gare ni balle yace bazan ji abinda yake min ba"


Haƙuri dai anty fannah ta dinga bani kamar kullum ni kuma na riga na gama kulle shafin sabit a rayuwa ta sai dai wani ba shi ba


Nunawa anty fannah nayi naji faɗan natan don haka sai ta tafi, tana fita na ɗauki wayata na tura masa da text kamar haka


```naji ashe da badia zaku tafi turkey tooo Allah ya kaiku lfy ya ƙara danƙon soyayyar ku amma wallahi ka sani ka sake naga ƙafar a gidana wallahi kaji na rantse maka sai na kira daddy ya raba mu```


Ina gama rubuta saƙon na kashe wayata, haba sabit daaa kenan zakai min ba tare da na ɗau mataki akan ka ba amma ba yanzu ba da kan mage ya waye


*******************


Sabit yana zaune a gidan sa yana ta haɗa kayan sa zai taho kano sallama da asmaun sa sam wannan tafiyar da badan ta zame masa dole ba da ba inda za shi


Tunda ya kira daddy ya faɗa masa maganar tafiyar yace masa da asmau za shi daddy ya soke tafiyar da ita yace ana sanyi ga yara basu yi ƙwari ba gwanda kawai ya tafi da badia in yaso ita asmaun sai ya kaita hajj yake jin wani iri a jikin sa


Sam ya kasa yi wa asmaun bayani a waya yafi son idan yaje can sai yayi mata bayani face to face ya san zata saurare shi kuma zata fahimta




Ƴar ƙara yaji daga wayar sa alamar message ya shigo, sam be damu yasan ko waye ya turo ba ya fison idan ya gama komai sai ya duba


Sai daya gama komai sannan ya ɗauko wayar da don ya duba sakon da aka turo masa


Yai mamakin daya ci karo da saƙon asmau, hankalin shi ya tashi sosai ya rasa abinda ke masa daɗi ya akayi asmau ta san da batun tafiyar sa da badia


Yasan muumy sam bazata taɓa faɗa mata balle kuma daddy, inbanda su biyun nan babu wanda ya sani sai badia


Badia tabbas badia ce ta faɗa mata rasa abinda zai yi don takaici


Ɗaukar wayar ta yayi ya fara trying a kashe ya jita, shit ya faɗa sannan yai jifa da wayar sa wai sai yaushe zasu samu zaman lfy da asmau ne


Ya daɗe ya na tanadin lkcn da zasu haɗu da asmau amma yanzu duk wannan budget ɗin nasa ya ruguje, mtsss, gashi ƙarshen satin nan zasu tafi


wallahi shi ya sa da daddy yace asmau baza ta je ba yace bazai tafi da kowa ba, daddyn ne ya matsa masa sai ya tafi da badia, yanzu gashi nan ga abinda aka jawo masa ya rasa abinda ke masa daɗi wannan wace irin rayuwa ce ace kullum ka rasa farin cikin da iyalan ka da komai


Sam baya ganin laifin asmau shi ne ya fara ɗora ta akan wannan hanyar ita kuma da ta tashi sai ta doke shi,


Lkcn da yake iskanci sam be taɓa hanata haƙƙin ta na aure amma ita da ta tashi ramawa nata ya fi ci masa tuwo a ƙwarya ta hana shi kanta ta hanashi ganin ƴaƴan sa


Kai wannan da me yayi kama


Zai ci gaba da trying ɗin wayar ta har ya samu ta shiga, don ya kamata ace lkc ya yayi da zasu daina involving mutane cikin maganar sha'anin auren su



Ya kamata idan ka girma ka san ka girma ƴaƴa uku tsakanin su, gaskiya lkcn da zasu zauna su magance matsalar sune yanzu ba lkcn da zai dinga ya maɗiɗi da duk wani ɗan saɓanin da suka samu bane



Wayar shi ya ɗauka yai mata reply kamar

```baby na don Allah idan kin kunna wayar ki ki kirani wallahi zan miki bayanin komai, na so ace na zo kano nai miki bayani ni da ke amma ganin text ɗin ki ya dakatar da ni don Allah call me```



Kwanciya yayi kawai akan gado yana me fatan Allah yasa idan taga message ɗin shi ta kira shi



Tun sabit ya jiran call ɗin asmau har ya sare, har badia ta zo, inda ranar da ta sauka ma sai da akai abunda aka saba don tana sauka ta fara masa maganar dashe wanda shi kuma ya taka burki wanda
hakan ya kai su ga faɗa


Har ranar da zasu tashi ba asmau ba labarin ta abin ya dame shi sosai bazai iya tafiya ba ba tare da yaji muryar ta ba



Ɗaukar wayar sa yayi ya kira anty fannah tas ya kwashe mata abinda ya faru ya faɗa mata sannan ya roƙe ta akan don Allah ta sa asmaun ta kunna wayar ta ko sallama ne suyi tunda ta hana shi zuwa gidan


Anty fannah ta tausaya masa sosai sam bata san haka abin yane ba kuma sam bata san cewar asmaun ta aikata hakan ba


Haƙuri ta bashi tare da yi masa alƙawarin zatai wa asmaun magana



Suna gamawa ta miƙe da ɗan cikin ta wanda a yanzu ya fara nuna wa tayi hanyar part ɗin asmaun,


Tana zaune tana bawa annur abinci sukuma twins ɗin suna baccin su da sallamar ta tashiga


"anty fannah yanzu nace bari in gama bawa annur abinci yaje wajen ki don in samu in bacci wallahi ya hanani da rigimar sa"


"ba dole yayi rigima yaro yaushe rabon da yayi magana da bbn sa" shiru nayi don bana ma son ayi min maganar sabit ko kaɗan


"yanzu asmau duk faɗan da nai miki rannan ashe baki jiba, sai da kika kira sabit kika ƙara tayar masa da hankalin, yanzu asmau dama an taɓa rayuwa a haka,


Kin ganni wallahi a gidan mu sam bamu san wai namiji yai maka laifi ba kace zaka rama, duk abinda namiji yai maka indai har ya dawo ya tuba wallahi sai ka yafe masa ku zauna lfy


Yau namiji yai miki kin yafe gobe ya miki kin kuma yafe wa wallahi jibi kunyar ɓata miki zai yi,


Amma idan kina yi namiji haka asmau kina ƙara ɓata masa rai kina ƙara nisan ta kanki ne da shi, lkcn da zaki zo ki so shiryawa sai kiga shi kuma ya riga yai miki nisa


Don me yasa duk abinda sabit yake miki ban taɓa cewa ki rama ba, saboda nasan kowane *AURE BAUTA* ne


Kuma duk matar da tace wallahi ba za tai haƙuri da jarabawar da Allah ya jarabce ta da shi a rayuwar auren ta ba to wallahi tallahi tai kuka da kanta


Kin taɓa jin inda akace wannan abin ibada ne kuna ya kasance ka same shi kasatan ba wani wahala ko wani abu


Wallahi ki nutsu, ke me kishiya, ma d more kike nisanta kanki da mijinki d more shima yake ƙara nisanta kanki da shi duk kuwa da son da ya ke miki za a wayi gari wataran yaji da ke da babu duk ɗaya


Duk matar da tai sacrificing farin cikin ta ga mijin ta wallahi ko ba daɗe ko ba jima sai ya dawo wajen ta, ko kin taɓa jin inda akace haƙurin wacce be mata rana ba sai dai a ce rashin haƙurin haƙurin wacce ya cutar ta


Kiyi haƙuri ki ja mijin ki a jikin ki, in shaa Allah wataran sai labari wataran ke zaki girbi abinda kika shuka walau khairan au sharran"


Tun da ta fara nake kuka nasan tsab anty fannah macece me haƙuri sosai da mai da komai ba komai ba shiyasa tunda muke da ita ban taɓa jin tace wani abu akan isma'il ba


Amma ni yanzu wai ace duk abinda sabita ya min in share in mai da komai ba komai ba to wai sai yaushe ne duk waɗannan abubuwan zasu zo ƙarshe


Ko da yake ance aure ibada ce kuma aure bautar Allah, muna fatan a wannan bautar Allah yasa mu kasance muna yin ta iyakacin iyawar mu


"in shaa Allah anty zan kira shi komai ya wuce"

"indai har da gaske kinji abinda na faɗa miki ɗauki wayar ki kira shi, kuma ki bashi haƙurin tayar masa da hankalin da kikayi"


Wayar na ɗauka na kunna sannan nayi dialing number sa, ringing ɗaya ta ya katse wayar daga dukkan alamu shi ya kashe kallon ta nayi alamar ta gani ko


Murmushi tayi sannan tace

"ki bari zai kira ki nasan yana wani abun ne"

"nasan ba wani abun da yake yi yana tare da badia ne suna ta shirye shiryen tafiya mtsss"


Kallona tayi sannan ta saki murmushi

"asmau manya duk kishin ne haka, ana so ana kaiwa kasuwa daaa kina kishin nasan kika bar mata shi, wa ya gaya miki ana bar wa kishiya miji, barin ma ita da suke tare kullum,


Wallahi asmau ki shiga hankalin ki da wannan wautar taki ta nuna halin ko in kula da sabit, yaro kina ganin shi sabon jini son kowa ƙin wanda ya rasa amma kina miss using damar ki


Yarinya idan yaje ya haɗu da ƴammatan lagos masu shegen naci, maƙale mata kya faɗawa ƴan garun ku"

Ta ƙarashe zancen ta da dariya

Kyakyaɓe mata fuska nayi kamar wacce zatai kuka a dai dai lkcn call ɗin sa ya shigo, kallo na tayi sannan tace

"tashi ki shiga ɗaki ku sha hirar ku zan ci gaba da kula da yaran sauran kar ki bashi haƙuri sauran kar ki kwantar masa da hankali wallahi ya kuma kawo min ƙarar ki sai dai ki nemi wata ba ni ba"


Miƙewa nayi jiki na asanyaye nayi hanyar ɗaki tare da ɗaukar wayar sannan na kara ta a kunne na tare da cewa


"hello daddyn annur ya lagos"
[10/05 09:53] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠





🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚





ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)







*ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN* 🤲🏻🤲🏻





*HIKIMA WRITERS ASSO.*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 30🌹






Sai kashegari da sassafe sannan muka kama hanyar a jirgi,


Muna sauka directly asibitin muka wuce inda na tarar da tashin hankali wanda ban taɓa gani ba


Sabit ne a nannaɗa kamar me, baka ganin komai nashi sai idon sa wanda yake a rufe sai kuma bakinsa sannan hancin sa wanda yake ɗauke da oxygen


Mummy ce a zaune akan sallaya tana addua, jikin ta ne na faɗa ina kuka, rungume ni tayi ita ma muka cigaba


Sallamar daddy muka ji, wanda hakan ya sa muka sake sakin wani sabon kukan

"nasiha ya zauna yai ta mama akan mu gode wa Allah tunda ba wani abun bane, karaya ya samu a cinyar sa ta dama sai kuma ƙafar sa ta hagu


Sannan hannun sa na dama ya samu karaya, na hagun kuma ya samu gocewar ƙashi da kuma tsage war sa" kuka na kuma saki sosai


Lallai bawa ba a bakin komai yake ba


"daddy kansa fa da a ka nannaɗe" na tambaya don ni sam ban yadda da naɗin kan na ba


"Ba komai ɗan bigewa yayi a kan"


Na ɗauka zasu gaya min abinda ya same shi sai naji sun yi shiru ni ma haka, ƙarasawa nayi kusa da shi na kira sunan shi


Amma sam be amsa ba kamar ma bacci yake yi ko a sume yake oho,

"mummy bacci yake yi ne"

Ajiyar zuciya tayi ba tare da tace komai itama kamar bata sani ba,

Likitoti dai sunce zai farka, zuwa yamma,

"Allah ya kaimu shine kawai abinda nake cewa"


Zuwa goma ƴan gidan an cika asibitin ana ta kuma jaje


Daga ganin su ba wanda ya san me ya same shi, don cewa sukai kawai kiran su akayi aka ce yayi accident, to me ya haɗa su da badia


Tabbas ko ba a faɗa ba nasan badia tana bayan wannan hatsarin nashi amma kuma Allah ne masani


Har zuwa yamma ba abinda ake bashi sai kunu, inda ake feeding ɗin shi ta hanci sam be ma san inda kansa yaba


Sai ledar ruwa da yake ta shaa,

Bayan magariba aka kuma cika ɗakin lkcn duk sun dawo daga wajen aiki, kusan anan suka ci dinner ana yi ana jajan tawa juna, isma'il ne yace


"shin mummy wai badia bata san sabit yai accident bane ni sam ban ganta ba"


Taɓe baki tayi taƙi cewa komai, ragowar ne suka dinga tankawa ni dai ban ce komai ba saboda kar ince wani abun ace kishi ne amma ni kaina naji haushi


Sai goman dare sannan aka tashi tafiya mummy ce ta kalle ni

"asmau kije gida ki huta kinga tunda kuka dawo twins suke gida sam basu gan ki ba, gwanda ki tafi, don ma nace a kai su can gidan mu ba naku ba, kije ki zauna acen har muga yadda hali zaiyi"


Kuka na saka mata

"wallahi mummy ba inda zani, jinyar mijina zanyi, mummy don Allah ki barni in zauna anan"


Na ɗauka zasu goya min baya sai naga kowannesu yana cewa in tafi in huta na dinga zuwa da safen tunda ba komai ake masa mummy ma ta isa



Kuka sosai na dinga yi, inda a lkcn daddy ya shigo yaga halin da muke ciki sosai ya musu magana akan su barni, gwanda in zauna ana hankali na zai fi kwanciya akan ina gida


Naji daɗin yadda daddy yayi supporting ɗina lallai shi kaɗai ne yasan halin da zan shiga idan na koma gida a wannan halin



Sallama sukai suka tafi, inda ni da mummy muka zauna, yadda aka tsara shine zan dinga zuwa gida sau uku ina bawa yara nono kullum ko a dinga kawo sun suna sha


Na yadda da wannan tsarin amma sam bazan yadda inyi nisa da mijina ba


Haka muka kwana lfy vba wani abu sam sabit ko motsi ba ya yi, sai dai in ya daɗe da kwanciya likitocin su zo su juya shi su gyara masa kwanciya wanda sam ko motsi baya yi idan an taɓa shi kamar wani matacce


Zuciyata tana karye wa idan naga wannan halin da mijina ya ke ciki wai wannan sheine sabit ɗin dana sani kai ɗan adam ya shiga uku



*******************



Tin muna sa ran farfaɗowar sa har abin ya fara bamu tsoro, likitocim ne suka bada shawarar za a kuma ɗauko wani likitan ƙwaƙwalwa ya duba ko akwai matsala a ƙwaƙwalwar ta sa wacce ta hana shi farfaɗowa


Likitan dr. jamal daga lagos ya zo, dole da accomodation ɗin shi da komai nashi su daddy ne suka ɗauka


Sai da ya zo sannan aka kuma yi wa sabit general check up inda aka gano ,akwai matsala a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login